Skip to content
Part 7 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya


Rikicewa Kulu tayi da ganin Gwaggo wacce ke kallonta tun daga sama har ƙasa da son gano abunda ta-ke ɓoye mata, tsawon daƙiƙun da ba zasu haura biyu ba Gwaggo taja tsaki, ta bar kusa da ita ta ƙarasa bakin gadon da Mairo ke kwance tana faɗin, “Abu ne mafi sauƙi a wajena na kori mutum ya koma inda ya fito matsawar ba zai kiyaye sharuɗan da na ke gindaya masa ba…saboda na ɗaukeki ina taimaka miki ba yana nufin dole kema kice zaki taimaka min ba, ba kowa na yarda da shi ba dan haka ki daina raɓar min Ƴaƴa”. Kulu dai da ke tsaye jiki a sanyaye sauraran Gwaggo da faɗanta kawai ta-ke, faɗan da ta-ke yi kamar bada ita ba, ta motsa laɓɓanta sannan ta ɗaga labule ta fita daga ɗakin.

Jikina sakayau na farka, sai ƙasan cikina da nake jinsa dai a ɗaure kaɗan, muka haɗa ido da Gwaggo wadda ke zaune tana ƙarawa Basma karatun ƙur’ani, kallo ɗaya tayi min ta ɗauke kai, bata kuma waiwayoni ba sai da ta sallami Basma, ba tare da ta kalla inda nake ba tace, “ya sauƙin jikin?”. Na ɗan yamutsa fuska nace, “naji sauƙi, ƙasan cikina ne dai yake murɗawa kaɗan”. “sannu Allah ya sauƙe.” Shi ne abunda tace dani kawai. Na sauko daga saman gadon, jinin da naga ya wanke min gefen zanena yasa a gigice na koma nayi zaman dirshen a kan gadon, na fara rarraba idanu kar Gwaggo ta ganni, gashi yana zubowa ta gefen ƙafata, ban san lokacin da kuka yazo min ba nayi saurin saka hannu na toshe bakina, jikina ya hau ɓari, yarfe hannu nake a zuciyata ina kiran mutuwa tazo ta ɗaukeni, _”na shiga ukuna.”_ itace kalmar da nake ta nanatawa cikin kaina, tabbas na miƙe Gwaggo tayi ido huɗu da wannan abu sai dai ta sake haihuwar wata Mairon, domin abunda nake tunawa wata hira dana taɓa jin Inna Zulai da Inna Amarya nayi kasancewar ranar suna ƴan mutunci, ban san dai akan me suke hirar ba sai dai naji Inna Zulai na cewa, “ai tunda muka shiga naga jini na bin ƙafarta nasan wannan da wuya idan ba jini ne ya ɓalle mata ba.”

Innata acikin jimantawa tace,”ai ba ƙaramin wuya tasha ba awajen haihuwar nan.” Na daddage na kurma wata uwar ƙara sannan na kwasa a guje na bar ɗakin Gwaggo na faɗa ɗakin Inna Amarya, ita kanta sai da ta firgita da yanda ta ganni, ta miƙe tana riƙo kafaɗuna tana jera min tambayar lafiya, cikin muryar kuka nace ma ta,”Haihuwa nayi.”

Adawiyya da ke zaune ta bushe da dariya tace,”ina jaririn?” “Ai ina bacci na haife shi ban ganshi ba ma.” Na bata amsa ina zubewa a ƙasa da ruzgar sabon kuka wiwi, hannuwana aka ina ci gaba da faɗin,”kuma wancan ranar Gwaggo tace idan na haihu banyi aure ba saita kasheni, sai ta saka min yaron a baki na cinye shi sannan zata yankani gunduwa gunduwa, na shiga ukuna wayyo Babana, wayyo Ya Kabiruna, wayyo, wayyo na shiga uku Ya Amaduna.” Adawiyya na min dariyar ƙeta harda hawaye ta kuma cewa,”Shikenan Mairo zata mutu, to ke dama taya kika yi cikin?”

Shashsheƙar kuka nake tamkar raina zai fice, na maida hankalina kanta ina jefa mata tambayar,”taya akeyi dama?”. Maimakon ta bani amsa saita kuma fashewa da dariya harda kifawa ƙasa tana riƙe ciki. Sadiya wadda ke zaune kan dakalin ƙofa ta wurgo min tambayar,”yaushe kika shiga ɗakin mazan da ba ƴan gidanku ba?” Nayi saurin girgiza mata kai da hannu,”nifa yanzu ne kawai dana farka a bacci naga na haihu amma wallahi ban taɓa shiga ɗakin maza ba…” “ƙarya kike yi, jiya da daddare ba ina kallo kika shiga ɗakin su Ya Kabiru a salallaɓe ba bayan kuma basa nan sai abokansu.” Na dire kan gwiwoyina nace,”to ai fa kawai cinnaka na ɗauka naje na sawa wannan Jawad ɗin da ya zagi Adawiyya a baki, kuma dana ga ya cije shi saina fito da gudu.”

Sai a yanzu Inna Amarya tasa baki, “ke dilla nutsar da hankalinki wuri ɗaya, babu wani haihuwa da kika yi”. “Allah Inna haihuwa nayi, kallafa jini na zuba ajikina kuma har akan gadon Gwaggo ma dana kwanta, dan Allah kice karta kasheni, na shiga uku”. Kuka nake wurjanjan kamar zan haɗiyi zuciya, dariyar Adawiyya ta fara ƙular dani na maƙuro wuyanta ina dukanta, “banza, muguwa, azzaluma, wawiya, doluwa, sokuwa, shashasha kawai, kuma saina faɗawa Gwaggo nace baki kaiwa Baaba Lami saƙon ba.”

Jin haka ta ƙwaci kanta da ƙyar ta shiga bani haƙuri akan na rufa mata asiri. Itama Sadiya ina jiyota tana cewa ai ni ce sokuwar ba Adawiyya ba, ban dai kulata ba saboda Ya Amadu yace na kuma yi mata rashin kunya sai ya zaneni. Inna Amarya wadda ta fita tun ɗazu ta dawo tana ce min na tashi na ɗaura zane akan kayana naje nayi wanka, bata barni na fita ba sai da ta natsar da hankalina wuri ɗaya. Na fito da kayan da na cire rungume ajikina ina kaffa kaffa kar wani ya gani, dan Inna tace duk wanda ya gani za’a yayatani a duniya ace na haihu babu aure, kuma idan Baba yaji da gatari zai faskarani tun kan Gwaggo ma ta yankani.

Naja botikin ƙarfe na zuba kayan aciki, da dasu zan shiga bayin sai kuma na ajiye daga bakin ƙofa ta wajen lungun wurin ta yanda babu mai iya gani. Shaf-shaf nayi wankan na fito dan baki ɗaya hankalina yana kan wankin dana ajiye, so nake har na wankesu kar wani ya shigo gidan, sai dai da mamakina ko dana duba babu botiki babu alamunsa, na ko rikice na kama hailala da salati, to wane yazo ya ɗauka?, kar dai a mazan gidan wani ya shigo, ina ƴan dube-dube na hangi Kulu na shanya kayan ajikin garu ta bayan ɗakinsu Lukman, “kutttt”. Na faɗa da ƙarfi cike da jin haushinta, da sassarfa na ƙarasa wurin da take, na kama ƙugu ina jijjige jijjige sai cika nake ina batsewa, ni nasan ban isa nayi mata komai ba amma tunanin makeken sharrin da zan ƙulla mata a wurin Gwaggo kawai na ke, ga mamakina sai gani nayi ta dubeni ta lafta min uwar harara tasa hannu ta kaudani gefe, duk da bata kallona amma haka na murguɗa mata baki sannan nace,”wai ke Kulu baki san kin girma bane, sai kita wani shishshige min ala dole sai nayi ƙawance da ke, akan mene na aje kaya zaki zo ki ɗauka ki wanke sai kace na saki, wannan ma ai shishshigi da ƙwala kai a faranti ne, to ni dai bana so karki kuma min irin haka ba ruwanki dani da al’amurana dan bana kula mahaukata irinki…”. Ɗiff bakina ya ɗauke ganin ta Ɗaga hannu a zafafe zata tsinkeni da mari, ban san me ya hanata ba naji ta sauke hannu, ta ƙarasa shanya zane sannan ta juya ta bar wurin, in da ni kuma a lokacinne na ɗago ina binta da kallon mamaki, abunda idanuna suka ci karo da shi a wuyanta shi ya ɗauki hankalina, abu ne kamar tambari na tauraro baƙi, kasancewarta fara ƙal gashi nan raɗau kana kallonsa, sai da ta ɓacewa ganina sannan na sami damar haɗe murfayen idona ina son tuna in da na taɓa ganin wannan tambarin, na fi daƙiƙa biyar a tsaye acikin wannan tunani sannan na buɗe idona, tabbas idan ba a wuyan Gwaggona ba to a wuyan Jawad ko shi ko Suhail ko kuma Ya Kabiru na taɓa gani. na ɗan ciji yatsana, to amma kuma ai kamar wannan tambarin an taɓa nuna shi a tv a masarautar larabawa, kenan ananne na taɓa gani irinsa?, kai bayan nan ma kamar na taɓa gani a tsakanin mutum huɗu nan da na ke zargi, ɗan ƙaramin tsaki nayi dan sai yanzu na tuna ma ashe a wuyan Basma ne, har nake tambayar Gwaggo ko ƙonewa Basma tayi tace a’a baiwace, nima kuma a lokacin har na ɗau madubi na duba nawa wuyan, da yake hasashe ne nake sai naga kamar nima ina da shi, da na bawa Gwaggo ta duba min sai tace kar na isheta da shirmen banza.

Sai da na ɗauki kayana na kuma wankesu sannan na wuce ɗaki, dan acewata wankin Kulu ƙazanta ne, tunda ban taɓa ganin tayi ba sai yau ɗin. Ko da naje ɗakin Inna Amarya sai tace naje wurin Gwaggo, a ɗarɗarce dai na shiga ɗakin Gwaggo sai rakuɓewa nake, ƙasan zuciyata ina ta biya_”dinkimma dinkim Allah ya kafe bakinki”._ dan ni saukar bugu kawai nake jira daga wurinta domin nasan tana sane da komai, jira kawai take Allah ya kawoni kusa gareta ta zartar min da ɗanyan hukunci.


“Idan kin gama raɓe-raɓen ga kaya can a leda ki ɗauka ki saka, karki sa wando sai kin manna waccan abar”. Gwaggo tace dani tana ficewa daga ɗakin.

Na ƙarasa na buɗe ƙatuwar baƙar ledar da ta min nuni da baki, na zazzage kayan ciki a ƙasa, na shiga ɗaga kayayyakin ɗaya bayan ɗaya ina dubawa, dogayen riguna ne da nake ganinsu ajikin labarawa idan munje kallo gidan Liman da azumi, a ciki kuwa harda shigen wadda likitar da tayi min allura ɗazu a asibiti ta saka, kalar shuɗi da fari da wasu azababbun duwatsu ajiki masu shegen kyau da ɗaukar ido, murmushi kawai nake wani sanyin daɗi da farin ciki na baibayeni, babu tantama wannan siyayyar Ya Kabiruna ce, gaba ɗaya rigunan guda uku ne, duk da ban san farashin kaya ba amma da gani kasan kuɗi ne ba ƙarami ba a wannan siyayyar, to amma aina Ya Kabiru yake samun kuɗi kwana biyu? aikin me ya samu?

Tunanina ya katse a sanda naji an kamo hannuna an miƙar dani tsaye, Kulu ce riƙe da hannuna da tattausan hannunta me matuƙar kashe min jiki a duk lokacin da ta taɓani da shi, kallona take da dara-daran idanuwanta wanda na kasa ɗauke ganina acikinsu, ban taɓa kallonta ido cikin ido ba, amma yau saboda tsananin kyawun da nagani acikin ƙwayar idanunta sam na kasa daina kallonsu duk da kwarjin da suka yi min, Magana take min da ido wadda tsab na karance me take nufi, saboda hakane na natsu ina dubanta da abunda tace na maida hankalina akai, wani madaidaicin kwali ta ɗauko a wata leda ta daban dake gefen wadda na buɗe, ta buɗe shi ta ɗauko wando ɗan ciki(pant), ban taɓa ganin irinsa ba dan irinmu Ƴaƴan Malam Audu na ƙauye ba irinsu muke sawa ba, gajere muke sawa irin na tsaffi wanda ake cewa bantai.

Kallon yanda take min bayanai da hannu nake yi, ta ɗauko irin abar da naga an rabawa su Adawiyya kwanaki a makaranta, ta ɓare ledarta ta zaro ɗaya ta manna ajikin wandon, sannan ta miƙo min. “me zan yi da shi?”. Na tambayeta cikin muryata da tayi sanyi.

A yanzunma dai da ido ta bani amsa, ganin zanyi gardama a maganartata yasa ta zare min ido har saida na firgita na rungumeta ita kuma ta tureni daga jikinta, ina ɓata rai na saka wandon ajikina wanda ya kamani tsam, naji wani banbanci na daban. Tana ganin na saka ta bar wurin, na bita da kallo ina maimaitawa kaina anya Kulu mahaukaciya ce?, ko kuma anya asalin Kulun dana sani a gidan nan ce ba masayen wata akayi ba?, ta ɗaga labule zata fita nace, “kiyi haƙuri da kalmar dana faɗa miki ɗazu.”

Shuɗiyar doguwar rigar na ɗauka na saka, na ɗaura ɗan yalolon mayafin dake tare da ita, kamar an gwadani kamin a siyo, inata duban kaina acikinta ina zullumin shigowar madubina gidan yazo ya gane min kyan da nayi, ni tun ina ƙarama ban san nayi kwalliya na duba madubi ba, Ya Kabiru shi ne madubina.

Daga tsakar gida na jiyo Adawiyya na ƙwala min kira, na ɓata fuska nai saurin tattara kayana na jefa ƙasan gado, ina tsaye na haɗe rai ta shigo banko dubi inda take ba, balle na amsa mata maganganun da take, kallona take tana ƴar iskar dariyar nan tata me ƙularwa, na juyo a fusace zan kai mata duka ta kauce.
“ya isheki Adawiyya idan ba haka ba zan gurza miki rashin mutunci, sanin kanki ne hankali ba gama ratsani yay ba walla saina ɗauka wannan langar na rantama miki a tsakiyar ka ki koma sahun su Kulu kema.”

Ta tsagaita dariyarta tana cewa, “Ke nifa banga dalilin da zai sa ki dinga hanani dariya ba, ai bance dake nake ba”. Nayi ƙwafa na girgiza kai tare da cewar,”karki fasa kici gaba”.
Dariyar ta daina tana faɗin,”yasin tawa tafi taki kyau”. Sai yanzu da tayi maganar ma na lura da kayan dake jikinta, doguwar rigace irin tawa amma tata ja da baƙi kuma kwalliyar tawa tafi tata, rigarma dai gaba ɗaya tafi dai-dai da jikina dan ita ta kamata, kuma tsayin yayi mata yawa, ni kuwa daga tsayin har faɗin rigar dai-dai dani, na ƙare mata kallo na kwaɓe baki nace,”arziƙina dai kika ci aka raɓa dake a siyan, kuma wallahi ƙarya kike tawa tafi taki kyau”. Sallamar Ya Kabiru a ƙofar ɗakin na bar inda nake da sauri na tafi naje na rungume shi, adu’a nake jera masa tare da sanya masa albarka, ya ɗago kaina daga jikinsa yana kallona, sai dai har yanzu hannuna na kewaye da shi, na ɗan doki ƙafa a ƙasa da cewa,”Ya Kabiru wannan kallon fa kamar yaune ka fara ganina”. Acikin sigar zolaya yace,”dama ni na taɓa ganinki ne banda yanzu, wace ke?”. Na shagwaɓe ina narkewa jikinsa sai dukan ƙafafu nake a ƙasa nace, “Ya Kabiru ni ce fa”.

Da kwaikwayon maganata yace, “ke wa?”. “ni Mairo”. Ya buɗe baki yana riƙe da haɓa yace,”Yaushe Mairon tawa ta zama balarabiya?”. Murmushi kawai nayi sannan na ɗago daga jikinsa ina riƙe da hannunsa nace,”Ya Kabiru kuma Allah daga yau karka kuma saya mana abu tare da Adawiyya, tun ɗazun tazo tasani agaba tana min dariya wai tata tafi kyau.”

Sai da ya dubi Adawiyya kana yace,”yo dama ita kalar ƙauye ina tasan kyau, baki kalla kayan ko amsarta ba suyi ba ta koma kamar dodo.” Na tuntsure da dariya ina mata gwalo, haushi ya cikata zata bar ɗakin ya janyota jikinsa yana cewa,”aike kika fara tsokanarta.”

Bai bar Adawiyya ta fita ba sai da ya sata dariya kana, ni kuwa har da zungurinta ina ƙara yi mata gwalo, tabbacin ta shaƙa yasa na ƙara da ce mata me wargajejen baki. Duk nauyin da Gwaggo ke cewa ina da shi Ya Kabiru baiji shi ba ya ɗorani saman ƙafarsa guda, ina wasa da gashin sajensa nace,

“Ya Kabiru baka taɓa saya min kaya masu tsananin kyau da tsadar waɗan nan ba, na rasa kalar murnar da zanyi, Ya wanne irin aiki ka samu baka faɗa min ba bayan kace ni ce sirrinka.”

Yana goga haɓarsa saman kaina yace,”wai ni Mairo wanne kaya ma kike nufi ne?”. Na zame daga jikinsa ina cewa, “Ya Kabiru waɗan nan mana”. Yay ɗan jim yana daɗa ƙare min kallo, bakinsa ya motsa kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, muryarsa a hankali ta fita da cewar, “Mairo yau kinfi ko yaushe kyau, kin ƙara kyau sosai, har kyan naki na neman kashe min idanu.” Daɗi ya kamani ina wasa da yatsunsa ina cuno baki gaba nace, “Ya Kabiru amma shi abokinka Jawad haka yace min wai mummuna dani sai rashin kunya, inda za’a bashi ni ma gidan zoo zai kaini.”

Yaja ƙaramin tsoki da cewa,”ƙyale wannan shashashan, komai shi baya masa kyau…kin sha ice cream ɗin dana kawo miki ɗazu?”.
Na kaɗa masa kai alamar a’a, “ai ban gani ba, wa ka bawa ya aje min?”. “a kusa dake na aje miki, ƙila Gwaggo ta ɓoye miki”. “ko kuma wannan kwaɗayyar ƴar tata ta shanye min ba dan nasan dai Gwaggo ba zata adana min ba ko zata ga ƙwari na shiga ciki”. Nayi kamar zanyi kuka na ƙwace hannuna daga nasa na fita a ɗakin ina cewa,”Allah Gwaggo in dai ƴarki tasha min abuna yau saina ɓallata acikin gidan nan”. Tace dani,”me zai hana ki ɓallata tunda kin samu kara.”

Ya Amadu kuwa ko da ya dawo sai cewa yayi ai Adawiyya ta fini kyau, kayanta ma sunfi nawa kyau, nawa ma kamar ba sabbi ba, yau ɗinma dana saka kayan larabawa maimakon nayi kyau sai nayi muni, Adawiyya kuma ta zama kamar balarabiya, Naji haushi sosai danni a komai so nake naji ance nafi ƴan gidanmu musamman Adawiyya da take sakuwata. Abincinsa ma da aka bani na kai masa ɗaki ina sane na faɗi da gangan na zubar, na kuma ji daɗi da Inna Zulai tace babu wani sai dai idan ya duba masu awara.
Da daddare na shiga ɗakin Gwaggo zan cire kaya, na ɗauki zanen Gwaggo da ke rataye jikin ƙofa na rufawa Kulu da ke kwance, saboda yanda naji garin da ɗan sanyi sanyi. Na gama sauya kaya zan fita maganar Gwaggo ta dakatar dani.

Dawo anan zaki kwana”. Nace mata,”bari na ɗauko kayan shimfiɗa”. “zo ki kwanta nan kusa dani”. a kan gadon ƙarfen nata da ta saba kwanciya ita ɗaya na kwanta kusa da ita, na takure zuciyata cike da taraddadi, can naji tayi nisa ta fara ce min.

“A yau kin shiga wata sabuwar rayuwa ta ƴa mace wadda tasha banban data ƙuruciyarki. Zina da dangoginta, Mairo na horeki da ki kiyayesu, idan ba haka ba zaki ƙare rayuwarki ne acikin ƙunci. Mairo kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina, dan wallahi wallahi sai kinji dama mutuwa kika yi akan rayuwarki, yanzu ke ba yarinya bace, kinyi girman da zaki san komai ki kuma san inda ke miki ciwo…wannan jini da kika ganki acikinsa ɗazu bana haihuwa bane jinin girmanki ne, ada idan namiji ya taɓaki za ki zauna lafiya amma banda yanzu, karki bari hawayen dana daɗe da tsaidasu na tsawon shekaru goma sha huɗu suci gaba da zuba a saman fuskata, ki taimaka ki barsu su tsaya iyaka zuciyar, dan duk ranar da kika kuskura kika ɗauko min abun kunya Mairo saina kasheki kamin baƙin cikinki ya kashe ni.”

Maganarta ta ƙarshe ita tasa na haɗiye wani dunƙulallan yawu a maƙoshina wanda ya wuce da ƙyar, tsoro ya shigeni, Zina! Zina! Zina, kalmar da nake daɗa nanatawa acikin kaina kenan tun bayan da naji Gwaggo tayi shiru,

“Kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina.”_ wannan kalaman na Gwaggo suka daɗa haskawa acikin kaina, mene sharrin zuciyar da har zaija na aikata zina?, wacce iriyar soyayya namiji zai nuna min har na aikata zina?, shin da ma ita zinar waɗannan abubuwa biyun ke janyota?, ya ya zinar take ne? Mecece ma ita zinar?, wanne irin hawaye Gwaggo tayi wanda take gudun sake zubarsu a yanzu?. Na rufe idanuwana na mirgina kwanciyata ina fuskantar rufin kwanon ɗakin, ayau dai na tabbata ba zan iya bacci ba cikin wannan daren, saboda maganganun dake tushe acikin kwanyata waɗanda ke neman tarwatsa min kai, ban warware zantukan Baba ba, ga Gwaggo ta kuma ɗura min wasu, na damƙe kaina da nake jin kamar zai rabe gida biyu.

Nafi awa biyu ina juyi bacci yaƙi ɗaukata, da na rumtse ido sai naji gabana na faɗuwa, na tuna da wani wa’azi da muka taɓa saurara a radio da azumi, hakan yasa na miƙe na zuro ƙafafuna domin na fita na ɗoro alwala nazo nayi nafilfili, sai naji maganar Gwaggo na tambayar ina zani?, na waigo muka haɗa ido da ita nace zanyi sallar dare ne. Ta kuma jefe min tambaya,”salloli nawa kika yi ayau?”. “duka nayi ɗazu dana farka”. “to kar ki ƙara yin sallah har sai kinga wannan jinin ya ɗauke miki, ba’a yin sallah idan ana yinsa”. Murya na rawa nace,”to Gwaggo yaushe zai ɗauke?”. “idan ya ɗauke za ki kalla ya daina zuba. Ki kwanta haka”. Na miƙa hannu na ƙaro hasken fitila na dubi fuskarta, muryata sanyi ƙalau nace,”Gwaggo kuka kika yi?”. Ta gyara kwanciya inda ta juya min baya sannan tace,”waya mutu da zanyi kuka, hammar bacci ce, ki koma ki kwanta dare yayi sosai”. “zanje fitsari”. Bata kuma amsani ba, na sakko na nemi ledar ɗazu na zari abar da Kulu ta saka min a wando, dan a karatun bebayen da tayi min a ɗazu har da nuni da sauyata akai akai, na raɓa ta gefen shimfiɗar kulu na fita, da ƙyar na shiga bayi saboda duk a tsorace nake, aikuwa na tsorata sosai da yanda naga jini ya wanke farar audugar, na zareta daga jikin wandona na buɗe murfin masai na jefa aciki sannan na manna sabuwa tukunna na mayar da wandona.

Fitowata daga bayi ina ƙoƙarin ɗauraye hannu, nayi saurin tarar butar dake neman faɗuwa daga hannuna ina cije fuska gudun kar aji motsi, ba ƙaramin razana nayi ba ganin Kulu ta shiga ɗakin Baba a wannan silasainin daren, na koma da baya na ɓuya, ina kallo ta fito ta shiga madafa ta ɗauki kwano ta tuttuli ruwa aciki sannan ta koma ɗakin, tana shiga kuwa nayi saurin fitowa na dawo na laɓe a ƙofar ɗakin Baba ta inda babu me iya ganina.

Maɗaukakin mamaki da al’ajabi suka lulluɓeni a sanda na jiyo maganar Kulu tana cewa da Baba, “daga ina Allon ya ke?”. Muryar Baba ta fita daga can nesa yana amsa mata da, “ɗaga wannan buhun yana wajen”. Shiru ya ɗan gimla kamin ya ƙara da ce mata, “kin tabbata ruwan saman kika tsiyayo?”.

A cikin hausarta da naji bata fita sosai tace,”ehh ina da tabbacin shi ne, dan jarkar naga Yaya ta tara daren jiya.” Nayi wata daskarewa a wajen, ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa da tarin tambayoyin dake cikinta, kenan Kulu ma matar Baba ce? Dama kuma tana magana? Kuma dama lafiyarta ƙalau?, to amma me yasa…?, cak na sume a tsaye ina bin Gwaggo da kallo wadda ta nufo hanyar ɗakin Baba, dai-dai fitowar kuma Kulu, ban mutu a tsaye ba sai da naji Kulu ta kira Gwaggo da,”Yaya”. Ta faɗi hakan muryarta na rawa. Gwaggo ta kama hannunta suka koma ɗakin tana cewa,”bana son kuka ki haɗiye shi.”
ba zan iya faɗar irin ruɗanin dana shiga ba, naja ƙafafuna da ƙyar na wuce ɗaki, sai dai ina shiga ɗakin na zube a ƙasa na zama mutun mutumi, lamuran daketa faruwa da ganina da jina a yau sunfi ƙarfin kaina.

<< Sirrin Boye 6Sirrin Boye 8 >>

1 thought on “Sirrin Boye 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×