Babu yadda Mama da Sakina basu yi da ita akan ‘ta fad’a musu abunda yake damunta’ ba amman tak’i! Mama data gaji mik’ewa tayi ta nufi hanyar k’ofa tana cewa “ai daman tunda aka ce ya kirawo ki na san a rina! In banda rashin hankali ma me ya kaiki shiga har d’akin shi? Ai kad’an kenan daga aikin ‘d’an da Sadiya da Usman suka haifa’, tunda ke dai ban isa in fad’a miki ki ji ba!” Tana gama fad’in haka ta sa kai ta fice tana cewa “Sakina su yi. . .