Skip to content
Part 12 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

A Razane Sarauniya Rahash ta saki wuƙar da ke hannunta, ta nufe shi jikinta na wata irin tsuma, A Matuƙar kiɗime, ta furta “Sarki gobrar!!” wani baƙin abu ne ya fara malala daga bakinsa a kiɗime ta saka dukkanin ƙarfin da ya rage mata ta fizo wani dogon abu daga gashin kanta ta chaka masa, suka ɓace baki ɗaya.

Baiyana suka yi tsakiyar ɗakinta, ita da shi Wata ƙakƙarfar ajiyar zuciya ta sauke, Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Arman, Karan, sarki Gobrar, Sarauniya Rahash, Sarki gobrar kuma, gaba ɗayansu a matuƙar rikice suke kallon sarauniya Rahash, fuskokinsu kuma sun nuna mamaki, Mai martaba Gobrar da yake gefensu Karan ne ya yi ƙarfin halin yin gyaran murya, sannan ya dube ta sosai ya fara magana yana nuna sarki gobrar ɗin da ya ke kwanche cikin fitar hayyaci da ƙyar yake jan numfashi jikinshi ya yi fari fat.

“Rahash!! waye wannan”? Jin rikitacciyar tambayar da ya jefo mata ya sanya ta saurin duban shi jikinta na wata irin tsuma, idanuwanta har wani sheƙi suke yi, ba su gama Alhinin shiga ruɗanin ba, ƙarinwani ruɗani suka tsinkayi muryar Karan yana faɗin; “Anum!! Waye wannan ɗin?” ya ƙarasa maganar yana ƙarasowa gurinta sannan ya nuna mata sarki gobrar ɗin da ke kwance.

Take suka kai duban su bakiɗaya kan wani karan ɗin da ƙarfi, suka ji muryar Armaan na tunkaro gurin yana faɗin; “Karaan da Sarki bibiyu!!” a razane suka dubi wani arman ɗin kuma ya zama arman biyu, karan biyu, Mai martaba biyu.

A Matuƙar ruɗe sarauniya Rahash ta fara ƙoƙarin magana, wata Sarauniya Rahash ɗin ce ta fara magana “Komai biyu! me ya faru haka? wannan wasan ya isa haka!!” Tsabar ruɗani da rikici cikinsu babu wanda ya yi ƙoƙarin amfani da ƙarfin sihirin sa, ja da baya Sarauniya Rahash ta ainahi ta fara yi ganin yan da wata irinta ta baiyana, kafin ta yi wani yinƙuri duhu ya mamaye su.

Wata mahaukaciyar dariya suka fara ji, ga wata guguwa tare da walƙiya, suna ta giftawa da wani irin gudu shu-shuuu…Tsagaitawa da dariyar Aka yi, sannan wani haske ya mamaye ɗakin ko wanensu cikin hanzari ya fara bin faffaɗan ɗakin da kallo.

A hankali Karan ya soma warware idanunsa akan FIRAlSH wanda yake zaune a ƙasaice, bisa wata haɗadɗiyar kujerar zinari, Yana sakar musu wani ƙayataccen murmushi, A tare suka waro idanuwa Suna furta..’Firaish!!’

Tsananin farin ciki ya saka su daskarewa, gaba ɗayansu babu wanda fuskarsa bata ɗauke da farin ciki a hankali Sarauniya Rahash ta tako har gabanshi, fuskarta ɗauke matsanancin farin ciki, Shi ma farin ciki ne kwance a kan fuskarsa, Basu wani ja lokaci ba suka ɓace ita da shi.

Wani ƙayataccen lambu suka baiyana mai tsananin kyau, ga wani ruwa na gudana sai kukan tsuntsaye ke tashi haɗe da ƙamshin furanni, mai daɗi iskar girin na kaɗawa a hankali, kai tsaye zaka iya samun natsuwa a gurin.

Saman iska suka zauna ita da shi, cikin mugun zumuɗi take kallonsa bakinta kumshe a tarin tambayoyi, a hankali ya soma dariya sosai kafin ya tsagaita, “Rahash!! har yaushe zaki samu ƙarfin sihirin da babu mai shi? yaushe ne zaki cika burin iyayenmu, a halin yanzu ba zan iya kwaɗaiyin Masarautun da ke akwai a YALAZ Burina ya tafi ne chan NASAAR kina da sani akan ƘASAR NASAAR dake ƙarƙashin duniyar WUTA…”

Zuba mishi idanuwa ta yi tana ƙare mishi kallo, tabbas shi ɗin dai ne, amma ya akai har ya samu irin wannan ƙarfin Tsafin, wane irin tambari ne a saman idanunsa.
Ina ne BIRNIN NASAAR shin dama akwai ƙasar da ta zarce YALAAZ wane irin Iko ne a babu shi a YALAAZ anya kuwa ba zata sake yin dogon bincike, ba Abun da ya yi tsawon shekaru goma rabonshi da duniyarsu ta mayu…

Ƙayataccen murmushi ya saki, tare da lumshe Manayan idanunsa masu ɗauke da ƙwayar ciki Arsh colour, hakan ne ya sake bata damar kallon zanen baƙin tambarin da ke a sama fatar idonsa na hannun haggu.

Buɗe baki ta yi zatayi magana ya tari numashinta, ‘Na riga da na san tambaoyin dake a zuciyarki, Ya akai na samu ƙarfin tsafi haka, wane irin tambari ne a idona, Wanne birni ne BIRNIN NASAAR, waɗanne ikuna ne da babu su YALAAZ! shin shirina ne duk abubuwan da suka faru da Karaan me marataba, Armaan. ko ba su ne tambayoyin da kike son fara min ba?.”

Cikin azama ta sauke numfashi, idanuwanta ƙem akansa, jin ya buɗe baki zai yi magana ya sata saurin faɗin, ‘Taya akai duk ka san wannan ɗin, ina son jin ƙarin bayani.’ ta ƙarasa maganar cike da ɗan zumuɗi.

‘Tsawon shekaru Goma da na yi bayan bari na YALAAZ! Na haɗu da wata Aljana mai suna Aljana Lailaah Ita ɗin ta kasance ta daban a cikin aljannu lokacin da na haɗu da ita, na ceci Rayuwarta ne daga tarkon wasu sheɗanun Aljannu da suke neman ganin bayanta dan ita ɗin ta kasance gimbiya lailaah a chan birnin NASAAR ita kaɗai ce ɗiyar mahaifanta.

Mahaifinta ya kasance daga cikin Tsatson Jajayen Aljannu, yayin da mahaifiyarta ta, kasance daga cikin tsatson fararen aljannu, Ita sarauniya Lailaah kyakkyawa ce sosai me ɗaukar hankali, tana da wani matsanancin ƙarfin sihiri da ya shallake na dukkanin mayun dake yalaaz. Ta kasance ɗauke da wata kalar ƙwayar ido mai ɗaukar hankali, Kalar bula sannan tana da ƙira wacce ke matuƙar jefa kowa ya kalleta a mugun tarko, a kallon idanuwanta kaɗai da zaka yi zata iya mallake ka, ka dawo ƙarƙashin ikonta, sannan dukkanin ƙarfin ikon da kake da shi zata malleke shi, Tana da wani irin gaahin kai mai matuƙar kyawun gaske fiye da dikkan tunanin mai tunani, duk irin yanda nake ji da Kaifin tunani da ba zan iya fasalta zubinta ba. kin san me ya Rikita zuciyata, ya haifar min da daina gani na wasu sa’o’i, zaki iya tuna wani a Ƙasar yalaaz mai irin wannan kyawun da zubin tare da ƙarfin sihirin?”.

Murmushi ta yi da ya baiyyana wani irin kyawunta, sannan ta ce “Aaliyaah tun da nake a rayuwata ban taɓa tozali da Mace kamarta, wata irin baiwa ce a ita, na rasa gane kan abu kwata-kwata!..”

Wata irin juyawa ya yi ma idanuwansa, wanda ya ɗan firgitar da Rahash, kafin ya fara magana…”A lokacin da na yi tozali da LAILAAH gaba ɗaya na sakan-kance Aaliyaa ce, amma sai daga baya ta tabbatar min da ita Lailaah Sunanta da asalinta, maganar da nake miki yanzu haka ina rayuwa ne Masarautarsu ta ƙasar NASAAR su ɗin suna da ƙarfin ikon da ya shallake dukkan tunanina, ni kaina a iya zaman da na yi da masoyiyata Lailaah na gano hakan, sannan ta mallaka min wani ƙaramin sashe daga cikin ƙarfin ikonta, Kin san tunaninmu ni da ita miye?” ya tambaya yana wani cije laɓɓansa.

Cikin hanzari ta girgiza kanta alamun bata sani ba, ci gaba a magana ya yi…”Muna so mu haɗe da NASAAR da YALAAZ wuri ɗaya, mu mulke su baki ɗaya, su dawo ƙarƙashin ikonmu” wani irin kallo ta fara bin shi da shi, cike da son nazarin abun da yake faɗa.

‘Wannan abun da kika ga na aikata kaɗan ke nan daga cikin ƙarfin ikon da nake da..Ko wa kike son na mallake miki ya dawo ƙarƙashin ikonki zan iya, sannan zan iya samar da waa bayan ke ki zama guda biyu kamar dai yanda na yi.’ ya ƙarasa yana sakin wata mahaukaciyar dariya.

Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta cike da tsananin shauƙi, gaba ɗaya farinciki ya mamaye fuskarta, sake maida kallonta ta yi sosai gare shi, sannan ta soma magana, “Zaka iya kai ni TEKUN JAZAAL!!”?

Dariya ya soma ba ƙaƙƙautawa fuskarshi cike da shauƙi ya ce, idan kina son na taso miki da AZLAA RIYAAD NAZAAN duka zan taso su, su dawo ƙarƙashin ikonki, sannan na mallaka miki ƙarfin Tsafinsu.

Da wani irin mamaki ta kafe sa da idanuwa, bakinta har kerma yake zuciyarta na wani irin bugu, ta kasa tantance wane hali take ciki, ita dai ta san tana cikin farin ciki amma kamar tsoro ya fara ɗarsuwa a zuciyarta, cikin sauri ta girgiza kanta tana ƙarawa kanta ƙwarin guiwa akan abun da zata cimmawa, tabbas ta saka a ranta sai ta Aikata dukkanin abubuwan da ta yi niyya, ko da zata rasa komai.

Buɗe baki ta yi ta ce, ‘Firaish ina so! ka taimake ni, ina son hakan ta faru. ka yi wani abu akai mana.,’ dariya ya yi ya ce “Hakan ba zata taɓa faruwa ba ai da jinin Aaliyah Zahir! dan itace kaɗai zata iya taso su, kin san watanni nawa na ɗauka ina bincike akan hakan?” Cikin sauri ta furta ”Aaliyaa! kuma, taya hakan zata kasance me yasa saida Aaliya, baki ɗaya bata a masarautar nan, a yanda nake jin labari daga gurin baiwata da take min leƙen Asiri a manaaj” jin ta kai ƙarshen maganar ya sanya shi lumshe idanuwanshi ya sake buɗe su akanta.

“A lokacin da na fara bincike na sha wahala matuƙa, na ga haɗarurruka da dama, Sai dai kwata Kwata bana ganin Aaliya a duk binciken da nake yi, sai dai duhu, na yi amfani da ko wanne kalar ƙarfin iko da kika san yana baiyyana Ko wane halitta amma ban samu nasara ba, Sarauniya Lailaah matata ta tabbatar min da duk sanda na kawo mata Aaliyaa, zata mallaka min Rabin ƙarfin sihirinta, da Dukiyarsu sannan zata bani goyon baya ta kuma taimake ni mu gudanar da aikin, haɗe YALAAZ DA NASAAR sai dai fa ba zata iya komai ba face da jinin Aaliya sannan kuma ta tabbatar min da ko wa yake son zuwa JAZAAL, zai je ne yana a ƙarƙashin ikonta.

Amma kuma wani abun mamaki da Rikitarwa shi ne Wasu su biyu sun yi tattaki har izuwa chan ɗin, kuma sun ɗauke makullan da aka kulle su AZLAA DA NAZAAN amma babu abin da ya same su, kuma ta yi bincike iyakar iyawarta, bata gano komai ba, dan haka shugaban bokayensu ya bata umurnin gabatar da Baƙin tsafi, a wani kogo kin san me ya faru bayan ta gabatar da baƙin tsafi?”

Da sauri ta girgiza kanta, dariya ya yi sanna ya ci gaba da magana…”Ba wasu ba ne Face Aaliyaa da wani namiji, amma kwata-kwata babu wani bayani da ta iya ganowa bayan wannan, a lokacin na yi ƙoƙarin tuno wani abu amma na kasa, kin san ni yanzu bana daga cikin Tsaton MAYU ni a halin yanzu ba maye bane.”

Dafe kanta ta yi da hannayenta guda biyu zuciyarta na tafarfasa, gabana na faɗuwa Aaliyaa ita ce mai nasara a ko yaushe me yasa hakan ke faruwa, maganganun da take yi ke nan a zuciyarta tana girgiza kai, ta kasa furta komai.

SANAAM
Zaune take gaban tsoho Arar fuskarta ta jiƙe sharkaf da zufa, a nutse ya ci gaba da magana, “Sanam na samu labarin dawowar Firaish na masarautar Su Gobrar, dan haka ya kamata ki yi taka tsan-tsan sosai, da farko an ƙudurci gabatar da yaƙi kwanaki Ukku baya da suka wuce, amma yanzu tsawon kwanaki biyar ke nan, ba ni da masaniya akan shirin Mayun amma, abin da na sani shi ne, Aaliya bata ƙona makullan nan ba, kuma suna tare da ita, sannan na yi iyakar yi na dan gano inda take amma na kasa. sai dai tabbas ta tsira tana cikin salama, irin wannan bayanin na yiwa mahaifinki da mahaifiyar ita Aaliyar, Amma yanzu haka ita ce abun hari dan ƙarfin ikon da take da ya shallake dukkan tunanin mai tunani, bugu da ƙari ita ɗin ƴar baiwa ce. ita ɗin ta daban ce ko a cikin MAYU game da ciwon mahaifiyarta, zan yi iyakar iyawata, ganin rayuwarta bata salwanta ba, sannan a kpda yaushe za a iya farmakata ni kaina…”

Cikin sanyin jiki shiga jinjina kanta sannan ta ce ‘Amma ta ya Zamu iya dakatar a yaƙe-yaƙen? babu wata hanya dole sai anyi yaƙin”? Numfashi ya sauke a hankali sannan ya ce, “Ko da za a iya dakatar da yaƙe-yaƙen sai dai ayi kala biyu na ukkun ne kaɗai mai hatsarin, kuma wanda zai kasance za a iya rayuwa ko mutuwa, za mu dakatar sannan ba kowa zai iya hakan ba fa ce Aaliya!”.

“Ita kaɗai ce zata iya tattaki izuwa TSIBIRIN BAMANUL ANSAR Idan har ta yi Tattaki izuwa gurin Aljani bamanul ansar zai iya dakatar da komai, sannan shi kaɗai zai iya faɗin hanyar da za a dakatar da yaƙin. Banda Aaliyaa babu mayen da ya isa ya je gare shi, itama saboda wata irin baiwa da take da ita wadda babu mai irinta, cikin mayinmu da wasu aljannun…”

Numfashi Sanaam ta ja sannan ta ce, “Kaka kana tunanin babu wani hatsari, dan gane da zuwanta? sannan za a iya dacewa idan ta je”? A hankali ya fesar da numfashin shi ma, sai ya ce “Tabbas za a dace! amma fa haɗarin zuwa duniyarsa ya wuce dukkanin haɗarurrukan da kika taɓa ji, ko karantawa a labaran jaruman duniya, matsalar ma idan ta je ya saurare ta, ya amince da buƙatar ta. sannan zata iya maƙalewa ta dawwama a chan ɗin har ƙarshen Rayuwarta.”

Miyau Sanaam ɗin ta haɗiye ƙut, jikinta duk ya yi sanyi, tausayin sarki da sarauniya Sarah duk ya kama ta, dan ta san irin ƙaunar da suke yi ma Aaliya, A ko da yaushe ita Aaliya burinta ta sanya su cikin farin ciki da nishaɗi, tana son Ƙasar a samu zaman lafiya, babu tashin hankali da zubda jini, tana burin ganin kowa cikin farin ciki, sannan ba ta da yawan damuwa yanzu ko wane hali take ciki? hawaye ne suka taru a idanun Sanaam baki ɗaya ta ji cewa zata iya aikata komai a domin Aaliya da mahaifanta, sannan zata iya bada tata rayuwar dan samun dawowar farin cikinsu.


Share hawayen idanuwanta ta yi cike da tausayi ta ce, “Na yi Alƙawari daga yanzu zan fara neman Aaliya, da yardar Abun bauta Aaliyaa tana cikin salamammiyar rayuwa, zan bata kariya bakin iyawata, zan goge dukkanin laifukan da na daɗe ina aikata mata, zan nuna mata tsantsar ƙaunata gare ta, da ban nuna mata ba. zan iya sadaukar da tawa rayuwar akan Aaliya Kaka ina jin fargaba akan laifukan da mahaifiyata ke aikatawa, bana son ta gano ka ta farmake, ka. zan ji ɗaci a zuciyata! kuma ba zan iya jurewa ba…” Kuka ne ya ci ƙarfinta, sosai take yin kukan zuciyarta ta karye idanuwanta sun fara duhu, hasken ya fara disashewa, Lallashinta ya soma cikin tausayawa.
Cikin Raunin murya ta ce, “Kaka wani lokaci da na yi yunƙurin farmakar Aaliya, ban yi nasara ba farmakin ya dawo kaina, kibiya ta soki zuciyata! kasan wa ya taimake ni?…” goge fuska ta yi cikin sanyin jiki, sannan ta ci gaba da magana, ‘Aaliyah ita ce wacce ta ceci rayuwata! don da a ce a lokacin bata sadaukar da wani sashe na ƙarfin ikonta ba, da izuwa yanzu an shafe tarihina, na daɗe da barin wannan duniyar. amma da ya ke ita ɗin mai kyakkyawar zuciya ce bata Aikata hakan a gare ni ba, Na sha farmakar ta, amma daga baya ta taimake ni. duk laifukan da na kasance ina aikata wa Sarauniya Saraah bata taɓa ɗaga idanu ta kalle ni ba, ko cin mutunci da ramuwa akan cutawar da na ke mata..’ shuru ta yi sakamakon wani dunƙulallen abu da ya tokare mata wuya.
Da ƙyar ya lallashe ta, ya samu ta yi shuru daga ƙarshe ya miƙo mata maganin sarauniya Saraah, ya kuma mallaka mata wani zobe ya ce, ‘Wannan zoben zai yi matuƙar taimaka miki, ki kula da shi sosai.’ ɗaga mi shi kai ta yi sannan ta kama hanya ta fice daga cikin bukkar, bayanta saka zoben.
Hannayenta ɗauke da wani ƙoƙo na maganin da ya bata, ta isa inda dokinta yake ta hau. suka fara gudu….

“`K_SHITU“`

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 10Sirrina 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×