A Razane Sarauniya Rahash ta saki wuƙar da ke hannunta, ta nufe shi jikinta na wata irin tsuma, A Matuƙar kiɗime, ta furta "Sarki gobrar!!" wani baƙin abu ne ya fara malala daga bakinsa a kiɗime ta saka dukkanin ƙarfin da ya rage mata ta fizo wani dogon abu daga gashin kanta ta chaka masa, suka ɓace baki ɗaya.
Baiyana suka yi tsakiyar ɗakinta, ita da shi Wata ƙakƙarfar ajiyar zuciya ta sauke, Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Arman, Karan, sarki Gobrar, Sarauniya Rahash, Sarki gobrar kuma, gaba ɗayansu a matuƙar rikice. . .