Skip to content
Part 4 of 22 in the Series Sirrina by K_Shitu

Cikin mamaki tace “To a wace duniya yake?” “A’a ba yanzu ya kamata kisan duniyar ba, zan sanar dake ba da jimawa ba yanzu ki koma masarauta, mu haɗu gobe.” “To! na tafi sai wani lokacin.”

Daga haka suka yi sallama, zuciyar Aliya cike take da fargaba, amma da ta tuno zancen mahaifinta sai taji, ƙwarin guiwa.

Masarauta ta dawo ta kwanta washe gari an tashi da wata rana mai tsananin zafi haka yasa, kowa ke shan iska.

Fitowa tayi bata kuma ɓata lokaci ba ta shirya tsaf, tayi kyau sosai dan dama akwai kyau iya kyau, ga ƙuruciya da ka ganta baza ta wuce 18-19 A gaggauce ta kimtsa ta nufi, inda suka saba haɗuwa ba tare da ta nemi rakiyar Risha ba.

Buɗe ta tarar da ƴar bukkar , kai tsaye ta shige ba tare da ɓata Lokaci ba, zaune ta same shi da wani littafi a hannunshi, hanklinshi ya kar-kata baki ɗaya kan littafin.

faɗa ɗa fara’arsa yayi, tare da nuna mata gurin zama, Fuskarsa cike da walwala zama tayi cikin zumuɗi dan tana san jin labari.

Wani farin turare ya bata yace ta shafa, shima ya shafa yayi ya gyaran murya ya fara magana.

ƘASAR YALAZ!

Asali kuma tushen ko wane maye na wannan, duniyar tamu daga yalaz ne.
Yalaz ƙasa ce kamar yanda kika sani ta mayu masu chike da ƙarfin iko da tarin dukiya ta ban mamaki, duniyar mu akwai dukiya akwai masu ƙarfin tsafi da bokaye, da kuma sheɗanun mayu masu ƙarfin sihiri.

A Yazlaz akwai abubuwan al’jabi da na ban mamaki, gwala-gwalan mu sun kasance masu wata irin daraja, muna kuma da ksuwanni da teku na da dajji-jika masu duhu,miyagun namun dawa masu haɗari, sai dai, basa chutar ga ko wane maye wannan tsarin yalaz ne.
SHEKARU ƊARI BIYU DA SABA’IN 270 DA SUKA SHUƊE BAYA.

A ƙasar yalaz maita ta kasance kashi biyu, akwai waɗan da ake haihuwarsu ba’a mayu ba, da ƙarfin iko ake mayar dasu mayu, akwai ainahin mayu akwai kuma waɗan da suke mayu masu kwaɗayin jini.

A zamanin anyi wani hamshaƙin maye mai tsananin dukiya da ƙarfin iko, babu wanda yasan iyayensa ko wani masa, kowa na shakkar shi yana da kwar jini sosai, sannan yana da izza sosai ana zaune kwatsam ya ɓullo da wani al’amari wai yana so ya zama sarkin YALAZ baki ɗaya, a lokacin ne waɗan da suka san halayensa suka fara tururuwar amincewa, bai nemi amincewar kowa ba yayi ginin masarauta iya masarauta da ta chinye rabi da kwatar birnin dan kafin kace zaka zagaye masarutar zaka iya wata, amma idan har kana da ikon ɓacewa, zaka dinga ganin komai a sauƙaƙe.


Wannan sarkin ya kasance mai suna NAZAAN, bayan hawam mulkin nazaan ya fara kawo musu gyara sai dai yana da sheɗanci sosai dan kallo ɗaya idan ya maka zai fahimci halayenka. Wani ƙarfin ikon da yake dashi a lokacin da ya hau mulki ya kai shekaru 40 amma kwata-kwata bai sauya, ba.

Babban abun da ya fara fizgar wasu sheɗanun mayun shine KYAWUNSA a tarihi ba’a taɓa mai makamancin ikon sa ba, sannan masu bincike sun san ba’a taɓa samun kowane jariri koda mai suffar sa ba.

Ana cikin haka wasu mayu suka fara tada fitin-tinu akan sarki ɗaya ba zai iya mulkar su ba dole a samu wani sarkin na daban, kuma dole a raba masarautun ukku, kawai sai ya sakar musu wani ruwa ayi kwanaki biyu ana yi.

Fitin-tinu sun ƙi ci sunƙi cinyewa, haka kawai aka samu wasu sheɗanun mayu masu kama ɗaya suffa ɗaya, wato AZLA DA RIYAD Tunda suka zo suke ɓanna shi kuma NAZAAN ya auri azla, domin idon ko wane maye ya dawo kanta gashi ba’a taɓa samun koda wacce takai rabin kyanta ba a yalaz.

Tana da ɗan tsayi dai-dai-dai ga gashinta da ya sauko har tsakiyar bayanta, sai dai ba baƙi bane amma yana da kyau da duhu da ɗaukar hankali, idanuwanta sunfi komai fizgar zuciyoyin mutane akanta, shu’umace sosai daga nesa zaka yi tunanin ko doguwar magana ba zata iya ba amma, idan tana son yin sheɗanci a natse take komai.

Babban ƙalubalen da mayun suka fara fuskanta shine, iyaka da aka musu da wani jeji wanda RIYAAD ke hutawa, sannan babu mahaluƙin da ya isa ya shiga kasuwa in har azla na ciki, kuma ko mai zai faru ba zaka shiga ba sai ƙamshinta ya ragu a kasuwar.

A lokacin da wasu mayu suka fara nuna, rashin ɗa’ar su Sarauniya Azla ta sako da wasu dodanni, marassa kyan gani kuma duk mayen da yake aiki ƙarƙashinta, da zarar ya munafurce ta akwai wani ƙaramin maciji a gashinta, yana fitowa sara ɗaya yake yi in tace, maye ya mutu shi kenan idan kuma bata ce ba za kayi ta fama da jinya, babu magani hanya dodanni, dajin neman magani Riyaad.
Mayu san jigata iya jigatuwa, amma duk da haka basu saduda ba ba kuma suyi ɗa’a ba.

Nazaan baya cewa komai, a cewarsa har sai sun saduda, sannan Azla ta gayyaci wasu mashahuran aljannu dan suzo su chanza fasalin masarautar manaaj, duk da a wannan lokacin babu wanda yasan aljannh ne sai Riyaad,nazaan, Azla.

Ga baki ɗaya, sun mayar da masarautar kamar wata hamshaƙiya, da dole aka ma masarautar tambari kowa na dashi. Mayu sunga babu wata hanya da zata ɓulle musu, dan babu kalar tsafin da ba’ayi amfani dashi ba, don kawar da koda maye ɗaya ne a cikin su, birnin yalaz ya koma wata Daula Mai ban mamaki daga shigowarka zaka fahimci hakan.

Tafiya tayi tafiya mayu sun fara biyayya, hakan yasa dodannin suka fara ragewa, sai dai dajin sai ranar da nazaan baya nan kowa zai iya shiga.
Wani binciken sirri Azla ta fara yiwa nazaan, dan ta gano akwai wani ɓoyayyen birni da suke ɗauke da wani zoben sihiri, zoben ƙarfin ikon dake jikinshi ya shallake dukkan tunanin mai tunani, da kuma nazarin mai nazari. Sai dai zuwa wannan duniyar akwai muhimmin haɗari wanda misalta shi ma ɓata lokaci ne.

Lokacin da ta sanarwa mai martaba nazaan, yayi farin ciki iya farin ciki haka suka yi zaman sirri da riyad da azlar sai nazaan, sun yanke hukuncin cewa, za’a ƙirƙiri wasu idan su sun tafi, sai riyad ya chigaba da mulki za’a ajiye wani riyad ɗin na bogi a jeji, sai shi ya koma suffar nazaan ya chigaba da mulki, sai a samar da azla ta bogi…

Sosai shima ya nuna farin cikin sa da kuma jin daɗin sa, basu wani ɓata lokaci ba suka hau shiri gadan-gadan, dan sun san fitina ce kawai kuma sun tara sun samu, tsawon kwanaki huɗu sukayi suna shiri sosai, Rana ta biyar suka yanke hukuncin barin masarautar zuwa BIRNIN FAHAR! cikin tsakiyar dare suka fita daga masarautar da dawakan su.

Wani baƙin daji suka dunfara gadan-gadan sun yi tafiya mai tsayi kafin su ƙaraso wani ruwa, sai suka tashi sama suka tsallake shi abin kamar almara.
Wata tafiyar suka ƙara, sun daɗe suna tafiya, dan ma akwai ƙarfin sihiri da kuma gudun da suke bankawa.
Ganin rana ta fito ya sanya su yada zango a ƙarƙashin wata bishiya, abinci suka ci dawakan su, suka sha ruwa suka kuma huta sai suka chigaba da tafiya, wannan karon wani abu ne, ya kare musu rana ga iska suna sha.
Tafiyar da nisa dajin akwai tsananin girma da duhuwa, dan ma sunyi amfani da ƙarfin tsafinsu haske ya samu shi yasa, sun kai awa bakwai suna tafiya, lokacin har dare ya fara hakan yasa suka yi wata bukka suka shiga dawakan su kuma, suka ci abinci da ruwa suma haka suka yi, sannan suka kwanta.

Baccin da suka yi bai fi na awanni ukku ba suka farka suka sake nitsawa cikin dajin.

Jefi-jefi sukan sakarwa junan su murmushi, tafiyar cikin kwanchiyar hankali suke yinta, duk da akwai miyagun namun daji.

Tsawon kwanaki bakwai suka yi suna tafiya, sau ɗaya suka samu matsala da ƙafar dokin, sarki nazaan ta turguɗe, kuma yanzu lafiya lau sun gyara.

Yau rana ta takwas kenan kuma sun kawo, kusan ƙarshen jejin RAZIB! Wata ƙorama ce daga ƙarashe, ta yanda babu wata hanya sai ciki wawakeken rami ne da yayi miƙe in har kana son fita, to sai dai ta ciki, gashi wasu dogayen shukoki ne a sama, ƙasan kuma ruwa ne kwanche.
Wani ƙaton tsun-tsu ne ya bayyana duk suka hau sai dai dawakan su, sun barsu a nan.

Tashi dasu sama yayi ya lula, ƙasa-ƙasa ya fraa yi, dan anzo inda ruwan dake ƙoramar da shukokin suka ƙare, sauka sukai suka shige cikin ƙoramar suka fara tafiya da ƙafafunsu. Sun sha Tafiya sosai, sosai har suka kawo iyaka. Hanya ce ta Rabe biyu ɗaya dama ɗaya miƙe, miƙewa suka yi sai kuma tsun-tsun ya bayyana.

Sararin samaniya suka lula tafiya kawai suke cikin gajimare, babu kama hannun yaro.

Jejina har ukku suka sake, wucewa tsawon kwana talatin da biyar kenan.
yau kwana na talatin da shidda yau suka ƙaraso birnin fahar, tun farkon shigowar su wani, wuri mai kama da sahara suka chanza suffa.

Wata suffa suka komai kamar wasu, ƙananan dodanni, tsanwaye sharr babu kyan gani tafiya suka yi, suka doshi cikin birnin.

Wasu halittun suka gani suka shige, cikin su suna ta kai kawo, a hikimce suke bugun cikinsu suna musu tambayoyi, abunka ga marassa wayau sai basu gane su ba suka saki jiki suna basu labarai kala-kala har da waɗan da basu tambaya ba.

Daga ƙarshe wani yace suzo gidan shi su kwana, cikin jin daɗi suka amince suka tafi. Kwanansu biyar kenan amma sun kasa samun hanyar shiga masarautar dan ɗauko zoben, yau dai nazaan yayi hikimar tambayar wannan halittar, za’a iya sama musu aiki a masarautar su.

Shi kuwa cikin rashin kula ya faɗa mishi za’a iya in yana buƙata, cikin zumuɗi yace dashi yana so, shi kuma yace toh ya bari anjima suje masarautar tare.

Kamar yadda ya faɗa da aka jima suka tashi don tafiya, masarautar ba tare da ɓata lokaci suka tafi.

Sun yi sa a ana ɗauka, haka aka ɗauki nazaan a matsayin mai share share.
Yayi kwana biyu yana zuwa har an fara sabawa dashi, yana ta nuna ɗabi’un arziƙi.

Kwanci-tashi yau kwananshi ukku, ya kuma tashi da son ɗauke zoben ko ta halin ƙaƙa.

Wani ɗaki da ya tabbatar shine ɗakin da zoben yake, ya bayyana jiki na ɓari yaga wani kambu, yana leƙawa yaga zobe, a gaggauce ya ɗauke ya kuma ɓace. Bayyana yayi gaban azla wacce take bisa tsun-tsun..

Kafin ya hau zoben yai haske, da mugun sauri azla ta fisge ta saka a jaka, dan a suffarta ta ainahi ta bayyana, shima ya koma nazaan ɗinshi, wata ƙara suka ji da hayaƙi kafin su ankare waɗan nan halittun sun dabai-baye su.

Gashi a ƙalla halittun zasu kai hamsin, kowa cikinsu na ƙoƙarin kai farmaki, cikin azama azla ta buɗe bakinta ta fesa musu wuta duk suka baje, cikin azama suka hau tsun-tsun su amma sai dai tun kafin su ida tashi sama wani halitta ya riƙe ƙafar azla, da ƙarfi halittun suka jawo su suka faɗo ƙasa tim, wani koren ruwa marar kyan gani suka watso musu, tuni nazaan ya fara tari azla ma haka, wani hayaƙi ne ya fito daga bakin azlar yayi kan su duk sai suka fara lullumshe idanu, da gudu suka miƙe suka sake hawa tsun-tsunsu, sun tashi sama cikin sararin samaniya kawai azla ta saki ajiyar zuciya, bayanta da zata kalla wannan halittar ne kwanche.

Wata razanan-niyar ƙara ta fasa tare da bugun tsun-tsun, kifewa yayi a sararin samaniya sun koma ƙasan bayan shi kamar an goya jariri an kwanta, rufe idonta azla tayi ganin sun fara yin ƙasa, kwata-kwaa dabara ta ɗauke mata bata yi yunƙurin dakatar da komai ba, nazaan ne ya lura da wani teku dake ƙasa kuma suna gab da faɗawa, da alama akwai tsayi da mugun zurfi, daga sama yayi toro ruwan sosai, bai kuma wuci su saka ƙafarsu ɗaya su faɗa baki ɗaya ba.

Cikin azama yayi amfani da ƙarfin ikonsa ya dakatar da hakan, suka tsaya ne chak babu mai motsi a cikin su dan motsi kaɗan zasuyi su zurma cikin ruwan hakan yasa suka tsaya ƙiƙam.
wata girgiza yayi tare da huro wuta sai suka dawo dai-dai tsuntsun ya lula sama da mugun gudu, wata wuta ya hura masa ya ƙara sauri, har suka bar ruwan kwata-kwata, wata tafiya suka chizga sosai, basu ƙara tsayawa ba har suka ƙaraso bakin wannan iyakar da suka bari.

Saukowa sukai suka ci abinci, suka lula cikin jeji sunyi tafiya sosai har suka cimma wannan ƙoramar.
Sun yi kwana sha huɗu suna tafiya, har suka ƙaraso jejen su na manaaj cikin farin cikin suka chi gaba da tafiya, har tsawon kwana sha takwas, lokacin ne suka ƙaraso ƙofar masarautar, ɓacewa sukai suka bayyana dai-dai inda zasu haɗu da Riyaad, haka suka isa gabanshi cikin farin-ciki, ya fara tambayarsu an samu nasara, basu ba bashi amsa ba face zoben da suka damƙa mishi a hannu ya kuma nuna tsananin jin daɗinsa, ranar aka chanza waɗannan mayun biyu da aka samar aka fara ƙoƙarin haɗa zoben. Saida suka ɗan kwana biyu sannnan suka fara haɗa zoben ta yanda zai zama mallakinsu har abada, cikin ɗan lokaci ƙalilan aka yi wani ƙaramin sihiri azla ta samu ciki! da wannan cikin ne mayun ƙasar suka fara nuna gajiyawarsu, dan yaƙi ne ya taso gadan-gadan babu kama hannun yaro.

Yaƙi ne ake ƙoƙarin gwabxawa na kirki a ƙasar YALAZ a koda yaushe mayun na cikin shiri cikin wata ukku aka gwabza yaƙin da aka zubda jinin mayu sosai ƙasar ta koma tamkar anyi gobara, yaƙin ya samu jarumai sosai duk da su nazaan da riyad da azla sun sha wahala amma ba’a ci galaba akan su ba, an samu mace-mace masu tarin yawa.

A wata na goma azla ta haifo santalelen yaranta mai wani irin kyau mai natsuwa, sosai nazaan yake cikin farin ciki wanda hakan yasa yayi ma mayun kyaututtuka, da basu ƴancina masu yawa, an kuma sami zaman lafiya.

Sai dai babbar matsalar da ta taso su gaba ita ce yaron sam baya jin magana tun yana da shekaru sha ukku aka fara samun muhimmiyar matsala, domin akwai ƙarfin sihiri sosai a tare dashi da kuma ɓanna ta babu gaira babu dalili.

Haka yasa mayun suka sake tada rigima kai Aliya na taƙaice miki saida aka sake yaƙi biyu sannan aka samu nasara wani, mashahurin boka ya samo wani sirri a wani teku, aka kulle nazaan aka kuma binne gawarsa a maƙabarta, itakam azla saida ta haifi yaranta ukku kafin suka samu galabar kulle ta dan ƴan ukkunta ba ƙananan mashahurai bane, sannan riyaad ma haka. Shi kanshi bokan ya mutu an binne sa a maƙabartar dan dama dole ne duk mayen da ya taka tekun zai mutu, daga lokacin ne aka yi sabbin masarautu biyu NAHAAR DA HIZAAR babu laifi suna kamanta adalci amma manaaj kam ɗan azla ne ke mulkarta, haka lokutta suka shuɗe har aka samu kwaɗayayyun mamulka suka hau banda zahir amma duk sauran kowa na ƙoƙarin haɗe masarautun gu ɗaya a chi gaba da mulka.

Wannan ne alilin da ya saka manaaj tafi ko wace masarauta, kuma tun bayan da ɗan nazaan ya hayayyafa, aka samu har zuwan su zahir.

Ajiyar zuciya Aliya ta sauke tace “Amma ya akai kasan tekun kuma yana ina?!.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sarrina 3Sirrina 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×