A hargitse ta k’arasa kanta ta d’ago ta, sannan ta hau dudduba ta tana cewa“Ke!! Wai lafiya kike kuwa?? Meye haka? Dukan ki suka yi?Mai ya faru???”
Rungume ta Jalila tayi ta fashe da wani sabon kukan. Duk da kwakwazon tambayoyin da Umma take jero mata hakan bai sanyata ta sarara ta amsa mata ba, sai da tayi mai isarta tukunna ta share hawayenta tace “Umma anya Kaka shi ya haifi Baba kuwa? Ki duba fa kiga yadda yayi talla ta a masallaci shekaru uku baya wanda ba don na gudu na b’uya Gidan kawu. . .