Skip to content
Part 27 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

A hargitse ta k’arasa kanta ta d’ago ta, sannan ta hau dudduba ta tana cewa
“Ke!! Wai lafiya kike kuwa?? Meye haka? Dukan ki suka yi?
Mai ya faru???”

Rungume ta Jalila tayi ta fashe da wani sabon kukan. Duk da kwakwazon tambayoyin da Umma take jero mata hakan bai sanyata ta sarara ta amsa mata ba, sai da tayi mai isarta tukunna ta share hawayenta tace “Umma anya Kaka shi ya haifi Baba kuwa? Ki duba fa kiga yadda yayi talla ta a masallaci shekaru uku baya wanda ba don na gudu na b’uya Gidan kawu Usman
ba to da fa tuni yanzu ina gidan malam mati mai wanki!

Kuma kina gani fa har yau ya dage akan shi zan aura, ba dan munata addu‘o’i ba na san da tuni yanzu an kawo kud’in an saka rana. Ya dage ya hura min wuta ya hanani auren saurayi amman ita Huda kiga yadda yake k’ok’arin aura mata mai kud’i saurayi kuma kyakkyawa!! Kamar ba ni ce jikar sa ba?”

“Ban gane me kike nufi ba!
‘Yana k’ok’arin aura mata’! Kamar yaya? Shin kin ji wani zancen ne bayan na fita?” Umma tayi mata tambayar da alamun tsoro wanda ya bayyana k’arara a kan fuskarta.

Murmushin takaici Jalila tayi sannan tace “Umma, a gaban idona Huda ta tafi d’aya daga cikin makarantun da ake ji da su a kaff fad’in Nigeria!! Kullum ce mini kike yi zaki saka ta dawo gida gashi har sai da tayi candy ta gama baki yi komai ba! Kuma na tabbata wannan saurayin nata yadda yake d’innan na san nan da nan zai nema mata jami’a ta tafi ni kuma ina nan ina wasan y’ar b’uya da Kaka!
Wannan wacce irin rayuwa ce saboda Allah?? Wallahi Umma sai dai in kashe kaina dan ba zan tsaya ina ji ina gani ta auri wanchan mutumin kuma tayi karatun da ni ban yi ba!.”

Da sauri Umma ta buge mata baki, sannan cikin fad’a tace “maganar kashe kanki ma bata taso ba!.
Sannan kin san Allah idan baki gaya mini abunda ya faru yau d’innan kin bar ja mini rai ba to sai na bubbuge ki yanzun nan.”

Share hawaye Jalila tayi sannan ta kwashe komai abunda ya faru yau d’in ta fad’awa Umma Dan ko lokacin da Sakina ta ganta tana lek’e da ta komo d’akin nasu ci gaba da lek’a su tayi, tsaf sai da taga komai. Sannan ta k’ara da cewa “kuma na san har wajen su Kaka ma yaje dan da wuya in ba a saka rana ba ma, tunda gashi har kud’in k’unshi ya bayar. Umma gashi wallahi tallahi ina son shi, sosai Umma!!..” Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka.

Takaici! Da ya ishi Umma bata san lokacin da ta daddage ta d’akawa Jalila duka ba! Sannan cikin fad’a tace
“Wallahi Yarinyar nan tun da nake ban tab’a ganin dak’ik’iya kamar ki ba!
Tun zuwan Yaron nan na farko nace miki ‘idan ya zo ki fita! Idan yazo ki fita!!’ Amman da yake y’ar iska ce ke!! Kina kuma so kisa inga abunda zuciyata zata buga shine kika yi zaman ki a d’aki kamar kumama!!”

Cikin kuka Jalila tace “Umma wai taya zan fita? Ko na fita na san ba lalle ya kulani ba! Ki kallafa yadda Hudan ta koma sannan ki kalle ni..”

Katseta Umman tayi ta hanyar cewa “Dan uban ki ban san abunda nake yi bane ba? Tunda nace miki ki fita d’in ai na san me nake yi ko? Naki aikin kawai shine ki fita ki tabbata kun had’a ido da shi daganan ki bar min sauran aikin…Amman sam kin kasa! Abu guda d’aya za kiyi tak Jalila amma kin kasa yi wajen shekara uku yanzu!!
Kalle ki, sai dai ki zauna kina ta kuka, tou wallahi idan baki yi wayo ba a haka zaki k’are!! Tunda ni dai ba nice zan yi aikin da kece ya kamata ki yishi ba! Shegiyar Yarinya kawai.

Idam kika ga wanda Bilkisun kawun ku Nasiru ma zata aura sai kin yi mamaki!! D’azun muka je ganin gidanta a sabuwar gandu, tamfatsetse mai gate da bene! Da ke da ita da Hudan duk kusan tare kuka taso, ga y’ar gidan Zainab itama mai kud’i sosai ya fito mata nan da wata biyu za a sha biki in sha Allah. Ke kuwa kina nan a d’aki, ke ko irin samarin nan masu motoci ma basa biyoki in kin fita, kina nan dai da malamin maths dan buhun uba mai shegiyar rowa, ni Allah yasa ma ba shine yayi miki asiri ba!”

Fashewa da kuka Jalila tayi. Ta fi minti biyar tana abu d’aya! Sai kuma ta fara bawa Umman tausayi, hakan yasa ta janyo ta ta rungume ta hau lallashinta, sai da taji tayi shiru sannan tace mata
“Jalila gaskiya nake gaya miki, ki fahimceta kin ji? Ba zan so ki je inda zaki sha wahala ba bayan ga sa’anninki suna jin dad’i ina gani.
Yanzu abunda nake so dake shine ‘duk ranar da saurayin nata ya sake zuwa to ki fita, ki tabbatar kin fita kafin ita ta fita, sannan ku had’a ido!’ Daga nan ki bar min aikin a hannuna kin ji??”

“To” tace, sai kuma tace “umma Kaka fa? Kina ganin ko Arshaad d’in ya dawo gurina Kaka zai yarda kuwa?
Kinga fa ya dage sai Mati!.”

Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Jalila ki yi yadda nace kawai, ta Kakanku mai sauk’i ce kin ji? Ai ko ina gadon asibiti ba zan yarda da Mati ba shima ya sani, ballantana kuma da lafiya ta.”

D’aga mata kai tayi tana share hawayenta. Dafa ta Umman tayi itama ta goge mata hawaye kafin tace “yauwa y’ar albarka, ki kwantar da hankalinki kin ji auta ta. ” Haka nan ta d’an saki ranta suka d’an yi hira kad’an, wadda rabin hirar duk k’ulla tuggu ne…daga baya kowa ta ja pillow suka hau bacci.

Washegari da safe Sakina cikin zumud’i ko karyawa bata yi ba, taje ta amso musu wayoyin su. San wayar bai k’ara shiga ransu ba sai da suka kunna, already an d’anyi setting d’in da suka kamata.

Sakina har da ihunta tana daka tsalle, sannan ta d’auko slum book d’inta na school ta hau juye nambobin k’awayenta tana saving..

Mama na d’akin Baba tana shara taji ihun Sakina, girgiza kai kawai tayi tace “Allah ya shirya” Baba wanda ya daya fito a wanka yana shiryawa ta kalla sannan tace “Jiya, wanda yake neman Huda ya zo baka nan! Ya kawo musu kayayyaki har da waya ya kawo musu ita da Sakina. Har cikin gidan nan ma ya shigo muka gaisa.”

Shiruu, Baba yayi bai ce da ita komai ba. Sai da ya gama shirinshi tsaf ita har ta ma manta tayi maganar, dan har ta fad’a wata duniyar tunanin…
Yana dedeta zaman Hular kanshi ya kalleta yace “Ko da wasa!! Idan kika sake bari Yaron nan ya shigo mini cikin gida to duk abinda nayi miki kar ki ji haushi na ki kuka da kanki!
Tunda ke abinda kwad’ayi ya ja miki bai kai ga zama izina a gareki ba, k’iri k’iri gashi zaki tura y’arki itama ta bi sahunki!!! To duk iskancinsu da za suyi su tsaya iyaka k’ofar gida kuma shima ki gayawa Hudan nace tace mishi ya daina yi min parking daf k’ofar Gidana! Tunda na san yanzu ina yin magana Kaka bayan ki zai bi!.

K’iri k’iri bani da yadda na iya an d’aura mini ruk’on shegiya tun tana jinjira! Amman ku tsabar baku san kara ba! Jalila na cikin gidan nan aka yo siyayya dan cin fuska babu ita kuma har kike iya gaya min ya kawowa Hudan da wata Sakina wadda itama bani da ikon hanata zuwa gidan, abubuwa. Sannan na tabbatar ko tsinke baku bawa Jalilan ba!!
Ba wai Ina gaya miki bane saboda kwad’ayi ko kiyi tunanin ina son abunku, ni abunku bai dameni ba, kawai dai inaso ki gane ta wajaje da yawa da na fiki!!” Yana gama fad’an haka ya juya ya sa takalmanshi ya fice, ko ‘a dawo lafiyan’ ta bai amsa ba.

Girgiza kai kawai tayi tace “Allah ya kyauta!” Sannan ta k’arasa aikinta ta wuce d’akinta. Kamar yadda tayi zato su Huda har sun gama abun karyawan gida, daman ita da safe ta yiwa Baba nashi tace musu ‘in sun shirya su d’aura na mutan gida’.

Tana shiga d’aki ta tadda su suna ninke kaya. Waje ta samu ta zauna a kan cafet d’in da yake malale a tsakiyar d’akin d’an gefe kad’an dasu sannan tace “Sakina kwaso min kayan da Arshaad ya kawo jiya, duka”
“To” Sakina tace sannan ta nufi wardrobe ta bud’e locker d’in chan k’asa ta d’auko kayan gaba d’aya waenda har yanzu suke cikin leda.
Juyesu suka yi a k’asa gabaki d’aya, sannan Mama ta hau rabawa gida biyu, abaya sunfi kala ashirin haka ta rabasu dai dai, hatta da rings dede ta raba su da su bracelet, bayan ta gama rabawa ta ware kashi d’aya a gefe sannan ta sake raba d’aya kashi Dayan gida biyu ta cewa “Huda da Sakina su d’auki kashi d’ai d’ai.

D’aya mai yawan kuma ta ce “su kwasa su zuba a leda su kaiwa Jalila.”
Har Sakina ta yunk’uro zata yi magana Hudan tayi saurin rik’e mata hannun alamun tayi shiru sannan tace “to Mama”. Ba yadda Sakina ta iya haka tana ji tana gani suka juye a leda suka fito.

Suna fitowa tace “yanzu dan Allah an…” Da sauri Huda tace “Dan Allah Sakina ki yi shiru mana meye a ciki idan mun bata? Ni daman ko Mama bata yi hakan ba ma dama inada shirin kai mata.”

Da sauri Sakina tace “Ai ni ba wai batan da akayi bane ya b’ata min rai ba, fin namu yawa da nata rabon yayi shi yafi yi min ciwo.”

Ita dai Huda shiru tayi mata dan har sun k’araso k’ofar d’akin Umma hakan yasa ta fara sallama. Ta yi kusan minti biyu tana sallama tukunna aka ce “shigo” Tsaki Sakina taja sannan tace
“Zan jiraki a nan dan ba zan iya kwasar takaici ba!” Haka Hudan ta shiga ta same su, da kyar Umma ta amsa gaisuwarta Ita kam Jalila iskar da ta kwasota ma bata kalla ba.
Hakanan jiki ba kwari ta ajjiye k’atuwar ledar da wata y’ar k’arama tace “gashi na Ya Jalila ne” sannan ta mik’e ta fito. Kamar ta biya su bashi ko godiya babu wadda tayi mata a cikinsu.

Suna fitowa kitchen suka nufa suka hau zuzzuba abinci. Sun zubawa Ya Ja’afar da su da su Umma nasu suka ajjiye, dan tun dawowarsu ba su ga Junaidu a gidan ba. Hudan tana son tambaya amma tana jin tsoron Mama.

Nasu suka d’iba suma ita da Sakina da Mama a kwano d’aya, daga nan suka fara k’ok’arin barin kitchen d’in.

Hudan ce ta d’auko kwanon ita kuma Sakina tana biye da ita a baya suna magana, saura k’iris ta juyewa Ya Junaidu abincin a gaban rigarsa sakamokon gwaren da suka yi da shi.

Kwata kwata bata san yana bakin kitchen d’inba, gashi tana tafe tana kallon baya ne. Da sauri ta ja baya ta rik’e kwanon da kyau, sannan ta hau sosa gurin da suka yi gwaren dan mugun zafi yake yi mata har idanuwanta sun kawo kwalla.

Hannunsa ya d’aura a kan goshin nata saman hannunta, da sauri ta janye hannun nata ta d’an ja baya kad’an…

Ganin da yayi wajen ya d’an yi jaaa kad’an yasa ya kalleta a hankali kamar wanda baya son yin maganar yace
“Sorry”, Jijjiga kai tayi alamun ‘ok’ sannnan tace “ina kwana”. Yanzun ma kamar ba zai amsa ba a hankali yace “lafiya” sannan ya kalli Sakina itama da tace mishi “In kwanan” ya amsa.
Hannunshi yasa ya karb’i kwanon hannunta ya mik’awa Sakina sannan ya cewa Hudan “Zo, ina son ganin ki.”
Yana gama fad’an haka ya juya ya wuce ya nufi hanyar d’akinsa.

Hudan, yi tayi kamar ba zata je ba, sai da Sakina tace “kije mana, baki san me zai gaya miki ba, kuma ko ba komai dai ai he’s your brother ko? kuma shi ai da hankalinshi a cikin y’an d’akin nasu.”

Shiru tayi hakan yasa Sakina kawai itama bata sake magana ba ta wuce tayi d’akin Maama.

Ta kusan minti uku a tsaye tukunna kamar mara gaskiya ta nufi hanyar d’akin bayan ta ware d’an kwalin doguwar rigar atamfar jikinta ta yafe shi daga kanta zuwa k’irjinta.

Tana isa tayi sallama a bakin k’ofar d’akin, ko k’arasa rufe bakinta bata yi ba aka ce “Come in”.

A hankali ta tura k’ofar ta shiga.
Yana tsaye a tsakiyar d’akin,
kallon d’akin take yi tana sakewa dan ya koma kamar ba shi ba, yadda ya gyara gidan gabad’aya, haka ya yiwa d’akin nasa nutsetsen gyara! Ya sha penti mai mugun kyau har da pop, ga tv k’atuwa! Da yake d’akunan gidan suna da girma sosai har yanka yayi aka yi mishi bayi a d’akin dan ga k’ofa nan.

“How have you been??” D’in da yace mata ne ya dawo da hankalinta gareshi. A hankali tace “Alhamdulillah”. Kujera ya nuna mata yace “Zauna mana.” A hankali ta girgiza kai, “Ok” yace, ya jinjina kai kafin yace “Ba ki nemi ni ba, kin kyauta kenan??”. Sunkuyar da kanta tayi tace “kayi hak’uri, ai babu wanda zan tambaya kai, Ya Jalila ka san ba wani shiri take yi da ni ba.”

A hankali ta sunkuyar da kai tana tunanin rabon ta dashi tun farkon shiganta ss2, haka kurum ya daina zuwa mata amman da farko farkon zuwanta makarantar kafin lokacin visiting ma yayi ya kan zo sau biyu sometimes har uku, sannan kuma duk visiting sai su Ummu sun zo da shi, dan har sak’o Mama take bashi ya kai mata kuma in yaje suyi waya da Maman! A ranta taji ya kamata ta tambayeshi, ko ba komai Ya Junaidu yana da kirki, dan haka tace
“Meyasa ka daina zuwa min visiting?”

Murmushin yayi, kafin
a hankali yace “ashe dai an damu dani, ko?” Bai jira jin amsarta ba yaci gaba
“Visiting da zuwa da nake yi akai akai Arshaad ne ya hana! Dan akwai time d’in da naje gate man d’in yace min ‘wanda ya kawo ku yace kar a k’ara barina ina shiga!’ Wai yazo aka ce mishi anyi exceeding zuwar miki sai dai ya jira next month. Shine yayi ta fad’a yace ‘kar a sake bari na In shiga’.”

Murmushi Hudan tayi kafin tace “Ya junaidu baka san halin mai gadin mu bane ba wajen iya had’a mutane. Ni na san ba wani Ya Arshaad da ya hana kawai dai baiga daman barin ka ka shiga bane! Amman shi Ya Arshaad ina ma ya iya fad’a, ba ruwanshi. Sannnan in da ace yayi hakan to da zai fad’a min. To gidansu Sakina fa? Me yasa baka je ba chan ba?”

Shiruuu, yayi dan ji yake kamar zuciyarshi zata fashe!! Yadda ta tak’ark’are take yabon Arshaad a gaban shi abun yayi mugun b’ata mishi rai! Ina ma laifin tace zata tambaye Arshaad d’in amman ji yadda directly ta fito tayi backing d’in shi…

“Ya Junaidu!” Yaji muryar ta, da kyar ya iya controlling kanshi, ya d’an seseta kanshi kad’an amman still idanuwanshi har sun sauya kala!
Danne abunda yake ji yayi kafin yace mata “Bayan naje school d’inku an hanani shiga, i think after a month aka yi muku hutu, and wallahi Huda that’s the longest month dana tab’a gani a rayuwana. Kullum Ina cikin duba date,
ranar ana yi muku hutu daman na san ba nan zaki zo ba dan naji Baba yana yiwa Mama kashedi a tsakar gida ‘kar kizo mishi kuma itama idan taje a bakin aurenta!’ Yana fita na shirya zan je wajenki. A tsakar gida Mama take bani sak’o in kai miki ke da Sakina ashe Umma tana d’aki bamu sani ba, sai kawai gani muka yi ta fito mana.
A take tace mini ‘in dai na taka k’afata naje gidansu Sakina to bata yafe min ba.”

D’azu na dawo daga Abuja, flight d’in asuba na biyo, kawai cikin bacci na ke jiyo muryar ki sama sama I tot qizo voice d’in naki ke yimini saboda yadda nake tunaninki day and night, sai da naji muryan Sakina tukunna na tabbatar ku d’in ne. Ya aka yi Baba ya barki kika zo? Yaushe kuka dawo?
Kun gama ko?” Ya jero mata tambayoyi yana kafeta da manyan idanuwanshi.

Cikin nutsuwarta tace “Wajen Kaka Mama taje, as usual, shine ya yiwa Baba magana. Jiya muka yi graduating
a jiya muka zo nan ni da Sakina.
Na ma yi jamb, kuma duk mun ci.”

“Alhamdulillah!” yace, sannan yace “Huda i think Mama itama is against our relationship, tunda tana ganin fa yadda nake ta son ganin ki but kin dawo ko a waya bata gaya min ba, kuma fa jiya ma na kirata na gaisheta.”

Shiru tayi sannan tace “Kawai dai bata son fad’a da Umma ne”

Bai ce mata komai ba, ya matso kusa da ita sannan yace “Forget all that. Yanzu let’s talk about us, ko?”

Kallonshi tayi sai kuma ta d’anyi k’asa da kanta ganin yadda ya tsareta da idanuwa.

“Um?”

Ya sake cewa, sannan ya d’aura da “Ina jinki, let’s talk tunda kin k’i yarda ki zauna a d’akin nawa, sai muyi a tsaya.”

Cikin rashin fahimtar shi take, “kamar akan me kenan za muyi maganan?”

Kamar an fisgi maganan a bakinshi taji yace “Yaushe kike planning yin aure?”

Da sauri ta d’ago ta kalleshi “Sai kuma ta maida kanta k’asa tace “duk sanda Allah yayi” sannan ta juya zata fita tana cewa “Mama zata nemi ni”

“Hudan!!”

Taji ya kira sunanta. Tsayawa tayi ita bata juyo ba kuma bata tafi ba. Takowa ya sake yi ya zo inda take tsaye sannan yace “I know what you are afraid of! Umma da jalila ko?
I promise you har k’arshen rayuwan mu zan kareki daga garesu. I won’t let them harm you in any way. Jalila sister nace, i have full control over her
Umma kuma Mahaifiyata ce amman na yi miki alk’awarin sai kina so ma tukunna zaki zauna a garin da take.
Hudan ko k’asar nan ne in kika ce bakya son zama to zan yi k’ok’ari inga na fitar dake! Duk inda business yake k’ok’ari nake yi inyi duk saboda ke, sannan ina aiki I promise you i‘ll give you all the happiness and luxury’s that you deserve!.”

D’agowa tayi ta kalleshi sannan tace
“Ya junaidu gani kake yi kaiima kamar kwad’ayi ne da ni?” Ganin da yayi kamar ranta yad’an b’aci ne yasa yayi saurin girgiza kai sannan yace “Sorry Hudan not at all, akwai abunda nake tunani ne wanda in ma hakan ya faru to ba za a iya yi min shige ba, kar kiyi misunderstanding d’ina, please.”
Ya k’arashe in a low tone.

“To” kawai tace ganin yadda ya marairaice duk sai taji wani iri. Tunanin ‘kar su tsaya b’atawa juna lokaci’ ne yazo mata dan haka kawai ta dake ta fara magana ba tare da ta yarda sun had’a ido ba.

”Ya Junaidu kai Yaya nane, ba zan so In yaudareka ba, kuma ya kamata in fad’a maka gaskiya tun yanzu. Babu amfani muyi aure iyayenmu basa farin ciki da auren, kai ka sani a dukduniyar nan babu wadda Baba baya so kamar ni, a ta dalilin Kaka kawai nake zaune a cikin gidan nan! Sannan Umma ita ma bata sona! Ga Ya Jalila itama
sannan Ya Ja’afar! Duk fa kowa naka kai kad’ai ne kawai kake sona and ba zan b’oye maka ba Mama itama bata son auren mu, duk a ta dalilin su Umma.”

Da sauri ya katseta ta hanyar cewa “Huda na fad’a miki i’ll take care of them, all of them i promise, ba wanda za a cuta in sha Allah.” Shiruuu, tayi
chaaan kuma, kamar an fisgi maganar daga bakinta tace “Na yiwa Ya Arshaad alk’awarin aure.”

Junaidu, da kyar ya iya had’a 1+1 d’in maganar a cikin kwakwalwarsa. Ji yayi jiri yana neman zubar da shi dan haka ya nemi waje ya zauna, a hankali yace
“Says the person that just finish saying ‘ba ta da kwad’ayi!’.”

Hawayene ya gangaro daga idanunta, a hankali tace “ba fa ka tab’a cewa kana sona ba tun farko and kuma kaga.”

K’arar fashewar center table din dake a tsakiyan d’akin ne yasa tayi saurin yin shiru sannan ta sanya tafukan hannayenta ta rufe kunnuwanta, tare da rumtse idanuwanta duk a lokaci daya!.

A zuciye ya taso yazo ya kama k’afafunta da k’arfi kamar zai karyata har sai da tayi k’ara! Bai damu ba ya fara magana cikin tsananin b’acin rai da d’aci!! “Ni kike cewa ban tab’a cewa ina sonki ba?? Makauniyace ke ko sokuwa? Ko kuwa dai renin hankali ko kuma Yarinya ce ke da zaki ce baki fahimceni ba tuntuni? Hudan tun kina baby, y’ar baby!” Yayi maganar yana kwatanta d’aukar baby da hannunshi,
sannan ya ci gaba da cewa “nake gwada miki so! I don’t think akwai need na inyi amfani da fatar baki in fad’a miki domin kuwa na san ko wanda bai tab’a sanin me kalmar so take nufi ba, abunda nake nuna miki, ya ci a ce ya bada full definition na wat luv is!!! Kin san irin bak’ar wahalar da na sha first zuwana Abuja da Lagos kafin in samu inyi settling kuwa??? All because of you!!!” Ya k’arashe maganar cikin d’aga murya sannan ya girgiza ta da k’arfi!.

Fashewa tayi da kuka. Tunda Mama ta kawota duniya bata tab’a ganin b’acin ran Ya Junaidu irin haka ba, gabaki d’aya ya birkice kamar ba shi ba, sannan idanuwanshi sunyi jazur! Sun cika da kwalla kamar zai fashe da kuka.

Kukan da yaga tana yi ne ya sanyashi yin shiru sannan ya runtse idanuwanshi! Ya fi 3 minutes a haka kafin ya bud’e idanunsa, ya kalleta tayi k’asa da fuskarta still kukan take yi.
A hankali ya cika mata kafad’a sannan ya juya ya fara tafiya yayi hanyar gado kafin yace “Get out!”

Har ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace “Ya Junaidu dan Allah ka fahimce.” Da sauri ya juyo ya had’e hannuwanshi guri guda alamun rok’o, sannan yace “Huda dan girman Allah ki fita, please!!”.

Hawayenta ta share sannan ta juya a hankali ta fice a d’akin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 26So Da Buri 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×