Skip to content
Part 7 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

Wani ƙaton kifi ne mai kama da shark ya biyo su, da gudu cikin ruwan yana wani wage baki yana hamma, cikin tashin hankali suka fara gudu na fitar hankali cikin ruwa, basu san sun iya ruwa irin haka ba sai yau.

Sun nutsa sosai, bigewa da dutsi yareema ya yi daga gefe, hakan ya tabbatar masa da sun zo wani gefe, dan haka da mugun Zafin nama ya fizgota suka mirgino waje. ban da numfashin wahala babu abun da suke saukewa su duka biyun.

Dafe kai Aliya ta yi dan ta tuno hutu ba nasu bane, a hankali a miƙe da ƙyar tana kallon ƙafarta babu abun da ya sameta, Numfashi ta sauke a hankali, sannan ta ci gaba da tafiya.


A nutse shima ya miƙe ya biyo bayanta, suka fara tafiya. tafiya ce suke yi sosai, basu sake tsayawa ba suna ta bi, a hankali gudun kar wani abu marar kyau ya sake faruwa.

Sun yi nisa sosai suna tafiya, wani ɗan gari-gari me mai haɗe da daji suka iso, daga ita har shi sannu-sannu suke bi, wasu ƙananan dodanni marassa kyan gani suka fara arba dasu, Suka yi wucewarsu ba tare da sun tsaya wani abu ba, tafiya suka ci gaba da yi, har suka iso tsakiyar ɗan garin, wasu bukko ki ne tsanwaye, babu gini kwata-kwata wasu daka-dakan donni saukai ta cin karo dasu amma ko wane da zarar ya gansu sai ya fara sunne kai ya chanza hanya kafin su waiwaya sun ɓace, duk da haka basu damu ba suka ci gaba da shan tafiya.

Wani ƙaton abu mai girma, ‘kato mai kama da buhu aka kifo musu daga sama, ya rufesu har ƙasa, cin azama dodannin suka janye ƙarshen ragar suje zuge, aka fara jan su ƙi-ƙi wata bukka aka nufa dasu aka shiga dasu sannan aka jefar dasu kamar kayan wanki aka jayo aka rufe.

MASARAUTAR NAHAAR
Cikin kiɗima da gigita Sarauniya Rahash ta fara gwada ƙarfin sihirinta akan Karan ɗin amma kwata-kwata ta gaza aikata mishi komai, izuwa lokacin jikinshi ya fara sauya launi, sai tsatstsagewa yake yi, wata wasiƙa ta gani ƙasa,cikin hanzari ta duƙa ta ɗauka, ta fara karantawa, ta sha mamakin ganin rubutun da jini, Aka yi shi. Jiki na rawa tsabar tashin hankali ta fara karantawa kamar haka, Hahhaha! na faɗa maka daman KARAN zaka yi mummunar nadama, zan makantar da kai zaka daina kallo har abada, Ina so ka sani ba a yaudarar SANAAM! sannan ina maka Albishir da, ka shirya tsayawa haka har ƙarshen rayuwarka, dan duk duniyar nan babu wanda ya isa ya warkar da kai, ko wane irin iko!! ba zai iya warkar da kai ba…_ Wata irin cimimiya ta yiwa wasiƙar tamkar wacce ta samu taɓin hankali, bata ankare ba ta fara jiyo wata irin mahaukaciyar dariya. ana faɗin; “Wannan somin taɓi ne daga Aikin Sanaam! zaku karɓi hukunci mai girma, dole Arman ya auri zulma dan duk wannan ɗin shiri na ne!.” “Ƙarya kike yi Ƙaramar Hatsabibiya! dole ne ki gurfana a gabana a ƙasƙance…”

Sanaam wacce take a saman iska ta ji, chakar kibiya tsakiyar zuciyarta, har ta ɓula wani baƙin jini ta fara fitarwa daga bakinta.


Sarauniya kanjam wacce take tsaye gefenta tashi sama itama a razane, kafin ta kai ga yin sama sosai Sanaam ta faɗo ƙasa yaraf.

Cikin tsananin ruɗu ta zube gabanta, tana ƙoƙarin zare kibiyar, sai dai kafin ta yi nasarar yin hakan Sanaam ɗin ta fizgo kibiyar da mugun ƙarfin inda jini ke ɗan zuba ya shafe bakin ta babu alamun ta sha ko ruwa bare jini ya fito.

Ta tashi sama da azamarta tana ƙyalƙyata wata muguwar dariya, daskarewa sarauniya Rahash ta yi, wani mugun Al’jabi ya bayyana kan fuskarta.

Wani haɗaɗɗen murmushi ta saki mai ƙayatarwa tana cewa “Rahash sai ki gaggauta zuwa dan ceton ɗanki, ARMAN.”

A gigice ta fara girgiza kai, Sannan ta fizgi numfashi da ƙyar ta ce “Zan dawo gareki…”

Cikin tsantsar kiɗima da ruɗu ta ce, “Sanaam duk ina kika samu wannan ƙarfin ikon?..” “Na daina goyon bayan ƙarya, zan tabbatar muku ni da na nema dena bin bayan ƙarya sabo da ni jinin ZAHIR ce!! dole zan dakatar da duk wani wanda ke ƙoƙarin ganin bayan ahalina, da ƴar’uwata Aliyaa….”
Da wani irin mamaki na wucin misali take duban sanaam. “Yau ‘ƴata ta cikina ta tsaya tana faɗa min magana ido cikin ido! sanaam anya ba musayarki aka min ban sani ba, maƙiyiyar Tawa Aliyaa kike ƙauna, tabbas wannan shine kuskure mafi muni da zaki aikata a rayuwarki!!”
Bata tsaya bata amsa ba, ta ɓace bat huci kawai Sarauniya kunjam ke saki cikin tsananin ɓacin rai, tabbas an zo gaɓar da zata cire ƙauna ta ganar da Sanaam kuskurenta.

Baiyyana Sanaam ta yi gaban Tsoho Arar kanta ƙasa cikin girmama ta gaishe da dashi sannan ta fara magana, “Dama Mai martaba ne ya turo ni na nemi afuwarka Akan abubuwan da na aikata maka waɗan da ba dai-dai ba.”

Murmushi ya yi cikin nuna Farin cikinsa ya ce, “Ai daman ban riƙe ku dan na san komai zai yuce, amma na yi mamakin chanzawarki farara ɗaya, mi ya kawo wannan chanjin sanaam?.”
Ƙara sunkuyar da kanta ta yi ta ce, “A lokacin da na fahimci tsawon kwanaki ukku Ƴar’uwata Aliyaa bata cikin manaaj, ga kuma matsanancin ciwon dake damun sarauniya sarah, sannan mai martaba na cikin tashin hanakali gashi ƴar’uwad Sahash aci amanata da saurn aminattuna, hakan ya sanya ni zaɓar bin bayan nagartattu, yanzu haka nazo neman afuwarka sannan ka bani magani na kai wa sarauniya Sarah”…

Maganin ya ɗauko ya miƙo mata, ta karɓa cike da ladabi “Ki kula Sanaam yanzu kece wacce magauta, zasu taso gaba dan haka ki kula da kanki sosai, duk abun da ya faru baya na gaarceki.” cike da murna ta amsa da “Na gode ƙwarai.” murmushi ya mata ta fice. Ɓacewa ta yi bata bayyana ko ina ba sai gaban sashen Sarauniya Sarah ta yi taku ɗaya biyu taji an fizgo gashin kanta ta baya, wani murmushi ta saki ba tare da ta jiyo ba ta ɗaga yatsanta ɗaya, Sahash ɗin ta faɗi ƙasa yaraf kamar marar lakka, ta bugu sosai cikin fusata ta nufi Sanaam da niyyar taɓa ta, tun kafin ta ida kai hannunta wani azababben shocking ya jata mai ratsawa cikin gangar jiki.

Tsabar raɗaɗin da ya ratsa ta sai da ta ga wata wuta fau ta gifta mata cikin fusata ta ɓace bata bayyana ko ina ba sai gaban sarauniya kunjam tana sakin wani irin huci mai zafin gaske.

Tun da aka Ajiye su Aliya ba’a kuma bi ta kansu ba sai da dare ya yi, daga ita har shi da ƙyar suke numfashi, gashi sun gaza aikata komai, banko ƙofar aka yi sannan aka ja su ƙii zuwa waje, sannan aka zazzage su gaban wata wutaa, ga wani ƙaton dodo rike da ƙatuwar takobi.

Ja da baya suka fara sai dai da sun waiga sai su kuma ganin shi a bayan nasu cikin ruɗewa suka fara ƴan zagaye-zagaye, ga duk dariyar dodannin marar daɗin sauraro ta cika musu kunnuwa.

Dandazon dodannin ne suka rufar musu aka rirriƙe su zuwan gaban babban dodan, wuƙar ya sanya cikin wuta ta jima sannan ya juya ɗayan ɓarin yana ƙoƙarin fito da ita, Runtse idanuwa Aliya ta yi tana karanto wasu kalar dalaasimai cikin zuciyarta, wuyanta ne ya fara haske dan haka ta watsar da duka dodannin, ta miƴe tsaye shima yarima ya miƙe, basu yi wata-wata ba suka ga sun ɓace bat.
Basu baiyyana ko ina ba sai bakin wani ƙayataccen wuri na gaban misali wurin ya kai ƙololuwar haɗuwa da kyau, ga ƙamshin wasu furanni dake tashi haɗe da, iska mai ratsa zuciya.
Tafiya suka fara a hankali har suka iso wani wuri da ruwa ke ɓulɓulowa ta ƙasa, mai haske ga ƙanƙara-ƙanƙara an zagaye gurin da wani baƙin jini da ya bushe an rubuta, *JAZAAL* cikin matsanancin farin ciki Aliya ta furta “jazaal!” jin hakan ya sanya haydar fahimtar wannan rubutun jazal yake nufi, dan bai iya gane da wani yare aka yi rubutun ba.

Duƙawa ta yi ta dangwalo ruwan sosai a hannunta, sannan ta watsa a wuyanta, duk da matsanancin sanyin haka ta jure sai a taga hayaƙi ya fito.
Basu ankare ba suka ji ƙasar gurin ta fara rugurgujewa, hakan ya sanya su faɗawa ba tare da sun yi wani yunƙuri, ba wani ruwa ne mai haɗe da ƙanƙara ya fara suka jisu cikinsa, wani azababben sanyi ne ya ziyarci ruhunansu mai shiga cikin ƙwaƙwalwa.

Kyarma suka fara cin Rauni idanuwansu suka rufe suka daina tantance komai, anfi mintuna goma a haka sannan sanyin ya koma wani irin zafi mai azabtarda gangar jiki.

Tsattsagewa jikin Aliya ya fara ko ina alamu an karce ta ko an yakushe ta, wani tsanwa-tsanwa jikin ke yi, cikin tsananin jarumta ta, ta tattaro sauran kuzarin da ya rage mata ta, matse wuyanta a ƙarfin gaske.

Ji kake zir famm….sun faɗa ƙasan ruwan chan ƙarshe, Wani wawakeken rami ne ta gani, ɗauke da wasu makullai masu haske da sheƙin gaske, a hankali ta sanya hannu ta ɗauka, wata irin rugurgutsa da juyi ruwan ya yi.

Wani ƙaton kifi ne ya tunkarota, wanda tun da take a rayuwara bata taɓa ganin irin shi ba ya kai girman wata kurar ƙatuwa, dumaro ta yayi yana wage bakinsa, Lumshe idanuwanta tayi a hankali ta riga ta sadaƙas sai dai, kafin ya haɗiyeta, wani tatsatsi ya wargaza sa babu abun da ya yi saura na kifin face jininsa.
Ɓacewa suka yi ita dashi basu bayyana ko ina ba sai cikin wani daji Mai kama da tsoguwar maƙabarta, jikin aliya duk ya yi rauni ko ina rauni ne a jikinta, gashin kanta ya wani kanannaɗe, idanuwanta a lumshe sunyi luhu-luhu.

Shima Yareema Haydar haka, cikin ƙarfin hali ya fara mas bayanin buƙatarsa, a kuma hatsarin ba tare da wani ɗar ba ta ƙarasa gaban wani ruwa cikin dauriya, sannan ta saka hannunta da iya ƙarfin ikon ta ta ciro *GANYEN BITIR* Wata irin tsawa aka yi da ta sanyata cije laɓɓanta sannan, ta miƙa masa cikin gaggawa, haɗe da danna wuyanta sarƙa ta bayyana ta fisgo ta damƙa masa.


Wani irin ruwa ne aka barke dashi na wucin gaban misali, cikin rashin sa’a ta ɗan buɗe idanuwanta, tare da damƙe sarkar, wani azababben raɗaɗi mai haɗe da yaji ne ya shiga idan nata wanda ya sanya zuciyarta da ƙwaƙwalwarta amsawa. Wani luu tayi zata faɗi yayi nasarar tare ta suka ɓace tare sai cikin sararin samaniya.

Sun daɗe suna ganin suna yawo kan iska, ita dai Aliya idanuwanta banda duhu ba bu abin da take gani, ta daina fahimtar komai banda tsananin raɗaɗin dake ratsata, babu abun da take ji ko take ganewa, Ƙarfen 11:25 na dare suka ƙaraso Masarautar jordhan, baiyyana suka yi cikin haɗaɗɗen katafaren sashin yareema Aliyu haydar, Babu kowa a parlourn ko ina fes amma tsit, a jigace ya wuce bedroom ɗinshi da ita akan kafaɗarsa, shinfiɗeta ya yi, ɗayan hannunsa riƙe da ganyen.

Ajiyar zuciya ya sauke jikinshi sai ciwo yake yi, kanshi na sarawa sosai, ga raunuka iri daban-daban a jikinshi duk ya kakkarce, ya taka ƙayoyi wani mugun abu ya cake sa amma tsananin fitina ya kasa jin raɗaɗi da azaba sai yanzu.

Ƙura mata idanuwa ya yi, yana ƙare ma kyakykywar fuskarta kallo, wani irin shauƙi ne ke ɗibarsa, ya rasa kalar wannan natsatstsen kyawun nata, mai samawa zuciya salama duk yanda ya ke ji da kyau aji izza amma yau yaga wacce ta kusa zarce shi. motsi ta fara da ƙafarta yatsun ƙafar suka fara mommotsawa idanuwanta, ta sake datsewa da ƙarfi sabo da irin azabar da take ji tana ratsa zuciyarta da ƙwaƙwalwarta.

A hankali ya tsaya daga gefenta ya sake gyara mata gashin kanta da ya barbaje, ya kuma rufe mata fuskarta kaɗan, kama hannayensa ta yi ta miƙe zaune. A.C ya kunna mata ƴar dai-dai sannan ya miƙe yana jin ƙyamar kansa dan ya san rabonshi da durzar fatar jikinshi har ya manta dan haka ya miƙe ya shige toilet, ruwa mai ɗumi sosai ya haɗa ya fara durje fatar jikinsa, kamar wanda ya yi wata bai yi wanka ba.

Ya daɗe yana wanka ya yi kusan sau ukku, sannan ya sanyo rigar wanka ya fito hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana ƙara tsane jikinshi, Tubakallah kyakykyawa ne sosai na wucin gaban misali, wani irin kyau gare shi irin mai sanyaya zuciya da kwarjini, Idanuwansa suna matuƙar tafiya da zuciya haɗe da ƙwaƙwalwar mutum suna rikita mutane da yawa da kuma ƴan mata, da ka

ganshi ka ga miskili na gaban kwatance, kuma mutum mai ji da izza.
Ganin yanda tayi tagumi duk da idanuwanta a rufe suke hakan yasa bai ɓata lokaci ba ya shafa mayuka masu kyau da tsada sannan ya fesa turarenshi mai sanyaya zuciya, lumshe idanuwanta tayi jin ƙamshi ya daki hancin ta, Army green ɗin jallabiya ya saka sannan ya iso inda take ya furta.
“Zaki iya yin wanka, ko na taimaka miki?” Bata bashi amsa ba sai turo dark pink lips ɗinta ta yi, sai da ya yi gyaran murya sannan ta ce “A’a ba zan iya tashi ba, ina ne nan?” jim ya yi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma ya ce “Masarautar Jordhan!” ba tare da ta bashi amsa ba ta miƙo hannayenta, ya kama sai sannan wani yanayi ya ziyarce su, a tare kowa yayi saurin kallon ɗan uwansa.

Lumshe idanuwansa ya yi jin wani ɗan shock kaɗan, miƙewa ta yi, sai kawai tayi tangal tangal zata faɗi ya riƙo ta suka faɗo kan gadon su duka, gashinta ya barbaje ya rufe fuskarta, hakan yasa yaji sha’awar gyara mata sannan ya ɗauke ta chak kamar ƴar baby ya nufi toilet ɗin da ita, Dama Aliya gwana ce fannin shagwaɓa da shegen san jiki dan haka ta riƙe sa gam ta kwantar da kanta saman ƙirjinsa.
Dire ta ya yi, ya haɗa ruwa mai ɗumi sannan ta ce “Ni zan fita kiyi wanka, ga towel nan na tsane jiki a gefen ki.” bata ce komai ba sai turo bakinta da ta yi, ficewa ya yi ya ɗaga waya ya kira malam surajo yana ɗagawa ya labarta masa komai, cikin farinciki ya ce, gashi nan tafe bai ɓata lokaci ba ya iso sashen dan dama tun da yareema yi tafiya ya tare a masarauta dan jiran dawowarsa.

Wani ruwa ne ya shigo dashi har ɓangaren nasu ya tsaya a parlour Haydaar ya kawo masa ganyen nan take ya sarrafa, ya miƙoma hardar ɗin yace “A dinga shafa mata a kanta kullum, in Allah ya yarda cikin kwanaki ukku zata warware.” jinjina kai ya yi ya ce, “Ina matuƙar godiya amma ita fa, yarinyar tana cikin ɗaki kuma bata gani sosai, wani ruwa ya miƙo masa da ɗan ɓallin ganyen ya ce, “Ka shafa mata a idanuwan zasu buɗe amma ka bata glass ta sanya sabo da haske da kuma idan suka shiga toh zata makance har Abada Amma zaka ga ta koma da tsoro da kuma wasu ɗabi’u na daban ka yi mata uzuri ruwan nan ne.”

Cikin gamsuwa ya karɓa ya yi godiya sannan ya shiga ya fito ya miƙa masa 3hundred thousand yace ya riƙe da su, haɗu in sha Allah zai cija babu kuɗi a gurinshi, ya amsa yayi ta godiya daga haka ya fice.

Komawa ya yi ya adana magungunan sannan ya nufi kitchen yana jan tsaki ganin kukunsa baya nan, Rasa mai zai haɗa ya yi dan haka ya ɗauko waya ya bugawa wani guard ɗin shi ya mishi ordern abinci mai kyau yana son pepper soup da chips daga haka ya kashe, jin shuru yayi yawa ya sa shi sadaƙaswa ya tura ƙofar toilet ɗin.


Yadda ya barta haka ya ganta, sai dai bacci ya yi awon gaba da ita, dafe kai ya yi ya isa yana ɗan tafa hannayensa firgit ta farka sannan ta wani marai-raice fuska, Ganin haka ya sa shi faɗin; “Wai tun ɗazu tsawon 30 mints ba kiyi wanka ba mai kike jira?.”

Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta ta mai daɗin sauraro ta ce “Ni fa bana ganin komai da zanyi wankan shi ya sa.” “Ya yi kyau zo kije ki kwanta haka.” bubbuga ƙafafuwanta ta fara yi tana faɗin ‘ni baan iya ba’ ƙaramin tsaki ya ja, ya ƙara ruwan ɗumi kawai ya ɗauke ta chak ya nufi kwamin waka ya fara ƙoƙarin cire mata doguwar rigar jikinta.

Cikin jin matsananciyar kunya ta riƙe hannusa ta ce “Yi ha’kuri zan kwanta haka!” ƙanƙance idanuwansa ya yi ya ce “hum yarinya jin makaro ni zan miki wankan., ko ki tsaya ko na barki ki kwana bayi macizzai su sare min ke.”

A tsora ce ta saki hannunshi ta wani turo baki gaba, cike da kunya ɗage rigar ya yi sama sannan ya cire ta baki ɗaya, wata irin halbawa zuciyarshi tayi sakamakon arba da ƙirarta, ita hannu tasa ta riƙe wata ƴar riga sharara da ta rage wanda ana iya hango ko wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fasaltuwa, take yaji wani irin mugun shauƙi na janshi, daurewa ya yi ya mazge kawai ya jan rigar itama sannan ya saka ta dukanta cikin bathtub ɗin mai ɗaukar mutane fiye da ukku dan girman shi gwanin burgewa tamkar sweeming pool.
Sake runtse idanuwanta tayi gam jin ta cikin ruwa masu ɗumi tsundu…, cikin wani irin yanayi ya kawar da kansa gefe ya ɗauko sabulu ya fara wanke mata jikinta cikin wano irin salo, har ya gama ya yi mas brush tan ƙanƙame a ƙirjinsa ta tusa kanta tsabar kunya duk ta jiƙe shi yana gamawa ya ɗaura mata towel ya fito da ita a hannunsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 6Sirrina 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×