Sahash na tsaye bakin ƙofar shiga fada ta bada baya, sanam ta bayyana cikin wata azama ta saki wata ƴar wuta a dogon gashin sahash ɗin, bata ji wuta a kanta ba ta dai ga gashinta yane kakkarewa, a hanzarce ta jiyo ta sauke idanunta kan sanaam wani ƙayataccen murmushibta sakar mata, tare da kashe mata ido ɗaya kafin tayi wani yunƙuri har ta ɓace.
A razane ta ɓace sai gata ɗakinta baya ta faɗa cikin wani ƙaton abu da alama bahan wanka ne, lokacin da ta kalli kanta a madubi tsananin baƙin ciki fasa mdubin tayi. . .