Skip to content
Part 20 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

Dafe kanshi ya yi, yana mamakin rashin ji irin nata, Bai bi ta kanta ba, ya nufi Bedroom ɗin, samunta ya yi ta baje saman gadonsa tana barci, girgiza kai ya yi, A fili ya ce, “Marar jin magana kawai.” Daga haka ya yi ficewarsa gidan bakiɗaya ma

MANAAJ.

Tamkar Almara haka tsoho Arar da su Sanaam suka ga Gimbiya Azeeya bnt Ansar, sanin yanayin halittarsu ne ya sanya tsoho Arar shaidata, cikin sauri ya ce, “Yarinya ina neman Alfarma a maido mana Aleeya” A mamakinsa sai ya ga ta yi murmushi, ta du’ka ta gaishe sa, Alamun girmamawa sannan ta soma kora musu bayinin Abubuwan da suka wakana. Wani irin farin ciki ne ya mamaye su, dukkaninsu sai kawai suka fara kukan murna suna godiya ga abin bautarsu. Tabbas faɗar irin tsantsar farincikin da suka shiga asarar lokaci ne, Lamarin ya tsaya a zuƙatansu da yawa suka shiga murna da farinciki, kowa na tofa Albarkacin bakinsa, Saida syka gama farincikin sannan ta fito da wata Wuƙa haɗe da wata baƙar ƙwarya ɓe cike da ruwan wuta, ta musu bayani Sarki zahir suke so ya ui amani da wuƙar ya yanka jikinsa jininsa ya zuba cikin ƙwaryar, sai ya sha ya yi wanka sannan ya zuba a magudanar ruwan sashen Aaleeya. Yanda ta faɗa musu haka suka yi, Tun da mai martaba ya aiwatar da hakan, aka soma ruwa kamar da bakin ƙwarya, Kuma ruwan Dukkanin masarautun ake yin sa, manaj, hizar, nahar.

Sai da ya yi duk wani abu da ya dace,ya gama, sannan ya tsaya kasuwa ya siya mata situru, sannan ya kamo hanyar gidan. Tun farkon shigewar sa yake jin wata nutsuwa haɗe da nishaɗi tattare da shi, A hankali ya ke taka matattakalar benen, cike da ƙasaita. A nutse ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, turus yayi ya tsaya ganin ta zaune ta miƙe ƙafafauwanta bisa gadon, amma ta jingine jikinta da kan gadon.

Cikin ƙasaita ya ƙarasa in da take, Ya zauna dab da ita, yana d’an kallonta, har lokacin kenan bata yi wanka ba, bata chanja kayan jikinta ba, Buɗe idanuwanta ta yi ta sauke su kanshi,Irin kallon da taga yana bin ta da shi ne, ya sanya ta ji zuciyarta ta ɗan buga.

Janye tata ƙwayar idon ta yi, tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon, Amma ta ji ya danne bazar rigarta, ta kasa sauka, ganin ba shi da niyyar tada mata rigar ya sa cikin tsiwa ta ce, ”Ka ɗaga min riga mana, ka wani danne ni mts!” mamaki ne ya cika sa wannan tatsitsiyar yarinyar ce zata masa rashin kunya, aikuwa bai yi wata-wata ba ya fizgota ta dawo gadon ya haye bisa jikinta, sai nishi ta ke, Sai da ya yamutsa fuskarsa kafin ya ce, “Yaushe na fara wasa da ke ne kika raina ni?” harararsa ta yi ta ce “Oho ban sani ba” zaro mata manyan idanuwanshi ya yi, aikuwa saida ta firgita, ta ƙwalla ihu sosai da gayya.

Saurin mirginawa gefe ya yi yana toshe kunnensa tare da sakin ƙaramin tsaki, ya ce “Ohh!” Yaja kusan 7mnts a haka kafin da ƙyar ya ce, “I think you’ve already know to take a bath.” tana jin sa amma ta yi banza ta ƙyale shi sai da ya sha mur sannan ya kuma faɗin, “Ke! bana son hayaniya da yawan surutu fa, maza ki je kiyi wanka ki brush ga kaya chan ki chanza da wani cikin waɗannan”.Tana jinsa amma ko kallo bai ishe ta ba, wata irin izza take ji ma da sarauta, sai kawai ta lumshe idanu.

Ƙaramin tsaki ya ja, dan ya fara gajiya da iskancinta, wannan karon cikin ɗaga murya ya ce, “Me ya sa ke ƙazama ce ne, wankan ma ba zaki iya yi ba”. kamar jira ta ke ta ce, “E, ba zan yi ba in kana da ƙarfi kazo ka min” ta ƙarashe mganar tana taɓa baki, yana kallo ta tattare gashin kanta, da gan-gan kuma ta sa ƙafa ta shure babbar jakar da ya kawo mata kaya. Ta gyara kwanciyarta ta bashi baya.Cije lips ya yi, ba tare da ya ce komai ba, ya tattare hannayen rigarsa har ta fara gyangyad’i saboda wahalar da ta sha ta buƙatar hutu, kawai ta ji anyi sama da ita, chak ya ɗauke ta ya nufi toilet da ita. Kiciniyar ƙwache kanta ta shiga yi amma fa kasa, sai dai kawai ta jita cikin ƙaton jacuzzie mai ɗaukar aƙalla mutane uku. sai da ya dire ta sannan ya fara haɗa ruwa tana ciki, ya nuna mata soso da sabulu da brushe da shampo ya ce “Oya maza kiyi wanka yanzu, bana son shirme” Cikin faɗa ta ce “Ba zan yi gabanka ba, ka fita to.”

Wata uwar harara ya watsa mata ya ce, “Ke maza ki yi wanka na ce bana son shashanci, me zan kalla gare ki ƙwaila kawai”.

Harara kawai ta ke aika masa don kalmar ƙwailar ta bata haushi. ganin yana ta tsayuwa bata da niyyar fara wankan ya sa shi jan tsaki, Cike da mugunta ya kanne idanuwansa, sannan ya nufo ta gadan-gadan ya turata dukanta cikin ruwan. Nan fa suka shiga kokowa waje cire rigarta, aikuwa ya samu nasarar yage ta daga sama har ƙasa. Aikuwa cikin jin haushi itama ta sanya akaifunta masu tsayi ta fizge rigar da ke jikinsa ya koma daga shi sai singlet, shi kuma tuni ya tafi wata duniya domin arba da chikakkiyar halittarta da ta ruguza dukkan lissafinsa ta kuma wargaza mishi komai na shi Jin da ya yi ta watso masa ruwa a ƙirjinsa ya sanya shi, kallon jikinsa ya ga ta raba shi da rigarsa, aikuwa ya zabura ya riƙe ta gam, saida ya yi mata wanka da dole ta yi brush, sannan ya sake ɗauraye mata jikinta ya wanke gashin kanta, ta yi wani irin haske, ya dirje mata ƙafafuwanta da suka yi baƙi.

Cikin kawar da kai ya janyo towel ya yafa mata a jiki sannan ya ce ta fice shi ma zai yi wankan. Cikin fushi da ƙunƙuni ta ce Ita sam ba zata fita ba, ya zare mata idanu ta ƙi fita ta zuba masa idanunta, ai kuwa cike da salon mugunta, ya soma cire jeans ɗin jikinsa, Ya zuge zariyar boxes ɗinshi ya yi ƙasa da shi. Wata razananniyar ƙara ta sake tare da yin luu, idanuwanta suka rufe.

Sai da ya yi wankansa ya gama tsaff, sannan ya dawo ya ɗauke ta chak zuwa bedroom ɗin, Sai da ya shafa mai ya fesa turare sannan ya ɗauko wata t-shirt da 3wter ya sanya ya gyara sumarshi, ya yi kyau sosai, fuskarshi ta yi, fresh gwanin ban sha’awa duk da sam babu fara’a cikinta. A hankali ya tako ya ƙaraso kusa da ita, ya yi saurin kawar da kansa ya juya ya zauna saboda rabin towel ɗin da kunce, wani irin abu yake ji mai kama da feelings amma ya kasa gasgata kansa. ya yi jarumtar shafa mata mai.

A zuciyarsa yana mamakin irin yanda baya jin wari a jikinta sai wani sanyayan ƙamshi ta ko ina, ga kuma halittar jikinta babu gashi sam sai dai kanta, sosai santala-santalan cinyoyinta farare ƙal masu taushi da sheƙi suka janye hankalinsa ya shiga shafa su a hankali, har ya soma kauce hanya, ƙaramin bakinta da ta turo sai ya ingiza shi, ba tare da ya hankalta ba, ya ɗaura bakinsa kan nata ya haɗe guri ɗaya ya fara aika mata zafafan kiss masu tsayawa a zuciya da ruhi. Sosai ya fice da nutsuwarsa.

Da ƙyar ta samu damar buɗe idanunta daga sumar da ta yi, wani zafi ta soma ji ƙirjinta na yi mata, cikin fargaba ta kai idanuwanta kan shi ya dage sai tsotsar jikinta ya ke.

Da ɗan kuzarin da ya rage mata ta ture shi, lokaci ɗaya ta fara jin haushinsa, ta miƙe tsam ta janyo towel ta ɗaura sannan ta nufi jakar kayan da ya siyo, wani sari ne aka yiwa ɗin riga da skirt, rigar bata kawo cibiya ba, kalar Coffee brawan, sai skirt ɗin milk colour, da ƙyar ta sanya rigar ta ɗan kama ta kad’an, sannan ta janyo skirt ɗin ma ta saka ya amshi yanayin ƙugunta, yayi mata daidai gwanin burgewa, sannan ta tattare gashinta guriɗaya, ta d’auki kayanta da ta cire ta saka, a wani ɗan basket, ta dawo ta tsaya gaban madubi tana ƙarewa kanta kallo.

Wani irin kyau ta yi, mai nutsuwa, mai ɗaukar ido ga Yanda rigar ta amshi zubin halittar ta, ta yi kyau sosai, wanda ,tsayawa fasalta shi ɓata lokaci ne, kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da jinin sarauta ce ita, wani man shafawar shi ta ɗauka ta laftawa jikinta, ta sake yin kyau sosai, sannan ta fesa turare kaɗan ta miƙe, tana kallon yanda k’afafuwanta suke sheƙin mai.

Lakuto man shafawar ta yi, ta sanya a baki, da sauri ta tofar tana yamutse face ɗinta,Saida ta gama komai duk yana kallon ta ta mirrow da ƙyar ya miƙe ya nufi toilet ya tsarkake jikinsa, yana jin cikinshi ya ƙulle sosai.
Saida ya gama komai ya fito shi ma gwanin burgewa, amma ya ɗaure fuskarsa sosai, karta Raina shi, a daƙile ya ce mata, “Ki biyo ni ki ci abinci in kina iyawa”.

Sai da ta lafta masa harara sannan itama ta soma saukowa daga benen, duk yanda taso amfani da ƙarfin ikonta ta zubar da abincin da yake ci, amma ikon ya ƙi tasiri. A fusace ta janyo kujerar Dinning ɗin ita ma ta zauna, sai cika ta ke tana batsewa.

Abincin da ke cikin kulolin ta buɗe, ƙamshin daddaɗan girkin ya doki hancinta, ai kafin wani abu ta cinye duka abincin da ke cikin kular, tana ta tsotse hannu, maida kallonta ta yi, ga abincin gaban shi da ya ke tsakura. Wata harara ya watsa mata ganin yanda ta cinye abincin tana kallon nasa, ya ja ƙaramin tsaki, a fili ya ce, “Kina so ki ƙara?” ɗaga mishi kai tayi alamar E, ya dunguri kanta ya ce, “Wai kuma idan na baki sake ci zaki, wai wane irin ciki ne da ke?”Ji ya yi tace “Irin naka” ya zaro mata idanuwa “Ke ina wasa da ke?” Wata muguwar dariya ta ƙyalƙyale da ita, cikin sauri ta miƙe tana dariya tana nuna mishi abincin gabanshi, Kallon abincin ya yi, ganin babu komai plate ɗin ma kamar an lashe, ya sanya shi miƙewa a fusace, ya biyo bayanta.

Kafin ya cin mata tuni ta shige, yana zuwa jikin ƙofar tana banko ta, ta rufe, har saida ya bugu, ya ce ”Assh”.

Dariyar mugunta ta sanya mishi, yana jin irin dariyar da take ya yi ƙwafa, ya wuce ya koma parlourn ya zauna,Ya jima yana kallon T v, sannan ya janyo, wayarshi, ya dannnawa Ammah kira, ta yi ringing, ta yi Ringing, Amma ba a ɗaga ba, Cikin damuwa ya ajiye wayar, yana jin babu daɗi A ransa, har kusan mintuna sha biyar Amma bata fito ba, wayarsa ya ɗauka, ya sake dannawa Ammah waya, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga bata ce komai ba, Cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ya ce, “Ammah fushi kike da ni?”,Shiru bata ce komai ba, ya sake cewa, “Ammah please ki min magana”. Kukan shagwaɓa ya sanya mata, ya ce, “I’m sorry Ammh yanzu muna tare fa” cikin muryar marasaa lafiya ta ce, “Aliyu yaushe ka fara ƙarya?” murmushin jin daɗi ya yi, sannan ya ce, “Zan bata waya” Miƙewa ya yi, cikin sassarfa, yana faɗin, “Wife. Ammah zata yi magana da ke” Shiru bata amsa ba ya saka wayar handsfree ya ƙwanƙwasa ɗakin, yana faɗin, “Ki fito” Cikin Barci ta ji yana magana, ta miƙe dan ita ta ma manta da abin da ya faru ta buɗe ƙofar tana ɓata rai, Kallonta ya yi bai sake magana ba, ya miƙa mata wayar, saida ta karɓa sannan ya ce, “Ammh” Zaro mishi idanuwanta ta yi, masu matuƙar rikitarwa, murya a harɗe ta ce, “da gaske?” harararta ya yi, ya ce, “Ina miki wannan wasan dama ashe”.

Sai kawai ta tuna abun da ta yi, sai kawai ta ji kunya ta kama ta. Duk abun da suke Ammah na jin su, wani irin farinciki ta ji ya cika ta, ta ɗan ɗaga murya ta ce, “Na yi fushi” Cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Ammh ina kwana” “ban gan shi ba” ita ma Ammh ta bata amsa, ƙafafuwanta ta ji sun riƙe, ta shige ɗakin ta zauna kan gado sannan ta ce, “Pulj Ammh ki yi ha’kuri” dariyaAmmah ta yi daga ɓanagaren ta, ta ce, “Please na koya miki fa ba Pulj ba”.

Fige Wayar Aliyu ya yi ya ce, “To Ammh kin yarda?” saida ta harari wayar sannan ta ce, “Umh-Umh tukunna dae”, “Please Ammh.”

“Ya na ga ka kira da line india?” shiru ya ɗan yi, sannan ya ce, “Muna chan ne”. Kwafa ta yi tace, “Da izinin wa ka tafi??” marai-raicewa ya ce, “Please ammh ki yi haƙuri…” ”Alright, ina so ku dawo Jordhan, sannan ka kira Mai martaba ka faɗa masa inda kake da kanka that’s all”.

Zaro idanuwanshi yayi ya ce, “Please Ammh..” Katse kiran ta yi, ba tare da ta jira ya ƙarasa magana ba, Ya dafe kansa cikin damuwa.

MANAAJ
Cikin wani irin yanayi suka dinga addu’a tsoho Arar da kuma Sanaam sai Risha, suna cikin wannan yanayin ne, aka fara Wani irin matsanancin ruwan sama, wanda ya tsoratar da su, tun cikin dare ake ruwan har gari ya waye ba a daina ba, ruwa ake sheƙawa kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin tsawa da ake yi, Tun da suke basu taɓa tsorata ba sama da wannan lokacin ruwan ya tada musu hankali.

Kallon Tsoho Arar Risha ta yi, a raunace ta ce, “Ina jin tsoron a ce ko dan Gimbiya ta rasa rayuwarta ne ake irin wannan ruwan”, cikin damuwa ya girgiza kai bai ce komai ba.

Allon Tsafinsa ne ya fara fitar da hayaƙi, ya matsa ya fara ƙoƙarin bincike, Rufe idon da zai yi, ya fara ganin abubuwan da suka faru da Aliya tiryan-tiryan.

Wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ji murya Khaaal Bamanul_Ansaar na masa magana, ”Ku faɗi buƙatarku da taimakon da kuke so” ya ce, “Muna buƙatar komai ya zo ƙarshe bayan an gabatar da yaƙin, sai wannan ruwan” Yana gama maganar ya ji, tsitt, ruwan ya ɗauke, ya buɗe idanuwansa, ya ga komai ya dawo daidai, ya yi sujjada wa abin bautarsu ya miƙa godiya, cikin tsoro su Sanaam suka shiga jera masa tambayoyi. Ya yi murmushi ya ce, “Komai na gab da zuwa ƙarshe.”

Ya labarta musu duk abubuwan da suka faru, suka zube cikin jin daɗi suna godiya wa Abin bautarsu.
Sai lokacin suka nutsu suka fahimci irin ranar da ta fito, Miƙewa Sanaam ta yi, tanufi ɗakin da aka killace sarauniya Kunjam ta buɗe ta, sannan bayyana a turakarta, ta shimfiɗe ta bisa gadonta sannan ta bar mata ɓangaren.

Cikin ƙan-ƙanin lokacin Ƙasar Yalaaz ta soma dawowa yanda take, dan Ruwan da aka yi gabaɗaya Ƙasar ne, ba iya Manaaj ba, Sarauniya Sarah ta dawo yanda take, Mai martaba ya kuma tada bayi da hadimai da kuma mayaƙa da fadawa.

An fara gyaran masarauta gadan-gadan, Da yake abu na Sihiri, kafin faɗuwar rana masarauta ta soma dawowa yanda take, mayu sai murna suke yi.

Kasuwanni da Tekuna da dajikan, duk sun soma dawowa yanda suke, komai ya fara daidaita. Sai sannan ne Mai martaba da kuma Sarauniya Sarah suka fara tunanin Aaliya ita ma, hankalinsu ya yi matuƙar tashi da ba su ganta ba, Hakan ya sa, suka buƙaci ganawa da tsoho Arar, anan ne ya yi musu bayanin komai sannan ya tabbatar musu da tana nan cikin ƙoshin lafiya, Bayan gama yaƙe-yaƙen zata dawo gare su.

Sannan kuma ƙalubalen da ke gabansu yanzu bai wuce na yaƙi, ba dan basu san rana ko lokacin gama yaƙin ba, kawai shiri ya kamata su fara.


SAHASH-KUNJAM
A hargitse Sahash ta kalli Sarauniya kunjam, ta fara magana, “Anum Ba mu kaɗai ne ke harin waɗannan masarautun ba! tabbas akwai wani bayan mu, duba da yanda waɗannan abubuwan suka faru, sannan kina jin raɗe-raɗen da ke yawo a fada wai Aaliya bata Ƙasar nan”.

Numfashi Sarauniya Kunjam ta fesar, sannan ta ce, “Na fara sarewa Sahash, amma ina so mu dakata na ɗan lokaci mu ga abun da zai faru, sannan mu fara sabon shiri” wani irin kallo ta yi mata, sannan ta ce, “Anum mu dakata fa kika ce! ke kin sani son sarauta a cikin jinina yake, ban san ya zan yi ba idan har ban samu Mulki ba, zan iya komai saboda sarautar Yalaaz…ni zan tafi” Tana gama faɗin haka ta ɓace.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 19Sirrina 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
0
Free daily stories remaining!
×