Skip to content
Part 10 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Ranar Monday aka yi canjen aji, sannan da yamma aka nad’a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam.

Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d’in bata samu ba ne suke samun matsala da ita.

Duk da k’ok’arin ganin an zauna lafiya da Maryam d’in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d’aya suke room d’aya aji d’aya kuma seat d’aya.

Washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English theacher d’in ya shigo tare da wani kyakkyawan saurayi sanye cikin khakinsa na nysc, kusan duk matan ajin ido suka zuba mishi.

Har suka k’araso bakin board suka tsaya da shi da English teacher d’in idanunsu na a kanshi, shi kam bai ma san suna yi ba don idanunsa suna a k’asa yana kallon k’asa yayin da su kuma ko fahimtar bayanin English teacher wanda yake cewa “ga sabon copper shi zai dinga yi musu English a yanzu for 10 months, daga nan idan ya gama service d’inshi ya tafi aiki zai dawo hannunshi kamar farko” ba sa yi, har sai da ya ce “Are u guys with me??”

Da d’an k’arfi, tukunna hankulansu ya dawo jikinsu, suka ce “yes sir.”

Banda Zainab wadda tayi mutuwar zaune, dan a lokaci d’aya ta ji bawan Allahn ya tafi da imanin ta.

Kasancewar Madu da Bashir sun gayawa Malaman su su dinga zaunar da su sit d’aya ita da Maryam ya sanya a kodayaushe suna tare, haka nan wani lokacin zainab sai ta kawo jaka ta saka a tsakiyar su wai kar jikin Maryam ya goge ta ta kwashi bak’in jini, amman yau kam zainab bata san lokacin da ta kamo hannun Maryam da k’arfi ba!

Ita maryam d’inma tsorata ta yi dan kwata-kwata hankalinta baya ajin, ya tafi ga takardar da take hannun ta tanata bitar debate d’in da za suyi da safen nan, kawai ta ji an damk’o hannunta kamar za a karya ta.

Kallonta ta yi amman sai ta ga hankalinta gaba d’aya baya tare da ita, wani wajen ma daban take kalla.

Da sauri ta kalli inda zainab take kallo ta ga englishi teacher yana ta zuba bayani a gaban board da wani balarabe a gefen sa da koren kaya a jikin sa, dan haka ta juyo gareta cikin kulawa ta ce, “Zainab menene?”

Kallon ta zainab d’in ta yi sannan tace

“Maryam kinga wannan kyakkyawa ko?. Dama haka ake ji a lokacin da ka ga wanda kake so? kinji yadda k’irjina yake bugawa kuwa? haka kike ji idan kika kalli ya Usman?”

Wani farin ciki ne ya lullub’e Maryam dan rabon da zainab ta yi mata magana mai tsaho haka har ta manta, dan haka ta saki wani k’ayataccen murmushin da ya sake fito da ainihin kyawun fuskarta sannan ta d’ago kanta domin ta kalla wanda y’ar uwarta ta haukace a kai haka cikin lokaci k’ank’ani. Tana d’ago kan nata daidai shikuma English teacher ya mik’a masa chalk yana cewa “introduce yourself to them.”

Karb’a yayi sannan ya d’ago daidai ita kuma Maryam ta juyo tana murmushi a take idanunsu suka sark’e a cikin na juna! Bai san ya aka yi ba kawai ya ji chalk d’in dake hannunsa ya fad’i ƙasa! Lokaci d’aya zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri.

Itama Maryam kusan hakan ne a nata b’angaren, jin yadda zuciyarta ke bugawa gashi ya tsareta da manyan idanuwanshi farare k’al masu kama dana mai jin bacci, hakan ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta k’asa.

Maganar Mr Solomon ce ta dawo da shi daga duniyar daya tsinci kanshi a ciki dak’ik’un k’alilan da suka wuce.

Chalk d’in da ya yar yaga yana mik’a mishi sannan ya sake cewa “introduce yourself to your students.”

A hankali ya saka hannunshi ya karb’a sannan ya sake juyawa ya kalli inda Maryam take a ranshi yana adduar Allah yasa ta sake d’agowa ya kalli fuskarta, domin kuwa baya jin akwai abinda ba zai tab’a gundurar sa a duniyar nan kamar kallon fuskar wannan extraordinary beautiful young lady d’in ba.

Ganin tak’i d’agowa ne yasa shi juyawa, a hankali ya k’arasa jikin black board d’in ya rubutu sunan shi kamar haka, ‘YAKUBU UMAR FAROUK M.T’.

Sannan ya juyo ya kalli students d’in ya ce “that’s my name, but u can all call me ‘ABBA’. I’m your new English Teacher.”

Cikin nutsuwa ya karanto musu tsarinshi kamar ‘baya son surutu a aji sannan yana son in ya bada assighment a dinga maida hankali ana yi.’

Sai da ya gama tukunna Solomon ya ce “akwai debate d’in da ya basu as an assignment group A B and C”.

Sannan ya mik’a mishi textbooks d’in da suke hannunshi ya juya ya fita.

Cikin kwarewa da nutsuwa Abba yake koyar da su, sun nutsu kuwa suna fahimta sosai don duk hankalin su yana a kanshi, sai da ya gama ya ce “Ina masu debate?”

Maryam ita take representing group A, dan haka ta mik’e tsaye. A hankali cikin sauk’e ajiyar zuciya yake kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya mayar kan group leaders d’in B and C da suka mik’e sannan ya ce “su fito gaban board”.

Topic d’in yana magana ne a kan who is more responsible a karatun Yara
A, parents
B, teachers
C kuma both.

Maryam ita ce mai parents. Haka suka dunga mahawarar a tsakanin su har kowa ya kawo gabad’aya points d’inshi.

Points d’in da Maryam ta kawo ko kai sheɗan ne dole ka san ita ce winner!

Dan haka ya bawa group d’inta 10/15 ragowar groups biyun kuma ya basu 6.

Bayan sun koma seats d’insu sun zauna ya tambayesu ko “akwai mai question”, suka ce “a’a”hakan yasa ya tattare books d’inshi, ya duba time table yaga sai Friday shida ya sake shigowa ajin. Daga haka ya yi musu sallama ya fita.

Ai kuwa kamar jira suke yi yana fita kowacce ta hau tofa albarkacin bakinta, wasu su ce balarabe ne wasu suce d’an India wasu kuma pakistan, gashi daga ganin sa ka san d’an masu kud’i ne! Nan ajin ya haukace da zancen sa har sai da malamar next period ta shigo tukunna aka samu ajin ya nutsu da zancenshi.

Kafin kwana biyu, gabad’aya makarantar ta d’au zancen copper Abba balarabe (sunan da suka saka mishi kenan).

Hatta junior section ba’a barsu a baya ba, masu love letters suna yi suke yi su je su zira ta saman glass d’in motarsa inda yake d’an bari kad’an a zuge saboda iska ya d’an dinga shiga.

Zainab tun ranar da ta fara ganinsa ta haukace bata da labari sai na Abba, hannuta kuwa kullum da kalar design d’in da za ayi da biro a cikin heart d’in a rubuta ‘Abba’ duk inda kuwa aka ce Fridays Mondays ko Tuesdays (ranakun da suke da English kenan) haka nan za ta rambad’a kwalliya ta yi skipping assembly kuma, dan kar a goge mata.

Kamar yadda y’an makaranta suka haukace da ganinsa haka nan shima zuciyarsa ta haukace tunda ya ga Maryam.

Yau satin sa biyu da fara koyar da su kuma zuwa wannan lokaci kam ya gama fahimtar son Maryam yake yi domin kuwa tun ranar farko daya ganta ya rasa nutsuwar shi gabad’aya bashi da burin da ya wuce yayi ta ganinta, har Allah Allah yake ranar da zai shiga ajinsu ta yi ya samu ya sake sakata a idanunsa.

Through out this week ko me yake yi kawai tunanin ta yake yi. Ganin da yayi yana b’atawa kanshi lokaci yasa kawai ya yanke shawarar gaya mata in his next period, duk da kuwa yana fargabar mai amsarta za ta kasance, duba da yanayin k’arancin shekarunta amma kuma ya san ‘a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.’

Yau Monday!! kasancewar Abba ba’a staff quarters yake da zama ba, gida ne guda mahaifin shi ya siya mishi saboda service d’in da aka turo shi. Ya sanya ya tashi da sassafe dan baya son ya makara, kuma akwai d’an tazara tsakaninsu da makarantar.

Har yayi wanka yayi breakfast yana murmushi jifa jifa shi kad’ai, kawai idan ya tuna zai ganta yau sai yaji wani farin ciki ya lulllub’eshi .

Duk saurin shi kuwa sai da aka gama assembly tukunna ya samu ya zo.

Zainab yau sneaking ta yi ba ta je assembly ba saboda ta shafa jambaki da powder ga kwalli ta saka kuma ta san indai aka ganta to punishment ne bayan an sakata ta goge.

Y’an aji suna fara shigowa suka ganta a zaune, wata classmate d’insu ce tace “wato yau sneaking kika kuma yi ko?Hmm bai ma fa san kina yi ba! Dan ko kallon ki ba ya yi.”

Dariya tayi kafin ta sake cewa “to shadow sai ki rubuta sunan y’ar uwarki, a cikin masu sneaking in dai ba son kai bane abun”.

Ta yi maganar referring to Maryam.

Ko gama zama ba su yi ba Abba ya shigo ajin hakan yasa zainab ta had’iye masifar da ta taso mata take shirin juyewa classmate d’in tasu tahau murmushi tana kallonsa.

Cikin dabara ya kalli wajen zaman Maryam yaga tana goge wajen zaman ta da duster kafin a hankali cikin nutsuwarta ta zauna sannan ta fara yiwa Zainab magana a hankali.

Ajiyar zuciya ya sauk’e a hankali sannan ya amsa gaisuwar da suka shiga yi masa.

Bayan ya kammala duk abunda ya kamata ya ce dasu “su ciro takarda zai yi test”.

Hakan kuwa aka yi. Lokaci yana cika ba tare da ya b’atawa kanshi lokaci ba ya kalli Maryam ya ce “ta tattare gaba d’aya papers d’in ta kai mishi office.”

Sai da ya ga fitarta tukunna ya bi ta a baya.

Jin kamar mutum a bayan ta yasa ta juyo, ganin shine ya sanya ta d’an tsaya sai da yayi gaba tukunna ta bishi a baya saboda daman ko taje Admin d’in sai tayi tambaya tunda ba sanin office d’insa tayi ba.

Office d’inshi kusan shine na k’arshe a jerin k’ananun offices d’in da suke wajen, suna zuwa ya saka hannu cikin aljihun wandon shi ya zaro key ya bud’e ya tura ya shiga sannan a hankali ya ce mata “Bismillah”

Sallama ta yi ta shiga office d’in d’an k’arami ne, sai dai ya had’u sosai, sai
k’amshi yake fitarwa, ga wata k’ofa a gefe wanda tanada tabbacin toilet ne.

Maganar sa ce ta dawo da ita daga duniyar k’arewa office d’in nasa kallo data tafi, jin yana cewa, “Zauna mana, ga seat.”

A hankali ta ajjiye takardun a kan tebur sannan ta girgiza kai ta juya za ta fita taji ya ce, “I order u to sit.”

Sai da tayi kusan 1 minute sannan ta zo ta zauna kan kujerar da take facing tashi benci ne kawai a tsakaninsu.

Sai da ya d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “from which state are you ?” “Kano” ta bashi amsa.

“Which area??”

“Gandun Albasa”

Ta fad’a a tak’aice.

“Are u sure?”

Yai mata tambayar kafin ya ce “cos banga alama ba, at all”

Da mamaki ta kalle shi, kafin ta ce “U too”, sannan ta mik’e ta ce,

“Please sir zan tafi muna da test.”

Mik’ewa shima yayi yana murmushi kafin yace “sai yaushe? Ba kiyi mini kwatancen gidanku ba balle in kawo miki ziyara idan an yi hutu, ko ba kya so in zo???“

Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’.

With surprise ya ce

“Y”

“Nothing”

Kawai ta iya ce mishi sannan ta sunkuyar da kanta k’asa, tana adduar Allah yasa ya bata izinin tafiya, dan bata san daliliba in dai suna waje d’aya ji take tamkar zuciyarta za ta
faso k’irjinta ne ta fito waje, tsabar bugawa.

Abba fahimtar da yayi kamar yana yin komai cikin sauri, kar kuma yaje ta k’i shi idan taga zalamarshi, hakan ya sanya ba dan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi ba kawai ya bata izinin tafiya.

Ai kuwa da sauri ta juya ta fita a office d’in.

Zama yayi a kan kujerar sa, sannan ya bud’a hannunshi kafin ya kaisu duka biyu bayan k’eyarsa kamar zai yi filo da su.

Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya fara tunanin duk wani possible hanya da zai b yayi getting close to her, dan ya lura he needs her attention first.

A bakin Admin block d’in ta ci karo da Zainab tana ta faman kai kawo, tana hango ta kuwa ta iso tana tambayarta inda office d’in nashi yake, kwatance Maryam d’in tayi mata daga haka tayi gaba, bata san ya suka yi ba.

A b’angaren Abba kuwa, a da ƙarfe 2 yake tashi ya tafi gidanshi, amman yanzu voluntarily ya yi exceeding time d’inshi har 10 pm (Time d’in tashi daga night prep) ko tsoron hanya baya yi, haka nan ya cewa mai principal kawai zai dinga supervising evening and night prep, Friday kuma zai samu aji ya dinga k’ari a sms. Da murna kuwa principal d’in ta yarda, dan ya ce ba sai an bashi ko sisi ba.

Kasancewar Maryam shadow ce ya sanya ba a ajin su take night prep ba, a jss2 take zama tana supervising d’insu.

Tana zaune kawai ta ji kamar an shigo tana kallon k’ofa kuwa suka yi ido biyu, kujerar teacher ya janyo ya kawo dai ‘dai gefen sit d’inta ya ajjiye sannan ya zauna kafin ya ce mata

“Good evening ma.”

Da sauri ta kalle shi sai kuma ta yi k’asa da kanta ta ce “evening sir.”
Murmushi yayi kafin ya ce “na takura ki ko?”

Girgiza kanta kawai tayi ta ci gaba da karatunta.

Jifa-jifa yake mata hira har aka tashi.
Tun daga ranar kuwa haka kullum zai shigo ajin da sunan supervising zai yi
amman su daya kamata ace sun hana yara surutu har a tashi bakin Abba baya yin shiru na minti goma.

A haka har aka yi sati. Yau friday Maryam tana ta murna ba zasu had’u ba atleast zuciyarta sa ta huta da bugawa da take yi.

Sai dai kuma tana zuwa sms d’in ta ganshi a bakin gate na main mosque yana tarar y’an makara, ai kuwa ganin tazo a makare ba k’aramin dad’i ya yi masa ba, sai da ya bawa kowa punishment sannan ya juyo ya fara tanbayarta “mai yasa ta makara bayan tana matsayin shadow?”

Uzurinta ta fad’a mishi, maimakon ya barta ta tafi ko yayi punishing nata, instead, sai kawai ya hau tambayarta ajin da take. Yaso ace itama d’aliba ce amman sai ya ji tace “ajin y’an Izu 60 take koyarwa, thou he was amazed.”

Ganin zata makara sosai ya sanya ya barta ta shiga taje wajen d’alibanta.
Sai da ya samu ajin da tabarmarsu take facing tata tukunna ya ce su zai koyar.

Idan ana maganar ‘nacii!!’ To shi Abba yake yiwa Maryam, tun bata sakewa da shi har ta fara, dan ya iya labarin ban dariya, sannan yana burgeta, thou har yanzu bata gama sanin ma’anar bugawar da zuciyarta keyi idan suna tare ba. A haka aka shafe 3 weeks.

Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep yana bata labarin mahaifinsa tana ta mamaki saboda ita dai ita da Mahaifinta they are like best friends sab’anin shi dan a yadda yake bada labarin Mahaifin nasa kamar wani boss na horror movie, he is not even close to him kwata-kwata, kuma wai a haka duk cikin y’aya’ansa yafi sonshi, saboda ya ci sunan mahaifinsa ne.

Hayaniyar wasu yara ne ya juyo da hankalinsu suna waigawa kuwa suka ga ana dambe! Da sauri ta tashi ta isa wajen, shima ganin hakan yasa ya biyota, garin k’ok’arin raba damben d’ayar Yarinyar jin an rik’e hannunta ta d’auka y’an class d’insu ne nan ta buge hannun Maryam d’in da k’arfi!! wanda bai sauk’a a koina ba sai a kan louvers na window kuma daman a fashe yake, nan da nan kuwa ta yanke jini ya fara tsiyaya.

Abba bai san lokacin da ya finciko Yarinyar ya wanka mata marin da har sai da ta fad’i kasa itama gefen bakinta ya fashe, sannan yayi sauri ya kamo hannun Maryam, ganin jini ta koina yana zuba duk ya ma rud’e bai san lokacin daya kama k’asan rigar shaddar jikinsa ba ya yaga ya kamo hannun ya d’aure da kyallen sannan ya fara janta yana cewa “ta zo su tafi clinic, a dubata.” Duk ya rikice, dan har kwalla Maryam ta hango ya taru a idanunsa.

Suna fita suka had’u da prep mistress d’in hakan yasa suka d’unguma har ita aka je aka yi mata dressing, a tafin hannuta ta yanke amman Allah ya taimaka ba’ai mata d’inki ba. Har suka je suka dawo yana jera mata sannu ko motsi tayi sai ya tambayi “mai takes o?” Har bakin unity gate ya rakata tukunna ya juya dan a lokacin an tashi daga prep.

Kusan bai samu ya yi ishashhsen bacci ba, juyi kawai ya dinga yi yana Allah Allah gari ya waye.

Allah ya taimaka ma washegari za ta kasance Tuesday ne, so yana da su har double period.

Kamar kullum yau ma Zainab tayi kwalliyarta suna zaune suna jiran shigowarshi, yau kamar da rashin mutunci ta tashi dan sai hararar Maryam take yi, tana fama yada mata magana har da cewa “ idan ma za ta ware gara ta ware tun wuri dan ba abinda za ta taya ta da shi.”

Ita dai maryam ta yi shiru tana fama da zugin da hannunta ke yi mata, ga idanunta da suka yi jaa, dan jiya bata samu isheshshen bacci ba.

Shigowarsa ce ta sanya ajin yin shiru kowa ta maida hankalin ta gare shi, shi kam yau k’arara kowa sai da ya lura da kalar kallon da yake yiwa Maryam dan tunda ya shigo daga bak’in k’ofa ya kafeta da idanu har ya isa inda bench d’inshi yake, garin kallon ta ma har da d’an yin tuntub’e.

Ganin tak’i d’agowa ta kalle shi yasa kawai ya amsa gaisuwar y’an aji sannan ya fara lesson.

Dictation ya fara kamar kullum dan baya musu note a board amma yaga Maryam d’in ta kasa yi, k’ok’ari take yi ta rubuta da hannun hagu amma ta gagara, ganin tana neman fama ciwonta ga ciwon kan da ya addabeta yasa kawai ta tura littafin gefe ta kifa kanta a benchi.

Abba kam zuwa yanzu ji yake kamar ya kori gabadaya y’an ajin ya lallasheta, ganin gabad’aya hankalinshi baya ajin kar yaje ya fara musu dictating shirme yasa yayi rounding up, sannan ya ce “akwai mai question?”

Mutane uku ne suka yi question ciki harda Zainab tana ta faman karairaya, shi bai ma san tana yi ba, ya bata amsa daga haka ya ce “Let’s call it a day”.

Sai a lokacin Maryam ta d’ago ta juya ta tambayi wata classmate d’insu ta ara mata note d’inta, bayan ta mik’o mata ta had’a da nata ta ajiye a kan bench, duk a kan idonsa. Har ya yi hanyar fita sai kuma kawai ya dawo ya d’auki littafin nata da na wadda ta karb’a za ta kwafa d’in, ya juya ya fita da sauri.

                 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 9So Da Buri 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×