Kamar yadda Baba Bashir ya rok’eta akan ‘ta rabu da Abba’ hakan take k’ok’arin yi.
Dan ko da a ce bai fad’a ba tabbas ba zata sake bi ta kan Abba ba, tayiwa kanta wannan alk’awarin! Ya ga soyayyar ta yanzu kuma zaiga fushinta In sha Allah ko shine autan maza ta hak’ura da shi.
Abu d’aya ne wanda Maryam ta yi domin Abba shi ne ‘sakawa y’arta suna Huda’ da tayi saboda shi, dan tun lokacin da take boarding school indai suna hira ya kance “idan Allah ya basa y’a. . .