Skip to content
Part 21 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

INDIA
Da farko matar ta fara yi wa Aaleeyerh wasu ƴan fizge-fizge kafin su fara karatun, amma kallo ɗaya ta yi mata da rikitattun idanunta ta shiga taitayinta, bata ma sake ko haɗa ido da ita ba, Cikin ƙwarewa ta fara mata bayanin ilimin boko, da hakima kuma ta fara tusa mata abun a ranta, ta daɗe tana mata bayanai sosai akan ilimin sannan ta tafi da niyyar gobe za su fara karatu. Miƙewa ta yi, bata ma ɓata lokacin tafiya ba, ta ɓace ta bayyana bedroom ɗin su, gado ta haye ta kwanta sai da ta huta sannan ta fito, lokacin Haydar ya fice, dining ta zauna ta tarar da sun dafa tuwon semonvita miyar ganye, ta yi kyau sosai sai ƙamshi me daɗi ke tashi.

Ta zuba abincin ta ci, amma sai ta ji ɗanɗanon wani iri, ta miƙe da gudu ta shige toilet ta fara kakarin amai aman bai zo ba, ta wanke fuskarta da ta ɗanyi ja, ta koma ta kwanta ta narke sosai cikin gadon, ƙarfe ɗaya da arba’in da tara ya shigo gidan, ya yi parking motarsa ya fito, ya nufo dinning ya ga abincin da ta sanya bata ci ba, ya taɓe baki ya haye saman benen Ya shiga bedroom ɗin ya hango ta, ta shige cikin bargo, ya yi wucewarsa kamar ya share ta, sai ya tuna amanar Ammaah ce ya d’aure fuskarsa tamau, sannaa ya dawo saitin gadon ya ce, “Ke! me ke damunki?” shiru bata amsa ba ta yi banza ta ƙyale shi, cikin ɓacin ran abin da take masa na shariya ya fizgo bargon da ta lulluɓe da shi, yana kallon ta, ganin idanuwanta a rufe suke ga kuma yanda take rawar sanyi ya sa ɗan sassauto ya rufe mata bargon, Ya zagayo inda take kwance ya ɗan zauna bisa gadon, ya sanya hannunsa saitin wuyanta yaji zafi rau, ya yi saurin janye hannunsa, Ita kam duk abin da yake yi tana jin sa amma ta sani cikin abincin da ta ci akwai sinadarin abincin da ta ci da mayu ba sa so, wanda ta kan ji ana faɗar sa a manaaj amma bata san menene shi ba, Ya miƙe ya nufi ɗayan ɗakin inda first aid box yake, ya ɗauko ya dawo ya kashe AC.n ɗakin, sannan ya ɗebo ruwa ya dawo, ya nannaɗe hannun rigarsa, ya tallafo kanta ya sa mata pillow a bayanta, still idanuwanta a rufe suke, ya fara saka wani farin ƙyalle yana matsewa yana goge mata goshinta.

Ƙanƙame jikinta ta yi, ta ci gaba da rawar sanyi, tana wata irin kyarma, muryarta bata fita sosai, ta ce, “Ka..kka daina” tsayawa yay yana kallon yanda dark pink ɗin bakinta ke motsawa a hankali, ya shagala sosai da kallonta ya tafi wata duniya ta daban, sai da ya nishinta sanann ya dawo hayyacinshi, ya tattare kayan ya ajiye ƙasa ya fara tunanin me ya kamata ya yi mata a matsayinsa na likita, Amma babu shawarar da zo masa, “Sanyi! sanyi” shi ne abin da take faɗa a hankali, ya kashe wutar ɗakin ya maida marar haske sosai, sannan ya fara rage kayan jikinsa, yana gamawa ya hau kan gadon, ya rge mata kayan da ke jikinta, ya gyara mata kwanciya Sannan ya dawo saman jikin ya yi mata rumfa ya ja blanket ya rufe su, duk da zafin jikinta haka ya daure. A hankali ta fara jin wani baƙon yanayi na ratsa ta, sannan ɗumin jikinsa ya fara dawo mata, wata irin kasala ta sake rufe ta, sakamakon ƙamshin turarensa mai jan hankali. Dukkansu basu sake sanin a wace duniya suke ciki ba, wani barci mai daɗi da nutsuwa ya ɗauke su a lokaci ɗaya.

MASARAUTAR NAHAAR
Cikin kwanakin nan me martaba Gobar ya fara gane kuskuren da su ke ƙoƙarin aikatawa sanadin kwaɗayin mulkin da tsantsar hassada da kuma zaluncin da yake yi a yankinsa, cikin ƙanƙanin lokaci ya fara gyara halayensa sai abin da ba a rasa ba, Kowa ya yi mamakin wannan chanzawar da yay, Sarauniya Rahash an yi binciken duniya amma babu ita babu dalilinta.

QSam cikin su babu wanda ya damu sai ma cewa da suke yi, ‘Ai duk inda taje da ƙafafuwanta zata dawo’ sai ma shirye-shiryen auren zulmah da Armaan da ke gabatowa dan me martaba yay alƙawarin sai an yi shi, hakan ya sa Armaan kwantar da hankalinsa. Yau sun tashi cikin farin ciki, dan yau ne ake baikon Armaan ɗin da Zulmah, Masarautar ta cika an kuma ƙawata ta sosai ta yi kyau sosai ko wanne maye ya fito a suffa mai kyau ya sake ƙarawa kansa kyau, sai ɓarnar zinarai ake yi, Gagarumin shagali na gani na faɗa Sarki Gobar ya shirya, ya aikawa sauran masarautun wasiƙar gayyata, daga nan aka ci gaba da shiri..Kafin fitowar rana har sun kammala duk shirin da ya dace, mai martaba ya chaɓa ado da gwala-gwalai da lu’u-lu’u, sai sabuwar sarauniyarsa sarauniya Mahira, wani babban fili mai cike da haɗaɗɗun shuke-shuken furanni masu ƙamshi, gurin ya ƙawatu, kowacce masarauta da shimfiɗar haɗaɗɗiyar shimfiɗar da aka musu, sai kuma bayi da hadimai, da gurin bokaye ma, kowa ne maye mai zaman kansa da zai halarci baikon akwai mazaunin da aka tanadar masa. Sai kuma gurin zaman Yarima da Gimbiyarsa. Guri ya ƙawatu sosai, fiye da tunanin mai tunani, ga ruwan turare mai sanyi da aka yi, sai ƙamshin ya haɗe da na furanni yake matuƙar sanyaya zuciya, ga shi babu rana ko alama an yi amfani da ƙarfin sihiri an yi wata rumfa-rumfar ganyayyaki ta kare ranar….Kafin wani abu Mayu sun fara taruwa a wajen ko wane cikin shiga ta alfarma, Yarima Tazaan da sarauniya Halsha da kuma ɗayar matar sarki Ahal gimbiya Jasina sai mai martaba Ahal, suma sun ƙaraso da tawwagarsu da kuma tarin dukiya ta ban mamaki da zasu bayar. Mawaƙan mayu da masu kaɗe-kaɗe ma duk sun hallara aka fara wasa Yarima Tazaan sai ɓarin zinarai yake musu, ya zamana Sarki gobar da Sarauniya Mahira da kuma Karaan da Armaan sai dangin Zulmah wato waziri da Mahaifiyar Zulmah, sai kuma tawwagar sarki Zahir kawai ake jira su hallara.

Mawaƙa da makaɗa da kuma masu bushe-bushe ne suka fara koɗa Tawwagar sarki Zahir, tun shigowarsa kowa hankalinsa ya ɗauku, na son ganin gimbiya Aleeyerh matashiyar budurwa mai kyawawan ɗabi’u da kuma madarar kyawu gabaɗaya sun ƙagu su ganta, har sarki Zahir da sarauniya sarah, da kunjam da su Sahash da Sanaam suka samu gurin zama suka zauna, ba a daina musu kirarin sarauta mai fasa kai ba, sai kirari ake musu, Sanaam ta dage ta dinga zuba kyauta da Lu’u-lu’u a madadin Aliyerh haka kuma sarauniya Kunjam da Sahash ita dai Sarauniya Sarah kawai duƙewa ta yi, tana murmushi, Sahash da Tazaan sai gasar ɓarin lu’u-lu’u da zinaai suke yi, ana sake musu kirarin da ke ruɗa su..

Sarki Gobar da sarauniya Mahira sun ƙaraso su ma cikin shiga ta kece raini, mai matuƙar ɗaukar hankali, sai yarima Karaan, Sai da kowa ya zauna aka nutsu sannan aka fara waƙe Yarima Armaan da Gimbiya Zulmah, shigowarsu ta yi kyau sosai dukkansu cikin baƙaƙen kaya sai kuma wata akyabba fara da suka shiga cikinta su biyun aka yi musu rumfa, har zuwa mazauninsu, suka zauna aka sake rufe su, sannan aka fara baikon bayan kammalawa, aka fara ɓarin dukiya ana zuba musu gwala-gwalai da lu’u-lu’u, sai wani turare mai masifar ƙamshi shi ma aka yayyafa musu a jikin alkyabbar, Ana tsaka da wannan nishaɗin an ci an sha ana ta raye-raye, Wani irin hadari ya taru lokaci ɗaya, mai matuƙar firgitarwa garin ya yi baƙiƙƙirin alamun da ko wane lokaci ruwa zai iya sauka, ga wata irin tsawa da aka fara mai razanarwa. Hankalin mayun ne ya fara karkata sosai ga ruwan da ya fara sauka a hankali, mai mugun zafi, miƙewa wasu suka fara yi, suna shirin barin gurin, haka tawwagar Sarki Zahir ma suka miƙe su duka suka bar yankin, hankalin bokayen ne ya tashi lokacin da suka bincika amma babu abun da suke gani face YAƘI….na gabatowa daga haka duk darajar madubin tsafi ko allon sihiri yake tarwatsewa, Sai kuma tambarin ko wace masarauta da ke, haske yana sheƙi sosai a jikin ko wane maye. Ruwa ake yi na fitar hankali, wasu bukkokin da gidajen Mayu duk ruwa ya ja su, tekuna da ƙorama duk sai ambaliya suke yi, duk yan da suka zaci ruwan ya wuce tunanin su, ga wasu irin tsawa da ake yi masu matuƙar ruɗarwa da tsoratarwa, hankalin mayun da shuwagabanninsu ya kai ƙololuwa wajen tashi. Ta ko wane ɓangare sun duƙufa suna bincike, amma da zarar sun fara nisawa cikin bincike allon sihirinsu ko madubin ke tarwatsewa.

MANAAJ

Zaune sarauniya Sarah take idanuwanta na fitar da ƙwalla ta dubi Sarki Zahir cikin sanyayyiyar murya ta fara magana, “Me martaba ina son ganawa da Aliya, ban sani ba wannan yaƙin akwai rabon mu sake ganawa da ita ko kuwa, ka taimake ni” ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa daga idanuwanta ta kuma haɗe hannayenta guriɗaya. Shi ma duk yanda ya so daurewa sai da ta fahimci damuwar da yake ciki, sun jima a haka bata sake magana ba, bai mata magana ba, amma yanda yake kwantar mata da hankali da ƙwayar idanunashi kaɗai ma saida ya sanyaya mata zuciya, ɗan zabura ya yi, sai da ya saki murmushi, sannan ya dube ta ya ce, “Na tuna da wata hanya da zamu iya ganawa da ita” Wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tana matsawa ta ƙanƙame shi, cikin farin ciki, madubin sihirinsa ya jawo ya fara aikin zana tambarin Manaaj ɗin, da wanda aka rubuta manaaj da wani salon rubutu mai kyau sosai, Sai kuma wata ƴar star alamar ta jinin sarauta.


INDIA
A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta hannunta na dama daidai inda tambarin masarautarsu yake ne ta fara jin zafi-zafi, ta kalli hannun ta ga yanda tambarin yake haske sosai, ta miƙe, a hankali ta ja rigarta ta sanya ta nufi toilet, tana shiga ta datse ƙofar ta fara bincike dalilin hasken, cikin ranta tana addu’a Abin bautarsu ya sa komi lafiya, Anim ya faɗo mata a rai, ta saki wani murmushi mai kyau, ta fiddo madubin tsafinta daga cikin gashinta, ta fara ƙoƙarin haɗa mudubinsu, ta zauna bisa wata kujerar da ke, gaban wani wuri cikin toilet ɗin da madubin kamar dressing mirror, ta nutsar da madubin cikin wanda ke cikin bayin, cikin sa’a madubin ya nuno mata Sarki Zahir da kuma mahaifiyarta sarauniya Saraah, zaune sun ƙurawa madubin idanu, Suka tsurawa juna idanuwa babu wanda ya iya ƙwaƙƙwaran motsi, Sai kawai suka ga hawaye kan fuskar Aliya, Cikin kiɗima suka haɗe baki suna tambayar ta, “Kina lafiya, me ke damunki??” ta yi wani murmushi da ya bayyana tsananin farin cikin da take ciki, ta sanya hannayenta ta rufe fuskarta, tana diddira ƙafafuwa, alamun shagwaɓa, Hararar wasa Sarauniya Sarah ta yi mata, sannan ta ce, “Mene ne??” dariya ta yi, sannan ta ce, “Ina kewar ku ne da yawa sosai”. Wata irin rikitacciyar tsawa aka yi, ita kanta saida ta ji ta razana, madubin kuma ya tarwatse, a rikice ta wuntsilo daga bisa kujerar tana doɗe kunnuwanta, tana kuma miƙewa da son sake haɗa madubin amma be yi ba, jin motsi ya sa ta yi gaggawar maido madubin yanda ta zo ta tarar da shi.

Cikin ƙanƙanin lokacin ta yi amfani da ƙarfin ikonta tana sarrafa abubuwa, ta yi wanka, sannan ta fito, daga toilet ɗin, xaune ta tarar da shi bakin gadon ya dafe kansa, idanuwansa a rufe, ta shirya, amma har lokacin be motsa ba daga inda yake. Bata bi ta kansa ba, ta fice daga ɗakin ta nufi, dinning table ta tarar da har sun jera abinci, ta zauna ta ɗiba ta ci, mai isarta, ta ƙoshi, sannan ta dawo Parlourn tana kallon Tv, Ta jima sosai tana kallon amma gabaɗaya hankalinta ba ya ga Kallon zuciyarta na a ƙasarta, ji take yi kamar ta koma yanzu ta ga halin da suke ciki, amma gargaɗin Khaal Bamanul_Ansaar na dawo mata, ta sauke ajiye zuciya ta fesar da numfashi a hankali, ta miƙe tana hamma ta hau bene ta buɗe ɗakin ta shiga, ta nufi bedroom, ta tura ƙofar ta shigo idanunta cike da barci, ita dai yanzu tana yawan jin mugun barci sosai ta rasa dalili. Ta nufi gadon da nufin kwanciya, amma ta ganshi har lokacin kamar yanda ta bar shi, bata kula ba ta hau gadon ta ja bargo ta kwanta, har ta kwanta bacci be ɗauke ta ba, mamaki ne kuma ya kamata da ta ga har lokacin bai tashi ba, kallon inda yake ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce, “Lafiya ka ke??” Shiru bai ɗago ba, kuma bai bata amsa ba, da ƙyar ya iya ɗago jajayen idanuwansa ya dube ta, muryarshi na kyarma ya ce, “Bana da lafiya”.

Zaro idanuwanta ta yi, ta ce, “Me ke damunka?” shiru bai bata amsa ba, har ta fitar da ran samun amsarsa sai kuma ta ji yay magana chan ƙasan ma’koshi, “Ciwon kai” Tashi ta yi, ta jingina da gadon ta tsaya tana kallonshi, sai kawae ta ji tausayin sa ya kamata, da ta tuna yanda ya taimaka mata jiya amma da tana sa ran bata isa jin sauƙi ba, lallai shi ɗin na daban ne kuma yana da kirki wasu lokutan.
Rufe idanuwanta ta yi, wata hoda ta fito a hannun nata ta murje a hannunta, sannan ta matso dab da shi, ta tallafo kanshi, ta shafa mashi a goshi.

Tana gama shafa mishi da kamar mintuna biyar, ya fara sakin ajiyar zuciya zufa ta fara tsattsafo masa, ya miƙe ƙafafunsa, ya maido jikinsa kan gadon yana nishi a hankali, tamkar an zare masa ciwon kan haka ya ji, gajiya kawai ke damunsa, ya ɗauki kusan 8mnts a haka, kafin ya miƙe ya shiga toilet, ya daɗe yana wanka sannan ya fito ya kimtsa ya shirya cikin sleeping dress masu matuƙar kyau da taushi. Ya zo zai kwanta ya ga yanda ta kwanta a takure, ya tsaya yana kallon ta, sai kawai ya ji shauƙi na ɗibarsa, ya yi saurin kawar da kansa gefe, a fili ya ce, Rigima!” ya gyara mata kwanciya, shi ma ya hau gadon ya kwanta, yana tunane-tunane akan zamansu. Shi dai ba sonta yake yi ba, yana zama da ita ne saboda Ammaah, yana cikin waɗannnan tunane-tunen barci ya ɗauke shi.

<< Sirrina 20Sirrina 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×