Skip to content
Part 28 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Babu yadda Mama da Sakina basu yi da ita akan ‘ta fad’a musu abunda yake damunta’ ba amman tak’i! Mama data gaji mik’ewa tayi ta nufi hanyar k’ofa tana cewa “ai daman tunda aka ce ya kirawo ki na san a rina! In banda rashin hankali ma me ya kaiki shiga har d’akin shi? Ai kad’an kenan daga aikin ‘d’an da Sadiya da Usman suka haifa’, tunda ke dai ban isa in fad’a miki ki ji ba!” Tana gama fad’in haka ta sa kai ta fice tana cewa “Sakina su yi sauri Kaka na jiransu.”

Sakina bata ci gaba da takura mata da tambaya ba. Da ta k’i cin abincin ma kyale ta tayi ta kwashe ta kai waje dan tana so ta d’an huce tukunna sai ta sake tambayar ta.

Haka nan suka shirya suka nufi gidan Kaka. A hanya ma Sakina labarin Yayan wata k’awar su wanda tun suna ss2 yake sonta ta dinga bata, nan take ce mata “ai jiya tana yiwa k’awar tasu magana a watsapp ta turawa Yayan nata numberta, daman duk lokacin da suka had’u idan anje visiting sai ya tambayeta bata da waya, ita kuma tsoron bashi na Ummu take yi
sai gashi kawai yau ya kirata.”

Murmushi kawai Hudan tayi. Tun lokacin da ta fito daga d’akin Ya Junaidu take ta tunani kuma a kaff lissafinta duk in da taje ta dawo to
lissafin nata nuna mata yake
yi ‘bata kyautawa Ya Junaidun ba!’.

Sai da suka jira Kaka, dan suna zuwa suka tarar ya fita sadaka shi da Madu a masallaci kuma sai sun yi azahar tukunna za su dawo. A nan Sakina ta samu damar sake tambayar Hudan
Nan Hudan ta kwashe duk yadda suka yi da Ya Junaidu ta fad’a mata sannan ta k’ara da cewa “ban yiwa Ya Junaidu halacci ba, duk tsahon zamana a gidan nan shi kad’ai ne in yana nan yake k’ok’arin kareni a ko da yaushe baya bari a cutar dani, ni yanzu ban san ya zan yi ba!”

Da mamaki Sakina take kallonta kafin tace “ban gane maganar ‘ba ki san ya za ki yi ba!? Hudan kina buk’atar peace a rayuwarki kuwa? Ya Junaidu fa d’an Umma ne Yayan Jalila k’anin Jaafar sannan d’an Baba!! Kin san me kike yi kuwa? Son shi kike yi?”
Sakina tayi mata tambayar da tsantsar mamaki shimfid’e a kan fuskarta.

Shiruuuu, Hudan tayi kafin chan tace “ba wai maganar so bane, ba zaki gane ba Sakina, ko tayaya zan yi miki bayani ba zaki tab’a ganewa ba.”

A hassale Sakina tace “Rabbi yasa kar in gane!! Duk abunda zai saka in yarda In amince ki auri Ya Junaidu ki bar Ya Arshaad to kuwa Rabbi kar ya fahimtar da ni!”

Shiru kawai Hudan tayi mata tana jin ta tanata faman k’ok’arin fahimtar da ita, k’arshe ma rufe ido tayi kamar mai bacci, nan kuwa Sakina ta k’ule ta rabu da ita ta koma gefe ta d’auko wayarta ta hau chatting. Har suka mik’e suka yi sallah ba wadda ta kula y’ar uwarta..
Hudan ta koma ta lumshe ido Sakina ta ci gaba da chatting d’in ta. A haka Kaka ya shigo ya same su. Cikin ladabi suka gaishe shi, bayan ya amsa ya cewa “Sakina ta tashi ta fita.”

Mik’ewa tayi ta cewa Hudan “ta sameta a d’akin Baaba Talatu idan sun gama zancen” Sai kuma ta cewa Kaka
“Kuma koma dai menene nice uwar gida!!” Dariya Kaka yayi yace
“Ja’ira!” yana mai kallon fitarta sannan ya juyo ga Huda. Babu b’ata lokaci ya sanar da ita. ’ Arshaad ne yake so ya zo ya gaida su, sannan a saka ranar da iyayenshi zasu zo’.

A hankali tace “Zan yi shawara da Mama tukunna!” Da mamaki Kaka ya kalleta kafin yace “Ita Maman naki ce tace min ai kun dedeta da shi Yaron sannan Muhammadu yayi duk wasu bincike a kanshi.” “Eh” ta ce, sannan ta k’ara da cewa “Amman dai ya d’an jira ina buk’atar lokaci.”

Shiruuu, Kaka yayi na y’an mintuna sannan yace “To! Amma tunda dai yace zai zo ya gaishe mu ba wani abun bane ba za a barshi ya zo d’in, maganar turo iyayen nashi kuma sai a jira in kin gama d’aukar lokacin naki ko?”

“To” tace.

Daga nan ya tambayeta ‘makaranta’ da kuma ‘gidan ba matsala ko?’ Nan tace mishi “komai Alhamdulillah a taya su da addua result d’insu yayi kyau!”
Y’ar hira kad’an suka yi sannan ya sallame ta ta tashi ta tafi.

Tun kafin ta k’arasa d’akin Baabaa Talatu take jiyo hayaniya. Da sallama ta shiga nan ta tarar ashe Hajiya Shuwa ce suke ta hira da Sakina kamar wasu k’awaye itama Baaba Talatu tana taya su.

Har k’asa ta durk’usa ta gaida Baaba Talatu dayake itace a farkon d’akin, cikin kulawa da sakin fuska ta amsa mata. Nan ta k’arasa wajen Shuwa itama ta gaida ita amman ko alamun taji ma bata yi ba! Maimaitawa tayi ta sake maimaitawa amman Shuwa tayi mata banza! Nan Baaba Talatu tace
“Taso ki zo ki zauna, zo ki bani labarin makaranta…” Haka jikinta duk yayi sanyi taje ta zauna kusa da Baaba Talatu, tana zama basu wani jima ba Sakina tace “ta zo su tafi k’unshi kar a haye musu layi.”

Nan suka yi musu sallama suka fito.
A hanya sai da Sakina ta bata hak’uri akan halin Shuwa, tace “wata rana zata daina.” Murmushi kawai Hudan
tayi tace “ba komai.”

Haka suka k’arasa wajen k’unshi aka tsantsara musu mai kyau Ma sha Allah, sai yamma suka koma gida a gajiye. Hudan bata waiwayi wayarta da ta bari a gida tun safe ba sai dare shima dan zata haska tayi wanka ne kasancewar garin da zafi sosai.
Tana d’auka kuwa taga misscalls d’in Arshaad, da messages kala kala.
Sai da tayi wankan ta sannan ta kira shi, bai d’auka ba sai da ya katse tukunna ya kirata. Tana d’auka yace “in sun gama waya ta tura mishi number Sakina, dan yaga ita tata wayar bata da amfani.” “Tou” kawai tace tana murmushi, sannan ta bashi hak’uri. Hirarsu suka sha sosai Hudan kamar tana gabanshi sai rufe ido take yi, Sakina na gefe tana chatting tana ta tab’e baki k’arshe ma barcinta tayi ta kyale ta.

Washegari da yamma ya zo, da yaga k’unshi nata kamar ya cinye hannun, yace mata ‘yayi kyau!’ Ya fi sau ba adadi. Duk da tace masa ‘Sakina ta d’auka zata tura mishi anjima amma hakan bai yi nasa sai da shima ya d’auka da wayarshi.

Suna tsaye mota tayi parking a k’ofar gidansu, ita bama ta san Junaidu bane ba dan motar akwai tint. Sai da ya fito tukunna ta ganshi! Ai kuwa nan jikinta ya hau karkarwa A tunaninta zai yi wani abun amman ga mamakinta ko kallon inda suke beyi ba, yayi wucewarshi cikin gida kamar
ma bai gansu ba!

Juyowa tayi taga shima Arshaad d’in Junaidun yake kallo, har ma Junaidun ya shige amman bai bar kallon k’ofar ba, da alama kuma wani tunanin ya tafi. Sai da ta kira sunan shi sannan ya juyo ya kalleta! D’an k’uraa! mata ido yayi kafin yace mata “How are you related to him??”
Cikin nutsuwarta ta fad’a mishi yadda suke a gidan da kuna yadda kakanninsu suke!

Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Hudan hope ba matsala dai ko?
Dan gaskiya na d’an tsorata kad’an! Tunda kinga shi na gida ne.”

Shiruu, tayi kaman tana tunanin wani abun sai kuma da sauri tace “Yauwa, Ya Arshaad, wai kai ne kace ‘kar a sake barin shi ya shiga wajenmu In ya je, a school?”

Shiruu ya d’an k’ura mata ido sai kuma yace “Inji wa?” Ajiyar zuciya ta sauk’e, wanda har sai da yaji kafin tace
“Daman tun jiya na fad’a mishi ‘k’arya me gadin mu yake maka, nasan ba zaka tab’a yin haka ba!’ Wai fa har da cewa kaje kana ta fad’a! Ni kuma na san bama ka iya fad’a ba! Shiyasa tun a nan na gane sharrin me gadin ne.”

Murmushi yayi sannan yace “ni ina na iya wani fad’a, um? Jiyan kun yi magana kenan?? I mean da shi Junaidun.”

“Eh!”

Ta ce.

Shiru yad’an yi kafin yace “Kin je gidan Kaka??” A hankali ta ce “Eh”

Bai yi magana ba itama bata yi magana ba. Chaan! Ta ce “ba wai ina son Ya Junaidu ba ne, amman gara komai ya d’an lafa tukunna, nan ta zayyano mishi yadda suka yi da Junaidun jiya sannan ta k’ara da cewa
“Idan nayi haka ban kyauta masa ba, yayi mini halacci sosai, tun ina k’arama yake raino na, har Mahaifiyarsa yake sab’awa fa duk saboda ni, in dai kaji suna fad’a da ita to akaina ne! Jiya naga b’acin ranshi sosai, kuma ban yi zaton ni yake ta jira ba har ga Allah! Yana ta plans ashe, ni duk ban sani ba. Yanzu idan yaji na banzatar da shi despite abunda ya faru tsakanina da shi a jiya amma kawai na sharesa naje an saka ranana or something like that a yanzun, it’ll break him. Dan Allah ka bani time abubuwa su d’an yi settling. In sha Allah nan da y’an wasu kwanaki, idan ya sak’k’o daga fushin I’ll talk and explain everything to him, daga nan sai ayi maganan mu. Amman yanzu idan wani abun ya faru gani zai yi kamar i don’t even care about him!
Shiyasa ma jiya da naje gidan Kaka…”

Nan ta fad’a masa yadda suka yi da Kakan! Sannan ta ce “Please Ya Arshaad don’t get me wrong, babu abunda ya chanja daga promise d’inmu, ba wai ina son Ya Junaidu bane, kawai Ina so ne in yi mishi halacci ko ta yaya ne, saboda abunda yayi min a rayuwa idan nayi mishi haka lokaci guda ban kyauta ba.”

Tunda ta fara magana Arshaad ya kafeta da ido ko kyaftawa ya kasa yi!
Sai da ta kai aya sannan yace “1 question please” Bai jira jin me zata ce ba yace “If to say, let’s just assume.
Junaidu yace miki yana sonki tun kafin ki tafi school tun farko, zaki kula ni???”

Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “Muna da issue sosai da family d’in Ya Junaidun, ko da ace na yarda Mama ba zata yarda ba.”

“Ba wannan nake tambayar ki ba!
Abunda nake son ji shine a zuciyarki, ki cire family d’inshi, just assume kamar ma babu family d’in nasa a duniya! Za ki iya aurenshi?? Do you love him?’.”

Shiruuu, tayi sannan tace “Ya Arshaad ai kai zan aura yanzu, mun gama wannan maganan. ”

Da d’an fad’a yace “Still kin k’i kiyi answering question d’ina! inda ba na nan da…”

Ganin yadda take kallon shi ne yasa yayi shiru, ya dafe kanshi, ya lumshe idanunsa for some minutes! Kafin ya bud’e yace “Sorry”.

A hankali tace “Ya Arshaad kai zan aura, please ka fahimce ni ba wai ina son shi bane kawa…”

Da sauri ya katseta yana murmushi yace “I understand dear, kawai dama i just want to check ko ‘you have feelings for him’ ne! That’s what the questions are for. ”

Zata yi magana yayi saurin sake katseta, ta hanyar cewa “Bara in tafi, ko?” Yayi maganar yana murmushi!
Bai jira jin me zata ce ba kawai ya bud’e motar ya shiga ya d’aga mata hannu sannan yayi reverse tana kallonshi ya fice a layin.

Jiki a sanyaye haka ta koma cikin gida.
Ko hijabinta bata cire ba Mama wadda gama wayarta kenan da Kaka ta rufeta da fad’a! Kamar zata cinyeta d’anya.
Sannan tace “su tattara kayan su ita da Sakina gobe da sassafe su tafi gidan Ummu, tunda ganin Junaidun da take yi ne yasa take k’ok’arin chanja ra’ayi.
Duk ranar data dawo cikin hankalinta sai ta dawo gidan ayi maganar aurensu ita da Arshaad! In ma bata son Arshaad d’inne tou ta nemo wani
amman ba Junaidu ba!.”

Ita dai Huda karshe ma kuka ta saka. Ta rasa meyasa mutane suke yi mata gurguwar fahimta akan halaccin da take son yiwa Ya Junaidu.

Da kyar Sakina ta lallasheta tayi shiru, kamar zata kira Ya Arshaad amman kuma sai tace bara ta kyaleshi dan duk da bai nuna mata komai ba amma gani take yi kamar ranshi ya b’aci

Washegari da safe da kyar Mama ta yarda suka tayata wanke wanke da girkin safe dan daa cewa ma tayi su tafi kawai, ita Hudan har mamakin Mama take yi, ko d’an motsi taji a hanyar d’akin Junaidu ko alamun za a fito nan zata ce mata ta tashi ta shige d’aki da sauri ko ta turata kitchen!
A haka dai har suka kammala aikin, ita bata ma yi wani aikin sosai ba dan k’arshe kawai Maman ma ce mata tayi ta shiga d’aki daga nan bata sake kiran ta ba! Suna gama breakfast lokacin Mama tana d’akin Baba tana aiki suka yi sauri sukayi wanka dan Sakina cewa tayi “wallahi ba zata fita fuska duk kwantsa ba”. Suna cikin shafa mai Maman ta shigo, tace su yi sauri su tafi ta mik’o musu kud’in mota. Sakina ce ta amsa suka ci gaba da shiryawa a gaggauce dan Mama tsayawa tayi a bakin k’ofa tace ba zata tafi ba sai taga fitar su. Sakina har hijabinta ta saka Hudan kuma tana cikin d’aura zani suka ji kamar jiniyar y’an sanda.
Kafin k’iftawar ido suka jiyo ta a kusa kusa, sai kuma da wani irin k’arfi suka ji an bugo k’ofar gidan!!!

Nan suka tabbatar gidan aka zo…
Hakan ya sanya Sakina da Mama saurin fita itama Hudan ta rarumi hijabinta ta saka ko ribbon da d’ankwali bata tsaya nema ba!

Tana fita jikinta ya hau karkarwa sakamokon sojiji da y’an sanda data gani sunfi ashiri dan taff sun cika gidan.

Kusan a tare Hudan da su Umma da Jalila suka fito, suma duk jikin su karkarwa yake yi ganin sojoji fuskar nan a murtuke, ga uban bundugu.

Wani a cikinsu ne ya k’araso gaban Mama, da kayan sojiji a jikin shi amman nashi ba kalar na ragowan ba ne, yana zuwa ya nuna musu id card d’insa kafin yace “Muna neman Junaidu Usman Bashir! Mun samu order daga sama! Here” ( yayi maganan yana nuna musu wasu takardu ) Ya ce “We have a search warrant and arrest warrant!”

Umma ce ta matso kusa da Huda, a hankali tace “Me kenan??” Kallonta Hudan tayi sannan ta juya ta kalla mutumin tace “Sir, for what please?”

Hannu mutumin ya mik’a baya
nan wani ya taho da gudu ya bashi wasu takardu sannan ya sara mishi ya k’ame! Takardan ya hau bincikawa, sai da yazo kan wata ta tsakiya tukunna ya zarota ya mik’awa Hudan. Da sauri ta sa hannu ta karb’i takardun ta shiga karantawa. Sakina wadda ta matso suke karantawa tare ce ta rafka uban salati sannan tace “Sir this cannot be true he h…” Bindigar da d’ayan ya saita mata a kai ne ya sanyata yin shiru lokaci guda! Jikinta na mugun karkarwa.

Umma kuwa fashewa tayi da kuka tana cewa “Me yayi ake nemanshi har da bundugu? Ku fad’a mana dan Allah!”

D’akunan gidan mutumin ya yiwa ragowan sojojin nuni sannan ya basu order! Nan da na suka shishhiga suka hau bincike…

Su Umma duk suna tsakar gida banda k’arar fashewar abubuwa da fad’uwa ba abunda suke ji…Har kitchen da band’aki sai da suka duba amman babu Junaidu ba labarinshi, basu samu komai ba.

Mutumin ne ya kalli Sakina yace “how are you related to him!” Nan ta fad’a mishi sannan yace mata “Akwai siblings d’inshi ko Mamanshi a nan?” (Duk da turanci).

Direct ta juya ta nuna mishi Umma…
Nan kuwa Umma ta sake rud’ewa ganin mutumin ya nufota tana cewa
“Dan uban ki me nayi kike nunani?”

Da gurbatacciyar Hausar shi yace mata “Ina wayanki?” “Tana d’aki” tace, sannan jiki na rawa ta cewa Jalila “ta shiga ta d’auko!” Ana kawo wayar ya karb’a ya mik’a mata sannan yace
“Ki kira Yaron ki, kice duk abunda ya kayi ya baro yazo yanzun nan, and kar ki bari ya zargi komai! If not, sai na fasa miki kai da bindigar nan”

Jiki na rawa Umma ta hau kiran Junaidu bayan ya umarceta data saka wayar a handsfree. Sai da ta kusan katsewa tukunna ya d’auka!
Daga muryarshi zaka fahimci bacci yake yi. “Kana Ina?” tace mishi. Shiruuu, ya yi. Chaan! Yace “I don’t really know! Ina zuwa, zan kira ki”
Har zai kashe tace “dan Allah duk inda kake kazo yanzun nan kaji??” “To” kawai yace sannan ya tsinke wayar.

Minti talatin mutumin ya bayar, dan haka yana cika yace “Umma ta sake kiran shi”. Misscalls biyar tayi mishi bai d’auka ba, tana shirin yin na shidda suka ji k’arar parking d’in mota! Bai dad’e ba ya shigo cikin gidan. Kayan jikinshi ne na jiya da yamma a jikinsa, amman kamar harda jini jini sannan duk ya yamushe kamar wanda yayi kokawa. Gabanshi ne ya fad’i dan daman tun a waje yayi karo da wasu sojojin, a tunanin shi ba gidan suka zo ba amma yanzu kam ya tabbatar gidan nasu aka zo. Dan haka ya k’araso da wuri! Yana zuwa yana k’ok’arin yiwa su Umma magana sojojin suka rufar mishi suka hau k’ok’arin datsa mishi ankwa!
Ganin haka yasa gaba d’aya suka fashe da kuka har Mama.

Da kyar Sakina ta iya tambayarsu ‘ina zasu kaishi?’. Ba b’ata lokaci mutumin yace mata “K’irik’iri maximum security prison!”

Babu irin kuka da burgimar da Umma bata yi ba har waje amman haka aka saka shi a mota aka tafi dashi! Duk ta tara jama’a. Shi kam Junaidu yama kasa magana dan gabad’aya kanshi a d’aure yake…

Da kyar su Mama suka ja Umma suka maida gida sannan Mama ta kira Baba da su Kaka ta gaya musu halin da ake ciki.

                 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 27So Da Buri 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×