Skip to content
Part 8 of 25 in the Series Sirrina by K_Shitu

Wata irin kunya take ji duk ta narke masa, dire ta ya yi saman gado yana hararta, sannan ya ce “Hala baki da suna”? ɗan turo baki ta yi ta ce “Toh ai baka tambayeni ba, Aliyaa kai fa?” Cikin ranshi ya maimata Aaliyaa a fili ya ce “Aleeyu Haydar.” Lumshe idanuwanta ta yi tana jin wani mugun bacci, mayukansa ya miƙo masa dan ta shafa, kallon man take yi cikin rashin fahimta, dafe kai ya yi ya iso gabanta ya fara shafa mata a hannayenta har gangaro cinyarta, haka ya yi ta shafa mata man man bayan ya gama ya nufi widrobe ɗin ya fara neman kayanda zai bata, ɗan tsaki yaja ya ya fito mata da wani boxes ɗinsa da jallabiya ya nufo ta ya fara kiciniyar saka mata, bai ɓata lokaci ba ya sanya mata sannan ya ɗauko abinci ya ajiye suka fara ci a tare.

Sosai Abincin ya yi mata mugun daɗi ta kasa daurewa ta dage ta cika cikinta tana al’ajabin wane irin abu ne haka mai shegen daɗi, Fresh milk ta sha, har saida ta shanye kwalba ɗaya, sannan ta yi gytsa ta marai-raice masa alamar ya ƙara mata harar ta ya yi tare da cewa, “Baki da ƙafafuwa ne? ki je parlour ki ɗauko man cikin fridge.” ɗan turo bakinta ta yi ta ce ”Miya falo firic kuma? ni ban san su ba.”

Dafe kai ya yi alamun ya soma ƙosawa fa zancen A daƙile ya ce “Me kike so”? Kwalbar fresh milk ta ɗaga masa cike da zumuɗi, hararar ta ya yi ya miƙe ya kwaso mata har ukku sannan ya ajiye mata bai ce komai ba, sa hannu tayi ta laluba ta buɗe da ƙarfi ta kwankwaɗe, sai da tasha mai isarta sannan ta aje kwalbar.

Taimaka mata yai ta dawo bisa gadon ta kwanta, cikin gajiya ya yi mata bayanin maganin da malam surajo ya bayar a kawo mata sannan kuma, da bayanin saka glass, ji ta ce ‘bata san miye glass ba ya sashi dafe kai, sannan ya ce “Zan baki shi ki saka, amma duk wanda yace ki cire ko da wasa karki cire dan zaki iya makancewa.” jinjina kai tayi alamar gamsuwa dan bacci take ji bilhakƙi.

Maganin ya shafa mata ya uamrce ta da kwanta ya aje mata pillow, ya ja mata blanket sannan ya fice, Palour ya koma ya kwanta bisa kujera 3seater sannan ya kwanta cikin natsuwa, ya kashe wutar ɗakin.

Kiran sallar farko ya farka daga nannauyan baccin da ya ke yi, idanuwansa sunyi wani iri sabo da gajiya da rashin isasshen barci. Bedroom ɗin ya shiga ya tarar da Aaliya kwance tana sharar bacci hankali kwanche, toilet ya shiga sharp-sharp ya yi wanka ya chanza jallabiya, ya fito ya kabbara sallah sai da ta yi raka’atainil fajir sannan ya yi nafila yai azkhar ya fara tashin Aliyaa.

Tana cikin barcinta mai cike da natsuwa ga tarin gajiya, kamar daga sama ta fara ji sassanyar muryarsa mai daɗin sauraro yana tashinta daga baccin da take yi, Tsunkulinta ya yi da ɗan ƙarfi kaɗan cikin mugunta jin taƙi ta tashi, A firgice ta farka tana buɗe idanuwanta, wani irin fayau take ganin komai, Sauke Lumasassun idanunta ta yi kan kyakkyawar fuskarsa, tana turo baki.

“Ki tashi ki je ki yi sallah.” a tsiwace ta ce “Bana yi”. ta faɗa ba da wata manufa tare da komawa ta kwanta, Taɓe baki ya yi yaja mata ƙofar ya fice masallaci cikin izza, tun da ya fito suka haɗe da mai martaba ya yi masa kyakkyawar runguma cikin tsantsar farin ciki da murna, Ya ta jera masa tambayoyi “Lion saukar yaushe? shine baka fara zuwa mun gaisa ba?.” murmushi ya yi ya ce, “Sorry Abbi Cikin dare ne jiyan shi ya sa, kuma bana son tayar da kai.” “Na fahimta zaki da fatan dai babu wata matsala ko damuwa ko?” ɗaga kai yai suka ci gaba da tafiya sabo da kar su makara.

Bayan sun gama sallah cikin masallacin masarautar ƴan’uwa suka shiga tururuwar yiwa Yarima haydaar barka da dawowa, cikin su har da ƙannensa maza biyu, sai ƙannin mahaifinsa da sauran mutanen fadar da abokananshi.

Tun kafin hari ya ƙarisa wayewa Kowa ya san da zuwar YARIMA ALIYU HAYDAR MAZAN FAMA! Yayin da maƙiya suka shiga tashin hankali marar misaltuwa, Kakarsa Hajiya Nafi wacce suke kira da hajiya ta shiga nuna farincikinta itama.

Abinci mai rai da lafiya aka shiga shiryawa masa, sai dai duk wannan abun dake aruwa Ammah na chan kwance, rai hannun mahaliccinta.
Duban haydar mai martaba ya yi bayan ya gama sauraron bayanin da yake masa ya ce, “Toh ya zaka yi da ita yarinyar”? kai tsaye babu wani ɗar ko shakka bare fargaba ya ce “I’ll marry her nd she will be come my wife my Princess! Amma ko wa ya tambaya zan faɗa mishi ita ɗin matata ce, dukda ba sonta nake ba amma sadaukarwar da tayi wa Ammah ya sanya zan taimake ta na aure ta, dan yi mata sakayya nd ina so wannan ya zama sirrin bana so wani ya san bana sonta in ba kai da Ammah ba, i hope you will be happy your highnest.”

Cikin tsananin farin ciki marar misaltuwa, ya ce “Da gaske kake Son?” tsadadden murmushinsa ya sakar masa wanda ba kowa ke ganin shi ba sabo da tsaar shi ya ce “Of course” Rungume shi ya yi cikin ƙaunar ɗan nasa ya ce “Naji daɗi ƙwarai da gaske haydaar! kuma ina wa gimbiyarka barka da zuwa MASARAUTAR JORDAN.”

Murmushi ya saki ya ce “Zan je gurinta, na barta ita kaɗai” daga haka ya nufi sashen shi, da isarshi har guards ɗinshi suna tsaya bakin ƙofar suna gadinta, suna da ƙiba da tsayi sun saka baƙaƙen kaya dukkan su sunbi da ba’kin glass, darewa suka yi suka bashi hanya, cikin girmama wa suka haɗe baki suna faɗin “U re highly welcome Our Prince!” Ɗaga hannu ya yi alamar amsawa sannan ya shige kukunsa Jameel ya gani sanye da kayan girkinsa ya ƙaraso yana gaishe shi ɗaga masa hannu ya yi kawai ya shige ciki.

Wayarsa ya ɗauko ya kira ƙaninsa yusuf bugu biyu ya ɗaga tin kafin ya ce komai ya tari numfashinsa a faɗin; “Good morning ya haydar!! wai ina ka je ne, i really missed you so much” “Morning! ina so yanzu yanzu ka fito da guards zamu fita s mall.” cikin zumuɗi ya amsa sannan dukkansu suka ajiye wayar.

Ficewa ya yi Ya tarar da motoci biyar jere a tsakiyar wani guard ya buɗe masa ya sa kai ya shige, gudu suke yi ba na wasa ba an sun san baya son driving ɗin wasa, Wani katafareb shopping mall suka ƙarasa na mutunci, unguwa guda da wasu ƙwayaye masu sheƙi da ɗaukar hankali aka rubuta PRINCE H SHOPPING MALL!! tun daga parking space ɗin zaka ahimci super market ɗin ta haɗaɗɗun jiga-jigan ɓasu kuɗi ce tsananin ƙawatuwar gurin ya wuce misali.

Shiga ya yi duka ma’aikatn suka fara rawar jiki wajen kwasar gaisuwa babu wanda ya yiwa magana face ɗaga hannu da yake yi, Umartar yusuf ya yi da ya jidi duk abun da yake so, cikin sauri ya fara kwasar kaya kamar me.
Ɓangaren kayayyakin mata ya nufa ya fara jide mata kamar ba zai biya ba, After dresses ne masu bala’in kyau da lifaya, gowns da ready made na traditional dresses, Saari, riga da wando Sleeping dress, jallabiyoyin mata, da sauran kayayyakin sawa, haka ya jidar mata inners pads, kamar bai san ciwon kuɗinsa ba, turaruka da hijjabai masu kyau sai mayafai da takalma high hills da flat duk ya kwasar mata da kayan kwalliya gold gold, su sarƙoƙi, zabbai, jakunkuna, man shafawa, sai glasses masu bala’in kyau da ɗaukar ido waɗnda basa bari a kalli ƙwayar idon mutum, sauransu sannan shima ya jidarwa kansa ƙananun kaya irin ɗaya da nata sannan suka nufi wajen biyan kuɗi shida ma’aikata biyun da suke riƙe da baskets ɗinsa, ATM ɗinshi ya bayar don su cire sai da suka koma suka sake ɗauko sauran baskets ɗin guda shia sannan aka tsaya dan fara lissafi, dan shi ƙa’idarsa ko da shi zai siya kaya sai ya biya, duk da Mall ɗin tasa ce.

Ganin za’a tsaya ɓata lokaci da lissafi ga kayan shi da na, Yusuf ya sashi bar musu ATM card ɗinshi dan sun san yanda komai yake, daga haka aka loda kayan cikin cars ɗin sannan suka tada damugun gudu zuwa masarauta…

Da mugun gudu motocin ke shigowa cikin masarautar, direct Sashen Yarima suka yi Yusuf ne ya shiga jidar masa kayan yana kai masa parlour har ya kammala, cikin Izza ya ɗauki trollies ya nufi bedroom dasu, ya fara kwashe kayan ciki yana jera mata a wardrobe, haka yaje ya kwaso ya jera mata duka, Tashin ta ya fara daga barci, a hankali ta soma buɗe kyawawan idanunta, masu rikitarwa cikin Rashin son magana ya ce “Ki shiga ki wanke baki, ki zo karya.” jinjina kanta ta yi shi kuma ya fice daga ɗakin baki ɗaya.

A nutse ta tashi ta shiga toilet ɗin, ta fara wanke bakinta, da brush kamar yanda ya yi mata jiya, sannan ta fito. Lokacin shi ya wuce ɓangaren Ammah Ta wata ɓoyayyiyar hanya, tun shigarsa ya fara mata addu’o’i sannan ya shafa mata maganin amma ko alamar motsi bata yi ba, hakan ya sa shi, dawowa ya fara cin Abinci bayan kukunsa bala ya zuba masa, fitowa ta yi daga ɗakin sai faman zare ido ta ke yi.

Ganin shi zaune bisa dinning yana breakfast, ya sanya ta saurin ƙarasawa inda yake, kujera ya ja mata itama ta zauna, sannan ya umarci Bala ya saka mata abinci, bayan ya kammala sanya mata ya tafi kitchen dan ya basu guri.
Bayan sun kammala cin abincin suka cin abinci suka shiga bedroom a tare dan ya fitar mata kayan da zata saka, wata baƙar jallabiya ce irin ta sa amma ta mata, ya fitar mata da dark brawn ɗin glass, sannan ya ajiye mata mayafi da inner wears, Duk ya nuna mata yanda zata saka kayan.

Shiga ta yi toilet ɗin ta yi wanka sharp-sharp ta fito, ya taimaka mata ta shirya cikin jallabiyar mai matuƙar kyau.

MANAAJ
Baiyyana Sahash ta yi gaban Sarauniya kunjam cikin tsananin ɓacin rai, sai huci take saki fuskarta ta yi jajir, golden eyes ɗinta har shining suke yi. Cikin kakkausar murya, ta fara magana “Kina ji kina ganin abun da sanaam ke aikatawa, amma ba zaki iya dakatar da ita ba”? Cikin hanzari ta miƙe tsaye, “Tabbas duk abubuwan da take aikatawa, ina sane, amma babu hannuna a ciki. ina jin ɓacin rai marar misaltuwa akan cewa SANAAM ce take da irin wannan ƙarfin sihirin ba ke ba, na yi iyakacin bincikena amma na gaza gano komai, dan haka shawarar da na yanke dole na sadaukar da ita ga baƙin maye, don cikar burinmu. ina da tabbacin zaki samu gano sarƙar da zata kai ki izuwa JAZAAL gargaɗin da zan miki shi ne, ki yi ƙoƙarin sarrafa fushinki. idan ba haka ba za’a samu matsala akan aikin, kuma ki sani ba ke kaɗai ke harin waɗannan masarautun ba, akwai wasu mayun bayan ke.”
Shu’umin murmushi ta saki, mai cike da ma’anoni sannan ta ce “Na rantse da abin da bautarmu, ba zan taɓa gazawa ba, akan cikar burina, na ɗau alwashin wulaƙanta rayuwar Aliya da Mahaifiyarta, wannan alƙawarina ne.!!”


“Na sani! zaki iya SAHASH ke ɗin ta daban ce ko a cikin mayu, hakan na ƙara samin tsantsar ƙaunarki a zuciyata. na miki alƙawarin aiwatar da komai dan cikar burinki.”

Kyakkyawan sumba ta sakar mata a goshi, “Ki shiryawa kwanaki takwas masu zuwa na , DAREN CIKAR JARIRIN BAƘIN WATA. zamu gudanar da namu aikin a cikin kwanaki biyar. gobe tsakiyar dare ki shirya fitowa don tunkarar baƙin maye, da buƙatarmu.”
Wani irin farin ciki ne ya dirar mata, jin kalaman Sarauniya kunjam ‘Karki damu Ummina zan aikatar da komai tare da kyakkyawar nasara!!’ murmushi ta sakar mata, daga haka sahash ta ɓace…

HIZAAR
“Anum A yau na baiyyana a gabanki, bisa ƙafafuna ina roƙonki, ki taimake ni na ɗauki fansa akan masarautar MANAAJ! nayi alƙawari ba zan taɓa yin yafiya ga Aliyaa ba, ina son na mallaki dukkanin masarautun, ina so ta zama ƙasƙantacciyar baiwaa a gareni! ina son na yi amfani da ƙarfin sihirina na mallaki masarautun baki ɗaya. ina buƙatar guddumuwarki, dan ɗaukar fansa akan ɗan’uwana Razaan da ya tsallake wannan duniyar tamu ya barmu sabo da ƙaunar Aliya.”

Wata mahaukaciyar sarauniya halsha ta saki, Lokaci ɗaya ta tsagaita ta dube shi duba irin na, da kyau yaro ta ce, “Na kasa yarda wai yau Tazaan ne a gabana yana roƙon, alfarma mafi soyuwa a gareni! kuma wacce na daɗe ina burin ya furta, ta a gareni, Ina maka albishir da na amince zan damƙa maka ragamar komai a hannayenka amma da sharaɗi…”

Tun kafin ta ƙarasa ya yi wata irin dariya da ta ke nuna tsantsar farin cikinsa ya ce, “Na amince da ko wane irin sharaɗi, zan aikata koma miye in dai akan muradina ne.”


‘lna son ka samo min RUWAN LU’U-LU’U!!’ “Kaɗai, shine abun da kike buƙata”? ɗaga mashi kai ta yi alamar eh, “To ki sa a ranki kin samu, dan wannan ba komai bane a gareni.” ƴar dariya ta yi ta ce “fatan nasara!!” Daga haka ya miƙe tsaye ya ɓace.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrina 7Sirrina 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×