Skip to content
Part 19 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

Tun daga kan ƙafafuwanta, har zuwa cinyoyinta sun zagwanye, haka har zuwa cikinta. A karo na biyu ta buɗe idanuwanta jikinta babu kuzari, ta haɗe hannaye gurid’aya amma ta kasa ko motsa laɓɓanta.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, ta share su tana sakin wani murmushi mai ciwo.

Lokaci ɗaya kamar ƙyaftawar ido, tamkar almara ta fara magana…..”A da! kafin zuwan wannan lokacin na kasance ina sa rai; Kai ne fatana na ƙarshe ga bakiɗaya wannan duniyar! amma abu mafi muni yau na samu damar ganawa da kai, sai dai ban samu damar cika burin mahaifana da ƴan’uwana ba, zan bar wannan duniyar…”. wani kalar tari ne ya sarƙe ta ta kasa ƙarasa maganarta.

Wani baƙin jini dunƙulalle ne ya fara zubowa daga hancinta, yana ɗigowa, jikinta.

Kallonta ya tsaya yana yi, ta ba shi tausayi sosai, amma ba zai iya taimakonta ba,Gabanshi ne ya yanke ya yi mummunan faɗuwa lokacin da ya hango yarinyarshi na kakari da wani irin aman koren abu.

Bayyana ya yi gabanta ya shiga kiran sunanta cikin firgici, “Azeeya!!..Azeeyaa!!” jijjigata ya shiga yi, jikinshi na kerma.

Take gurin ya kama da wuta! wata wuta ce ta dinga fitowa daga idanuwanshi tana shiga jikinta amma ko gizau bata yi ba, a firgice ya ɗaga d’an yatsanshi ɗaya, ruwa ya fara malala ta ko ina, kafin ya sake wani yunƙuri jikinta ya fara zagwanyewa.

MASARAUTAR MANAAJ
Hankali tashe Tsoho Arar ya ke ƙoƙarin dakatar da faruwar abun da suke gudu na maƙalewar Aliya.
Ƙarasowa gabanshi Sanaam ta yi, Fuskarta ta yi jawur, idanuwanta sun kumbura, launin su ya sake rikicewa, ta dube sa hawaye na ta zubowa daga idanuwanta, cikin sassanyar murya ta ce, “Shi ke nan! yanzu rana ta faɗi mun rasa Aaleeyer….Kaka ka cece rayuwarta saboda Abin bauta, ka taimaka Kaka kar mu rasa ta, na roƙe ka.”. ta ƙarasa maganar kuka na kufce mata.

Sharce zufa ya yi, Jiki ba kuzari ya ce, “Sanaam na sani ba zan iya aikata hakan ba, ƙarfin Addu’a ma bana da tabbacin zai iya tasiri, Amma na kurɓi ruwan tsantsar mamaki, da ya kasance cewa Sarkin Bamanul Ansar bai taimake ta ba”. Kuka sosai Sanaam ta fashe da shi, Cikin Baƙin cikin abun da ke faruwa ta ce, “Na gaji! na gaji! Ina son Nima na bar wannan duniyar har abada” Saurin girgiza mata kai ya yi, ya ce “Ta ya zaki ce haka? ki natsu sosai muyi addu’a yanzu.” Sake Fashewa da matsanancin kuka ta yi, jikinta sai karkarwa ya ke.

BAMANUL ANSAR
Cikin ƙaraji ya kira sunanta ”Azeeyaah!” har saida ko ina ya amsa.
Cikin mugun zafin nama ya ƙarasa gaban Aliya ya fara magana, “Daga zuwanki, kina so na Rasa ƴata bayan Amfani da suffarta da kika yi, to zan shayar da ke gubar azaba kafin ki bar wannan duniyar.”

Wani tambari dake bayan wuyan Aziyar ne ya yi haske, sosai, Ita ma Aaliya tambarin da ke bayan wuyan nata ya soma haske, yayin da hasken ya soma haɗewa, da na Aliya da na Aziyaa.

Lokacin da ya ga haka sai wani matsanancin Farin ciki ya lulluɓe shi, ya ɗauko wata ƙwarya, mai d’auke da ruwan Wuta ya watsa musu su biyun.
Bai ɗauki mintuna uku lafiyayyu ba, da watsa musu jikinsu ya soma dawowa dai-dai ko waccensu fatarta ta komo dai-dai.

Ajiyar zuciya ya sauke, ya hura wata iska. Zaune Aleeyah ta ganta gabanshi ga yarinyar shi Azeeya a gefe da kuma matarshi duk Aleeyah suka Kallo, magana Sarauniya Mohina ta fara cikin farin ciki, “Mun san zaki yi mamakin Ganin ta yanda aka yi muka ceci rayuwarki ko?” Saurin girgiza mata kai Aliyaah ta yi, alamar A’a, ci gaba da magana ta yi fara’a shimfiɗe a kan fuskarta.

”Idan Zaki iya tunawa; A lokacin baya, kin taɓa cin karo da wata Yarinya ƙarama cikin mawuyacin hali, da mahaifiyarta, Ke kuma kika taimke su, yayinda kika musu magani, har kika haɗa jininki da na yarinyar ta rayu, daga lokacin kuma suka bar ki?”.

Ɗaga mata kai ta yi ta ce, “Tabbas na tuna a lokacin ma da ban taimake ta da jinina ba, da ta rasa rayuwarta”.
”Aleeyah Ni ce da ‘yata Azeeya kika taimaka!, Abun da ya sanya baki mutu ba, Tambarin da kika yi wa yarinyar ne. Kuma tambarin yana tasiri ta yanda idan wani mummunan abu zai sameki na gagarumin Sihiri idan kina kusa da ita to zai same ta, haka itama idan zai sameta in kina kusa zai same ki. Bacin da Sarki ya gane hakan ta ƙarfin ikonsa da kin dad’e da barin duniya, Amma muna baki haƙuri, an karɓi buƙatarki Ƙasarku ta YALAAZ zata gyaru za a yi yaƙi biyu, ba za a yi na ƙarshen ba, zaku samu salamammiyar rayuwa, amma ke zai kasance bakya nan za ayi yaƙin, zamu mayar da ke wata ƙasar da zaki samu salamar rayuwa, zuwa lokacin da komai zai lafa, yanzu haka mukullan suna tare da mu. zamu sanar da Ararda mahaifinki komai sune zasu jagoranci yaƙin”.

Wani irin matsanancin Farinciki ya ratsa ta, ta sauke ajiyar zuciya fuskarta ɗauke da murmushi ta ce, ”Na gode sarauniya! bana da bakin godiya.”

Suka rungume juna ta sumbaci Aziyaa daga haka, Sarki ya watsa mata wata Hoda, ya ce da ita, “Kar kiyi kuskuren komawa Yalaaz sai sanda komai ya zo ƙarshe.” daga haka ya hura hodar ta ɓace.

Ƙarfe 8:30 na safiyar Asabar, Jirgin Yarima Aliyu Haydar ya sauka Ƙasar India. Tun bayan da ya kammala abun da ya dace, ya hau Privet Jet ɗinshi Aka tuƙo shi zuwa India, yake jin sassaucin ɓacin ransa duk da ya rasa na miye.

A hankali yake taka matattakalar jirgin yana saukowa, har ya ƙarasa saukowa, sannan jirgin ya ɗaga sama, shi kuma ya nufi wata baƙar mota, mai azabar kyau ya shiga dan Already ya yi, waya ne a kawo ta yana da key a hannunsa.
Kasancewar Akwai d’an nisa tsakanin gidansa da in da jirgi ya ajiye sa ya sanya ya ke tuƙin da ɗan gudu sosai, kamar daga sama idanuwanshi suka hasko masa Mutum tsakiyar titi gaban shi, wani wawan burki ya ja, mai haɗe da ƙura Ƙi…..!!

Numfashi ya sauke sannan ya fito a zafafe, dan ganin wane ɗan kasadar ne zai yi wannan gangancin, Dai-dai lokacin da ya ƙaraso dai-dai lokacin ta faɗo kan motar idanuwanta a rufe hannunta dafe da kanta.

Sake ware manyan idanuwansa ya yi a kanta, Kamar mafarki Ubangiji ya sake haɗa sa da wannan Yarinyar, daga yanayin gashin kanta da kuma fuskarta kaɗai da ya kalla dole ya shaidata, amma daga guiwar ƙafafuwanta duk sun yi baƙiƙirin kamar baƙin tukunya, ganin ana danno musu horn Ne ya sanya shi yanke shawarar ɗaukarta zuwa cikin motar.

Chak ya ɗauke ta ya saka ta cikin motar, ya ja ta da gudu ya ci gaba da tafiya.

Har ya ƙaraso haɗaɗɗen gidansa yana tunane tunane, me ya kawota India, me yasa take irin wannan shigar. tambayoyi barkatai ya dinga yi wa kansa dai, har ya yi magana aka buɗe masa gate ya shigo da motarsa.
Tun da ya shiga Ma’aikatan sai rawar jiki suke wajan gaishe sa, wasu da yaren india wasu da turanci.
Shigewa da ita Parlourn gidan ya yi, ko ina tsaf-tsaf.

Wasu bayi ne, guda biyu na masarautar Jordhan da suke aiki gidan suka fito suma duk mata suka gaishe shi, daga haka ya haye sama, su kuma suka shiga shirya masa Girki.

Kwantar da ita bisa gadon ya yi, shima ya kwanta yana sauke Numfashin gajiya.

Ya ja kusan 5mnts a haka, kafin ya miƙe zaune ya fara rage kayan jikinsa, ya faɗa toilet don yin wanka.

Sai da ya yi 25mnts sannan ya fito sharp-sharp, ya shafa mai, ya feshe jikinsa da turaruka, sannan ya nufi wani madai-daicin fridge ɗin da ke ɗakin, ya ɗauko freshmilk ya sha, sannan ya ɗauko Ruwa mara sanyi sosai ya nufo gadon.

Buɗe murfin Rubbern ruwan ya yi, sannan ya ɗan ranƙwafo saitin fuskarta…ya zuba ruwan a hannunsa sannan ya shafa mata a fuska, ajiyar zuciya ta ja mai ƙarfi tare da buɗe idanuwanta, suka haɗa idanu da shi, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke wani matsanancin farinciki ya kama sa, fargabarsa ta gushe, Wata nutsuwa ma ya ji ta zo masa.

Wani abu ne ya dinga tsarga ma kowannen su, tun da suka haɗa ƙwayar idanu.

Lumshe na ta idanun ta yi, tare da ɗan turo bakinta gaba kaɗan.

Cije lips ya yi, sannan ya zaune gefen ƙafafunta ya kafe ta da idanu cike da tuhuma, ya shiga jera maa tambayoyi, Cike da masifa.

“Ke meyasa kika bar Masarauta? wai ke baki san ma matar Aure bace kike yawo duk jikinki a buɗe, ji yanda kika fiddo jikinki.”

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙirjinta da gashin kanta da yatsa, shi kuma yana kawar da kansa gefe tare da cizon laɓɓansa.

Yadda ya yi maganar a hankali ya sanya ta jin wani iri, ga kuma muryarsa da taji ya yi maganar kamar ba faɗa ba ya fi kama da me shagwaɓa.
Har ta yi shiru sai kuma ta kalli in da ya nuna da yatsanshi.

Wani kalar abu ta ji ya ratsa ta, ganin Yanda ya nuno ƙirjinta, rigar da ta sanya ta ɗan zamo kaɗan ana ganin tudun ƙirjinta sosai.

Duk da kasancewar a al’darsu hakan ba komai ba ne, amma tun fil’azan ita bata iya buɗe jikinta ko yaya, tana yawan sanya alkyabba dan rufe surar jikinta, hakan ya sa wannan karon kunya ta kamata.

Cikin shagwaɓa da turo baki ta ce “Ni ka aura wai yanzu”? kafe ta da idanu ya yi, ya ce “Yeah ni mijinki ne”
Fashewa da dariya ta yi, sosai take dariyar kuma ta yi mata kyau sosai sai jijjiga jikinta take.

Samun kansa ya yi, da kasa ɗauke idanuwansa a kanta, ita kuma saida ta yi mai isarta sannan ta kuma duban shi tana gimtse dariyarta.

“Mi ye abin dariya?” ya tambaye ta yana sake haɗe fuska tare da jefa mata harara. Nuna shi da yatsa ta yi, sannan ta ce ”Kai!”

Zare mata fararen idanunshi ya yi, aikuwa ta kuma fashewa da dariya, tana kai hannunta saitin ƙwayar idonshi zata taɓa.

Wannan karon cikin san tabbatar da abin da zuciyarshi je zargi ya ce, “Ke miye haka, lafiyarki?” kawar da kanta ta yi gefe, ba tare da ta ce komai ba, sai kuma ta matso kusa da shi, ta fara shinshina jikinshi ta na dariya.

Gasgata abun da zuciyarsa ke raya masa a kanta ya yi, na Samun matsalar ƙwaƙwalwa ko jinnu.

Lokaci ɗaya ta tsayar da dariyarta ta haɗe fuska, cikin tsiwa ta ce “Kai yunwa nake ji.” wani Kallon rainin wayau ya jefe ta da shi ya ce “Oh really?” Kafin ya rufe baki ya ga Abinci gabanta tana ci idanuwanta a lumshe, kafin ya yi wani yunƙuri tulin abincin da ke gabanta wanda ko mutum goma basu iya cinyewa ya ‘kare plates ɗin wayam.

Mamaki da al’ajabi ne suka ziyarce sa, ya fara kokonto anya Ita ɗin mutum ce ma ko kuwa.

Kafin ya gama tunaninsa ta diro daga kan gadon tana faɗin, “Abinci! Abinci! ban ƙoshi ba fa…”

Buɗe ƙofar ta yi kamar walƙiya ta fice.
Cikin zafin nama ya mara mata baya, Biyar biyar take haɗa steps ɗin amma shi biyu biyu ya ke haɗawa kafin ya yi wani yunk’uri ta sauko, da sauri ya cimmata, Kitchen ya ga ta shiga, shi ma ya biyo Bayanta, Abincin da ke kan gas ta ɗauke duk da tukunyar ta aje ƙasa, ta zauna cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye cikin ƙatuwar tukunyar duk da turirin mugun zafin da abincin ke yi.
Addu’o’i ya fara yi, cikin fargaba, an ya fara sarewa da lamarinta, gabaɗaya ma ya lula duniyar tunani, Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai kallon shi gare ta, saidai babu ita babu dalilinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 18Sirrina 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×