Skip to content
Part 20 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Kamar yadda Baba Bashir ya rok’eta akan ‘ta rabu da Abba’ hakan take k’ok’arin yi.

Dan ko da a ce bai fad’a ba tabbas ba zata sake bi ta kan Abba ba, tayiwa kanta wannan alk’awarin! Ya ga soyayyar ta yanzu kuma zaiga fushinta In sha Allah ko shine autan maza ta hak’ura da shi.

Abu d’aya ne wanda Maryam ta yi domin Abba shi ne ‘sakawa y’arta suna Huda’ da tayi saboda shi, dan tun lokacin da take boarding school indai suna hira ya kance “idan Allah ya basa y’a mace zai saka mata suna ’Huda’ saboda yana matuk’ar son sunan, idan kuma Namiji ne zai saka mishi ‘Aslam’. Zai barta ta zab’i duk sunan da take so a duniyar nan amman lak’abin ya zama Huda ko Aslam.”

Da matar Yayanshi ta haifa mai sunan shi shiyasa ta zab’i lak’abin ‘Aslam’ yanzu kuma ta sakama yarinyarta suna Maryam ana kiranta da Huda ba dan komai ba sai dan kawai tasan ba a tab’a chanjawa tuwo suna, tana so wannan ya zama last abu da zata yi mishi a matsayin sa na Mahaifin Hudan.

Baya ga haka! Duk wasu memories na Abba k’ok’ari kawai take yi ta goge su, ta samu ta cire sa gabad’aya daga kanta har abada.

A lokacin data dawo Sadiya shiri take yi da ita sosai, musamman ma data lura da yadda y’ay’anta suke son Maryam d’in da Bilkisu, idan zata tafi yawonta haka nan zata kwaso su ta kawowa Maryam d’in suyi ta wasa suna d’ebe mata kewa, dama ita Maryam tana da son Yara sosai suma suna sonta, musamman ma Jalila wadda a lokacin da Maryam ta dawo shekararta 1 yanzu kuma tana shirin rufe biyu. Har sati Jalila takan yi a wajen Maryam, sunanta ta fara kira a duniya kafin ma na Mahaifiyarta! Tun tana ce mata ‘miya’ har ta fara ce mata ‘mama miya’ daga baya ta koma ce mata ‘Mama’ kawai.

Shak’uwa ce sosai ke a tsakaninsu, ana yaye ta kuwa Maryam duk da a lokacin tsohon ciki gareta, haka Jalila ta dawo wajenta dan tak’i yarda da kowa sai Maryam d’in.

Yanzu kuwa da Sadiya taga auren Maryam ya mutu!! Gashi ko idda babu a kanta, tun daga lokacin taje ta d’auke Jalila, su Junaidu suma ta hana su kula Maryam d’in sai dai suyi a b’oye.

Tashi d’aya Jalila duk ta bi ta rame kullum cikin kuka take tana cewa “ita wajen Mama zata tafi amman furr!! Sadiya ta hana. Dan zuwa wannan lokacin ko gidan taje ba kula Maryam take yi ba sai dai idan ita Maryam d’in ce ta kulata tukunna za ta amsa da kyar shima kuma ciki-ciki take amsata ba tare da ta kalli ko inda take ba! Idan kuwa iyaka su biyu ne a guri tofa in Maryam zatayi mata magana sau goma ba zata kulata ba!

Duk akan Mijin da bata sani ba shi tun lokacin da Maryam ta dawo yake ta addua Allah ya bashi ikon raba aurenta da Abba! Ranar kuwa da Abba ya saki Maryam a gabanshi suna gama gudun famfalak’in karnuka bayan sun dawo gida ya cewa su Madu idan ta fita idda shi har yanzu yana sonta!

Ranar da ta haihu kuwa shi so yayi ma a d’aura musu aure a ranar! Sai da su Baaba Talatu suka yi masa da gaske! Tunkunna ya hak’ura.

To yanzun ma ya sake tada balli. Hakan yasa kawai su Madu suka yanke shawarar d’aura musu aure amman Baba Bashir ya ce “zai fara tambayar Maryam d’in tukunna, tunda ita yanzu bazawara ce basu da hurumin zab’a mata Miji.”

Shi dai Madu bai biye Baba Bashir d’in ba ya tashi ya fita yana mai ce masa “idan yayi fixing date ya fad’a masa zai bayar a sanar a masallaci! Dan shi kam ya gama zab’awa Maryam Usman.”

A b’angaren Maryam kuwa duk yadda ta kai ga k’in Ya Usman bata isa tace ‘a’a’ ba a gaban Mahaifinshi wanda yayi mata gata! Bai duba yadda ta gudu ta sanya d’anshi a garariba haka ya rik’eta kamar komai bai faru ba!

Shiyasa yana zuwa mata da maganar tashi d’aya ta amince nan take.

A cikin sati d’aya aka gama komai aka d’aura auren Usman Bashir Da Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu ashirin lakadan ba ajalan ba.

Murna a wajen Ya Usman a wannan rana abun har sai da ya bawa wasu mamaki!!! Sadiya kuwa daman b’oye musu auren aka yi.

Ranar taje wajen Baba Laraba suna hira kawai taji ana d’aura aure a masallaci, tun a lokaci ta fara hauka kamar tab’abb’iya! Tana cewa “Maryam ta ci amanarta, dan haka wallahi sai ta koya mata hankali!.”

Tun lokacin take hauka kwata kwata ya ma k’i ta saurari kowa, babu yadda Baaba Laraba bata yi akan ta tsaya ta nutsu ba amman tak’i! Ko y’ar kissar nan ma ta mata ita kam ta kasa kwatantawa.

Tsautasayi ya kaita bayan an kai Maryam ta shiga har d’aki kafin Ya yaman ya shigo, wai sai ta yi mata duka!! Ita kuwa Maryam ta tare ta!

Dambe suka fara gadan gadan daidai Ya Usman yana turo k’ofa ita kuma Sadiya tayi sa’ar kifawa Maryam mari a kan idanunsa!

A zuciye ya k’araso, sai da yayi mata Mari kwarara guda uku!! sannan ya k’ara mata da saki biyu daman ya tab’a yi mata d’aya! Hankali a tashe! Sadiya ta fara bashi hak’uri, ita kanta Maryam d’in ta tsorata dan bata yi tunanin wannan hukuncin a Sadiya daga wajen Ya Usman ba duba da Yaran dake a tsakaninsu.

Ganin da Sadiya tayi ba zai saurareta ba yasa ta mik’e ta zari mayafi ta nufi wajen su Madu. Duk inda aka bi aka duba babu aure a tsakaninsu! Idan ma zata koma to sai tayi wani auren, kuma da sharad’in ba na kisan wuta ba.

Tana gama idda wani gurgu ya fito mata. A nan bayan layinsu Amaryar sa take amman shi yana Sumaila da Matansa biyu. Bata wani damu ba ta amince bayan ta fito k’iri-k’iri ta gaya mishi auren kisan wuta take so suyi shi kuma ya amince.

A lokacin nuna mata yayi ya amince aka yi shirin komai, ranar da aka d’aura aure iyayenshi suka zo suka tafi da ita Sumaila, bayan da farko ce mata yayi a kano zata xauna dan kayan d’akinta ma d’akin daya nuna gefen na Amaryarshi a nan aka jera mata.

Haka nan ta tafi Sumaila ta bar kowa nata daga ita sai Jalila suka tafi.

Bayan sati biyu ya zo da kansa ya kwashe kayan jeren ta aka kai mata Sumaila aka jera wasu, dan kusan rabin kayan karshe sai siyarwa tayi saboda ba zasu shiga d’akin ba.

Sadiya bata tashi sanin Garbati yaudararta yayi ba sai ranar daya fito mata a mutum yace mata “shi fa ba zai saketa ba!” Jalila ma data taho da ita cewa ya yi “ba zai rike ba” haka nan tana ji tana gani aka karb’e Jalila aka dawo da ita gidan Babanta wajen Maryam bayan shi ga nasa y’ay’an guda goma sha takwas kuma duk ranar girkinta sai ta girka musu abinci ta basu.

Sadiya taci kuka ranar da aka karb’e Jalila kamar ranta zai fita! Ita kuwa Jalila murna ma ta dinga yi ta dawo wajen Maman ta.

Maryam duk wani kulawa haka ta had’a yaran nan guda hud’u take basu kamar ita ta haifesu duka, Jalila ta taso da k’aunar Huda a ranta dan babu wadda takeso kamar Huda! Abu kad’an ‘k’anwata’ komai ita dai k’anwarta, ko abu ta ci a makaranta sai ta rago ta kawowa k’anwarta.

Lokacin da aka saka Huda a makaranta kuwa taga gata wajen Jalila da Junaidu wanda tun a lokacin Junaidun yake cewa “shi kam ina ma ana auran k’anwa to da zai auri k’anwarsu Huda”. Gata kala-kala ba wanda baya nuna mata, ita ma Jalila yadda take ji da Huda kamar tsoka d’aya a miya! In ka tab’a Huda to ko d’an gidan uban waye kai sai taje har d’akin uwarka da jibgeka, dan one thing about Jalila bata da kunya kuma ba ta da tsoro ko kad’an! Dan ma Mama tana taka mata burki.

Ya Jaafar ne kawai baya shiga harkar Hudan sosai, saboda shi daman chan akwai shi da son girma kuma miskiline na ajin k’arshe. Shekarunsa suna d’an yin sama ya daina yi musu dariya ma kwata-kwata, ko
hira ake yi haka nan shi sai dai ya shige d’aki.

Shiru-shirun sa ya fara damun Mama dan haka ta saka mishi ido, ai kuwa nan ta gano ashe yawan baccin da yake yi shaye-shaye yake yi tuk’uru.

Hankalin Mama ba k’aramin tashi yayi ba dan a lokacin kwata-kwata shekarun Jaafar 15 kuma koma ba dan ta shekarun ba shaye-shaye ba abu bane mai kyau. Shiyasa ta dage ta tsaya tsayin daka da addua da komai da kyar aka samu ya shiryu ya daina.

Tsakanin Maryam da Ya Usman kuwa! Soyayyar sati uku kawai ya nuna mata bayan aure daga nan ya birkice ta kasa gane kansa. Haka kurum sai ya tisa ta a gaba wai sai ta fad’a mishi wa tafi so tsakanin shi da Abba! Wasu lokutan a rana d’aya sai ya buka’ceta sau hud’u idan ya ga dama ko sama da haka a cewar sa ‘sai ya yi wanda yafi na Abba yawa!’

Gabad’aya wadansu irin abubuwa yake yi marasa ma‘ana wanda sam ta kasa gane kanshi kwata kwata.


LTabbas Ya Usman yana sonta ta yarda da hakan amma wasu lokutan har hanata abinci yake yi wai yana so ta ji yadda yaji a lokacin data gudu ta barshi dan a wannan lokacin har kwana hud’u ya sha yi bai ci abinci ba.

Hanyar gidansu Abba kuwa ko waye nata a arean bata isa ta bi ta je ba, ko dubiya ne ko kasuwa taje in dai yaji labarin sun wuce ta hanyar gidansu Abba to sai tayi sati tana shan azaba a hannunsa. Babu abinda ya fi sosa mata rai kamar yadda Ya Usman yake nunuwa k’iri k’iri kaff a fad’in duniyar nan babu wadda ya tsana sama da Huda! Haka kurum sai yayi ta kyarar ta yana hantarar ta, wani lokacin har duka! Tun Hudan bata gane ba har ta gane, dan sai da ya zamana ko muryarshi ne idan taji da gudu haka zata shige d’aki.

Hakan ya sanya hatta Jalila da Junaidu da suka fahimta suma sai daina kula shi, har sai da Maman ta gane ta bud’e musu ido tace “basu isa gaba da Mahaifinsu ba”, tukunnan ba yadda suka iya suka sak’k’o amma idan yana yiwa Huda abu wani lokacin har kuka suke yi.

Lamarin Ya Usman ya kai idan gida akwai mai suna Abba to zai hana Maryam mu’amala da y’an gidan kwata-kwata! A cewarsa wai ‘da gangan take zuwa gidan saboda idan an kira sunan Abba ta dinga tuna Abba…’

Abubuwa kala-kala dai, tun abin yana damunta har ta hak’ura ta rungumi y’ay’anta ta yaye lamarin shi a kanta.

A bangaren Sadiya kuwa sai da tayi shekara 9 tana shan azaba a hannun Garbati, k’arshe ma rufe mata baki yayi ita da iyayenta suka daina neman saki a wajen shi, Allah ma ya taimaki Sadiyan bata yarda ta haihu a gidan shi ba saboda dama ta ce ‘bata ga guri ba!’.

Su Jalila sukan je su dubata su kai mata kayan abinci da zannuwa, da farko da Maryam suka fara zuwa amman tun zuwan farko da ta saka Yara suka yi mata ihu shikenan Ya Usman da yaji labari ya hanata zuwa kwata kwata.

Sai da zama ya kare tukunna Allah ya karb’i ran Garbati a hanyar shi ta zuwa Niger (minna) ganin Mahaifiyarsa.

Yaranshi ne kad’ai suka yi kukan rashinsa amman matan sa da y’an unguwa har ga Allah murna suka yi domin kuwa kai tsaye zaka kira Garbati da mai mugun hali gashi duk wani hali na mugunta ya sani ya kware a kai.

Tana gama idda ta fara yiwa Usman zirya. Haka kurum za taci kwalliya ta ta zo gidan wai ta zo ganin y’ay’anta! Shi dai Usman ba ma ya bi ta kanta dan ya ce ‘daman a rashin Maryam ne ya hak’ura ya zauna da ita!’.

Idan tazo gidan ta dinga habaice habaice kenan, ko Jalila ba kulata take yi ba sai Maryam tayi da gaske tukunna suke gaisheta, Jafar ne kawai yake biye mata.

Ana cikin haka aka yiwa Mijin Zainab transfer shima ya dawo Kano, lokacin Yaranta uku mata biyu Aisha (momy) da khadija sai auta muhammad, itama da yake malamar makaranta ce sai ta nemi transfer aka kaita makarantar mata ta nan gandu take koyarwa.

Ai kuwa tun daga nan duniya ta yiwa Mama zafi, domin kuwa k’awancen Zainab da Sadiya sake k’ulluwa yayi da yake itama Zainab d’in nan kusa Mijinta ya kama haya ba nisa, dan haka kusan kullum suna tare.
Haka nan za suzo gidan suyi ta neman ta da fad’a! Ita dau ba kula su take yi ba.

Bilkisu a lokacin Yaranta biyu. Itama ta kammala karatunta na law tana aikin ta! Kowa dai da y’ar sana’ar shi ko wani means of samun kud’i dan hatta Sadiya business d’in kaya take yi, amma ita Maryam a duk lokacin da ta ce tana son yin karatu ko sana’a tashi d’aya Ya Usman zai ce “a’a!!
Salon tayi kud’i ta gujes a!.”

Ranar da abun ya isheta daman ko kayan sallah baya yi musu ita da Huda idan ka gansu kullum cikin tsumma, Baba Bashir da Baba Talatu ne suke dan k’ok’artawa suyi musu sai ko Bilkisu, hakan yasa ta d’auki waya ta kira Baba Talatu tana kuka tana gaya mata. Ashe Shuwa na gefen ta a lokacin suna tare Baba Talatu batayi auni ba taji Shuwa ta karb’e wayar!

Maryam zata iya cewa ta manta rabon da taji muryar Shuwa amma maimakon magana mai dad’i sai kawai Shuwan ta rufeta da fad’a ko gaisuwarta bata tsaya amsawaba, tace hau fad’a tana cewa “Ai ta riga tabar gini tun ran zane! Lokacin da su Zainab da Bilkisu suka yi nasu karatun a lokacin da ya dace ai ita saurayi tabi, sai yanzu god’ai god’ai da ita ne zata wani ce tana so zata koma makaranta??!.

Kawai ta zauna idan Usman d’in yaga dama yayi mata to, idan kuma bai yi mata ba ta hak’ura, sannan tama daina k’ok’arin had’a kanta ‘jahila! Mara aikin yi! Da su Bilkisu masu ilimi masu aikin yi dan in dai tace haka zata yi to kuwa wahala zata sha!..”

Tana gama fad’in haka ta kashe wayar.

Haka rayuwa taci gaba su Shuwa ko k’ofar gidansu har yau har gobe sun hana Maryam zuwa ballantana Huda, ko Bilkisu ta je gani idan emergency ya taso sai dai su had’u a waje ko a gidan Baba Bashir.. Sunce ‘ai tun ranar data saka k’afa ta bi Abba suka cireta a matsayin y’arsu, su bama su da ita ba.

Ana haka rana d’aya kawai Usman Ya mayar da Sadiya aka d’aura aure.

Da farko su Baba Bashir sun so hanawa amman yadda ya nuna kamar idan bai auri Sadiya a ranar ba to tabbas zai iya mutuwa! Ne ya sanya kawai aka d’aura musu aure ta tare.

Tun daga wannan lokacin kuma Ya Usman d’in sai ya zamana kamar irin tsoron Sadiyar ma yake yi, baya son ganin b’acin ranta baya iya hanata abu.

Tana dawowa gidan ta janye y’ay’anta duk wahalar su da Maryam ta ci ba a yi shekara uku ba gabad’aya hankali Jalila ya koma kan Mahaifiyarta, tun bata kulata har ta fara kulata daga baya data gane uwarta kuma sai ta fara yiwa Maryam rashin kunya da rashin mutunci kala kala tun bama data lura da Maryam d’in bata so a tab’a Huda ba, nan ta samu abun yi.

Saboda ita aka cire Huda daga makarantar islamiyyar da suke yi aka chanjamata boko kuwa sai da suka san yadda suka yi k’iri k’iri aka hanata zuwa.

Junaidu tun yana dukan Jalila har Sadiya ta bud’e mishi ido ya daina.
Haka kurum sai su rufe Huda da duka babu laifin tsaye babu na zaune..

Maryam bata samun sauk’i a kaf fad’in duniyar nan sai in tana karatun Alqurani ko kuma idan Bilkisu da yaranta sun zo. Sakina itace Babba watanni uku Hudan ta bata amman irin Yaran nanne masu garin jiki
shiyasa ta zama kamar ma ta girmi Hudan, sai k’anwarta Sumayya.

Sakina irin yaran nan ne da basa barin takwana, takan zo wasu lokutan tayi weekend a gidan itama Hudan takan je musu, amman fa duk ranar da Sakina tazo sai an kwashi y’an kallo ita da Jalila duk da kuwa Jalilan mugun duka take yi mata amman takanci nasara itama akan ta itama wasu lokutan.
Akwai ranar da suka yi wani dambe! Jalila tayi mata duka ita kuma da taji zafi ta rarumi dutse ta bugawa Jalilan a kai wanda har saida ya kaita ga suma.

Ya Usman da Sadiya kuwa suka d’aukowa Sakina y’an sanda, su kuma y’an sanda da son banza suka zo zasu tafi da ita. Suna shirin sakata a mota kenan daman Babansu ya taho d’aukarsu kuma Mama ta kirasa dan haka ya k’araso a rikice.

Ya ji haushin abun sosai dan haka fad’an ya koma na manya akai baram baram da shi da Ya Usman.

Tun daga nan suka hana Yaran su zuwa gidajensu.

Shiyasa ko lokacin da Bilkisu ta ce zata d’auki Huda Shuwa ta hanata a cewarta ba zata bari matsalar Maryam ta shafi aurenta ba.

*****

Mama bata ji shigowar Sakina da Ummu ba, dafa ta d’in da
Ummu tayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.
A hankali ta juyo gareta tana kallonta fuskarta sharkaf da hawaye.

Numfashi Ummu ta fesar kafin ta tsugunna a gabanta sannan ta shiga share mata hawayen har sai da taga tayi shiru tana sauk’e ajiyar zuciya.

Motsa hannun da Huda ta yi ne ya katsewa Ummu maganar da take shirin farawa.

.A hankali take bud’e idanuwanta da suka chanza kala suka k’ank’ance.
Tana gama bud’ewa hawaye suka shiga zubo mata.

Rad’ad’i take ji har yanzu a wajen da Ya Ja’afar ya daketa da katako ga ciwon kan da take ji kamar zata mutu!

Sakina ce ta hau kan gadon ta zauna ta wajen kanta kafin ta kamo hannunta ta kuma shiga share mata hawaye tana cewa “ta yi hak’uri tayi shiru karta k’arawa kanta ciwon.”

Da kyar dai itama Hudan tayi shiru. Bayan Likita ta shigo ne ta chanja mata d’aurin ruwa sannan ta yi mata wasu allurai ta ce “ba zai yiwa sallame su yau ba sai dai gobe”

Kasancewar dare yayi sosai hakan ya sanya Mama ta lallab’a su Ummu suka wuce gida. Ya junaidu kam sai da ya tabbatar sun kintsa ya nemo musu duk abun buk’ata tukunna ya wuce
shima.

Washegari da sassafe su Ummu suka zo musu da breakfast, bayan sun biya gidan Hajiya sun ajjiye Sumayya dan itama jikin nata sai a hankali.

Kamar jiya yau ma har dare Ummu tana wajensu, saboda zazzab’in da ya sake lullub’e Hudan ya sanya likitocin suka fasa sallamarsu aka kuma k’ara mata allurai masu nauyi da magunguna ta wuni tana barci. Sakina Ummu ta sake aikawa taje gida tayo musu girki ta dawo. Suna zaune wajajen 8 daman kamar Mama ta sani tana ta cewa Ummu ta tashi su tafi sa dawo gobe amman tak’i! Kawai sai ga kiran Hajiya Shuwa, Ummu na d’auka ko gaisuwarta bata amsaba ta hau zazzaga mata bala’i tana cewa “taya zata tafi ta bar mara lafiya haka!?

Tabi duk ta wani d’aga hankalinta akan wata Huda, koma meye ya sameta ai sune suka jawa kansu!
Tayi maza ta dawo yanzun nan idan ba haka ba ranta sai ya b’aci!”.

Sarai Mama taji abinda Hajiya tace saboda wayar Ummu irin mai volume d’in nan ce amman sai ta nuna kamar bata ji ba. Ummu kam jikinta duk yayi sanyi ko tambayar jikin Huda Hajiya bata tsaya yi ba tace a taho a barsu su suka sani.

Haka nan dai jiki duk ba kwari, ta d’auki jakarta bayan ta tabbatar ta biya komai kuma tabar musu isheshshen kud’i a hannu da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo In sha Allah.

Suna shirin fita Junaidu kuma yana shirin shigowa da ledoji a hannunshi. Gaisawa suka yi da Ummu sannan yayi mata sai da safe ya shigo. A gefen gadon wajen k’afafunta ya nemi waje ya zauna bayan ya gaida Mama.

A hankali yake kallonta yana jin wani zafi a ranshi kafin yace mata “ya jikin?”. Sai da ta gaisheshi bata damu da rashin amsawar shi ba tace masa “da sauk’i”

Shiru d’akin yayi babu mai cewa komai kafin a hankali Hudan tace “Mama zan yi sallah.” “To”
Maman tace sannan ta mik’e ta fara k’ok’arin d’aga Hudan wadda azaba tasa ta fara yin wani kuka mara sauti abin tausayi.

Runtse ido Junaidu ya yi kafin ya ce “Mama idan ba zata iya ba gara kawai a nemo kwano da ruwa, tayi alwala anan tunda daman yanzu jikin nata zai yi tsami sosai.”

Hakan kuwan aka yi da kyar ta iya zama sannan ta samu tayi alwala tayi sallar.

Bayan ta idar ne ya janyo ledojin da ya shigo dasu ya fara bubbud’ewa.

D’ayan fresh milk ne da su maltina, sau d’ayan kuma gasassun kaji ne mai yawa, da zafin su sai maik’o da kamshi suke yi.

Mik’ewa yayi ya d’auko plate da cup, kazan ya fara zuba mata kamar rabi, har ya d’auko fresh milk zai zuba mata sai kuma ya d’ago manyan idanuwanshi ya kalleta ya ce
“Me zaki sha??” Cike da jin kunya, dan ya kamata tana kallon kazar daya zuba matata nuna mishi Maltina.

Murmushi yayi sannan ya ajjiye fresh milk d’in ya d’auki Maltina ya zuba mata kafin ya sake mik’ewa ya dawo kusa da ita ya ajjiye plate d’in akan cinyarta, cup d’in kuma a kan drawer gefen gadon, shi kuma ya tsaya a kanta kafin yace “Bismillah”.

Har ga Allah so yake yad’an zauna kusa da ita amman kuma yana jin kunyar Mama.

Da kyar ta iya cin rabi, daga nan tace masa “tak’oshi” dan ji tayi cikinta har ya cika taf! Amma da farko lokacin da yana zubawa kamar ta ce masa ya juye duka.

Gyara tsayuwar shi yayi sannan yace “ko ta cinye ko ya d’ura mata!”

Ba yadda ta iya haka ta dinga turawa saida yaga tana k’ok’arin yin amai tukunna ya kyaleta.

Gabad’aya Mama itama a takure take, kayan kunya da nauyi duk ya kanainaiyeta.

Har ga Allah idan aka tsareta ba zata iya nuna makusa guda d’aya a tare da Junaidu ba. Yaron yana da hankali, gashi yayi karatun shi yanzu haka ma masters yake yi, part time.

Yana kuma sana’a dan yana da zuciyar nema, sanna ta san yana son Hudan tsakaninsa da Allah sosai.

To amman matsalar d’aya ita ce iyayen shi, da ace Junaidu ba d’an Sadiya da Usman bane ba da ita da kanta zata tsaya tsayin daka ya auri Huda.

Tsakanin d’a da uwa sai Allah dan ta d’auki lesson akan Jalila, duk runtsi wata rana dole yabi maganar Mahaifiyar shi kuma itama Hudan dole ta yiwa Sadiya biyayya tunda uwar Mijinta ce, ta san Huda ba k’aramin wahala zata sha a hannun Sadiyar ba.

Ita kuwa tana ganin wahalar da Huda ta sha daga yarintarta kawo yanzu ya ci ace ta samu kwanciyar hankali a gidan aurenta!

Apart from all this ma, ta san Sadiya da Usman ba za su tab’a yadda da auren ba sai dai wani tsananin rabo.

Sallamar Baba Bashir da Baaba Talatu ce ta katse mata tunaninta, ta yi saurin d’agowa tana kallon k’ofa.

                   

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 19So Da Buri 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×