Wani ƙaton kifi ne mai kama da shark ya biyo su, da gudu cikin ruwan yana wani wage baki yana hamma, cikin tashin hankali suka fara gudu na fitar hankali cikin ruwa, basu san sun iya ruwa irin haka ba sai yau.
Sun nutsa sosai, bigewa da dutsi yareema ya yi daga gefe, hakan ya tabbatar masa da sun zo wani gefe, dan haka da mugun Zafin nama ya fizgota suka mirgino waje. ban da numfashin wahala babu abun da suke saukewa su duka biyun.
Dafe kai Aliya ta yi dan ta tuno hutu ba nasu bane, a hankali a. . .