Rikicewa Kulu tayi da ganin Gwaggo wacce ke kallonta tun daga sama har ƙasa da son gano abunda ta-ke ɓoye mata, tsawon daƙiƙun da ba zasu haura biyu ba Gwaggo taja tsaki, ta bar kusa da ita ta ƙarasa bakin gadon da Mairo ke kwance tana faɗin, "Abu ne mafi sauƙi a wajena na kori mutum ya koma inda ya fito matsawar ba zai kiyaye sharuɗan da na ke gindaya masa ba...saboda na ɗaukeki ina taimaka miki ba yana nufin dole kema kice zaki taimaka min ba, ba kowa na yarda da shi. . .
Thanks