Skip to content
Part 9 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State

“Bullshit! taya za’ai Yemi zaiƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin daya fara take umarnina?”

Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin dake zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin dake kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar acikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin dake sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa.

“Ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours”. Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin da Dr Emanuel ya miƙo masa ya fita.

2 hours Passed

Emzor Pharmaceutical Industries Limited

Emzor Kamfanin ne na ƙera magunguna wanda aka kafa tun a shekarar 1984 a ƙasar Najeriya.

Kamfanin da aka kafa da manufar yin samfurori masu inganci na magunguna.
Kamfanin yana daga cikin jerun mayan kamfanunuwa guda goma da suka shahara a nigeria. Tun bayan da Obafemi Afafa mamallakin kamfanin ya rasu, Babban ɗansa me suna Tosin Afafa yaci gadon kamfanin kasancewarsa ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifin nasa. To shi ma ayanzu ya maida Babban ɗansa me suna Dr Emanuel Tosin Afafa the CEO of the company, wanda ya kasance mai ƙwazo da himma wajen ganin kamfani na samun ci gaba ƙwarai da gaske. Duk da a baya bai taɓa zaton zai iya ɗaukar ragamar nauyin kamfanin ba, dan acewarsa ba ya jin zai iya ɗaukar all those responsibilites na shareholdings, business trip and rest, to amma da ya ke mahaifin nasa General Tosin tsayayye ne wanda ba ya magana biyu haka dole ya haƙura, ya ke kuma gudanar da ayyuka yanda ya kamata, kuma a sabbin tsarinsa da ya ke son aiwatarwa a yanzu yana so ne Mahaifinsa ya yarje masa ya shigo da sauran ƙannensa cikin wannan harkar, to amma mahaifin nasa yaƙi ba shi dama, ya sanar masa suma da akwai sauran kamfanin da yake son buɗewa wanda kuma yake tunanin watsa ƙannen nasa aciki wato Joseph da Obi.

Duk da shi ɗin arnene da babu hasken musulunci tare da shi, amma kuma yana da kwarjini, cikar zati haɗe da wani irin farin jini da ko acikin musulmai ba kowa ubangiji ke mallakawa irinsu ba, shi yasa da yawan musulmai da suka san kyawun halayyarsa suke masa adu’ar Allah yasa ya musulunta. Tafiya yake da irin taku mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali na irin mutanen da jin daɗi har yay musu yawa, bai san talauci ba domin bai taso acikinsa ba, haka kuma bai san wahala ba dan bai saba da ita ba, sai dai kuma shi ɗin mutum ne mai tsananin tausayin talaka da son taimaka masa, walau ɗan’uwansa kafiri ko kuma musulmi.
Tun da ya sanyo ƙafa cikin kamfanin ya sauya yanayin fuskarsa in da ya tamketa, dan sam baya bawa ma’aikatan fuskar da za su aikata abun da suka ga dama acikin ma’aikatar saɓanin yanda yake so su kasance. A duk wani taku da yake Oluwa na biye da shi a baya, hannunsa ɗaya riƙe da ash suite ɗin Oga ɗayan kuma riƙe da brief case nasa, har san da suka ƙaraso bakin office ɗinsa ne kuma ya miƙawa sakatariyarsa Joy kayan ta ƙarasa shiga da su. Joy ta shigo ta rataye rigar suite ɗin ajikin hanger, sannan ta kai brief case ɗin ta aje kan table tare da daɗa gyara wurin, ta tsaya tana kallon Dr Emanuel wanda ke tsaye a bakin window, ya zuba duka hannayensa cikin aljihun wando, yana ƙare kallo ga yanayin garin damunar da hadari ya haɗo a yanzu idanu na nuna ruwa na gab da sauka, ko da Joy tayi masa magana sai da ya ɗauki tsawon daƙiƙa kamin ya juyo yana zare baƙin glass ɗin da ke kewaye saman siririyar farar fuskarsa, Joy tayi saurin janye idanunta daga kallon nasa, ta rissinar da kai tana wasa da yatsun hannunta zuciyarta kuma na bugawa, har ya ƙaraso yaja kujera ya zauna bata sani ba sakamakon lulawa da tayi acan duniyar tunanin da ta ke yinsa a kullum na son ace yau ta mallaki Oganta.

A hankali ya motsa laɓɓansa kamar wanda bai son yin magana, “ki cewa MD ina son ganinsa yanzu”. Ta ɗago ido cikin rissinar da kai tace masa, “Bayani dangane da Vitro Health su na so ne mu haɗa contract da su akan magungunan da za’a fitar ƙarshen watan nan.”

“Ki aje takardun zan yi tunani akai first kamin nayi singining, ki kuma ƙara min bincike akan kamfanin sosai kamin na bar office”. Ta amsa masa da to sannan ta ƙara da cewa, “Jiya bayan fitarka babu jimawa kayi baƙi daga EDIG, yanzu haka ma su na reception su na jiranka”. “dama ina da appointment da su ne a jiya da yau ɗin?”. Daga yanda yayi mata tambayar ta san tayi ba dai-dai ba, dan haka sai da ta haɗiye wani yawu a maƙoshi kana ta amsa masa,”a’a baka da, hasalima cikin watan nan kaf baka sanya appointment da kowa ba”. Ya bar shafa computer ɗin da yake ya kwantar da kansa jikin kujerar da ke juyi da shi, hannayensa a dunƙule ya lumshe ido sannan yace da ita,”amma me yasa kika barsu su na jira?”. Jikinta ya hau tsuma ta fara inda-indar magana,”Naji sun ce ne maganar da za kuyi tana da muhimmanci, shi yasa har na amince musu akan su dawo a yau ɗin”. Tai maganar tana aikin sosa ƙasan kuncinta.

Ya girgiza kai a lokacin da yake kallonta ta gefen ido, a ransa yana ƙirga irin matsalolin da Joy ke haifar masa tun zuwanta kamfanin watanni biyar kenan, dama wannan ne last mistake da yake so ta ƙarayi sannan yaywa tufkar hanci. Jin shirun nasa yayi yawa yasa ta ƙara cewa da shi, “Sir zan iya yi musu iso?”. “Am not available, so ki san yanda za ki da su”. Sanin cewar ko da ta kuma yin magana ba zai saurareta ba ta juya ta fice da gwiwa a sace.

Bayan wucewar daƙiƙu biyar da fitarta MD Simon Ya turo ƙofa ya shigo, har san da MD ya ƙaraso ya zauna a kujerar da suke fuskantar junansu Dr Emanuel bai ɗago ya dube shi ba, sai dai a yanda yaga yana karanta takardun dake aje kan table ɗinsa da kuma yanda ya dunƙule hannu ɗaya yasan cewar akwai damuwa, sai dai bai yi hanzarin katse shi ba har zuwa lokacin da Emanuel ya ɗago ya dube shi tare da tura masa takardun zuwa gabansa. Md ya ɗauki takardun yana karantawa, ya kalli Emanuel a sanda ya gama karantawar sannan yace, “amma Joy bata yi maka wani bayani dangane da shigar report ɗin ba?”. “na kore ta”. Md ya maimaita maganar tasa,”ka kore ta?”. “yes”. Md ya jinjina kai da faɗin,”amma dai a wannan karan bani zan sake nemo maka wata sakatariyar ba ko?, dan na gaji da nemo maka kana korarsu ɗaya bayan ɗaya haka kawai babu wani dalili”. “Ba zan iya zama da marar gaskiya acikin aikina ba, kai kuma duk marasa gaskiya kake kawo min, so this time around na hutar da kai da kaina zan nemo”. Md yay murmushi kawai, dan yasan a ƙarshe dai dole shi ɗin zai sa ya nemo masa.
“ka san babban abunda ya ɓata min rai?”.
Md ya kaɗa masa kai yana me ƙara duban takardun hannunsa cike da takaici.
“me yasa tun farko Yemi da yasan mutanen nan bana ƙwarai bane yaƙi sanar damu sai bayan da mu kai accepting contract ɗin nasu sannan zai dawo da takardun yace min ba zai sa hannu ba.”

“Dr ka ƙara duba sosai da nazari akan wannan lamarin, in har ba akwai wani mugun ƙullin a zuciyar Yemi ba, Babu yanda za’a ce morethan two weeks yana sane yaƙi signing kuma bai sanar ba sai a yanzu da ake son gama shigar da komai sannan zai ce contractor ɗin yayi rejecting, no way dole akwai wani abu a ƙasa.”

Emanuel ya ɗaga kafaɗa, “abun ya min ciwo amma kuma ba zai dame ni ba.”
“me yasa zaka faɗi haka? Wannan fa faɗuwa ce ke neman shafar kamfaninmu”. Emanuel ya dube shi sosai sannan yace,”ai tun farko nace bana son kamfaninmu ya haɗa contract with any other companies, amma kai da Dad kuka ce ai NDBH ba abin yadawa bane, dan haka ni na cire hannuna, faɗuwarku ba daga ni bane daga gareku ne, kuje ku shawarta yan da za kuyi.”

Md ya dunƙule hannu ya doki table, “Ya za’ai ana talking of billions kace wai zaka zame hannunka aciki, kasan kuwa irin asarar da kamfanin zai samu, da kusan quarter ɗin kuɗinmu fa mu kai amfani.”

Yanda Emanuel ya ɗaga kafaɗa irin ko ajikinsa hakan kuwa ya ƙular da Md, ya kuma bi shi da ido har zuwa inda ya zauna kan cushion ɗin cikin office ɗin, ya ɗau coffee yana kaiwa bakinsa. “har wani lokacin shan coffee ma kake da shi?”. Emanuel ya kalle shi ta cikin reflection glass na cup ɗin, ya motsa laɓɓansa kan ya kurɓi coffee ɗin sannan ya aje cup yace da shi, “me kake so nayi kuma?”. Md ya girgiza kai ya miƙe ya koma kan kujerar Emanuel ya zauna, ya zari farar takarda yay short rubutu ajiki, Sannan ya miƙe yay tattaki zuwa inda Emanuel yake ya ajiye masa takardar a gabansa, ba tare da Emanuel ya dubi rubutun dake cikin takardar ba ya miƙa hannu ya karɓi biro daga hannun Md sannan yay signing a in da Md yay masa nuni. Cikin lokacin da basu haura daƙiƙa biyar ba Md ya buga takardar ya ninke yasa a envelop sannan ya fice daga office ɗin ba tare da yaywa Emanuel sallama ba, yana kuma jin san da Emanuel ɗin ke cewa da shi zai ɗauko ɗan arewa a matsayin sakatare na shi, yay banza da shi bai ce masa uffan ba domin ba abune mai yiwuwa ba dan Dad ma ba zai bar shi ba.

1hour passed

Ta cikin Kamfutar da ke aje saman table Emanuel ke video call da ƙanensa Obi, tambayarsa yake dangane da halayyar abokinsa ɗan arewa da su kai aiki shekaran baya. Obi ya buɗi baki yace,”Brother kana da study of psychology, dan haka a ɗan iya zaman da mu kai last time da Ahmed na san ka gama karantar halayensa”. Emanuel ya kaɗa masa kai alaman haka ne sannan yace masa,”ku yi magana da shi kaji idan zai iya zaman Lagos, ina so zan ɗauke shi aiki matsayin sakatare mai kula da harkar shige da fice na office ɗina”. Obi yay tsalle a saman royal bed ɗin da yake kwance, “what a great news, amma gaskiya brother naji daɗi sosai akan wannan tunanin da kayi na ɗaukan Ahmed aiki domin shi ɗin mutumin kirki ne, sam bashi da mugunta acikin zuciyarsa, ni shaidansa ne a zaman da muka yi na karatu da shi”. Emanuel ya ƙara tambayarsa da cewar, “mene full name nasa?”. “Ahmedu Adamu Bichi”. “is he single or married?”. “no he is single, amma ban sani ba ko zuwa yanzu yayi aure dan mun ɗau tsawon lokaci ba muyi waya ba since time da na bar nigeria.”

“I hope ya iya turanci tun da kaga mu nan ba jin hausa ake ba.” “ehh bross yana da speech me kyau, shi fa kawai dan dai yazo a mutumin karkara ne.”

Emanuel yace da shi,”to kayi gaggawan sanar da shi yau, becouse within next tomorrow nake so ya fara gudanar da aiki, idan yana da iyali yana tunanin ba zai iya barinsu ba you should let me know za’a samar masa gida cikin gidajen Dad na GRA.”
“Okay bross.” “Ina Mommy?”. Emanuel ya tambaya a san da ya kai apple baki ya gutsira. Obi yace, “Mommy sun je church ana bikin ƴar gidan Pastor Eze”. “what about Dad?”. “yana ɗakinsa, na fuskanci yau mood ɗinsa is not good, dan ko da naje gaishe shi bai amsa min ba kai ya ɗaga min kawai, kuma har na fito idonsa a rufe yake”. Lokaci ɗaya hankalin Emanuel ya tashi, yay decline call ɗin ya ɗau wayansa ƙarama yay dialling numban mahaifinsa, har sai da ta yi ringing biyu ta katse sannan mahaifin nasa ya kira shi, ya ɗauki wayar murya ɗauke da damuwa ya shiga jerawa mahaifin nasa tambaya ba tare da ya ko amsa gaisuwar da Dad ɗin nasa ke masa ba.

“Dad meke faruwa da kai? Baka da lafiya ne?” Daga can ɓangaren General Tosin Afafa yace da ɗan nasa,”babu Wata matsala Son, ya office naka?” Emanuel bai yadda da maganar mahaifin nasa ba, ya dai ji shi ne kawai, saboda daga yanayin muryarsa za ka fahimci akwai damuwa tattare da shi. “Dad komai lafiya, sai dai ina so zan biyo jirgi gobe nazo na ganku”. “no ba sai kazo ba mu ma ending this month zamu dawo, na gama gudanar da aikin da ya kawoni, ni kaina na gaji da zaman ƙasar nan…i dont know what is exactly happening to me amma hankalina gaba ɗaya yayo nigeria”. Emanuel zai kuma magana Dad ya tari numfashinsa da cewa,”Son ka bar kallon news ne?”. “a’a Dad, jiya ne dai da yau ban kalla ba saboda aiki da ya min yawa a office…yauwa Dad ko Md ya sanar da kai yan da ake ciki game da Contract ɗinmu da NDBH?”. Dad yace da shi,”Son for now ka manta da wannan tukunna, ɗazu ina kallon news akwai yaran da akayi kidnapping from university, and the kidnappers are talking about 4millon kana su bayar da su, iyayen yaran kuma basu da kuɗin karɓo su, infact ma suna maganar cewar idan gwamnati ba zata taimaka masu ba zasu bar musu ƴaƴan tunda basu da yanda za suyi, so ina so ka fitar da wannan kuɗi aje a amso yaran daga nan zuwa yamma kaji ko…and dont let your Mum know about this issue plss”. Emanuel ya amsa umarnin mahaifin nasa kamin kiran wayar nasu ya katse.

Kano, Masarautar Bichi

Zaune muke a wani tamfatsetsen falo na gidan saurauta wanda aka ƙawata shi da kayan alatu iri-iri na mo re rayuwa, ni dai tun shigowarmu bin ko’ina nake da kallo ina jin dama ace mune acikin wannan daular, Adawiyya da ke kusa dani ta zungureni na juyo na dubeta, tana wani yatsine fuska tace,”Wai ke sai ance mana ƴan ƙauye”. Na harareta nace,”to da su wane? Kinga ki rabu dani na kashe kwarkwatar idona yanda zan ji daɗin bada labari wataran, kuma sarai kin sani daga yau ba kuma shigowa zamu yi ba.”

Tasa hannu ta toshe dariyar da take ƙoƙarin yi, saboda ina nunawa Habiba wani abu kamar bal yana juyawa ta saman cikin ƙwai yana fesar da hayaƙi da ke bada daddaɗan ƙamshin a cikin falon. Ni tun ina jin daɗin zaman ma har na fara gajiya na fara jan tsaki, ga shi Ya Kabiru da ya kawomu yasa ƙafa yay tafiyarsa tun ɗazu da shi da Suhail.

Na miƙe tsaye saboda yan da na gaji da zaman, baiwar da aka sa kula da mu ta doka min tsawa akan na koma na zauna, nayi firr da idona nayi ma ta banza kamar ban jita ba. Sai gata ta taso daga in da take cikin sassarfa tayo kaina, dukana za tayi kome oho mata, nasa hannu na dakatar da ita da cewar, “ke ni ba ɓarauniya bace balle kiyi zaton ko sata zanyi muku, ki bar ganin girman masarautar nan taku da daular da ke ciki to wallahi ba ku da abun da zan sata, dan ina da godiyar Allah a matsayin da ubangiji ya ajeni ciki, tashin da kika ga nayi tafiyata zan yi na gaji da wannan zaman shanyar da akai”. Za tayi magana sai ga Jawad ya fito daga saitin ƙofar da mu ke tsaye, kunnensa sanye da abun jin kiɗa hannunsa kuma riƙe da waya yana dannawa, tafiya yake ko kallon gabansa bai yi, baiwar ta zube ƙasa tana jera masa kirari irin nasu na ƴan maula wanda har haushi sai da ta bani naji kamar nasa ƙafa na mangareta gefe. Bai ko bi ta kanta ba yazo wucewa ta kusa dani na taɓe baki naja ƙaramin tsaki wan da shi kaɗai ya iya jinsa, nan ya dakata da tafiyar ya ziro hannunsa ta wuyana ya ɗalle min baki, acikin kunnena yake faɗin,”yarinya idan tace zata min rashin kunya acikin gidanmu wallah sanyawa zan yi fadawa su zane min ita, koma nasa a maida ita tarihi sai naga da wanda zata kuma yi”. Idan ya barni ma da jin zafin ɗallemin laɓɓa da yayi kaɗai ya isheni, banda kuma take ƙafa da yay min da wani shegen takalmi da ke ƙafarsa irin na ƴan sarauta, ya san da cewar naji zafi tun da yaji bakina ya ɗinke, amma duk da hakan bai ƙyaleni ba sai da ya kuma sa yatsa ya ɗalle min laɓɓana, zafin da naji a wannan karan yafi na ɗazu, idona ya cicciko cikin zafin nama na ɗauke hannunsa daga saman wuyana na wurgar da irin yanda shi ma zaiji zafi, na jiyo na fuskance shi da ƙarfi nace,”Allah ya isa mugu azzalumi, kuma wallahi nima sai dai idan baka shigo ƙauyenmu ba sai na rama”. Ya kuma kawo hannunsa zai gwaɓe min baki maganar dattijuwar da ke shigowa ta dakatar da shi. “Jawad me na ke gani haka?, yara na wajenma kai ba zaka ƙyale ba”. Yay min duba kaɗan sannan yace da ita, “Ammi bata da kunya ne, ba ki kalla yan da take zumɓurowa mutane baki ba”. Ta nufi kujera tana zama tace,”wani abun kayi mata shi yasa, ya kamata ka rage zafin zuciya, haka kawai dai yarinya ba zata zumɓura maka baki ba babu abun da kayi mata, wuce ka bamu wuri”. Maimakon ya wuce kamar yanda ta umarce shi sai ya nemi ɗaya daga cikin wasu tsinannun kujeru na alfarma ya zauna akai, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yaci gaba da danna wayarsa. Ni kuma na tsuguna na gaida matar, ban san ya akai ta lura da goge ƙwallar da nayi ba sai ji nayi tana cewa,”ka kalla har kuka sai da ka sanyata tsabar mugunta irin taka Jawad, yarinya taso kizo nan kinji, ya sunanki?”. Nace da ita, “Mairo”. Kan tace komai Jawad ya bushe da dariya yana cewa, “ji wani suna wai Mairo, kai ƴan ƙauye ma da kayan haushi su ke”. Na ɗago kai na dube shi nace, “kaima ai sunan naka ba daɗi ne da shi ba, mene wani Jawad ko daɗin ji babu suna sai kace za’ai amai”. Wata tsohuwar mata da ta shigo ta doka min tsawa da cewar ya isheni haka ko yanzu asa bayi su sokeni tun da ina yiwa Yarima rashin kunya. Na harareta ta ƙasan ido sannan nayi tattaki zuwa gaban dattijuwar kamar yanda ta umarce ni, kuma har na ƙarasa gabanta kaina na ƙasa ban ɗago ba dan tun shigowarta ma ni ban kalleta ba, sai yanzu da ta sa yatsunta ta ɗago da haɓata tana cewa, “ba kyau yiwa Babba rashin kunya karki ƙara kinji Maryama, idan kuma ba haka ba zansa a cire sunanki daga waɗanda za’a kai makaranta, kina so nayi hakan?”. Na kaɗa mata alaman a’a, take kuma Yawun bakina ya ƙafe da amsar da zan bata, sakamakon kallon fuskarta da nayi wanda ta sani faɗuwar gaba da ban da taɓa jin irinta ba. Kallon fuskarta nake da ɗumbin mamaki da al’ajabin kamannin da nagani a fuskarta, kamannin da suka so ruɗar dani suka kuma nemi zautar da ni. Na rumtse idona sosai ina jin shigar wani abu ajikina dalilin kamo hannuna da tayi ta zaunar kusa da ita, in banda kar nayi saurin rantsuwa zan rantse nace hannun nan ya taɓa riƙeni, Na ƙara kallonta kamin na lumshe ido, idanuna da ke rufe na hasko min hoton halittar dana jima da sani a saman fuskar wannan matar, yanda zuciyata ke ayyana min shi ne kawai mafarki nake, dan haka na buɗe idona a zabure na saukesu akan manyan akwatuna guda uku da aka aje agaban Ammi, tare da jakar bakko guda uku suma shaƙe da kaya, hakan ya kuma tabbatar min dai da ba mafarki nake ba, ta gefen ido nake bin Ammi da kallo ta yanda ba zata gane ba har san da na sauke idona kan zarazaran yatsun hannunta, ni dai tabbas idan ba tunanin da ya cika min kai a kwanakin nan bane ke neman zarar dani ba, to babu tantama akan abun da idanuwana suke gane min.

Ya Kabiru da shi da Suhail su kai sallama a falon, hankalin kowa ya tattara kansu ban da ni, wacce na zuba idanu a wuyan Ammi da son gano abun da nake zargi, sai dai har na gama ƙare mata kallo ban hasko komai ba.

Na maida hankalina ga maganar da ake wacce ta shafi tafiya makarantarmu, Suhail ke cewa da Ammi, “Ammi ba dai Mairo har ta zama ƴar gidanki ba.” Tai murmushin manyace kana tace masa,”ka bari Suhail, yaron nan Jawad ne daga shigowarsa ya sata kuka, ko ce masa akai su Ziyan ne da ya saba cin zalinsu.” Wanda ya shigo bayan shigowar Ya Kabiru yana zama kan kujera yace,”to ai yarinyar ce kamar su Ziyan ɗin, gata nan kamar a hure ta faɗi, kuma da alama abun da ya tsana tayi masa na turo baki dan gashi nan na gani da idona, kinga ko Ammi ai dole ya sata kuka”. Na ɗago ido na kalle shi ina daɗa turo bakina gaba nace,”ni fa bakina ne a haka”. Kowa na gurin ya dara har da Ya Kabiru, shi kuma wanda naji Ammin ta kira da Ashraf ya daɗa cewa, “A’a Mairo wannan ɗan ƙaramin bakin naki kam da gani da gan-gan kike turo shi”. Sai kuma ya gyara zama yana fuskantar Ammi wacce ke complain ɗin wai Suhail ya cire mata hoto. Shi kuma yana cewa ba yin kansa bane Mai Martaba ne yasa shi, ta ɗan kaɗa kai kaɗan kana tace, “ai shikenan, amma sanin Mai Martaba ne hoton nan shi nake gani naji daɗi a ƙasar nan…amma ba komai Suhail kai da ka biye masa naka laifin zanta gani”. Ta ƙarashe maganar da murya mai ban tausai wadda har sai da na juyo na dubeta, dan a yanda muryar tata taso sarƙewa sai tai min kama da sautin dana taɓa ji, sai dai ba zan tantance sautin wane ba. Ashraf yace,”Ammi mun gama komai dangane da tafiyar yaran nan, sai dai fa da ƙyar muka shawo kan Baba ya amince, dan haka Gwaggonsu da kuma Inna Amarya su na miƙo tarin godiyarsu ga wannan masarauta da kuma shi Suhail da ya zama sila, irin tarin adu’oin da su kai sai dai nace kema ki bisu da irinsu kawai”. Ammi ta gyaɗa kai sannan ta mayar masa da magana acikin wani yare na daban wanda ba hausa ba, hakan yasa ban fahimci mai suka ce ba, sai naga ta miƙe ta wuce ciki ta barmu da Jakadiyar da ke mana bayani da kyautar kayan tafiya makaranta da Ammi tayi mana.

<< Sirrin Boye 8Sirrin Boye 10 >>

1 thought on “Sirrin Boye 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×