Cikin mamaki tace "To a wace duniya yake?" "A'a ba yanzu ya kamata kisan duniyar ba, zan sanar dake ba da jimawa ba yanzu ki koma masarauta, mu haɗu gobe." "To! na tafi sai wani lokacin."
Daga haka suka yi sallama, zuciyar Aliya cike take da fargaba, amma da ta tuno zancen mahaifinta sai taji, ƙwarin guiwa.
Masarauta ta dawo ta kwanta washe gari an tashi da wata rana mai tsananin zafi haka yasa, kowa ke shan iska.
Fitowa tayi bata kuma ɓata lokaci ba ta shirya tsaf, tayi kyau sosai dan dama akwai kyau iya kyau, ga. . .