Wasa-wasa tun Aliyu na ɗaukar jikinta da rashin sabo har ya fara tsorata, wani irin zazzaɓi take yi da ciwon kai, kullum cikin shan drip take, ta yi wata irin rama, hankalinsa ya kai ƙololuwa wajen tashi, tun yana ɓoyewa har Ammaah ta fahimci halin da suke ciki, daga ƙarshe da abun ya tsananta Part ɗin Ammaah aka mayar da ita, ita ke kula da ita, ga wani irin mugun haske da ta yi sai idanuwa da karan hanci kawai ta faɗa sosai, idan ka kalle ta dole ta baka tausayi. Tamkar Aliyu ne ke ciwon shi. . .