Ranar Monday aka yi canjen aji, sannan da yamma aka nad’a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam.
Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d’in bata samu ba ne suke samun matsala da ita.
Duk da k’ok’arin ganin an zauna lafiya da Maryam d’in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d’aya suke room d’aya aji d’aya kuma seat d’aya.
Washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English. . .