Skip to content
Part 5 of 24 in the Series Sirrina by K_Shitu

Numfashi yaja yace, “Aliyaa akwai wata sarƙa da na mallaka sai dai ba zan iya faɗa miki, inda na mallaketa ba zan baki ita idan kika saka, ki hau farin tsun-tsu zaku yi tafiya ta kwana biyu kachal sabo da ƙarfin ikon sarƙar bayan tafiyarki za’a kawo min farmaki, ke kuma zaki haɗu da wanda zai ceci rayuwarki. Sarƙar ya ɗauko ya miƙa mata, “Aliyaa kiyi ƙoƙarin gabatar da komai cikin gaggawa dan sauran kwanaki ukku a fara yaƙi, da zaki iya tafiya yau da kin tafi.” “Amma mai martaba fa?” murmushi yai irin nasu na manya ya ce, “Yaro yaro ne! babu wanda ya isa taɓa sarki Zahir yana da tsawon rai sosai, ya faɗa miki wannan maganar ne dan tabbatar da jarumtarki, dan haka ki kula matuƙa.”

“Ko zaki tafi kar kiyi gigin faɗa masa, dan zai iya dakatar dake ko wani ya saurari tattaunarku ya karɓe sarƙar daga gare ki, idan kin isa ga jazal ki ɗauko makullan kiyi Amfani da dafin tsafin manaan ki ƙona, tokar kuma kiyi kyakykyawar addu’a ta yanda ko da, sun dawo zasu kasance na gari, ba za’a zubda jinin kowa ba, sannan mahaifiyarki ita kanta zaa samu kuɓuta daga maƙiyanta, da suke gab da raba ta da wannan duniyar.” Cikin gamsuwa ta amsa masa, ta tashi da niyyar tafiya, yai saurin faɗin “wannan sarƙar a wuya zaki saka ta.” zaro idanu tayi ta ce, “Amma babu wanda zai ganta?.” jinjina mata kai yai, ɗaura sarƙar tayi, ta fice ɓacewa tayi bata bayyana ko ina ba sai ɗakinta.” Shiri Aliyaa take yi sosai, na san ran rayuwa ko mutuwa dan tana ji, a jikinta dawowarta MANAAJ za’a jima sosai hakan yasa take yin duk wasu abubuwa da suka dace.


MASARAUTAR JODHAN
Zaune yarima Aliyu haydar yake gaban malam surajo, bincike yake yi sosai, kafin ya ɗago duk ya haɗa gumi ya ce “Yarima Haydar! zuwa tekun jazal ba abu bane mai sauƙi, amma da yake Muslunci rahama ne zan iya amfani da inuwar taurarun wata Gimbiya da ta kasance a wata duniya itama zata yi tattaki izuwa chan sabo da, wata matsalar ƙasarasu dan haka itace zata iya tsinko maka ganyen bitir cikin sauƙi sai dai akwai matsala dan zata yi mugun rauni, za kuma takai tsayin lokaci tana ciwo sakamakon wannan abun da tayi.”

“Dan haka ya zama wajibi ka sanar da ita matsalarka da kuma taimakon da zata maka, idan kayi haka komai zai zo cikin sauƙi, sannan kaine zaka cece rayuwarta, dan idan ta chiro za’a yi girgiza mai tsanani da kuma wani ruwa, idan har aka yi ruwan idanuwanta zasu makance ko su samu babbar matsala, dan haka ka kula kayi addu’a sosai, Sannan akan abun da taje nema, za’a iya mayar da ita ko wace kalar halitta! mai haɗari, karka guje ta bayan ta chiro maka ganyen, dan a halin yanzu duk duniya babu wanda zai iya takawa chan sai ita, sabo da wata ɓoyayyiyar baiwa da take da ita.” Ajiyar zuciya ya sauke yace “Idan dai wannan ne nayi alƙawarin aikata komai da ya
dace, in Allah ya yarda.”


“Yarima zaku haɗu da hatsarurruka, da dama yayin tafiyar ka kula sosai….lokacin dawowarku akwai abubuwan da Zasu kusan taɓa ƙwaƙwalwarku, dan haka ku kula matuƙa.

Shiri sosai Aliya ke yi, bata bari kowa ya ganta ba hatta risha, ta chanza kaya ta ɗauki duk wasu abubuwan buƙatar ta, a ɓace gaban tsoho Arar a bayyana ya haɗa ta da wani fein tsun-tsun ta hau, yai mata fatan nasara, sannan suka lula cikin sararin samaniya, Ganin da malam surajo ya yi, Haske da inuwa sun bayyana yasa shi faɗin, Yarima kayi gaggawar shiryawa, Yanzu zata yi tattaki izuwa jazal, cikin sauri ya sauya kaya ya shiga sashe sarki Mansoor Ali Ya tabbatar masa da zai yi tafiyar gaggawa zuwa tekun ya amsa masa, ya yin da shi kuma ya tafi, wani Tsohon Aljani malam sirajo ya haɗa shi dashi ya bayyana tamkar tsun tsu, Aliyu haidar ya hau suka lula cikin sararin samaniya Aljanin kuma na bin inuwar Aliya.

Tun da suka doshi tafiya gadan-gadan jikin yarima ke karkarwa, abun ka ga ɗan adam sanyi ya masa yawa ga gudun da aljanin ke yi.


Aliya kuwa tun da suka nutsa cikin sararin samaniya, suke gudu sosai har biji-biji take gani tafiyar taƙi ci taƙi cinyewa.

Wata guguwa na dunfaro su, amma da sun kusa cinmata sai ta koma baƙin hayaƙi, haka suka chi gaba da tafiyar…

Sun jima suna tafiya cikin gajimare, kafin Tsun-tsun Gimbiya Aliyaa ya sauko ƙasa, gurin wani baƙin daji kwata-kwata ko hannunka baka iya gani, wani farin haske ne, ya fito daga idanun gimbiya Aliya ya ɗan haska jejin, kallo ɗaya da zaka yiwa dajin zuciyar ka tayi kyakykyawan bugu mai razanarwa, dan kwata-kwata jejin yafi shige da wata maƙabarta-maƙabarta ko kuma wani kurkuku ko’ina kukan halittu ne mai tsoratarwa ke tashi ga hayaƙi na fitoea fari wanda sai ka natsu zaka fahimci Hayaƙin da sauri da sauri yake fitowa wata jar ƙasa ce shimfiɗe jajir a ƙasa, sai korayen ciyayi da sun wani yi kaco-kaco ba kyan gani.
Ba tare da tsoro ko firgici da fargaba, ba Aliyaa ta fara nutsawa cikin dajin, wasu ƙananan dodanni ne baƙaƙe suka fara yo mata caa tamkar sun ga nama, Sama ta tashi a mamakinta suka saman suka tashi, hakan yasa ta furzo da wata hoda ja daga bakinta duk suka fara faɗowa ƙasa.


Cikin azama ta ci gaba da tafiya a sama, wasu korayen halittu ne masu kama da shaho, suka zagaye ta suna wani kuka da ƙarfi sosai, marar daɗin sauraro, jiri ta fara gani ahankali cikin jarumta ta ɓace, a maimakon ta bayyana gaba sai ta komo farko, tunowa da zanchen macijiya da tsoho arar ya mata ne ya saka ta duƙewa ta sunkuyar da kanta ta zama macijiya, ta fara tafiya sili-sili har ta kai gaɓar shiga kusan farkon dajin wani ƙaton icce ya ɓallo zai faɗo mata, cikin firgici tama rasa yanda zata yi kawai ta runtse idanuwanta, duk da macijiyar ƙarama ce sosai amma mai kyau, yarima Aliyu haydar da ya tare ƙaton iccen iya ƙarfinsa ya yi nasarar tunkuɗa shi gefe gudun kar ya faɗo.


Hannunshi ya kalla daya ke fitar da jini, bai bi takan hannun ba ya ci gabaa nutsawa cikin dajin, ganin ba wani hatsari kuma ya aliya bayyana a suffarta ta mutum, da sauri ta ci gaba da tafiya duk da ƙayoyin da take tajawa, tana jim raɗaɗi hakan bai sa ta daina tafiyar ba.

Cikin hanzari take tafiyar har ta wuce sa kamar walƙiya, duk da irin zafin naman da yasa, ko da yake ita tana da ƙarfin sihiri.


Tafiyar ce taƙi ƙarewa gashi ko kwatan dajin basu fara hangowa ba.

Chak suka dakata da tafiyar da suke yi,sakamakon ƙafafuwansu da suka ji wasu abubuwa sun kanannaɗe kamar majizzai kamar wata igiyar ƙarfe.
kamar kuma tsutsotsi masu kauri, abun sai nannaɗowa yake yana yin sama-masa, wani farin haske ya fito daga tafukan hannayenta ta haske dai dai ƙafar, abun ya zagwanye yai zube ƙasa ɗauri ya warware.

Cikin dakiya da kamewa ta tafa tafiya, yarima kam ganin ta samu kuɓta ya saka shima ya fara iya ƙoƙarin shi amma abun yaci tura, sai sama yake yi, har ya kawo gurin guiwar ƙafarsa. Chak ta tsaya daga tafiyar ta juya kanta a sunkuye, ta saka hannun shima abun ya warware, da hanzari ta ci gaba da tafiyar ta, tamkar ya bita amma izza da jin kai ya hana shi cikin basarwa ya ci gaba da tafiya da kuma zafin nama.

Sun jima suna tafiya Dare ya raba sosai baka jin komai sai koke-koken tsintsaye da gurnanin namun dawa masu haɗari.

Aliyaa na cikin tafiya, kawai wani tsun-tsu mai kama da shaho ƙaton gaske da fuka-fukai, ya damƙe mayafin da ta yane fuskarta, zuwa gashinta, ya fara kiciniyar tafiya da ita sama.

Lafiya lau kan shahon irin na mutane amma jikinsa daban, wasu zaƙo-zaƙon akaifu ya saka ya shaƙo wuyanta ya fara janta ƙasa.

Sarƙewa numfashinta ke yi fuskarta ta yi wani tsanwa-tsanwa tsabar fari duk da ba sosai ake ganin ita kanta Aliyar ba amma Yarima haydar ya hango abun da ke wakana.

Sai a sannan Yarima ya rarumo wani abu ba tare da ya san ko miye ba, ya wulla ma shahon a kai, sakin gimbiya aliyaa ya yi, ita kuma ta fara wani irin tari, yayin da kan shahon ya ara zubar da wani ɗorowan ruwan mai kauri da yauƙi.

Ɗan yatsa ɗaya yasa ya shafe gurin, ruwan ya tsaya gurin ya shafe, tamkar yanda yake da.

Tari sosai Aliya ke yi zuciyarta, tana zafi wuyanta na fitar da jini inda ya huda mata.

Ɗaga hannuwansa shahon ya yi, sama ya fara ɗago da su biyun sama, ba tare da ya taɓa su ba, sama-sama ya dinga ya dasu sai da yazo ssu gab shi, ya matse su guri guda da hannunshi ɗaya, yana ƙare musu kallo a yellow ɗin idanuwansa.

Dogon halshensa ya fiddo mai wani irin wari da ƙarni, ya nufo fuskokinsu dashi..

Cikin zafin nama ta fizgo hanunta haske ya fito daga tsakiyar tafin hannun ya haska shahon mai kama da dodo, sakin su yai ya ja da baya yana wani rin gunani da kuka ba daɗin sauraro, da sauri ta miƙe tana ci gaba da haska shin duk da ƙafarta da ta gurɗe saka makon yaddo sun da ya yi, Shahon girman shi da tsayin shi ya wuce duk yanda za’a fasalta ko a kwatanta. Wata Ƴar ƙarama ta koma sosai kamar ƴar tsana, akan shahon ɓacewa ya yi, ya bar hayaƙi gun da ya ɓace ɗin shi dai haydar kallonta kawai yake yi, ita ajiyar zuciyar ta sauke cikin azama ta karkaɗe jikinta, ta fara tafiya da sauri tana ɗingisa ƙafarta ga jinin da ya ɗan zuba a ƙafar dan ta taka wata ƙatuwar ƙaya.

Sai sannan ya gane lallai wannan ita ce wacce malam sirajo ya labarta masa suffarta, ta yaya ma zai iya tunkarar ta da wannan batun, tunowa da halin da Ammah ke ciki ne da ya yi ya saka shi, sauri bin bayanta da sauri.


Wani guri mai wani kalar santsi suka zo, a hankali suka natsu suna tafiya har suka kawo gaɓar wasu ƙattinan wawaka-wawakan ramuka masu tsantsar zufi da faɗi, babu wata hanya da zasu bi sai ciki, ɗaga kanta tayi tana ƙarewa saman kallo ko zata iya taki amma wasu fararen yanannaki ne masu wata kalar saƙa mai firgitarwa.

Da sauri ta ja baya tana ƙoƙarin faɗawa cikin ramin tsakiya, Shima da sauri ya yi baya. tana kallonsa ta wutsiyar ido, runtse idanuwanta ta yi ta faɗa cikin ramin. tare suka faɗa wani irin guri ne babu iska kwata-kwata hakan yasa numfashinsu ya fara, ‘ko’karin ɗaukewa.


Ƙasan wata ciyawa suka faɗo, da sauri suka miƙe suna shaƙar iska suka chigaba da tafiya.

Wata hanya ce ta rabe biyu, ɗaya dama ɗaya haggu, tsaya dukansu suka yi suna tunanin shin wace ya dace subi, Bata ɓata lokaci ba tayi ɓarin dama, shima abun da ke ransa ke nan hakan yasa ya yi damar.


Kukan kura suka fara ji na doso su, basu dakata ba suka ci gaba da tafiya, baƙar kura ce ta bayyana gabansu idnuwanta jajir tana wage baki, tana gurnani har sai da jejin ya amsa.

Tunkaro su ta fara yi, cikin zafin nama suka fara ja da baya, suna ƙoƙarin guduwa, ƙasar gurin mai haɗe da ciyayi da ƙayoyi suka fara rugurgutsewa, suna farashewa alamar zasu rabe. Rabewa ƙasar ta yi, ya zaman tsakanin su da kurar akwai ƴar tazara.

Hanya suka chanza daban, suka nufi haggu wani haske ne suka gani sosai, ga wani tanƙamemen gida, an zagaye shi da furrani da fulawoyi masu kyau da ɗaukar ido. Zuciyarsu ce ta fara fizgarsu da su shige kawai, A natse Aliyaa tasa hannu ta taura ƙofar ta sa kai ciki, turus taja ta tsaya ganin hayaƙi na fitowa daga ko wane sassa na gidan.

Wani ƙaton maciji ne ya far tafiya sil-sil, Ta bayanta ba tare da ta sani ba, bisa kanta ya hau ya biyo ta fuskarta zai wuce, wata iriyar ƙamewa ta yi ta ɗauke numfashinta har ya sauka.

Cikin gaggawa ta nufi ƙofar da niyyar buɗewa, wasu ƙananun macizzaine suka fara daddaɓeta da ƙyar tayi nasarar bankaɗowa waje.

Yareema haydar da yake zaune ya miƙe ƙafafu yana maida numfashi kawai ya ganta tamkar an hankaɗota. Macizzan ne suka fara fitowa masu mugun yawa dunƙule guda, da gudu suka kwasa daga shi har ita, bin su macizzan suka suma. mamaki ne ya kama haydar ashe dama maciji na da mahaukacin gudu haka.

Gudun ceton rai suke kawai, ga ƙaton macijin shima ya biyo su, ga tsananin tsayin shi, yana gab da cin masu.

Kwata-kwata dubarar amfani da ƙarfin iko bata zo wa Aliyaa, ba. ita tun da take bata taɓa makamancin wannan gudun ba, A rayuwarta.

Ƙaton macijin na ya zama rabin sa wanni halitta, daga kansa zuwa ƙugu, sauan kuma a maciji, hakan yasa ya ƙara ‘kaimi gurin gudun.

Sun mishi mugun nisa amma ganin wani, tafkeken rami mai duhun gaske da zurfi ya hana su saka ɗaga ƙafafunsu.

Ganin da suka yi saura ƙiris macijin babba ya cinmusu ya sa su, sadaƙaswa suka faɗa ramin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 4Sirrina 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×