Skip to content
Part 26 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Abun duniya duk ya bi ya taru ya ishi Mamy. Hakan yasa ta mik’e, hijab d’inta kawai ta d’auka ta nufi gidan Mom.

Tana shiga kuwa kamar had’in baki ta tarar da Ummi itama a falon. Sai da ta nemi waje ta zauna suka d’an gaisa tukunna tace “Alhamdulillah! Da na sameki a nan.”

Murmushi Ummi tayi kafin tace
“Me kuma ya faru yanzu?”

Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e sannan tace “Aaima da Arshaad ne! Wai ace Yaran nan har sun san su had’e mini kai suna k’usk’us a tsakanin su?” Sai a lokacin tukunna Mom tayi magana, tace “Haba Mammy, ai abin farin cikine ma ace y’ay’anka sun had’e kai, kinga bakida matsala kenan dan babu mai iya shiga tsakaninsu!”

Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Na san da wannan Adama, amman abunda nake so ki gane shine ‘da ace abun kirki suke k’ullawa to da sai nafi kowa farin ciki !’.

Kin tab’a jin labarin wasu Yara da Aaima take gaya min Arshaad d’in ya kai ya had’ata da su?”

Shiruu, su Mom d’in suka yi kamar masu k’ok’arin tuna wani abun kafin chaan! Mom tace “‘Sakina’ kamar naji tace ko? Wadanda take cewa d’ayar Yarinyar tana kama da Aslam.”

“Allah yayi miki albarka Adama, su dai. To wai d’ayar fa yake so, shine suketa k’us k’us d’insu.

Jiya Arshaad d’in inaga har kuka yayi wai ko tak’i d’aukar wayarshi ko fad’a sukaa yi, Oho musu dai.”

Ummi ce tace “amman Yaron nan anyi ja’iri! Yanzu ya za muyi da maganar Khadija?? Kin san ko jiya sai da na had’u da Mahaifiyarta a wajen gyaran farce. Tana ta tambaya ta ya sirikinta
harma take gaya min next week khadijan zata dawo ta kammala masters d’inta.”

“Banda Arshaad ma dai da abinshi, da class d’insa da komai amma shine zai je ya d’auko mana wachchar?? Daman wallahi ni jikina sai da ya bani.

A yanayin labarin Aaima kamar fa har provision shi yake yi mata lokacin da suke makaranta.” Cewar mom

Da sauri Mammy tace “kinji ko! D’azun nan kuma ya gama cemin ‘ai she’s very rich waye waye kawai dai iyayenta sunyi choosing ta tafi a scholarship ne waye waye’.”

Murmushi Mom tayi tace “k’arya yake yi! Aaima ai ta tab’a bawa Auwal Labari, tace Yaran ko ishashshen turanci basu iya ba, ita ta dinga yi musu lesson lokacin tana chan, da zata tafi ma sai da ta had’asu da wasu.
Waenna Yara da suka samu good foundation a makarantar kirki ne za a ce basu iya turanci ba saboda Allah??
Kawai dai k’ok’arin watsa mana k’asa a ido yake yi.”

Mammy kamar zata yi kuka tace “Ni ba wannan ne problem d’ina ba, dan bai auri Khadijah ba (ya watsamin k’asa a ido) shi ya sani!! Ni babban bak’in ciki na kar ya d’auko min Yarinyar da bata waye ba! Bana son had’a jini da su kwata kwata, zuciyata zata iya bugawa! Kuma yadda yake son Yarinyar nan, in dai ya aure ta to shikenan ni da shi sai dai kallo daga nesa! Dan na san janyeshi zata yi gaba d’aya, gata kuma y’ar matsiyata na san ta dinga sakawa yana yiwa iyayenta abubuwa kenan, a gindinsu kud’insa zasu k’are!”.

Murmushi Ummi tayi sannan ta dafa kafad’arta kafin tace, “Ki kwantar da hankalinki, Granpa fa ba zai tab’a yarda da wannan had’in ba, kin san yadda yake.”

“Um um fa! Granpa d’innan ba a gane mishi alk’ibla, kar mu dogara dashi yaje ya watsa mana k’asa a ido, mu dai nemo wani solution d’in gaskiya, dan wallahi koni naji bana son Yarinyar tun kafin a je ko’ina, kuma daga gani yana sonta over ma kuwa! Kina ji fa wai jiya har da kuka , k’ato dashi.”
Cewar Mom.

Ummi ce tace “na san ba a ganewa Granpa alk’ibla amman dai kin san ya fiki k’in son had’a jini da talakawa ko? Ki tuna Aisha fa.”

Mom ce ta katseta ta hanyar cewa “Ai bamu gama confirming ya yanayin gidan su Yarinyar yake ba! In aka yi rashin sa’a kuma ta fito daga middle class kinga ai an gama magana, dan Granpa ba lalle ya hana ba. Kawai mu bama son Yarinyar ne, in ya aure ta akwai matsala kar ya manta da mu da uwar shi, and ke kinfi kowa sanin ulterior motive d’inmu akan auren shi da Khadija, ko?”

Shiru Ummi tayi sannnan tace “hakane kam gaskiya, to anjima ki sa Auwal ya bugi cikin Aaima mana, na san ba zata san lokacin da zata fad’a mishi komai ba.”

“Bama magana da shi, amman zuwa anjima d’in ke ki kirashi ki tamabaye shi maybe zai yi.”

“Me ya had’aku, har ba kwa magana?“
Ummi ta tambayeta da mamaki akan fuskarta.

Murmushi Mom tayi sannan tace “ba komai, ki manta kawai wani issue ne daban”.Tana maganar tana satan kallon Mammy. Ita kam Mammy gaba d’aya hankalinta baya kansu, ta tsunduma duniyar tunani, kawai zooming take yi gashi har anyi auren Hudan da Arshaad, Hudan tasa Arshaad ya daina kulata, ita kuma sai bauta yake yi mata daga ita sai iyayenta! Yana ta kula da ita ‘Hudan’ baya son ganin b’acin ranta ita kuma ‘Mammy’ an ajjiyeta a gefe.

Sai da Ummi ta d’an tab’a ta tukunna ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi. Fahimtar yadda duk ta gigice da suka yi ne yasa sukaita k’ok’arin kwantar mata da hankali tare da alk’awarin zasu saka Auwal ya bugi cikin Aaima, daga nan sai su san abun yi.

Da kyar dai suka samu Mammyn ta d’an kwantar da hankalinta.

Da yamma kuwa, Auwal yana dawowa daman Ummi tayi mishi message ‘tana son ganinsa’, hakan yasa wanka kawai yayi ya nufi gidan. Bayan sun gaisa ne take gaya masa dalilin kiran “So suke yi ya bugi cikin Aaima, akwai wata Yarinya budurwar Arshaad da suka fahimci yana mugun so har Mammy yake yiwa jainja a kan Yarinyar, bayan already anyi maganarshi da Khadija!
Therefore, suna son sanin gidansu da yanayin Yarinyar, daga nan sai su san abun yi.”

Murmushi kawai Auwal yayi bayan ya gama ji, sannan ya mik’e tare da yi mata alk’awarin ‘in shaa Allah zai binciko musu!’. Daga haka yayi mata sallama ya fita a gidan ranshi fess!!!

Yana komawa b’angaren su direct d’aki ya wuce ya d’au waya ya kira main driver na estate d’in na yanzu,
dayake daman shima duk bakin su d’aya Micheal! Cikin girmamawa, Micheal ya gaishe da Auwal, nan Auwal ya zayyano mishi abunda yake so yayi mishi sannan ya kashe wayar, yana wani killer smile.

A ranshi yake tunanin abunda zai yiwa Arshaad, tunda dai gashi an tabbatar mishi yana mugun son Yarinyar!
Su Ummi kuma ko sun sake yi mishi maganar kawai zai ce musu ya manta ne dan bayaso su shigo case d’in ba tare da ya gama abunda ya shirya ba.

Su Arshaad suna fita a farm center suka fara tsayawa, ya na shiga direct shagon wani mutum inda yake siyan abu a wajenshi especially games ya tsaya. Yana zuwa mutumin ya dinga gaidashi yana cewa “ai da yayi waya da kawai gida za a kawo mishi”
Murmushi kawai Arshaad yayi yace mishi “sauri yake yi shiyasa, sunada iPhone 12, mini?” Da sauri mutumin ya zagaya ya hau fito mishi da su birjik kala kala sabbi k’al sannan yace suna da second ma..”Da sauri Arshaad yace
“No need for second!” Duk colours d’in ba suyi mishi ba dan babu blue a ciki, hakan yasa ya tanbayi mai shagon.

“Eh bamu da blue gaskiya, amman akwai case blue kala kala sak wanda ka zab’a!” Jinjina kai Arshaad yayi yace “a kawo”.

Colour d’in da Aaima ta gaya mishi royal blue ya zab’a mata mai mugun kyau sannan yace “a saka mishi d’aya a leda a bashi accnt number” har zai tura kud’in sai kuma yace “a kawo iphone 11 mai kyau itama da case”
Nan aka bada, ya sayi sim biyu ya had’a yayi mishi transfer mutumin sai godiya yake yi, har mota ya rako shi.

Suna shiga ya nuna mata wayoyin, murna sosai ta dinga yi tun bama da taga harda ta Sakina ba, ta san za suji dad’i sosai.

Daga nan shopping mall suka nufa suka yi mata siyayyar duk abunda suke tunanin tana so, itama Sakina suka d’an siya mata, sannan suka fito suka kama hanyar gidan su Huda.

Jikin Aaima ba k’aramin sanyi yayi ba, da taga yanayin gidan, duk sai taji tausayin Hudan ya lullub’e ta duk da kuwa cewa an mugun gyara gidan ga sabon fenti anyi wanda duk aikin Junaidu ne, business din gidan gona yake yi kuma sana’ar ta mugun karb’ar shi dan har mota ya siya da fili, yana gininshi mai kyau.

“Ya naga kin yi shiru? Nace ki d’auka ledan da zaki iya ki shiga, sai ki ce mata Ina waje.” Muryar Arshaad ta katsewa Aaima tunani. Ledan wayoyin da wata k’arama a baya Aaiima ta d’auka ta shiga gidan. Tun kafin ta k’arasa shiga ta hango Huda na sharar tsakar gida, a hankali ta k’arasa shiga ta ce “assalama alaikom” Hudan da taji kamar ta san muryar ce ta d’ago, ai kuwa suka had’a ido! Dariya tasa tace
“Laaaa Aaima!” Wanda hakan ya jawo hankalin Sakina da take wanke wanke a bakin rijiya, itama tana ganin ta kuwa ta taso tayo wurin da sauri.
Bud’e hannuwanta Aaiman tayi ta d’an kar katar da kanta tana murmushi kafin tace musu “Surprise!!”Ai kuwa da gudu suka je suka yi hugging nata sunata dariya.

Mama da take a d’aki, jin hayaniya yasa ta fito tana cewa “Huda, waye ne?” Ita a tunaninta ma Ummu ce ta zo. Ganin yadda suka ruk’unk’ume Aaima suna k’ok’arin kayar da ita ne yasa Mama ta hau salati ta fara yi musu fad’a tana “meye haka, ni Maryama yaushe Yaran nan zaku girma ne? Ku cikata mana ta k’araso.”
Cikata suka yi sannan ta samu ta k’araso cikin gidan. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Mama.

Da sauri Mama ta kamo ta tace “sannu da zuwa Aaima, ya gida? Yau ke ce kika zo mana, barka bismillah shigo.”

Dariya Aaima tayi tace “a’a Mama bari dai in ajjiye mayafi na in yaso sai in taya Anty Huda aikin.” Da sauri Hudan ta b’uya a bayan Sakina tace “Kaii Aaima Allah bana so.” Murmushi duk suka yi sannan Mama tace “Ai sun ma k’arasa, shigo ki huta, ko?” Ba yadda Aaima ta iya haka nan tabi Mama d’aki, sakina ta kawo mata ruwa sannan ta koma d’an k’arasa wanke wanken data kusan k’arasawa.

Sai after kamar 5 minutes haka tukunna Hudan ta shigo ta zauna suka sake gaisawa da Aaima. Ledojin da ta shigo dasu ta mik’awa Mama tana cewa “wai gashi inji Ya Arshaad,
d’ayan na Huda ne, wannan
kuma, tayi magana tana zaro iphone 11 d’in tace “na Sakina ne” Daidai kuwa da shigowar Sakina. Da sauri ta k’araso, tana kallon ledar, tana gama ganin yanayin wayar ta daka uban tsalle tana murna! Hannu ta sa zata karb’a wayar a hannun Mama, Maman ta buge hannunta tana harararta. Tura baki tayi tana sosa wajen, nan kuwa Aaima da Huda suka dinga yi mata dariya.

Mama ce ta katse dariyar tasu ta hanyar cewa “Aaima ba za’a yi haka ba! Waennan wayoyin ai sun yi musu girma! Ina lefin irin tawa mao tachila tafi sauk’i sauk’i ai, duk da ban san kud’in waya ba amma waennan wayoyin daga ganinsu na tabbata za su yi tsada! Ba a son maida hannun kyauta baya, shiyasa ba zan ce ba za a karb’a kwata kwata ba amma ga wayoyin in kin koma gida kice mishi nace ‘ya chanjo musu mai tochila irin tawa, an gode’.” Aiima har zata yi magana kawai suka ji Sakina ta fashe da kuka!!

Maficin da yake ajjiye a gefen gado Mama ta hango, ai kuwa ta rarumoshi ta yunk’uro kanta, da gudu ta mik’e tayi hanyar k’ofa tana share hawaye tana cewa “haba Mama taki wayar fa bata chatting!” Kanta da taga Mama tayo gadan gadan tana shirin maketa ne yasa ta k’arasa fita da gudu.! A bakin k’ofar tana fita suka yi gware da Jalila wadda ta lab’e har da d’an sake turo kai! Ture ta Sakina tayi tace
“Shegiya munafuka!! A haka zaki k’are!.”

Jalila dake duk kunya ta isheta ga kuma kishi da al’ajabin daya rufeta ‘tabbas wannan Arshaad d’in da gaske yake fa!!’ Shiyasa kawai bata kula Sakina ba ta wuce ta kyale ta tayi d’akin Ummanta.

A tsakar gida Sakina ta nemi waje ta zauna tanata karantowa Mama addu’o’i akan ‘Allah yasa ta barsu su rik’e wayoyin’, irin wayoyin da take gani a hannun Malaman su y’an gayu da kuma wasu students ne fa da suke shigowa dasu a b’oye!.

A d’aki kuwa babu yadda Aaima batayi ba, amman Mama ta dage akan ‘sai dai
a mayar a karb’o musu mai tochila!’
Haka nan Aaima ta hak’ura ta cewa Mama “Ya Arshaad d’in ma yana waje yana son ganin Huda ne.” Fad’a Mama ta hau yiwa Aaiima tana cewa “ai da ta fad’a tun wuri, an barshi a waje ko ruwa ba a kai mishi ba…” Huda ta cewa “ta nemi ruwa ta kai mishi akwai ragowan pure water a cikin randa ta nema cups ta d’aura a tray ta fitar mai da shi.” Hakan kuwa aka yi, Huda ta fita iya kuma Aaima ta je tsakar gidan wajen Sakina.

Yana cikin mota a zaune yana waya da Aslam. Tana fitowa kamar ance ya d’ago..yana d’agowa ya ganta sanye cikin wani maroon hijab har k’asa wanda ya sake fito da ainihin kyau da hasken kalar fatarta, tayi kyau matuk’a!

Ba wani kwalliya tayi ba dan ba komai a fuskarta sai k’asan eyelid d’inta da ta zizirawa kwalli amma tayi kyau sosai.
Tsayawa kawai yayi yana kallonta! Ya bar Aslam yanata ‘hello hello’ shi kad’ai! Karshema ajjiye wayar yayi a gefe ya d’aura hab’arsa a kan sitiyarin motar yanata kallonta.

Ta cikin glass d’in gaban motar taga irin kallon da yake yi mata hakan yasa ta ja hijabinta ta rufe fuskar gaba d’aya.

Murmushi yayi ya bud’e motar ya fito ya k’araso inda take yasa hannu ya karb’a tray d’in sannan yace “Thankyou, but pls ki bud’e fuskanki, dan wallahi idan kika fad’i anan dariya zan yi.”

Hannu tasa ta d’an ja hijab d’in fuskarta ta bayyana amman ba duka ba, yana kallon yadda take chuno d’an k’aramin pink lips d’inta. Murmushi kawai yayi sannan yace “how are u?” yana mai k’arasawa inda motar take ya d’aura tray d’in a kai. “Alhamdulillah” tace mishi sannan ta gaidashi. Cikin kulawa ya amsa kafin yace mata “tana son wayar? Tayi mata ko a chanzo?”

Murmushi tayi tayi masa godiya, kafin tace “Amman Mama tace sai dai a mayar a karb’o mana mai tochila.”

“Woow!” Yace, yana zaro ido sai kuma ya d’an yi dariya kafin yace “Haba Mama dan Allah tayi hak’uri, mai torchlight kuma? Ta yaya zamuna yin chattn tou da su video calls?”

Murmushi kawai tayi tace “Haka itama Sakina tace” sai kuma tayi dariya tace “Sakina har da su kuka.”

“Ai da gaskiyan ta, bari kiga da kaina zanje in rok’i Mama.” Da sauri Hudan tace “A’a Ya Arshaad, kayi hak’uri
Mama fad’a zata yi min bayan ka tafi.”

Murmushi yayi yace “zan yi yadda ba zatayi miki fad’a ba, kinji cute Baby.”

Tafukan hannayenta ta sa da sauri ta rufe fuskarta tana murmushi k’asa k’asa, shima murmushin yayi yana bin hannun da kallo kafin yace “Yaushe zaki yi k’unshi? irin black henna d’innan da ake zanawa a bayan hannu, yana kyau sosai, i like it.”

Murmushi tayi kafin tace ana yi a mak’otan gidan Kaka, daman yana nemana ya ce ‘inje gobe’, idan naje daga nan sai in yi.”

“No ki bari akwai wata ta iya sosai a instagram na gani zan kaiku ayi muku har da su Sakina.” Dasauri tace
“Suma wannan d’infa sun iya sosai ma…”

Murmushi kawai yayi kafin yace “Okay, as u wish, my cute Baby.”
yana d’an kallonta yana murmushi..
Murmushi itama tayi sannan tace “Ya Arshaad”

“Naam, Babyn Arshaad”
Ya amsa still yana kallonta yana murmushi. Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “Na gode sosai, dani da Sakina mun gode da yadda ka taimaka nayi karatu, if not bcause of you da ba zan yi ba, i don’t think i can ever repay you.”

Murmushi yayi yana d’an cizon lower lips d’inshi kafin yace “Babu godiya fa a tsakaninmu Baby, na fad’a miki tun rannan, so ki daina yi mini godiya
Ok??” D’aga mishi kai tayi alamr ‘to’.
Dariya ya d’anyi sannan yace “Idan ma akwai wanda za muyi wa godiya tou wannan Karen ne daya tuso ki ya kawo ki har inda nake.” ya fad’a yana dariya. Itama dariyar tayi sannan ta d’an b’ata rai tace “Allah ni ka dai na, ba na so” cikin sigar shagwab’a. K’ok’arin gimtse dariyar yayi yasa hannu ya d’an d’aura akan lips d’inshi sannan ya ci gaba da cewa “Dama ace zan sake ganin Karen nan, to da waje guda zan ware a gidan gonata a gyara a yi ta kiwon shi har k’arshen rayuwarshi. Saboda a ta dalilinshi ne na gano cewa real true love da kuma love at first sight yana existing…

Maganar ‘yadda za kiyi repaying d’ina kuma just marry me Huda, promise to be mine forever shine kawai abunda zaki yi, and also ki soni kamar yadda nake sonki, koma bai kai haka ba, just try ki soni ko yaya ne kuma ni kad’ai, saboda I don’t think it’s possible ki soni ma the way I’m loving you dan son zai iya haukataki! Saboda ni kaina wani lokacin in kika fad’o min a rai sai na had’a da addu’o’i, sometimes fa har gizo kike yi min. So kawai ni dai just love me, love only me and marry me yadda zan nuna miki ragowan so da k’aunan da nake miki! That’s all I’m asking for, it’s more than enough.”

Gani yayi Hudan na shirin nitsewa cikin k’asa sannan sai k’ok’arin b’oye fuskarta take yi. Shi dariya ma ta bashi, shi kam wannan kunyar ta Huda gaskiya tana cutar dashi da yawa, shi kenan bashi da daman expressing abunda yake ji Murmushi kawai yayi yace “To nayi shiru na daina, kar ki nutse k’asa Dan Allah.”

Still bata d’ago ba dan ita kam ya gama kafe ta ne awajen yau kam.

Murmushi ya sake yi Sannan cikin k’ok’arin son ganin ta sake dashi yace “tou bara in baki satar amsar kiran da Kaka yake miki, kina son ji?”

Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’ amman bata d’ago ba. Kamar wani k’aramin Yaro haka ya mak’e kafad’ar shi sannan yace “Na k’i wayon, sai kin d’ago tukunna zan fad’a.”

Murmushi tayi kawai ba tare da ta d’ago d’in ba, hakan yasa yace “ok shikenan, kyaji In kinje gobe.
And one more thing, ranar Sunday in Allah ya kaimu zan kawo miki babban bak’o! Yayana zai dawo daga Uk Saturday in sha Allah so Sunday za muzo.”

Murmushi tayi kafin tace “Allah ya nuna mana.”

Hira sosai Arshaad yayi mata (dan ita Hudan duk kunya ya hanata sakewa) daga baya yace “ga kaya ta shiga dasu sannan tayi mishi iso shima zai shiga ya gaida Mama.”

Hakan kuwa aka yi bayan ta gayama Mama ta shimfid’a darduma a y’ar varender simintin gefen d’akinsu
Sannan ta fita ta ce mishi ya shigo kamar yadda Mama ta umarceta.

A tare suka shigo gidan da tray d’in d’azu a hannunta hakan yasa ta wuce kitchen bayan ta nuna mishi inda zai zauna. Tana ajjiyewa ta shiga d’aki ta cewa Mama yana waje ita kuma suka zauna suka ci gaba da hira da Aaima.

Mama tana fitowa, a chaan nesa da shi ta samu waje ta zauna suka d’an gaisa. Bayan sun gama gaggaisawa ne yace mata “kyauta ne, wasu ma suna mota, kawai dama yaga ya dace ne ya bawa Sakina da Hudan, dan Allah a karb’a kar ace a’a.” “Angode” kawai Mama tace, dan bata iya doguwar magana da shi, gaisuwar ma da suka yi duk gefe take kallo tana ta faman sunkuyar da kai.

Sallama yayi mata yace “ya gode, bari su tafi yanzu.” Bayan ya fita Mama ma mik’ewa tayi ta shiga ta cewa Aaima yana jiran ta sannan ta had’o mata su tsami gaye da gullisuwa da alawar madara harda kuka da tsamiya ta bata tace “ta kaiwa Mamansu tace tana gaisheta.”

Aiima ba k’aramin dad’i taji ba, har ga Allah Mama ta shiga ranta, in ka kalli matar kwata kwata ba zaka tab’a bata shekarunta ba, baza ma ka ce ta haifi Hudan ba! A hakan kuma Hudan tace mata ‘sai da aka yi 10 yrs ma tukunna aka haifeta’ Ga matar kyakkyawa over, gata da son ado ba zaka tab’a cewa bata dashi ba kullum tas tas da ita, tun ranar farko da suka fara had’uwa taji matar ta burgeta, ga kawaici da kirki.

“Muje ko in raka ki sannan in yiwa Ya Arshaad godiya.” Aaima taji muryar Sakina, itama Hudan mik’ewa tayi suka d’unguma suka fita dan yi mata rakiya.

A bakin mota suka ganshi a tsaye, tun daga nesa da ya kalli Sakina ya gane tayi kuka dan fuskar nan tayi jajir abunka da farar fata sannan manyan idanuwanta har sun k’ank’ance. Murmushi yayi dai dai suna k’arasowa yace “Sakina rikici! Sis kuka ya k’are ko? Mama ta bar ki ki rik’e wayarki.”

Murmushi tayi tace “Ya Arshaad ai Maman ce Allah kuwa, wai fa me tochila dan Allah, ita gani take yi me tochilan nan itace first class a duk wayoyi, ai bari inyi charging wayana idan na kunna mata flash sai ta tsorata.” Dariya sosai Arshaad yayi sannan yace “Mama ma fa kenan, wannan ban san ya kike yiwa grannies d’inki ba”

Itama dariyan tayi sannan tace “Ya Arshaad mun gode sosai Allah ya saka da alkahairi.”

“Ba komai sis take care, but register fa ya za ai dashi na sim d’in?”

Kar ka damu ana yi a nan ba nisa harma settings na wayoyin anjima duk zan je in sha Allah.”

“Ok, hakan yayi” yace sannan ya zagaya ya d’auko ledojin biyu yace
“Naki d’azu Aaima ta shiga dasu, ungo wannan ki taya wifey d’auka!” Ya fad’a yana kallon Huda wadda ita shi d’in take kallo.

B’ata rai yayi dan kar ma ta fad’i abunda yake tunanin tana shirin fad’a…Ganin ya b’ata rai yasa kawai tace “Mun gode”

Sannan ya zaro kud’i a aljihu bandir y’an 500 ya bawa Sakina yace “su saka kati kuma gobe ta raka ta gidan k’unshi ta tabbata anyi mata, jibi zai zo ya gani in sha Allah.”

Dariya Sakina tayi tace “kar ka damu Ya Arshaad ko gida yanzu haka ba zan shiga ba zan wuce in kama mana layi, gobe In muka je ko waye a wajen dole ya matsa ayi mata.”

Dariya Aaima da Arshaad suka yi, ita kuwa Huda sai k’ok’ari take su had’a ido da Sakina tayi mata warning da ido dan bata san taya zasu shiga gida da wannan kud’in ba! Kayan ma tunanin da take tayi kenan. Sakina sarai ta ganta amman ta shareta…A haka cikin raha suka rabu kamar kar Aaima ta tafi…

Motar tana wucewa Hudan ta finciko Sakina tace “Sakina baki da hankali ko? Kin iya jan rigima!! Mama zaki nunawa kud’in nan kice mata ‘an bamu mun sa hannu mun karb’a’, ko wa kike tunanin nunawa??”

Dariya Sakina tayi dan k’arara take hango tsoro da firgici a idon Hudan…
Hannu tasa ta fakaici idonta ta fincike mayafinta sannan ta k’arasa soro ta ajjiye ledan hannunta da kud’in akai tace “gashi ki k’arasa da su ciki na tafi kama layi, a yi miki fad’an ke kad’ai!”
Tana dariya haka ta wuce ta barta a wajen.

Hudan rasa ya zata yi tai, idan tace itama ba zata shiga ba, za ace sun dad’e, idan kuma ta shiga fad’a ne!
Ba yadda ta iya haka nan ta kwashi kayan ta kai d’ayar ledar ta ajjiye a bakin k’ofar d’akinsu, ta dawo ta d’auki d’ayar itama ta wuce ciki.

A bakin k’ofar d’akin nasu taga Mama tana duba ledar…Kallonta take yi tana kallon ledan da kuma wadda ke rik’e a hannunta kafin tace “Daga ina?”
K’asa Huda tayi da idonta tace “duk shi ya bayar.”

Ai kuwa nan Mama ta rufeta da fad’a….har da cewa ta kai k’arar ta wajenshi shiyasa ya shigo yace “tai shiru” waye waye, ta inda take shiga bata nan take fita ba, tunba ma da Hudan ta nuna mata kud’in k’unshi da ya bayar ba.

Sai da Mama ta yiwa Hudan tass tukunna ta kyale ta, kuma tace “ko da wasa in ya sake bata abu ta karb’a ranta sai yayi mugun b’aci, kuma kar ta kawo mata shi ya rok’eta!”.

Allah sarki Hudan har da kukanta, dan in akwai abunda ta tsana to fad’a ne, gashi Mama yau tafi awa d’aya tana abu d’aya, sai tayi shiru sai taci gaba.

Wani abun takaicin Sakina bata dawo gidan ba sai wajajen 5, tana shigowa Hudan ta had’e rai! Ba yadda bata yi ba amman tak’i kulata, daga k’arshe dai hak’ura tayi ta kyaleta taje ta samu Mama tace mata “bara taje ta kai wayoyin register daga nan tanaso zata je gidan su Kaka sunada solar, sai ta saka charji.”

“Ai kun fi k’arfi na yanzu, kuyi duk abunda kuke so.” Shine abunda Mama tace.

“Kiyi hak’uri Mama” Sakina tace tana d’an rausayar da kai.”

“Umm”

kawai tace taci gaba da aikinta da Huda tayi tayi akan ta bari ta tayata tak’i yarda.

Ganin gidan ya koma kamar gidan makoki yasa kawai Sakina ta d’au wayoyin ta d’auki abun buk’ata ta fice.

Bayan ta gama yi musu register taje ta jona musu wayoyin su, bata dawo ba sai bayan isha lokacin har Hudan tayi bacci. Kusan tare suka shigo gidan ita da Umma wadda ta fita unguwa tun safe!! God knows where.

Sakina ko gaisheta bata yi ba tayi wucewarta dan har yanzu tana jin haushin abunda Jalila tayi. Tana jin Umman tana zaginta harda ce mata “y’ar karere! Gidan sai kace na ubanta ne.” Uffan Sakina bata ce mata ba, ita abun ma dariya ya bata.

Umma kuwa takaici kamar ta had’iyi zuciya. Haka ta shiga d’akinta tana cewa “Allah ya kaimu gobe sai dai Alhaji ya zab’a ko ni ko wannan mara kunyar Yarinyar data raina mutane kamar kashin gindinta!”

Duhu d’akin sosai! Hakan yasa tace
“A’a Jalila wai har kin kwanta ne?
Ko kuwa dai kawai yau bid’ar zama a duhun kike yi?” Tana maganar tana k’ok’arin kunna fitilar wayarta.

Tana kunnawa fitilar ta haske dai dai kan fuskar Jalila wadda ke kwance kan gado!Ba a gane fuskartata tsabar kukan da taci, tayi sharkaf da gumi!

Da sauri Umma tayi kanta tana rafka salati.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 25So Da Buri 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×