Skip to content
Part 24 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Successfully, Kaka da Baba Talatu suka amince da batun makarantar Huda, Kaka shi ya sanar wa Madu wanda shima bai hana ba bai kuma ce taje ba kawai dai ya jinjina kai alamar ya ji kuma ya fahimta.

Kaka ne ya yanke shawarar Hudan ta tafi gidan su Ummu tayi koda sati ne, bayan ya kira Baba da Umma da Jalila yayi musu fad’a sosai!! Sannan ya cewa Jalila “tunda y’ar daba take son ta zama kuma iyayenta sun kasa tsawatar mata to ta tabbata tana gama ssce d’inta ta fito da Miji idan ba hakaba to zai bada hotonta a masallaci duk wanda ya zo kuma shi zata aura koda kuwa gurgu ne!.”

Jalila kuka wiwi haka suka baro gidan Kaka, Umma sai mita take yi wai ‘anyi son kai!’ Idan ba haka ba dan maiyasa ba a yiwa Sakina fad’an dukan da ta yiwa Jalila ba?!.

A Daren ranar da su Ummu suka koma gida suka samu takardun Sakina itama har sun zama ready.. Duk wani preparation na exams d’in yi suke dan Arshaad har wata lesson teacher ya d’auko tayi musu isashshen lesson ranar asabar da lahadi wanda da farko shi yaso yi musu lesson d’in amman sai aka tura shi wani aiki Abuja sai monday da yamma tukunna zai dawo.
Sakina tana fahimtar lesson d’in sosai amman Hudan kam sai dai godiyar Allah, matsalar da aka samu shine ita lesson teacher bata jin Hausa ita kuma Huda turancin sai a hankali.

Sai da ya zamana duk abinda lesson teacher ta fad’a sai an mata translating da Hausa! Duk k’ok’ari da hak’uri irin na matar sai da ta k’ule a cikin kwana biyun. Da kyar Hudan ta tsinci iya abubuwan da zata iya tsinta ranar Litinin kamar yadda aka fad’a Baban Sakina da Ummu suka kaisu makarantar domin su zana jarabawar.

Hudan har kusan kukan murna tayi da taga jarabar tasu zab’i ka tik’a ce! Saboda daman adduar da take ta yi kenan. Sai dai kuma duk da hakan
da kyar da sid’in goshi ta iya amsa question biyar a cikin guda d’ari biyun da take tunanin ta gane wanda hakan ya d’auketa sama da awa d’aya.
Tayi kokari wajen ganin ta amsa ragowan dan bata so ace ta fad’i jarabawar nan tana mugun son tayi karatu a rayuwarta amman kwata kwata sai ta kasa. Har kuka tayi a exams hall d’in, bata ankara ba taji ana cewa “20 minutes remaining!!” idan ta fahimta sauran minti ashirin kenan a tashi! Hakan ya sanya
kawai ta rufe idanunta ta karanto sunayen Allah ta nemi nasara da sa’a sannan ta d’aga pencil d’inta ta fara sheding, duk shed d’in da zata yi sai ta kira sunan Allah tukunna ta tik’a…
Haka tayi daga Ar Rahman zuwa As Sabboor, ta sake dawowa Ar Rahman a haka har ta gama wanda yayi dai dai da fara amsar takardun nasu.
Sai da ta tofe takardarta da addua tukunna ta bayar invigilator d’in yana ta tsokanarta.

Kasancewar y’an hall d’in su Sakina sun rigasu shiga yasa tana fitowa suka had’u da Sakina a k’ofa tana jiranta.
Sakina na ganinta ta k’araso da murnarta tana cewa“Hudan jarabawar tayi sauk’i ko? kinga duk abinda malamarnan ta koya mana kusan duk sun fito, kamar ta sani.”

Da mamaki Hudan ta kalleta kafin tace “Tab! Ni fa biyar kawai na gani irin wanda tayi mana, a maths d’in kuma naga irin wannan mai kamar triangle d’in wanda kika sake koya min da daddare dayawa amman duk sun chanja nambobin.”

Lumshe ido Sakina tayi a hankali sannan ta bud’e, kafin tace mata
“Ai numbers d’in kawai suka chanja, kin dai yi ko?”. Hudan bata b’oyewa Sakina ba ta gaya mata yadda tayi..
Jikin Sakina duk sai yayi sanyi amman gudun kar ta sace mata guiwa ya sa kawai tayi ta bata kwarin gwiwa.

Suna shirin wucewa aka ce “kowa ya tsaya akwai d’an guntun orientation da za ayi musu, babu isheshshen lokacine amman da it’s sopposed to be for weeks..” Haka nan suka d’unguma aka fara orientation d’in. Ita kam Huda zuciyarta duk a dagule, bare ma da aka fara orientation d’in nan ta sake ji makarantar ta shiga ranta, duba kuma da abunda ta rafka a exams d’in duk sai hankalinta ya sake tashi.

Sai da aka yi rounding up sannan suka kama hanyar inda su Ummu suka yi parking, Hudan har da y’ar kwallarta,
da kyar Sakina ta d’an lallasheta ta bata kwarin guiwa tukunna aka samu hankalinta ya d’an kwanta.

Suna zuwa nan ma Ummu da Baban Sakina suka shiga tambayarsu, ita dai Hudan k’arshe ma kuka ta saka, dan gani take yi kamar har ta fad’i ne, sai da su Ummu suka yi ta bata baki tukunna ta hak’ura tayi shiru.
A haka dai duk jikinsu yayi sanyi jin Hudan bata yi wani abun kirki ba, suka k’araso gida.

D’aki suka wuce ita da Sakina sai da suka yi wanka suka shirya suka yi waya da Mama sannan suka fito suka ci abinci suka d’an yi hira da kallo sama sama isha nayi kowa ya nufi gado. Ranar Hudan bata yi bacci ba kwana tayi tsayuwar dare tana rok’on Allah yasa suci jarabawar nan.

Washegari ma da safe haka ta tashi duk jiki ba kwari har dare, kamar jiya yau ma bata yi bacci ba, kwana tayi tana sallah.

Haka ta kasance kullum, itama Sakina daga baya tayi joining d’inta a sallar daren, a haka aka yi sati.

Ranar litinin da yamma sai ga Arshaad ya zo. Su bama su san yazo ba, suna falo suna kallo, sun gama waya da Mama kenan! Wayar Baban Sakina ta shigo layin Ummu, d’auka tayi suka yi magana bayan ta ajjiye ta kalli Sakina da Huda tace “kuje Babanku yana son ganinku, Arshaad yazo da result d’in jarabawar da kuka yi.”

Da kyar gabansu yanata fad’uwa suka iya mik’ewa suka nufi d’aki, bayan sun d’auko hijabansu suka tafi parlourn Baban Sakinan. Sakina ce tayi sallama aka basu izinin shiga, ita ta fara shiga sai Hudan a bayanta kansu a k’asa suka gaida Arshaad. Cikin kulawa ya amsa yanata satar kallon Huda wadda ta kusan yin fitsari a wando tsabar fargaba! So take kawai taji me za a ce.
Baban Sakina ne ya mik’a musu takardun yace “ga results d’inku”
Da kyar Sakina ta iya mik’ewa taje ta amso sannan ta dawo kusa da Huda ta mik’a mata d’aya… har rige rigen bud’ewa suka hau yi.

Hudan tana bud’ewa taga 149/200 sai kuma daga chan k’asa anyi stamping ‘PASS’ da green rubutu! Sai da ta kalli sama sai taga sunan ba nata bane ashe takardar Sakina ce. Murna ta hau yi dan taji dad’i duk da fargaban rashin ganin nata amman atleast Sakina ta wuce. Ita kuma Sakina tana bud’ewa taga sunan Huda, da sauri Hudan ta lek’o, bata san lokacin data ce
“Kaiii!! nawa ne kuwa?” Da taga 185/200 itama an mata stamping ‘PASS’. Ai kuwa da sauri suka rungume juna a wajen suna dariya suna maimaita kalmar “Alhamdulillah” Hudan har da kwallarta a ranta tana aiyyana “Yanzu kenan itama zata yi karatu kuma a wannan makarantar y’an gayun data gani zata je tayi karatunta.”

Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Arshaad a ransa yace “So she’s this happy and it’s all because of him? Ai kuwa In shaa Allah he will make it his life’s mission to keep her happy.” Ya ji dad’i sosai dan bai san lokacin da shima ya fara murmushin ba. Tabbas Yarinyar tana son karatu, he wonders why iyayenta basu barta tayi ba, ko saboda halin babu ne maybe shiyasa.

Maganar Baban Sakina ce ta katse mishi tunani. Godiya ya sake yi mishi kafin ya juya ya cewa su Hudan
“murnar ai ta isa haka ko? Ko godiya fa baku yi mishi ba.” Nan suka had’a baki suka ce “Mun gode, Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen, ba komai.” Kawai yace dasu daga nan Baban Sakina yace su tashi su tafi. Sai da suka fita Arshaad yace “akwai interview d’in da ake zuwa ayi kuma du, amman dai shi ba wani issue bane tunda sun riga sun yi passing wannan.” Godiya Baban Sakinan ya k’ara yi mishi. Bayan Arshaad d’in ya
sanar dashi date na interview d’in ya wuce.

Successfully, suka je suka yi interview d’insu daga nan kuma aka fara preparation d’in tafiya.

Baban su Sakina ne yayi yayi musu provision da komai da komai har books, da farko Asrshaad yaso yi amman ya hanashi kwata kwata.
Sai a lokacin kuma Shuwa taji labarin tafiyar Huda da Sakina makaranta. Ita dai bata cewa Mama komai ba tunda daman ai ta dad’e da cire harkar ta a ranta amma Ummu kam ta sha fad’a! Wai “taje ta had’e kai da y’ar uwar ta sun b’oye mata abu, kuma Baban Sakinan da Mijin mama yayiwa rashin mutunci shine yanzu ta tura shi yake yiwa Maman abu salon wani abun ya sake faruwa ta jawowa kanta matsala a Auranta!” harda cewa “ta raba Huda da Sakina dan ita tana da nata asalin.” Haka nan dai tayi ta mita. Ita dai Ummu hak’uri tayi ta bata, sannan tace “Kaka ne yace Hudan taje gidanta ta d’an zauna” Tukunna Shuwa ta d’an sauk’o.

Sai ranar lahadi tukunna Ummu ta bar Huda tazo gidansu. Washegari da safe ta saka sabon uniform d’inta ta shirya tsaf sai a lokacin Mama taji kuka ya zo mata, itama Hudan kuka tayita yi ahaka Ummu da Sakina itama data shirya suka zo suka samesu.

Da kyar suka lallashi kansu sannan Ummu ta kai Huda da Sakina d’akin Umma dan su yi mata sallama. Kasa b’oye bak’in cikin su suka yi, tun ba ma da sukaji sunan makarantar ba!
Ita dai Ummu bata bi ta kansu ba ta sanya suka yi musu sallama suka fito suka tafi.

A gate d’in makarantar suka had’u da Arshaad da k’anwarsa Aaima wadda tana ganinsu Huda ta dinga jansu a jiki kamat sun shekara da sanin juna.
Duk wasu formalities aka yi aka gama sannan Aaima ta sanya aka taya su kai kayansu hostel, sunata kuka ita tayi ta lallashinsu ta jasu suka tafi. Su Ummu da Arshaad ma suna ganin shigewarsu suka juya suka wuce bayan doguwar godiyar da suka yi ta jera mishi, shi kam abun ma sai ya fara bashi kunya.

Bayan shekara uku!
After 3 years (present day).

Yau Monday kuma yau su Hudan za suyi graduating. Arshaad tare da Aaima suka zo, su suka fara zuwan ma su Huda dan sun riga su Ummu ma zuwa..

Bayan an kai su Sakina makarantar shekaru uku da suka wuce Aaima ce ta tsaya a kansu especially Huda har
personal lesson take yi musu.

Tana son Yaran ba kad’an ba, ranar graduation d’inta kam sunci kuka, da kyar suka warware daga baya suka yi friends.

Daga nesa ta hango su cikin graduation gown d’insu sun yi kyau sosai sun zama y’anmata sun yi fresh hasken fatar su ya k’ara fitowa.

Basu lura da ita ba saboda duba wayar da suka ara domin kiran su Ummu da suke ta k’ok’arin yi, dan sunga har an kusan farawa amman shiru basu k’araso ba. Sai da Aaima ta k’araso ta dafa kafad’ar Huda, tukunna
suka lura da ita.

Ai kuwa da sauri suka yi hugging d’inta suka hau murna, nan shima Arshaad ya k’araso, da murmushi a kan fuskarsa yake bin Hudan da kallo… Dukda cewa duk visiting yakan zo ya ganta amman yau d’in sai yaga gaba d’aya ta chanza, tayi wani kyau kamar yayi irin shekaru d’innan bai ganta ba. Sakina ce ta fara gaidashi sannan itama Hudan ta sunkuyar da kanta ta gaidashi dan ita har ga Allah yanzu wata kunyar shi take ji saboda tun lokacin da zasu fara zaman extension da yazo kawo musu books da abubuwan buk’ata yake gaya ‘yana sonta’ shikenan har yau bata iya ko had’a ido da shi.

Murmushi yayi ya amsa gaisuwar yana mamakin kunya irin ta Huda.
Sallamar da su Ummu suka yi ne ya juyo da hankalinsu. Tun da suke zo makarantar sau biyu taje gida hutu a lokacin tana ss1, bayan nan a gidansu Sakina take hutunta kuma Mama bai fi taje sau d’aya ba dan ko visiting Baba hanata zuwa yake yi.

Shiyasa yau take ta adduar Allah yasa azo da ita, ranar farin ciki ya kamata ace tana kusa da ita.

Ai kuwa tana d’agowa da Maman suka fara had’a ido, ba tayi wata wata ba ta tafi da gudu ta fad’a jikinta, ji tayi kawai kuka ya sub’uce mata Itama Maman harda y’ar kwallarta amman sai tayi saurin sharewa.

Sai da ta cewa Hudan “zata koma idan bata yi shiru ba”tukunna tayi shiru ta goge hawayen ta tana mai sauk’e tagwayen ajiyar zuciya. Aaima ce ta fara matsowa ta gaida Mama dan ko ba’a fad’a mata ba ta san itace mahaifiyar Huda, daga nan ta gaida Baban su Sakina da Ummu sannan ta hau tsokanar Sumayya tana cewa “ta zama y’a mata” ita kuma Sumayyan tana murmushi tana cewa “bata so” daman sun saba.

Sai da Sakina ta k’arasa dai dai gaban Arshaad ta tsaya tayi snapping fingers d’inta tukunna yayi firgigit! Ya kawar da idanunsa daga kan Mama da ya kafe da idanu, sannan yayi saurin juyo da hankalinshi kan Sakina yana murmushi. Kallon da yaga Sakina tana yi mishi tana kuma waiwayawa tana kallon inda taga yana kallo ne yasa shi cewa “Itane Maman Huda??”

Murmushi Sakina tayi sannan tace “Ai ni na d’auka wata kake kallo, baka ga har na had’e rai ba? Ashe Mama kake kallo.” Ta k’arashe maganar tata tana murmushi. Shima murmushin yayi sannan yace “kina tayata kishi bayan ita ko kishin nawa batayi, I don’t even think ma tana sona!”

Yayi maganar yana langab’ar da kai yanayin kalar tausayi. Dariya Sakina tayi sannan ta d’an matso ta sa hannunta ta kare bakinta ta gefe kamar zatayi rad’a, tace “Kar ka damu zan yi maka campaign mai zafi!”
Dariya yayi yace “woow!! really? tnx sis, you are the best!” Yayi maganar yana yi mata tumbs up. Dariya tayi tana d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan at the same time tana d’aga girar ta,
hakan yasa gaba d’aya suka kwashe da dariya, sannan tace mishi zo muje ka gaisa da surukarka, yau ne had’uwar ku ta farko so you better act decent!”
Dariya kawai yayi, sannan ya bi bayan ta suka k’arasa inda su Maman suke tsaye.

Sai da ya d’an russuna sannan ya gaida Mama. Cike da kunya ta amsa dan tunda ya nufo su Ummu tace mata “ga Arshaad” Su ummu ma cikin ladabi ya gaida su suka amsa mishi da kulawa. Daga nan suka d’unguma gaba d’ayan su suka yi hall d’in da ake taron bayan sun gaggaisa cikin mutunta juna.

Suna zuwa kamar su kad’ai ake jira nan aka fara gudanar da programs of event, Hudan aka kira ta bada speech wadda in mutun yaji kalar turanci da accent dining Hudan sai yace ba ita bace ba.

Bayan ta gama aka fara raba gifts sai da ta karb’i hud’u!!Best in English
Physics Most decent damost beautiful.
Sakina kuma ta karb’i Best in maths
Most popular da Da gift d’inta na social prefect da aka had’a mata. Mama dai sai share kwalla take yi sunata murna. Bayan nan akayi pictures da ragowan abubuwa daga nan kowa ya watse. A waje ma sai da Aaima ta sake yi musu kowa hida kowa Sannan tace sai Huda ta tsaya anyi mata da Arshaad, da kyar ta tsaya kuwa dan sai da ma ta fakaici idon su Mama taga sun d’an juyo sun basu baya.

Haka nan cikin farin ciki suka nufi gida. A gidan su Sakina suka yada zango. Arshaad a falon Baban su Sakina suka tsaya, a nan aka kai musu ruwa da abinci suka ci.

Su Hudan suna cikin cin abincin suma Baban Sakina ya shigo ya cewa Hudan “taje falonshi” sannan ya nufi hanyar d’akin shi. Sai da Ummu ta sake maimaita mata tukunna ta mik’e kamar munafuka tana jan Sakina tana kallon Mama wadda ta d’auke kai tayi kamar bata ji su ba.

Sai da suka je d’aki suka chanzo hijabai sannan suka nufi falon. Babu yadda Sakina bata yi da ita akan ta fesa turare ta shafa powder ba amman fur tak’i! Haka suka fito Sakina tana ta faman b’alla mata harara ita kuwa Hudan sai dariya take yi. Suna zuwa dai dai k’ofar falon kuwa bayan sun bud’e Sakina tasa duka k’arfinta ta turata ciki sannan ta juya da gudu tana yi mata dariya itama.

Cike da kunya ta d’an juyo tana kallon Arshaad wanda shima dariyar yake yi mata dan ya san wannan aikin Sakina ne. Turo baki tayi kafin tace
“Ya arshaad kana gani ta turoni kuma baka ce min sannu ba kake min dariya?” Murmushi yayi kafin yace
“Nasani ko tirjiya kika yi? Kika ce ba zaki zo wajena ba shiyasa ta turoki?”.
Sake turo bakin tayi.

Ganin haka yasa yayi saurin kama bakin nashi da y’an yatsun shi yana dariya k’asa k’asa, kafin yace “Afuwan wifey! Zo ki zauna tou nayi shiru ba zan sake cewa komai ba.”

Yayi maganar yana mata nuni da gaban kujerar da take facing d’inshi.
Da sauri taja gaban hijabinta ta rufe idanunta sannan tazo ta zauna a wajen da ya nuna mata ta sake sunnar da kanta k’asa. Tafi minti uku a haka jin shiru yasa ta d’ago kanta a hankali a tunaninta ko wani abun yake yi a waya amman tana d’agowa sukai ido biyu dashi da sauri ta kuma sunkuyar da kanta.

Murmushi gefen baki yayi kafin yace “Hudan”. “Um” Tace. “Hudan”
Ya sake kiranta. A hankali tace “Na’am” Sai da ya d’an yi jim! Tukunna yace “Pls ki cire wannan hijabin daga idonki, I want to talk to you about something that is very important, kinji”.

A hankali ta d’an jashi sama, face d’inta ya fito.

Ajiyan zuciya ya sauk’e kafin yace “Last time da naje wajen ki a school!
I told u what i feel towards you amman baki ce komai ba har yanzu.
Inaso in san matsayina dan i think is about time da ya kamata in san where i stand ko?” Yayi maganar yana d’an lek’o fuskarta.

Shirun da tayi ne yasa yace “Um? Please don’t say you need more time Hudan, Allah kad’ai ya san what I’m going through! Ko menene just say it, in ma bakya sona ne ki fad’a min zan d’auki k’addara.” A hankali yaji tace
“Ya Arshaad nifa ban ce bana sonka ba.” Zuciyan shi har wani bugawa take yi, cikin k’aguwa da son jin amsar ta yace “Does this means kina sona?”
Murmushi tayi sannan ta d’aga kanta alamar ‘eh’ “Alhamdulillah”. Taji ya furta tare da sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya sake cewa “zaki aureni right?” Murmushi tayi sannan ta d’aga kanta still alamar ‘yes’
Kunyace taji tana shirin nutsar da ita shiyasa ta tashi da sauri ta fice a falon, tana jinsa yana cewa “No pls wait bamu k’arasa ba” amman ta fice cikin sauri.

Arshaad ya kusan 1 hour a parlourn shi kad’ai a zaune yanata murmushi da day dreaming na yadda rayuwanshi zai kasance tare da Huda. Yanata plans shi kad’ai kala kala, bai san lokaci ya ja har haka ba! Kiran sallar la’asar ne ya fargar dashi, gashi yanada meeting d’in gaggawa a company wanda Granpa ya turo mishi d’azu akan za suyi su biyu @5pm! Bai san akan menene ba. Da sauri ya d’au wayar shi ya buga kiran Aaima yace “ta sameshi a mota yanzu yanzu.”

A gurguje Aaima ta yiwa su Mama sallama, dan taji kamar Yayan nata yana cikin sauri ne.

Tana zuwa kuwa ta fad’a motar yaja suka fita daga gidan. Gudun da taga yana yi ne ya sanya ta tambayeshi
Nan yake ce mata “Granpa ne yace mishi ya sameshi a office bai san mai ya fari ba.” “Allah yasa lafiya.”

Shine abinda Aaima ta fad’a sannan ta jingina da jikin kujera ta lumshe idanunta ta fara tunanin Auwal. Yau kwana biyar kenan bata gansa ba kuka ko ta kirashi baya d’auka! Daman kwana biyun nan rashin mutunci yake ji dashi, dan kawai yace tayi mishi abu tak’i yi! Ita wani abun na Auwal sai take ganin kamar iskancine amman friends d’inta na nile su ce mata suke yi ‘hakan wai wayewa ce, its a normal thing and dan yana sonta ne shiyasa yake demanding, inda iskanci ya so yi to da ba zai na demanding peck da kisses ba, he would have ask for something different!’.

To ko dai tayi mishi kawai tunda ba wani abun bane ba, dan ita dai har ga Allah, Allah ya d’aura mata son Auwal, bama ta san wanne irin so take yi mishi ba! She don’t ever want to see him angry, besides she is in level 2, tana ganin yadda mates d’inta suke kula da samarin su. Maganar Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa
“Wai tunanin me kike yi ne haka?”
Cikin fad’a. Firgigit!! Ta bud’e idanunta. K’ura mata ido yayi sannan a hankali yace “anjima around 9, ki sameni a parlourna.” “To” kawai tace, sannan ta bud’e k’ofar ta fita, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya nufi mosque d’in jikin estate d’in yayi sallah, yana idarwa ya d’anyi addua, sannan ya fito ya shiga mota ya nufi office.

Yana zuwa bai tsaya b’ata lokaci ba ya nufi hanyar office d’in da yake mallakinsa a cikin building d’in dan Granpa yace mishi “a nan zasu had’u”
kuma kamar yaga d’aya daga cikin motocin da Granpa d’in yake hawa a parking lot shiyasa a gaggauce ya dinga amsa gaisuwar securities da wasu ma’aikatan da suke ta gaidashi yana mai k’arsawa office d’in nasa.

Key ya zaro zai bud’e k’ofar amman yana d’aurawa yaga ashema k’ofar a bud’e ne hakan ya bashi tabbacin Granpa ya rigashi k’arasowa kenan!! Agogon hannunshi ya kalla yaga ya k’ara 5 minutes akan time d’in da yace masa ya sameshi. Ajiyar zuciya ya sauk’e kawai yayi ‘bismillah’ ya tura kai ya shiga.

Yana shiga ya hango Granpa a kan kujerar shi ya juya baya. Sai da yayi addua sannan ya k’arasa inda yake D’an gyaran murya yayi sannan cikin girmamawa ya gaidashi. Ba tare da ya amsa gaisuwar tashi ba yace “I’ve waited for you, for six minutes!”

Arshaad zai yi magana Granpa ya katseshi ta hanyar mik’o mishi wasu takardun. Karb’a ya yi ya fara dubawa.
Cikin no nonsense voice d’in shi yaji Granpa d’in yana cewa “3 days ago mun samu embezzlement, ko kuma in ce theft from an insider, munyi ta bincike da ni da Auwal at long last mun gano waye!” Daidai nan idanun Arshaad suka kai kan abunda takardar ta k’unsa! Gabanshi ne ya hau fad’uwa babu k’akk’autawa! Naira miliyan dubu d’ari tara ne suka b’ata! Kuma shine yayi signing, gashi kuma a d’ayan takardan an nuna ya shiga personnel account d’inshi! Da sauri ya d’ago ya kalli Granpa a mugun firgice yace Grandpa, i don’t know anything about this! Maybe mistake ne ko kuma someone is trying to frame me, amman wallahi i have no clue..”

Kura mishi idon da yaga Granpa yayi ne ya sanya shi yin shiru. Cikin kakkausar murya Granpa yace “Who’s trying to frame you? Um? Ni ko Auwal? Use your words! Dan mune muka yi binciken, just the two of us!.”

Shiruuu, Arshaad yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa. Granpa yaci gaba da cewa “For your information nayi suspending Auwal d’in kanshi for a week! Did you know wat he did??
I ask him to investigate, and after he finds out kai ne b’arawon he hid it from me! Bawan Allah n nan was even trying to pay back the money from his own pocket duk dan kar in gane kaine mu samu matsala da kai. ”

Da k’arfi Arshaad ya runtse idanunshi, har ga Allah Auwal fa ya fara kaishi mai’ura da makirce makircensa!
Shi da yake a matsayin MD amma wai yana yi mishi bak’in cikin treasurer d’in da aka bashi! For wat!?? Sai kace ba y’an uwa suke ba?

Maganar Granpa ne ya dawo dashi daga tunanin daya fad’a jin yana ce mishi “take this!” Hannu Arshaad yasa ya karb’a jikinshi duk yayi sanyi.
Mik’ewa Granpa yayi ya gyara suit d’in jikinshi, sannan ya fara tafiya yana dogara sandarshi, sai da ya kai bak’in k’ofa ya juyo ya kalli Arshaad
Sai a lokacin yaga bai ma duba takardarba, yana nan tsaye yadda ya barshi ya lumshe idanuwanshi.
Bud’e k’ofar Granpa yayi sannan yace mishi “the door is open and ranar Monday zamu fara zaman kotu da kai!” Da sauri Arshaad ya kalleshi sai kuma ya hau duba takardun hannunshi, ta farkon takardar kora ce ta biyun kuma takardar sammaci ce!.
Da sauri ya k’araso gaban Granpa yace “Granpa pls i… ”

“OUT!!” D’in da Granpa yace mishi da k’arfi ne ya sakashi saurin yin shiru dan yaga alamar kamar ran Granpa ya soma b’aci dan haka kawai sai ya yanke shawarar tafiya. Jiki a mugun sanyaye ya sa kai ya fice daga office d’in! Yana fita yaga Granpa ya d’aga sandarsa ya buga a jikin k’ofar dai dai inda glass d’in da aka rubuta sunanshi yake ‘Muhammad Arshaad Yahaya MT’
Nan take sunan ya tarwatse ya zube a k’asa. Da sauri Arshaad ya juya ya fara tafiya da sauri. Bai tsaya a ko ina ba sai a bakin motarshi, yana zuwa ya bud’e ya shige ya kunna ya bata wuta.

Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida, saboda uban gudun da yake zubawa.
Yana yin parking ya fito ya nufi gidansu Auwal. A parlourn farko yana shiga ya hango shi a bakin kitchen da cup yana kurb’a da waya a hannunshi!
Gadan gadan yayi kanshi yana zuwa ya zuba mishi naushi! Auwal bai ga shigowar mutum bama, kawai naushin da aka yi mishi yaji wanda yayi sandiyyar fad’uwar waya da cup d’in dake hannunshi da kuma fashewar hancinshi. Jikin bango ya kama dan sauran kad’an ya shima d’in ya zube k’asa! Sannan da sauri ya d’ago dan ganin waye. Suna had’a ido da Arshaad kawai ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya har da rik’e ciki!
Arshaad bai kula shi ba sai da ya barshi ya d’an tsagaita tukunna yace masa “why? And how do you do it??”
Murmushin gefen baki Auwal yayi sannan ya lakato jinin da yake bin hancinshi wanda ya sauko har kan k’irjin shi, kallon jinin yayi kafin ya gogawa Arshaad d’in a daidai kan kirjinshi wajen heart d’inshi, sannan yace “Na tabbatar zafin da nake ji a face d’ina da jinin dana zubar bai kai wanda kake ji anan ba”. Buge mishi hannu Arshaad yayi kafin yace “ I don’t have time for this, just tell me, me nayi maka haka? What do you want from me?”. Murmushi Auwal ya sake yi kafin yace “Yanzu kam i want nothing from you, a time d’in da nake neman abu a wajenka ai k’in yi mini kayi. Kai ka san waye ni bana mantuwa kuma bana yafiya!

Zaka iya tuna ranar da Khadija tazo wajenka akan kayi mata signing ka k’i yi!? A time d’in I called you Arshaad a whole me ina a matsayin MD nace maka kayi signing d’innan, I’ll explain later amman saboda taurin kai irin naka da kuma son kayi proving wasu silly principles d’inka ka k’i yi! A whole me ace wai in saka ka kayi abu amma ka k’i yi! Who do you think you are??”

Da mamaki Arshaad yake kallon Auwal, kafin ya ce “Yanzu saboda wannan ne kake son lalata mini image da carrier da future d’ina gaba d’aya?
Auwal Granpa ya kai ni court!! I’ve been sued by my own family for theft!! wanne company ne kake tunanin zasu bani aiki da wannan pent d’in da kayi mini??”. Gyara tsayuwanshi Auwal d’in yayi kafin yace “Actually Arshaad maganan court was my idea, although ban fad’awa Grandpa direct ba kawai dai na bashi labarin wani Abokina da yayiwa mahaifinshi haka shikuma Mahaifin nasa ya kaishi court! That’s all i said i was hoping yayi same thing to you, and look! He did!!”

Ya fad’a yana murmushi kafin ya ci gaba da cewa “Arshaad!!you should have known me by now, bana son shishshigi…actually akwai abubuwan da kayi mini dayawa a company d’innan, tun dawowarka da aka baka position d’inka shikenan ka saka mini ido dayawa, I’m the MD bai kamata ka dinga bin al’a’mura na ba amman kwanaki har investigation ta k’ark’ashin k’asa kayi mini. Duk wasu abubuwan da kake yi ina sane da kai.
I warned you twice amma baka ji ba!
A tsarina bana maimaita magana sau uku.

Da Khadija ta zo, na kiraka nace kai signing mata, ko nawa ne zasu fita ta acc d’in company Ina ruwanka??
amma still u refuse. On a serious note Arshaad nayi tolerating Dinka more than yadda nake tunanin zan iya ma.
And you should stop saying wai nayi tarnishing image naka akan small thing cos this is not a small thing to me, remember i hate nonsense, and small thing su suke komawa manya shiyasa nayi deciding in yi dealing with you now!.”

Yana gama fad’in haka ya juya har ya d’an yi gaba sai kuma ya sake juyowa yace “sai mun had’u a court, i‘ll make sure na kawo wasu takardun da zasu sake girgiza ka!!

Don’t underestimate the power of your MD, wannan ma ina baka san ya aka yi suka fito ba ko?” Bai jira jin me Arshaad d’in zai ce ba ya ci gaba
“A daa abokin fad’a ne da kai! Yanzu kam you’ve made an enemy that too a powerful one so be afraid!!” Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ya kyale shi a wajen.

A hanyar main k’ofa na shigowa ya hango Mom da alamun yanzu ta shigo amman tabbas taji komai dan da mugun mamaki take kallon shi, d’an takowa tayi tana lek’a inda Arshaad d’in yake taga bai juyo ba har yanzu,
Yana ganin ta matso kusa dashi da alamun tausar shi zata yi a take ya b’ata rai yaja d’an gajeren tsaki kafin k’asa kasa ciki b’acin rai yace “What a terrible timing u have! duk inda ake abunda bai kamata ki sani ba sai an ganki a wajen!! Anyways it’s on u, cos I’m not gonna change or do anything for you. Kece kika ce inyi k’ok’ari nayi winning MT and that’s wat i’ve been trying to do.” Yana gama fad’an haka ya wuce yayi hanyar stairs d’in side d’inshi.

Mom bata so Arshaad ya ganta a wajen, amman shock d’in da Auwal ya bata ya sa ta daskare a wajen ta kasa matsawa.

Gabad’aya kullum Auwal sake rainata yake yi kamar kashin gindinshi, why?.
Tana a haka har bata san Arshaad d’in ya k’araso ba, sai muryarshi taji yana gaisheta.

Da kyar ta iya amsawa tana tunanin yadda zasuyi da Mammy idan case ya fito, ta san Mammy k’awar ta ce amma yadda take son Arshaad ko uwarta fad’a suke yi da ita akansa.

Amsawa tayi cikin basarwa da nuna kamar bata ji conversation d’inshi da Auwal ba.

Arshaad kam bai ma wani lura ba ya wuce dan duk jikinshi a mace yake, sannan har ga Allah bai san ta ina zai fara zaman court da Granpa da Auwal ba!!.

Mom kuwa ta dad’e a wajen tana lissafin nemo yadda zata b’ullo wa alamarin, ganin bata da wata mafita ya sanya kawai ta hak’ura ta wuce d’akinta tana mai jiran k’arasowar Mammy dan ta san tana hanya muddin zancen yaje kunnenta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 23So Da Buri 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×