Skip to content
Part 5 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Yinin kwana ɗaya da na karanci Suhail na fahimci shi mutum ne irin Ya Kabiruna, rayuwarsa me sauƙi ce, yana da son mutane, yana da wasa da dariya, ga fuskarsa tamkar ta Ya Kabiru cikin fara’a a kowanne lokaci.

Yau Inna Amarya ce da girki, tana kammalawa ta ƙwala mana kira ni da Adawiyya da Jamila akan mu kai karin Kumallo ɗakinsu Ya Kabiru, mu kuma sanar musu na baƙi ne idan bai isa ba wani acikinsu yazo ya ƙara musu. Na ɗauki kwanon koko, Adawiyya kuma ta ɗauki tasar ƙosai sai Jamila ta ɗauki kofuna. A bakin ɗakin muka tsaya muka yi sallama suka amsa sannan muka shiga, daga gefe muka tsuguna kowa ya aje abunda ke hannunsa sannan muka gaishesu gaba ɗaya, Sai dai ni atawa gaisuwar sai dana banbace iyakka inda na isar da ita, dan sai da na kama sunan kowa banda na Jawad, banma kuma lura da yana ɗakin ba ko bai nan, ni dai tunda na hangi Ya Kabiru da Ya Amadu wanda ke daga kwance ma bai tashi ba amma dai ba bacci yake ba, sai Suhail ɗin dake zaune kusa da Ya Kabiru wanda da alamu daga wanka ya fito ya shirya.

Jamila ta faɗawa su Ya Amadu saƙon Inna Amarya, Suhail ya murmusa yace,”Allah sarki Inna kuce mata mun gode, Allah ya saka da alkhairi, muna mata sannu da aiki.”

Adawiyya da Jamila suka amsa da to atare, zamu fita muryar Ya Amadu ta sauka a kunnuwanmu “ba’a koma makaranta bane yau?”. Ya tambayemu cikin kakkausar murya, tare muka haɗa baki wajen ba shi amsa da ehh an koma. “to uban me kuke yi da baku shirya ba har ƙarfe bakwai, kunfi so kullum ku sai kun makara, to kamin na fito ku shirya ku bar gidan nan”. Cikin sauri dukanmu muka fito, ni da Adawiyya kuma harda rige-rigen shiga bayi yin wanka, sai dai kamin ta kai ga sa ƙafa tuni na faɗa naja ƙauren langa-langa na rufe inata mata dariya, ita kuma tana min aikin masifar saura na zauna.

Tare mukayi karin kumallo da Innata, sai dai mu ba irin wanda ta yiwa ƴan gidan suka ci bane saboda tasan bana son koko duk da bawai sha ne gaba ɗaya ba nayi ba, idan nasha ne ya kan sani amai wasu lokutan, ya kuma zamana saina jigata in dai nayi. A kuɗin da mahaifiyarta ta aiko mata da shi jiya, Dama wannan aiken duk sati saita yi musu shi kowacce dake gidan aurenta, shayi ne ruwan bunu da biredi da ƙwai ta bawa Saleh ya siyo mata, bamu ci wainar ƙwan ba ita wannan a kwanon abincina na makaranta ta saka min. Na gama shiryawa cikin sabbin uniform ɗin da Baba ya karɓo mana daga ɗinki daren jiya, na kuma goya sabuwar jakata na zauna ina saka sabon kambas ɗina, Adawiyya ta shigo wadda tuni ta gama nata shirin, ta gaida Inna sannan tace min,”kiyi sauri fa mu fita ga Ya Amadu can ya shigo”. Ina zaro ido waje nace ma ta, “haba?”. “wallahi sun shigo su na ɗakin Inna suna gaisheta, ki sauri kamin su ƙaraso nan”.duk kazar kazar ɗina yau babu shi, wajen ɗaure igiyar takalmin ne ya ɓatan lokaci, ina zaune inata fama da ɗaure igiga Ya Kabiru yayi sallama ɗakin sannan yasa kai y shigo, yace da Inna za’a shigo gaisheta, nan da nan kuwa muka ɗan kimtsa wurin muka shimfiɗa tabarma sannan yay musu iso suka shigo, sai da Inna tayi musu nuni da tabarma kana suka zauna, cikin girmamawa da ladabi duk suka gaidata, da zasu tafi Suhail ya fiddo kuɗi cikin aljihu sabbi ya ajiye mata a gefe, duk yanda tayi akan ya ɗauke yaƙi yace a’a, ta kuwa yi musu godiya sosai tare da sanya albarka. Acikin kuɗin Inna Amarya ta bamu kuɗin makaranta kowannenmu naira ɗari ni da Adawiyya, tayi min adu’a kana na fito na nufi ɗakin Gwaggo, Ko dana shiga ɗakin zaune na sameta bisa darduma ƙafafunta a miƙe ta zuba tagumi, da alamu dai tunda ta idar da sallar asuba bata miƙe daga wurin ba. Irin wannan yanayi shi ne matuƙar ƙololuwar yanayi dana tsani tsintar ganinta aciki, yana damuna yana kuma tada min da hankali, saita zauna tayi shiru ta zuba tagumi, wani lokacinma ko da kayi mata magana da ido kawai zata bika ta baka amsa da hannu.

Ƙafafuna a sanyaye na ƙarasa wurita na zauna, na kuma zare mata tagumin, sannan ta farga da shigowar tawa, na rungumeta tarin hawaye na cika min idanu, Muryata na rawa nace, “me ya sami Gwaggona? Me aka mata? Waya taɓa min ita? Meke damunta?”. Na ƙarasa maganar ina fashewa da kuka a hankali tare da daɗa manna kaina a ƙirjinta, ina jin tausayin mahaifiyar tawa na ƙaruwa a raina fiye dana ko yaushe. “ke ni ban san shirmen banza, mene da sanyin safiyar nan za ki sakani gaba da kuka, kina nufin makarantar ce ba za kije ba?” Maganar ta-ke da ƙoƙarin kawar da damuwar dake tare da ita, da kuma ɓoye wani abu da bata so na fahimta, sai dai kuma ta makaro dan tuni na fahimci wannan manyan idanun nata irin nawa hawaye suka.yi, idan saɓanin haka kuma to tabbas kwana suka yi basu runtsa ba, cikin biyu dai dole anyi ɗaya, wanda kuma hakan ya ƙara ɗaga min hankali kawai saina fashe da kuka mai sauti, itama kuma sai kukan nawa ya ɗaga nata hankalin tasa hannu ta kewayeni ajikinta, haɓarta bisa kaina, kukana ne kawai ke fita a ɗakin sai bugun zuciyarta dake sauka a kunnena, na rage kukan da nake sai shashsheƙa, na kuma buɗa baki cikin muryar kuka na kuma jera mata wancan tambayoyin da nayi mata. Nauyayyar ajiyar zuciya naji ta sauke tare da faɗin,”Girmanki Mairo”. Nayi saurin ɗago kaina na dubeta, idanunta na kallon wani gefe can daban. “Gwaggo me girman nawa yayi? Ko ba kya sonsa ne?”. Bata bani amsa ba har saida ta rufe ido ta buɗe kana tace,”idan nace bana son girmanki Mairo ai na shiga lamarin ubangiji, Ina dai tsoronsa ne”. “to saboda me Gwaggo?”. “saboda bana so kiyi min nisa, ina sonki ina ƙaunarki, burina a kullum shi ne naga na buɗe ido na ganki a kusa sa dani, ina jin muryarki, ina ganin kai da komowarki, a taƙaice dai Mairo ina so ne kiyi rayuwa ta har mutuwa a kusa dani. To amma sai dai aure ƙanen mutuwa dole zai rabani dake, zai nisanta tsakaninmu, Nan da shekaru biyu zuwa uku nasan Malam zai ce zai aurar da ke, kin gama wayon da zaki karanci rayuwa cikin lokaci ƙalilan…”. Ban bari ta ƙarasa ba nasa hannu na rufe mata baki, saboda yanda naji muryarta tayi rauni har tana Neman sarƙewa, nasa hannu na rufe mata ido saboda ruwan hawayen da suka taru su koma. “Gwaggo dole zan girma tunda Allah shi ke da halittarmu, amma sai dai nayi miki alƙawarin girmana ba zai kawo barazanar nisanta kusancinmu ba, wallahi ba zanyi nisa dake ba Gwaggona, in har Aure ne zai rabani dake to na rantse miki da Allah ba zanyi auren ba, ai dai har saina kawo saurayi gidan tukunna Baba zai aura min shi ko, to wallah ba zan kawo shi ba tunda nasan Baba ba zai yi min auren dole ba, idan ya zama dole kuma zanyi auren to sai dai a zaɓa cikin biyun ɗaya, ko mu tare acikin gidan nan ko kuma na fasa auren gaba ɗaya, saboda haka Gwaggona ki kwantar da hankalinki babu abunda zai nisanta ni dake, ina kusa dake har ranar yankewar numfashina”. Murmushin daya tsaya iyaka leɓenta naga tayi, wanda fassararsa tafi kama da ba zaki fahimta ba. Zan ƙara yin magana ta tari numfashina da bagarar da zancen da muke, tana ɗagani daga jikinta tace,”karfa ku makara azo ana sai kun kawo klin da sauransu”. Ta faɗi hakan tana gyara min fuska da cewa,”Allah yayi miki albarka Mairo, ya tsare min gabanki da bayanki, yayi riƙo da hannayenki”. Sai kuma ta hau yi min nasihohi na tsoratarwa akan rayuwa, ta kama kaina ta karanto min adu’ar da ta saba yi min a duk sanda zamu fita, tun banfi shekara shida ba na haddace Adu’ar da nake ji na fita daga bakinta agareni, “a’uzu bikalmatillahi tamma, min kulli shaiɗani wahamma, wa min kulli ainin lamma”. Daga tsakar gida na jiyo Adawiyya na ƙwala min kira, tana faɗin takwas saura. Gwaggo ta ƙarasa tofeni da adu’oi tare da faɗar “tashi kije Allah tsare hanya, a kula sosai don Allah don Annabi”. Sai dana kai bakin ƙofa zan fita ta kirani na dawo, ƙasan filo ɗinta naga ta ɗaga ta ɗauko wani abun hannu mai tsananin kyau sai ɗaukar ido yake, ta kama hannuna ta sanya min, magana nake so nayi akansa amma mamaki ya hanani, sai tambaya ɗaya da ta tsaya akaina, aina Gwaggo ta samo wannan warwaron me kama dana sarakai?, banda me bani amsa dan nasan ko na tambayeta ba zan samu amsar da nake so ba.

Fitata ɗakin Baba na shiga, na sa me shi ya kamalla karin kumallon safe yana zaune yana sauraron radio, na ƙarasa na zauna gefen dama da shi na zauna ina gaishe shi, fuskarsa ɗauke da annuri ya amsa min yana cewa,”har an fito makarantar?”. “ehh Baba mun fito zamu tafi. Baba a bamu kuɗin makaranta”. Ya zura hannu a aljihu ya ɗauko naira hamsin ya bani yace na ɗauka ashirin na bawa Adawiyya ashirin, goma kuma mu bawa Saleh.

Na ƙara matsawa kusa da Baba kamar yanda ya umarce ni, shi ma kaman dai yanda Gwaggo tayi min haka yay min, hannunsa na dama saman kaina yana karanto tarin adu’oi masu yawa yana tofa min, Tun shigowata ɗakin na lura da wani yanayi tare da Baba wanda ban saba ganinsa aciki ba, kai bama na ganinsa aciki, dan shi ma yau bashi da walwala, kuma a kallo ɗaya zaka gane akwai abunda ke damunsa, kusan dai irin yanayin dana sami Gwaggona aciki, sai dai shi ko da ya ɗago fuskata murmushin farinciki naga yanayi, sai dai kuma ni Mairo me wayo ce, dan tuni na gama karantar wannan murmushin na ƙarfin hali ne, sai da yayi gyaran murya tukunna naji yace,”a irin wannan ranar aka haifeki Mairo, ita ma kuma ranar da aka haifeki an kwana ana ruwan sama, saboda haka ina tayaki murnar zagayowar haihuwa Ƴata, Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki, ya kareki daga sharrin mazan zamani, yay riƙo da hannayenki”. Adu’oi ne iri-iri Baba ke jera min su, kamin shi ma ya ɗora min da tasa nasihar, nasiha me kamanceceniya da irin ta Gwaggo, Sai dai tasa akwai banbanci da irin ta Gwaggo, dan tun daga farko har yanzu da ya nunfasa cikin nasihar fitar kowacce kalma me isar da saƙo ce, kum duk zurfin tunanin da mutum zaiyi zai ɗauki lokaci kamin ya gama nazartar abunda ake son isar masa. Jikina gaba ɗaya naji yana neman mutuwa saboda wasu ƙalmomi na ƙaddarori da naji Baba na min karatu akansu, karatun kuma da naketa so na fahimta amma na gagara, dan kamar karatun yafi ƙarfin kaina a yanzu, amma wataƙila anan gaba na iya fahimta, to amma me yasa aciki ya tsoratar dani sak da irin tsoratarwar da Gwaggo tayi min?, lokaci ɗaya na haɗa maganganunsa da nata suka zama ajimlace, dukansu karatu iri ɗaya ne sai dai kowanne da yanayin da yay koyarwarsa, idan baka da saurin ganewa za kayi tunanin karatu ne daban-daban, to amma duk dana gane karatu ɗaya ne na kasa warware kalaman da nasan saƙo ne da yake mallakin wanda ake karantawa.

Ganin kaina na neman fashewa na haƙura da abunda ya girmi tunanina, na daɗa fuskantar Baba da tambayarsa shekaruna nawa a yanzu?. Ya bani amsa da,”shekararki goma sha huɗu cif Mairo”. “to amma Baba me yasa Gwaggo ke cewa Sha uku?”. “ita zaki wa wannan tambayar. Yanzu tashi ku tafi kar a makara”. Na sauke numfashi tukunna na miƙe da ƙafufuna da suka yi sanyi, nayi mishi sallama na fito a ɗakin.

Adawiyya nata jefa min tambaya da sauyawar yanayina, sai dai ban bata amsa ba har muka ƙaraso ƙofar gida, a zahiri a duniyar nake amma hankalina ya cilla can wata duniya ta daban.

“Mairo, Mairo, Mairo”. Kiran da Ya Kabiru ke ta min kenan, amma ko ɗaya banji ba sai da ya ƙara dana huɗu sannan na dawo firgigit daga duniyar tunanin dana faɗa, ya tsareni da idanu tare da jefo min tambayar, “ke me kike tunani haka za ki je ki kashe kanki a banza.”

Tambayar yayita ne a sanda yake janyoni daga tsakiyar hanya zuwa gabansa, sam banda yanzu da hankalina ya dawo jikina ban san ma nayi wannan tafiyar me tsayi ba, na san dai na fito daga ɗakin Baba da tambayar da Adawiyya keyi min, amma daga nan ban san inda hankalina ya cilla ba.

Na dabarbarce na rasa ma me zance, sai naji ya sarƙe yatsunsa da nawa ya daɗa matso dani gabansa sosai, ya ranƙwafo da kansa kaina tare dasa yatsa ɗaya ya ɗago da fuskata na kalle shi, numfashina Da nasa suka gauraye wuri ɗaya, cikin wata iriyar murya da ban taɓa jinsa da ita ba yace,”Menene Mairo?”. Murya a hankali ya tambayeni, na lumshe ido na buɗe sannan na bashi amsa da cewar kaina ke ciwo. “shi ne kuma ba za ki faɗa ba za ki wuce makarantar a haka?” “Ai yanzu ne ya fara ciwon”. Maganar Ya Amadu ta dakatar da Ya Kabiru da abunda yake son cewa. “ciwon kai ba?”. Ya faɗa yana taɓa shatin jijiyar goshina da ta fito raɗau, Na ɗaga masa kai kawai saboda yanda nake jina jiki duka ba ƙwari, bakina har wani ɗaci yake yi, cikina kuma na ɗaurewa.

Kasancewar su Suhail sun fito zasu tafi, sai Ya Kabiru yake ce musu dan Allah bari Ya Amadu ya bisu su saukemu ko a hanya ne zai kaini asibiti, Suhail yace da shi,”ka jika da wani zance Kabiru, ko motar aini mai bayarwa ne akaita, su fito mu tafi”. Ya Kabiru yay masa godiya ni kuma ya buɗe min bayan motar na shiga, ganin Jawad aciki nace Allah ya kasheni in dai da shi acikin motar nan ni kam ba zani ba ƙwamma na mutu, Ya Kabiru ya doka min tsawa da rashin hankalin da yaga ina neman yi, ciwon ma har naji ya tafi. Shi dai Suhail kallona kawai yake da darun da nake bugawa, ban nutsu na shiga hankalina ba sai da Ya Amadu yazo.

Da Adawiyya muka tafi aka sauketa a makaranta, Ya Amadu kuma ya bada uzurin rashin zuwana, sannan muka ɗau hanyar asibiti, ina jin Ya Amadu na cewa da Suhail na gwamnati za muje yace a’a bari mu wuce private, idan akace na gwamnati ne ciwon nawa har sai yayi worst basu duba ni ba, amma can inda za muje akwai file na ƴan gidansu sai a duba ni da shi.

Kai tsaye wani haɗaɗɗen asibitin kuɗi muka je, sai dai ko kusa ban iya karanta sunan dake jiki ba dan rubutun kamar na aljanu, duk da cewar na iya karatu sosai amma nafi ƙwarewa a iya karanta Hausa, babu ɓata lokaci aka dubani aka kuma tula min magunguna, allura kuwa da akazo yi min nayi kuka na gode Allah, nurse ɗin kuma tasha Allah ya isa tafi cikin ludayi, na tsani allura ko ba’a kaina ba. A dubu Goma kaɗanne babu shi ne kuɗin da aka cajemu, kuma duka ba Ya Amadu ne ya biya ba Suhail ne ya biya, haka da muka fito daga asibitin ya saya min kayan marmari yace tunda tafiya zai yi ga kayan dubiyarsa. Ina jinsu su na maganar su zasu wuce ne gidan Sarkin bichi, Jawad na cewa Allah yasa idan sunje Fulani bata nan, Suhail kuma na cewa shi dama ba wurinta za shi ba, wurin Ammi zai je, dan akwai kyakykyawan albishir ɗin da zai kai mata. A yanzu ne kuma na fahimci Suhail da Jawad ƴan’uwana ne ba wai abokai ba.

“Mairo ban yarda da amsar soyayyar kowanne namiji a waje ba, in har kika yi hakan Mairo ba zan yafe miki ba kuma zanyi miki Allah ya isa, duk wanda ya nuna yana sonki da aure kiyi masa kwantace da gidanku, ni kuma a ranar da yazo zan aura masa ke a lokacin ba tare da ɓata lokaci ba”. Tun shigarmu motar haya bayan saukemu da su Suhail su kai muka hau, maganganun Baba dake ta aikin tariya acikin kaina kenan, kalaman da yayi minsu a kausashe kuma acikin faɗa.

Muna dawowa gida na zube a ɗakin Gwaggo riƙe da ciki ina murƙususu a ƙasa, tun ina nishi har na daina na koma kuka wiwi ina kiran sunan duka ƴan gidan akan suzo su taimakeni, mutuwa ne zanyi. Mutum na farko da nasan yazo kaina Kulu ce, cikin tsananin tashin hankali da firgici ta tarairayoni jikinta, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni shimfiɗe a gadon Gwaggo. Gabana yayi mummunar faɗuwa ganin yanda Gwaggo da Inna Amarya da Kulu ke tsaye a kaina, kowanne fuska ɗauke da tsantsar damuwa, ni Gwaggo ma sai naga kamar tana jifana da mugun kallo da idanuwanta da sukayi jawur. Nayi saurin rumtse ido sakamakon wani abu me girma da ya fito daga gabana.

<< Sirrin Boye 4Sirrin Boye 6 >>

2 thoughts on “Sirrin Boye 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×