Skip to content
Part 11 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

A fusace Momma ke kallonta tana sakin huci, “That’s good! kin yi dai dai yanzu kin ɓata komai hankalinki ya kwanta, abubuwan da na daɗe ina planning kin ruguza,ki sani wallahil azim, babu ruwana idan wannan fitinanen ya ɗauki wani mataki akanki ki san ta ya zaki kare kanki, totally bakya iya controlling kanki sometimes mtseew” Tana gama maganar ta fice tare da janyo ƙofar ta rufe ta baki ɗaya a matuƙar fusace. kife kai mufeeda ta yi, zuciyarta na wata irin tafarfasa, take kuma ta ji wata muguwar tsanar Aaliya ta dirar mata.

Tun da suka fito daga ɓangaren galadima jikin Aaliya ya yi sanyi, tafiyar ma cikin Rashin kuzari take yinta, hanakalinta ya yi mugun tashi, gabanta na ta faɗuwa fargaba ta lulluɓeta akan abun da zata taras a sauran ɓangarorin, Ɓangaren matar Sarki Sarauniya Bilkisu suka nufa, tun daga ƙofar Aaliya ta fahimci an narka dukiya kamar banza, an ƙawata ɓangaren sosai kamar aljannar duniya, komai ta kalla sai ya burge ta sabo da gini ne, babu ha’inci mai matuƙar kyau, da gani maƙwara ne maginan, ga shi komai cikin tsari aka yi shi, Shiga suka yi cikin katafaren Parlourn na alfarma, wanda ya ƙayatu fiye da zaton mai zato da tunanin mai tunani, komai ya yi kyau a parlourn kamar ba a Duniyar mutane ba, tabbas anyi ɓarin maƙudan kuɗaɗe na gaske a ɓangaren.

Ga wani ni’imtaccen ƙamshi da ke tashi, hadimai ne ke ta kai kawo gwanin burgewa, sanye suke da uniform masu kyawun gaske ɗauke da tambarin masarautar jordhan.

Kafin wani abu an cika musu gabansu da kayayyakin motsa baki da abinciccika iri-iri, sai ƙamshi ke tashi, ga juice masu sanyi da Botle water.
Babu abun da suka ɗauka hasalima shi fiddo haɗadɗiyar wayarshi ya yi ya fara daddanawa, Jakadiya ce ta zo ta, gaishe su sannan ta tabbatar musu da Sarauniya na sane da zuwansu tana nan tafe.

Daga haka ta ba su guri dan su samu damar sakewa, Takun takalminta ne ya sanar da su zuwanta, ƙwas ƙwas A hankali Aaliya ta ɗago idanuwanta dake cikin glass ɗinta, ta sauke su kan hamshaƙiyar matar, mai ji da haiba cikin ƙasaita ta dunfaro su fuskarta cike fam da fara’a, cikin izza ta ƙaraso ta zauna bisa kujerar da ke facing ɗin su.

A nutse Aaliya ta gaishe ta, ta amsa fuska a sake. Dagowa ya yi slowly ya ce”Barka!” daga haka ya ci gaba da latsar wayar ta sa, faɗaɗa fara’ar ta ta yi s ce, “Barka dai yarimana, ai ni nayi fushi da kai kwata kwata ka daina leƙo Amminka” murmushin gefen baki ya saki ya ce “Ayya sorry Ammi amarya ce ta ɓoye ni!” Ya ƙarashe maganar yana sakin murmushi, Ɗan zaro idanu ta yi tana ɗan hararshi, “Haba no wonder! amma gaskiya na yi fushi baka kyauta min ba kayi aure ba tare da sanina ba kuma baka kawo min amaryar na gani ba”.

Murmushi ya sake yi sannan ya ce “Aaliyaa!” daga haka ya miƙe yana faɗin to ‘Sai an jima mun wuce, zan rakata sauran parts ɗin’ yana gama faɗar haka ya ja hannunta suka nufi hanyar fita, ita kuma sai bin shi take yi abun ka ga wacce ba hausa ba ko kuma ta rayu cikin mutane, bare ta yi tunanin ba dai-dai yanda ta kwanta a jikinsa. Daga nan suka shiga ɓangaren Waziri sun saɓu tarba mai kyau sannan suka nufi ɓangare na ƙarshe, da zash je, dan ya ce ya gaji.

Sashen Ummi suka nufa wacce ta kasance uwa ga Sarki Muhammad Ali, tun daga yanda ta ga ɓangaren ta tabbatar da ko waye mamallakin Sashen ana matuƙar ji da shi, wata jakadiya ce ta musu iso zuwa tsararren Parlourn Ummi, kishingiɗe take hadimai sai saman tausa suke mata, ga kuma masu labari, gabanta cike yake da fruits masu yawa, tun da ya shigo ta ɗago ido ta kalle shi, ganin Haydar ɗin manne da wata budurwa, wacce ta fi mata kama da balarabiya.

Zare siririn farin glass ɗin dake maƙale a idanunta ta yi, sannan ta kuma dubansu a karo na biyu fuskarta ɗauke da mamaki, tun kafin su idasa zama ta fara magana, “Aliyuu! ina ka samo wannan budurwar haka, a iya sanina gaba ɗaya danginmu babu ko mai kama da ita, haka dangin A’isha..” tun kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin ‘Matata ce!’

Wani irin kallo ta bishi da shi ta yi wuf ta miƙe, “Ka yi dai-dai Ali, to bari ka ji ko ubanka mahammadu bai isa ya zo min da wannan zancen banzan ba, gidan uban wa kayi aure ban sani ba. ashe rashin mutuncin naka ya kai haka, to bari ka ji wallahi ba zai yi wu ba, dole ma ne ta koma gaban ubanninta, mufeeda ita ce matarka ba wannan mai zubin aljannun ba” dafe kai ya yi cikin ƙwarewa da rainin wayau ya ce “Haba dai ni fa ba Muhammad ɗin bane, kuma wannan matata ce ta sunna halak malak zan iya sauke ko wanne nauyi na gareta, komai ma nata mallakina ne!”

‘Ƙarya kake Ali kai ɗin banza wanda uwarka ta haifa gabana, to miye zaka min taƙama da shi nauyi ya wuce wanda ubanka ya sauke, bari ka ji tsarin masarautar nan ko uwarka sai da muka tabatar da mutuncinta, bare wannan mai siffar Aljannun dan haka wajibi ne kowa ya san ta ɓarar da shi ko kuwa, sannan bama maraba da wannan yarinyar, dan kowa ya san waɗannan ƴan’matan basu san halacci ba da zarar sun samu ciki suke ɓarar da ahi su tsallake su bar ƙasar, kuma makirai ne su baki ɗaya, shi ya sa sam na fi so ka Auri ƴar’uwarka Mufeeda.’
“Woww!! kina son sanin sirrinmu ke nan, to ni fa ban ma fara wata mu’amula da ita ba dan ina tausayinta, gata zankaɗeɗiyar budurwa ko ina laushi sabon jini ɗanya shakaf, shi ya sa”.

“Aliyu ni ka ke chaɓa ma magana haka, kayi dai dai tashi ka tafi bana buƙatar cewar ka da ubanka zan yi” taɓe baki ya yi ya ja hannun Aaliya suka fice yana sakar mata shu’umin murmushi.

Ƙaramin tsaki ya ja, dan ya gaji matuƙa fitinanniyar tsohuwar ta saka shi magana da yawa, dan dama ya san ita ce mutum ta farko da zata ba shi matsala amma ya san maganinta.

Ɓangarensu suka nufa, suna shiga Parlour ya janye jikinsa daga nata suka shiga bedroom a tare, faɗawa ta yi kan gado tana maida numfashi, sannan ta shiga duniyar tunani akan maganganun Umminsu, amma ta gaza fahimtar komai.

Rage kayan jikinsa ya yi ya faɗa toilet, dan yin wanka ya yi a ƙalla mintuna talatin yana wanka sannan ya fito ɗaure da towel sai kuma ƙarami wanda yake goge ruwan da shi.

Gaban dressing mirrow ya tsaya ya fara shafa mayuka da turaruka kala-kala sannan ya zura jeans 3quater da T-shirt fara, sannan ya sake feshe jikinshi da turaruka masu ƙamshi.

A hankali ya hauro gadon dan ya gaji sosai, kwata-kwata ya manta da Aaliya dan barci ke idonshi sosai, bai fi mintuna biyar da kwanciya ba barci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.

Ammah ce tafe tare da mai martaba zuwa ɓangaren Ummi, tun da suka shiga Parlournta yana yin tarabar da ta nuna musu, duk da tsawon lokacin da Ammah ta ɗauka kwanche cikin halin ciwo, bata nuna tsantsar farin cikinta ba, hakan ya sa Ammah fahimtar lallai Haydar ya kwafsa dan dama Abbi ya bata labarin komai, jikinta duk ya yi sanyi.

Juyowa Ummi ta yi sosai ta fuskanci mai martaba, sannan ta sake tsuke fuskarta, cikin faɗa ta soma mishi magana.

“Mahammadu!! ina son jin Ainahin zance dangane da wannan yarinyar da suke maƙale da juna da fitsararren ɗanku shin auren sunnah ne suka yi, kuma da saninku ko kuwa, ina son jin gamsasshen bayani” Nutsuwa sosai mai martaba ya sake yi ya dube ta da kyau ya ce “Idan dai na fahimta Aaliya kike magana, to gaskiya dai ita ɗin tana gab da zama matarshi amma ba ta zama ba, ta zo ne daga wata masarauta ita ma, yaƙi aka yi shine ya taimake ta ya dawo da ita, daga ƙasar da ya je nemawa Mahaifiyarsa magani, kuma ya nuna yana son aurenta, cikin satin nan ya ke son ta zama matarsa.”

Sakin fuskarta ta yi kaɗan jin itama jinin sarauta ce, “Yanzu na ji, batu kuma na amince ya aure ta, amma gaskiya kar ku manta da zancen ƴar’uwarsa” Murmushi suka yi “Ummi mun yanke hukuncin ɗaurin Aure ranar Juma’a ƙarfe 2:30 jibi ke nan in sha Allah gobe za’a buga invitation card sannan bikin hawan doki kawai za’ayi.” “Haba shi ma mai gidana matsalata da shi fitsararre ne ba shi da kunya ko kaɗan, gaskiya wannan ba halin A’isha ba ne, amma shi ke nan”
Sun ɗan jima suna tattunawa daga ƙarshe Ummi ta bawa Ammah wasu magungunan gargajiya na tsari suka bar sashenta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 13Sirrina 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×