Skip to content
Part 3 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Sahash na tsaye bakin ƙofar shiga fada ta bada baya, sanam ta bayyana cikin wata azama ta saki wata ƴar wuta a dogon gashin sahash ɗin, bata ji wuta a kanta ba ta dai ga gashinta yane kakkarewa, a hanzarce ta jiyo ta sauke idanunta kan sanaam wani ƙayataccen murmushibta sakar mata, tare da kashe mata ido ɗaya kafin tayi wani yunƙuri har ta ɓace.

A razane ta ɓace sai gata ɗakinta baya ta faɗa cikin wani ƙaton abu da alama bahan wanka ne, lokacin da ta kalli kanta a madubi tsananin baƙin ciki fasa mdubin tayi, da sauri ta fito a fusace dan ji take yau ko ita ko sanaam, sai dai ta duba ga baki ɗaya masarutar babu sanaam babu dalilinta, sashen mahaifiyar ta taje sosai sarauniya kunjam ta tsorata da ita, haka dai tai ta tausar ta amma tace ita ko mai martaba bai isa hana ta ɗaukar mataki ba jin ta riga da ta yanke hukunci yasa mahaifiyarta tattara zancen ta watsar gefe.

MASARAUTAR NAHAAR


Zaune yake gaban mahaifiyarshi suna shirye-shirye dan suna jiran nan da kwanaki ukku, komai ya wuce dan sunyi gagaru-min shiri sun baza ƙarfin iko, tsafinsu na maita, sihiri iya sihiri abin si wanda ya gani zai tabbatar, tambaya e watso ma karan ɗin wacce baibyi zaton ta ba.


“Ka kuwa yi nasara kan Sahash?” cikin ɗan diri-ricewa yace
“Tun lokacin da mukai maganar nan, na rabu da ita.”

“Amma ita sanaam fa!?”

“Ai tun lokacin da ta samu, labarin ina tare da sahash tayi min wulaƙanci ni kuma nace, har abada kar ta sake nuna tasan karan!”

“Da fatan dai baka yi sakaci da ƙwan zinaren nan ba?”

“Yana nan na ajiye guri mai sirri!”
“Ka kula sosai.”

Arman ne ya shigo yana ɓaɓɓata rai, dubanshi mahaifiyarshi tayi tace “wa ya taɓa min yarima arman ɗina?”

“Wai mai marataba ne ke so na aure wata ƴar abokinsa.”

A Razane tace “Wane abokin daga ciki?”

“Nima ban sani ba nadai ji yana maganar zasu zo nan.”

Yau kwana biyu kenan kullum sai mai martaba ya koya mata abubuwa da dama, faɗa kuma dama ta iya yanzu kuma tana ƙara koyo ta ƙware sosai ya bata, kyautar wani zobensa da yake matuƙar ji dashi, sannan yayi mata gamsasshen bayani a kan zoben, Yau rana ta ukku kenan kamar yanda, ya faɗa sunyi faɗa sosai, sannan ya ɗaura mata wata sarƙa mai kyau a wuya, ya kuma faɗa mata a koda yaushe ta kasance cikin shiri, dan gobe ne BAƘIN WATA! ke kamawa.

Haka ta bar sa cikin mamakin to mai zai faru goben, ita dai bat yi wani yunƙuri ba ta kwanta hankalinta kwanche dan har dare ya fara, kuma tana da yaƙini da wani abu ne tsoho arar zai gaya mata.

MASARUTAR HIZAAR


Tsakiyar dare sarauniya halsha ta tashi ta hau shiri gadan-gadan dare da sarki ahal, babu ɓata lokaci suka gudanar da baƙin tsafi, suka nufi babban gate ɗin masarutar, dan ficewa zasu iya, doki ɗaya suka hau suka suka fara tafiya da gudu dan akwai tafiya, sosai sun daɗe suna tafiya har suka yi amfani da ƙarfin ikonsu suka isa da wuri, Wata tsohuwar maƙabarta suka shiga, sun wuce kabarbura masu yawa wasu kabari guda ukku da suka fi sauran suka tsaya, a tare suka ɗaga farin tulu suka fasa a kabarin tsakiya, wata guguwa ce da iska haɗe da hayaƙi suka taso suka rufe kafin wata tsohuwa ta umurce su da su, ɗauki tulun cikin kabarin, ɗauka sukayi suka ɓace fuskokinsu ɗauke da farin ciki.

MASARAUTAR MANAAJ

Cikin sauri-sauri sahash ke shiri tana gamawa ta kama hanyar fita ba tare da kowa ya ganta ba, maƙabarta ta nufa.
Kallo ɗaya zaka mata kasan ba chikakkiyar mutum bace! tafe take tana rangaji cikin maƙabartar, wani ƙaton madubi ne ya bayyana ɗauke da wat matashiyar budurwa wacce take kwanche bisa wani makeken gado, a gaggauce ta fara ƙoƙarin ƙona mata fuska, cikin barci taji kamar ana ƙoƙarin chutar da ita.

A firgice ta tashi tare da ɗaukar madubin tsafinta wani murmushi ne ya suɓce mata ganin yanda sahash keta ƙoƙarin ƙona mata fuska, wani farin haske ne ya fito daga idanunt yayi cikin madubin, sahash na tsaye kawai ta faɗi a kufle ta nutsa cikin masarautar, wani kabari taja ta tsaya, amma shine na farko sai guda biyu kuma, wae wuƙa ta fiddo ta yanka hannunta jini ya zuba saitin kabarin.
a firgice ta fara jera masa tambayoyi, “kaka suwayi waɗan nan?”

“Daman nasan zaki tambaya waɗan nan sune wasu shaharrun sheɗanun mayu waɗan da aka shafe su da daɗewa, amma an tdo su saboda samun sarauta, kuma kowa nason haɗe masarutun ukku a chigaba mulka, amma hakan ba zai taɓa yiwa bai sai anje tekun jazal an samo abunda zai dawo da su, yasa su komo ƙarƙashin iko, saidai kuma duk cikin su babu wanda yasan wace duniya tekun yake.”

“Toh amma kai kasan inda tekun?”
“Eh na sani! amma aliya kece kaɗai zaki iya zuwa ki ɗauko kafin su gano dan hana faruwar yaƙin.

<< Sirrina 2Sirrina 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.