Ta-ke idona ya firfito waje, gumi ya jiƙe min jiki, tashin hankalin da ban taɓa shigarsa ba ya dirar min, tsorona Allah tsorona irin wawan kallon da Gwaggo ke jifana da shi, na haɗiyi wani wahaltaccen yawu a maƙoshina, na runtse ido ƙirjina na dukan tara-tara, kafin na kai ƙwaƙwalwata ga fara tunanin laifin dana aikata naji wani ƙullutun abu ya faɗo ta gabana, na daɗa rumtse ido sosai saboda zafi da ya ratsani.
Da gudu-gudu kuma naji abu kamar ruwa naci gaba da fita daga gabana me ɗumi, na. . .