Skip to content
Part 6 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Ta-ke idona ya firfito waje, gumi ya jiƙe min jiki, tashin hankalin da ban taɓa shigarsa ba ya dirar min, tsorona Allah tsorona irin wawan kallon da Gwaggo ke jifana da shi, na haɗiyi wani wahaltaccen yawu a maƙoshina, na runtse ido ƙirjina na dukan tara-tara, kafin na kai ƙwaƙwalwata ga fara tunanin laifin dana aikata naji wani ƙullutun abu ya faɗo ta gabana, na daɗa rumtse ido sosai saboda zafi da ya ratsani.

Da gudu-gudu kuma naji abu kamar ruwa naci gaba da fita daga gabana me ɗumi, na mayar da kaina kwance idanuwana a rufe ina cije leɓe, tsawon wasu daƙiƙu dana ɗauka ƙasan cikina na min azabar ciwo sannan na fara dawowa cikin hayyacina dana bari, numfashin wahala nake saukewa da sauri da sauri, daga can na jiwo muryar Gwaggo na fita acikin faɗa.
“rashin hankali ne kawai irin nata, Amarya zuwa yanzu ya kamata ki daina goyon bayan Mairo akan duk wasu abubuwa da take wanda ba dai-dai ba, haba wacce iriyar rayuwa ce wannan da za’ace mutum zai yi ba dai-dai ba a zuba masa ido baza’a nuna masa kuskurensa ba, ni wallahi kuna ɓata min rai idan kuna cewa yarinya ce.”

Inna Amarya ta fitar da murmushi me sauti sannan tace,”to ai sai yanzu girman ya risketa ko, daga yanzu ne ita ma zata fara sanin kanta da kuma inda ke mata ciwo, wanda da kanta zata gane kuskuren abunda bai dace ba”. Shiru na tsawon daƙiƙa biyu Gwaggo bata ce komai ba, sai can naji ta ambaci sunan Kulu tare da cewa mata, “ki duba magungunan muji yanda suke kamin ta farka, allurar kuma za ki yi mata ne ko ya?”. Abunda na sani Kulu bata magana dan haka ko a yanzu da idanuwana ke rufe banji fitar muryarta ba da amsar maganar Gwaggo, haka kuma maganar da Gwaggo tayi bana da tabbacin da ita tayi, dan magana ce da aka alaƙanta ta da masu hankali bata mahaukata irinsu Kulu ba, to amma sai dai kuma me? a ɗazu dana farka bayan Gwaggo da Inna da Kulu babu wani bayan ni, ko kuma wani ya shigo bayan rufuwar idanuwana ne?, lokaci ɗaya nasa shakku akan maganar Gwaggo, duk ta yanda naso nayi wani tunani akan lamarin sai na kasa, saboda yanda kaina ke sarawa.

Har yanzu zuciyata na cikin fargabar laifin da nayi wanda ban sani ba, da kuma taraddadin hukuncin da zan karɓa daga wurin Gwaggona, saboda haka ne na kasa buɗe idona nayi kamar ina bacci, duk maganganun da suke yi inaji, har lokacin kuma da naji ana batun yi min allura, ai lokaci ɗaya tashin hankalin da nake ciki ya ninku, na ƙara rumtse ido gam ina jin kamar kar na buɗesu, alokacin da naji an ɗaure min hannu da igiyar roba na ƙwallara wata ƙara na miƙe zaune babu shiri ina neman hanyar guduwa, Gwaggo ta buga min wata uwar tsawa da ta saisaita hankalina, hawayen da ke maƙale cikin idona suka shiga zuba kafin na ɓare baki na fashe da kuka. Duk da idona rufe suke amma yanda naji an jawoni zuwa ƙirji an rungumeni ya bani tabbacin Inna Amarya ce, bayana ta-ke shafawa tana min magana cikin sigar lallashi, daga can inda Gwaggo kuma ke zaune naji ta kuma ɗaga murya acikin faɗa tana cewa,”wai ba za ki yi ki mata bane kin wani yi tsaye kanta kina kallonta, ke ni nafa gama ganeki, babu wani abu da kike so a yanzu fa-ce baƙin cikin da ke daskare a zuciyata ya ƙarasani, idan kuma na ƙarasa wallahi kece sila, hakkina kuma ba zai barki ba”. Ban san dawa Gwaggona ke wannan masifar ba, dan a ƙanƙame nake da Innata, ta kauda kaina ɗaya gefen ta yanda ba zan kalla allurar da za’a min ba, sai dai naji tausayin koma wanene Gwaggo kema wannan masifar cikin hargowa da ƙaraji.

Ban aune ba naji shigar tsinin allura a hannuna, na kurma uban ihun da saida Innata tasa hannu ta rufe min baki, kuka nake wiwi ina kiran sunan Baba da Ya Kabiru da Ya Amadu, acan ƙasan maƙoshina kuma ina jera Allah ya isa ga wanda yay min allurar, a hankali nake sauke ajiyar zuciya Innata na aikin ban haƙuri da lallashi, har sanda bacci ya ɗaukeni ba tare dana sani ba.

Dawowar Malam daga wurin aiki ya wuce ɗakinsa, inda Inna Zulai wadda girki ke hannunta ta tarbeshi da kyakykyawan abincin da ta dafa na dambun acca kasaancewar Malam ma’abocinsa ne, zaune suke su na taɓa hira shi da ita, tana sanar masa da zancen maganar auren saurayin Sadiya da yake so a bashi izinin turowa.

Gwaggo ta shigo bakinta ɗauke da sallama, cikin ladabi ta duƙa tana miƙawa Malam baƙar leda me ɗauke da takardu aciki. “gashi ɗazu Liman ya aiko Muntari ya kawo yace a baka.” Malam ya buɗe ledar, takardu ne guda uku kowanne da rubutu ajiki, ya dudduba ba dan ya san meke rubuce aciki ba.

Ya mayar cikin ledar ya ɗaure sannan yace,”to Madallah bari na ajiye idan yaran nan sun dawo sa duba muji mene ƙunshe a ciki.”

“Yayi kyau.” Gwaggo ta faɗa tana yunƙurawa zata miƙe ta fita Malam ya maida ita.
Yay ɗan jim yana daɗa nazari akan maganar da Zulai tazo masa da ita, kamin yay gyaran murya ya fara magana da dukansu.
“to ke Zulai a maganar da kika zo min da ita nayi duba wanda magana ce mai kyau, sai dai ina so ya ƙara bamu ɗan lokaci…sannan a yanda nafi so na kuma gama tsarina tuni, so nake na haɗa yaran nan duk su uku na miƙasu ɗakinsu a lokaci ɗaya, duk da nasan da cewar hakan hidima ce babba amma babu komai Allah zai yassare yanda za’ai.”

Sai a yanzu ya ɗago kai ya dubi Gwaggo wadda ke fuskantarsa tana sauraronsa yace,”Suwaiba ita Mairo bata taɓa zuwa miki da zancen kowa bane? Ina so ne na haɗasu su duka ukun na sauke hakkin da ke kaina.”
Gwaggo tace,”ni ban gama gane maganar su uku ba, Sadiya da Adawiyya da kuma wa?” “Mairo Mana.”
Gwaggo ta gyara zama tace, “a’a dai Malam, Allah na tuba Mairo gaba ɗaya nawa ta-ke, bata ma yi girma da hankalin da za’ace za’a aurar da ita a yanzu ba ai…aiwa Yayyun nata dai ita ma idan lokacinta yayi sai a haɗata da sauran ƙannenta”.
Zulai ta ce,”ke kuwa Suwaiba wanna girma kike so Mairo ta ƙarayi, idan kuma ba so kike tayi girman da zata taddomu ba. Ga sa’anninsu nan gaba ɗaya anata aurar da su, wasu ma harda ƴaƴansu.”

“Ke kika ga girman, ni dai banga girman da Ƴata ke da shi ba, shekara sha uku ne fa, shekarun da basu da maraba da shekara bakwai zuwa takwas”. Malam ya murmusa fuska ya ce, “yanzu Suwaiba idan ba ƙin gaskiya ba har ace macen data shekara sha huɗj bata girma ba?”. Ta karkata kai gefe tana tura baki gaba kamar ƙanƙanuwar yarinya,”ni ƴata ba tayi wannan shekarun ba, ni dana haifi abata nafi kowa riƙon shekarunta, dan Allah dan Annabi ma ni a daina sawa shekarunta ido”

Malam ya sauke numfashi kana yace,”to anji ƴarki bata yi wannan shekarun ba, amma dai kuma ai kin san ta isa aure ko?”

Gwaggo dai taɓe baki tayi bata ce ƙala ba, har sai da Malam ya kuma yin magana sannan tace, “ni fa Malam canji nake so a samu daga kan ƴata, ba aure nake so ayi mata ba, Karatun zamani nake so tayi me tsayi”. Tunda Gwaggo ta faɗi haka bata kuma jiran cewar bakin kowa ba ta ɗaga labule ta fita, Malam ya bita da kallo cike da ɗumbin mamaki, ta sauya sosai fiye da tunani, duk ta yanda yaso yayi magana da ita saita tirje taƙi bashi dama, yanzu harma wani ƙin zama ta-ke yi tare da shi, idan shine kuma ya shiga ɗakinta zama na ƴan mintuna ne zasuyi ta tsiri bacci da bata shirya ba.

Zulai taci gaba da faɗin ita kuwa ba za’a sa ƴaƴanta su lalacewa ba, dan haka Malam ma ya bar tunanin haɗa auransu da Mairo, duk ranar da Mairo ta jawowa gidan magana uwarta zata gane ba gata tayi mata ba.

Ɓangaren Gwaggo kuwa tana fita su kai karo da Kabiru ya shigo, wanda dawowarsa daga aiki kenan, yay mata sannu da gida ta amsa masa, Ya tambayi jikin Mairo tace masa da sannu dan har ma tayi bacci tun ɗazu. “Allah ya sauƙe.” Ya faɗi hakan tare da nufar ɗakin Gwaggon, a kusa da kanta ya ajiye mata robar ice cream ɗin da ya siyo mata, ya kuma ɗora ayaba da kankana akai.

Fitowarsa ya sami Gwaggo ta shimfiɗa tabarma ta zauna tana aikin zogale, yaja kujera ya zauna yana buɗe kwanon abinci, ita kuma ta fara magana kamar ba da shi ta-ke ba.
“Kabiru ka faɗawa Babanku muhimmacin karatun zamani, ka fahimtar da shi karatun zamani ko babu aiki anfi ƙarfin dai a cuci mutum balle a raina shi.”

“Gwaggo wani abu ya faru ne, ko yace yaran nan zasu tsaya da karatunsu ne?”. “yana nufin haka mana, tunda yana kiran aurar da su zai yi, saboda Uwar masu gida tayi magana. To ni kuwa ba aure zan yiwa Mairo tah ba, karatu za tayi ta karanci aikin kotu.”

Ta faɗi hakan tana ci gaba da zagar zogale, Kabiru yay murmushi, maganar da zai yi ta katse sakamakon sallamar Amadu. Shi ma wuri ya nema ya zauna gefen Gwaggo akan tabarma, jikinsa da alamu na gajiya, Kabiru yace da shi,”wai dama ba kai na gani a masallaci ba”. Amadu yace da shi,”ni ne mana, Mai gari ne wai yake neman matasan da suka yi karatun boko a wannan ƙauyen, shi ne na kai sunayenmu”.

Ya kalli Gwaggo yace,”Gwaggonmu ai mana adu’a Allah yasa a dace”. Tace,”insha’Allahu ma za’a dace, ga dai Babanku nan ai yana nema ya yiwa karatun Mairo togaciya, yana ikirarin wai aure zai yi musu, saboda Uwani tayi magana.”

Amadu ya miƙe daga kishingiɗen da yake,”aure kuma Gwaggo!”? Ya tambaya da mamaki. “uhmm”. abunda ta iya cewa kenan. Ya shiga girgiza kai,”inaa dole ma Baba ya sauya tunani”. Kabiru ma yace,”ai yama zama dole, ta ya su ɗin da aka samu suka fara katun kuma ace za’a dakatar dasu, karatun nan fa shi zai ji daɗinsa.” Gwaggo ta kuma cewa, “Ni dai na faɗa kuma zan ƙara faɗa ko za’a tsayarwa da kowa karatunsa banda Ƴata, dan insha’Allahu Mairo sai tayi karatun zamanin mai zurfi har ta zama lauya.”

Amadu ya ce,”ah Gwaggo karatun likita dai ai mu shi ne burinmu akan Mairo, tunda tana da hazaƙa”. Kabiru ya ɗora da faɗin, “kuma karatun likita ai yafi kowanne karatu muhimmanci da amfani a wajen Ƴa mace.” Gwaggo ta taɓe baki, “in dai babu karatun banza ai babu laifi dan Mairo tayi karatun lauya, dan haka karku sa ma ta ƙahon zuƙa akan wani karatun likita, ku barta tayi karatun da zata shiga kotu ta gwabza da kowanne shege ta ƙwatowa Babanku gonakinsa.” Kan su ƙara cewa wani abu Gwaggo ta miƙe ta nufa wurin ruwa dan wanke zogalen da Kabiru ya tayata zagewa.

Kulu dake zaune bakin ƙofar ɗakin Gwaggo ta faki idon kowa ta faɗa ɗakin, har yanzu Mairo bacci ta-ke bata tashi ba, ita haka kawai Allah ya haɗa jininta da yarinyar, tana sonta sosai wanda in da mahaifiyarta ta san irin son da ta-ke yi ma ta da ta mallaka ma ta ita.

Ta ƙarasa bakin gadon cikin hanzari tai saurin ɗauke robar ice cream ɗin da Kabiru ya ajiye, dama a ɗazu tana kallon lokacin da ya ajiye kasancewar tana sallah, ta bar ma ta sauran ayaba da kankana, ice cream ɗin kuma ta zura shi ƙarƙashin sif ta yanda babu mai lura da shi.

<< Sirrin Boye 5Sirrin Boye 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×