Skip to content
Part 30 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

D’akin da d’an duhu amman ba chan sosai ba sakamokon side lamps d’in da suke a kunne wanda hakan ya bashi daman hango ta kwance a kan gadon.
A hankali ya k’arasa ya zauna a gefen gadon.

A kwance take, rigingine, pillows wajen uku aka d’aura kanta a kai hannayenta duka biyu tayi folding d’insu a kan cikinta! Kalar fata ta iri d’ayane da ta Aslam, sai dai shi ya d’an fi ta haske kad’an. Babu d’ankwali a kanta, wanda hakan ya bawa gashin kanta damar baiyyana wanda yake nan rabinsa bak’i rabi furfura! Mai santsi da shek’i had’e da tsaho sosai.

Shekarunta ba zasu wuce hamsin ba…kallo d’aya tak! Zakayi mata ka gano kyakkyawa ce ajin farko. Yanayin hancinta ne Aslam d’in ya d’auko sai dai nata har ya d’an so yafi nashi tsayi da tsaruwa amma saboda yanayin na Yarinta yasa za’a iya cewa ya fita kyau.

Hannunshi ya saka ya kamo nata sannan ya d’aura d’ayan hannun nasa a kai ya dunk’ule a hankali ya saka guiwowin hannayenshi a kan gadon for sopport kafin ya d’aura fuskarshi a kan hannayen nasu!

Tunani ya fara ‘rabonshi da ita yau shekaru bakwai! Kenan.

Tun lokacin da psychiatric Doctor d’inta yace musu “the last option d’in da suke dashi shine a kulle su a d’aki d’aya, daga ita sai shi sannan a d’aure hannayenta da k’afafuwanta gudun kar ta cutar da shi ko ita kanta. Hatta abinci ana so ya zamana shi ne zai dinga bata a baki, yayi mata alwala yayi mata komai for 24 hours! May be daga hakan tayi snapping out, ta dawo cikin hankalinta.”

Tun a 12 hours Aslam ya ga ba zai iya ba domin kuwa tak’i chin abinci kuma daga ya matso kusa da ita sai ihu! K’arshe ma suma ta fara yi. Gabad’aya duk ta firgice. Ganin haka yasa ya d’auki waya ya kira Dad wanda shima d’in jin da yayi tanata suma yasa yace “bara ya zo ya gani.” Sannan ya kira Doctor, shima Doctor d’in yace gashi nan zuwa.

Dad d’in yana zuwa yayi knocking k’ofa Aslam ya bud’e, basu ankara ba kafin ya shigo ta taho da gudu ta hankad’o Aslam d’in waje ashe ta kunce hannayenta ba tare da ta bari ya lura ba! A take ta saka key…

Ba suyi wata wata ba Aslam ya fara k’ok’arin b’alla k’ofar Dad kuma ya tafi ya d’auko spare key!…Amman ko da ya zo ya saka k’ofar k’in bud’uwa tayi sakamokon barin key d’in da tayi a jiki ta ciki. Suna cikin kiciniyar bud’ewa suka ji k’arar fad’uwar abu kamar kujera, a rikice Aslam yayi kan 3 seater d’in da take a parlourn ya cewa Dad “ya zo ya kama mishi”. Haka suka kinkimi kujerar da kyar, suka yi kan k’ofar da gudu da k’arfi suka buga!
Allah ya taimake su kuwa ta bud’u.

Aslam kasa motsi yayi sakamokon ganin k’afafuwanta a sama suna lilo kanta kuma tayi hanging a jikin chandelier d’in d’akin, sai dai k’afafuwan nata still suna d’an motsi!!.

Dad ne yayi k’arfin halin shiga da gudu ya d’auki kujerar data taka ta sak’ale kan nata ta yar! Ya saita mata ya d’aura kafafun nata a kai sannan ya hau ya kunto ta, sai dai zuwa wannan lokacin bata motsi!.

Shi dai Aslam duhu kawai ya fara gani daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba.

Sai da ya farfad’o tukunna ya fahimci ashe suma yayi. Yana farfad’owa Dad da Arshaad suka yo kanshi suna tambayar shi jiki. Cikin tsananin tashin hankali , muryarshi tana rawa yace “Dad ta mutu ko? Shikenan nayi silar mutuwar mahaifiyata!!”

Da sauri Dad yace mishi “Bata mutu ba Aslam, suma kawai tayi.”

A tunanin Aslam kwantar mishi da hankali kawai Dad yake k’ok’arin yi, shiyasa yak’i yarda da zancenshi har sai da Dad d’in ya kaishi ya ganta ta window tana zaune Gwaggo Asabe tana bata abinci a baki hannunta kuma ana mata k’arin ruwa!.

Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace
“Alhamdulillah” Ba a dad’e bai aka yi discharging d’inshi. Auna komawa gida ko gama dedeta parking d’in mota bai bari Dad yayi ba, ya fito cikin hanzari ya nufi cikin gidan.

A d’akinsa Dad ya sameshi yana ta kiciniyar had’a kayayyakinsa, gaba d’aya ya sauk’o da akwatina ya hargitsa d’akin da alamun komai da komai yake son tattarawa dan hatta games d’insa suka har yayi parking nasu a daban.!

Da sauri Dad yaje ya rik’e mishi hannu. Yana juyowa yace “Dad please! Don’t stop me i’ve to do this..”

“Shh” d’in da Dad ya ce mishi ne ya sanya shi yin shiru. Ji yayi Dad d’in ya rungume shi ya fashe da kuka.

Sai da Abba da Daddy suka shigo tukunna suka iya lallashin Dad! Dan Aslam shi kam ya ma kasa cigaba da magana in banda ajiyar zuciya babu abinda yake ta faman sauk’ewa!.

Bayan sun yi shiru ne Abba yayi suggesting “Aslam d’in ya je side d’inshi ya zauna, ba lalle su dinga had’uwa da ita ba in yana chan.”

Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e kafin yace
“Abun nata kamar har da aljanu fa, dan indai suna a waje d’aya tou bata sakewa koda kuwa basu yi ido biyu ba!
Daman wajen da yafi dacewa yaje idan irin haka ta faru shine gidan Gwaggo Asabe tou itama yanzu mijin nata ya rasu a gidan itama take! Sannan y’ay’anta(Gwaggo Asabe)duk ba wani girman Aslam d’in suka yi ba ballantana a ce yaje gidansu ya zauna!
Babbar 3 years ta bashi, k’aramar kuma 2 months.

So kawai ni a nawa tunannin gara in tafi dashi Abuja…”

Aslam d’in ne yace musu “Dan Allah kawai yana son barin k’asar gaba d’aya! In komai ya lafa sai ya dawo…”

Haka nan ba yadda suka iya, ganin halin da yake ciki yasa suka amince ya tafi’

Kiran sallar farko ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi!
A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, idanuwan nan nasa sun kad’a sun yi jazir! Sannan jijiyoyin goshinsa duk sun yi rud’u rud’u!
A hankali yace “Mommy, please this time around don’t push me away!
Ko menene kike ji ki yi k’ok’ari ki danne ki yi fighting…..i don’t want to run anymore! All my life tun Ina js 1 nake boarding school, hutu kuma sai dai inje inyi a wani waje! I don’t want this life anymore, it sucks it hurts, i need you…” A hankali yace “I’m all alone, please get well.”

Motsi yaga ta fara alamun zata farka hakan yasa ya d’an matso da hannunta (wanda tun d’azun yake a cikin nashi) saitin lips d’inshi, a hankali yayi kissing hannun nata sannan ya mayar mata shi kan cikinta ya mik’e da sauri ya fita dan yaga motsin nata ya tsananta

Sai da yayi sallah yayi azkar. Ya dad’e yana karatu tukunna bacci mai dad’i ya kwasheshi around 8:40 am.

Jin ana tab’a shi ne yasa ya fara k’ok’arin bud’e idanunsa, dishi-dishi yake ganin Arshaad kafin ya fara ganinshi sosai yana yi masa murmushi. Mik’a yayi yai salati sannan ya d’an Mike ya gishingid’a a jikin gadon kafin yace “Morning,
You look energetic! Amman ni kam to me yau d’in lazy Sunday ne..so good bye, baccin bai ishe ni ba.” Yana shirin sake komawa ya kwanta Arshaad ya rik’esa, sannan yana dariya ya zaro wayarshi ya nuna mishi screen d’in.
Kalla Aslam yayi sai kuma ya zaro idanu yana kallon shi kafin yace “you serious!! 2:00 as in 2:00 na pm?”
Dariya Arshaad yayi, cikin gatse yace “a’a, na am.”

Da sauri Aslam ya sauk’o akan gadon yana cewa “subhanallah ya akai time ya tafi haka! Ban yi sallah ba fa!”
Sannan ya fad’a toilet cikin sauri, bai fito ba sai da yayi wanka. D’aure da bathrobe bak’a ya fito kanshi na digar ruwa, a gurguje ya zura jallabiya sannan ya tada sallah. Sai da yayi addu’o’i bayan ya idar, tukunna, ya mik’e ya nufi akwatinshi.

Arshaad wanda yake chattn da Huda, yanayi sama sama yana kallonshi yana mamaki yadda Aslam d’in yake shiryawa, dan duk k‘ak’ale k’ak’alenshi Aslam kam ya fi sa. Ya shafa wannan ya fesa wanchan ya goga wannan duk shi kad’ai! Sai da ya gama tsaf tukunnan ya zaro wasu riga da wanda masu masifar kyau, wandon black rigar kuma grey.

Sai da ya fara saka wandon tukunna ya zare jallabiyar ya saka singlet da rigar ya sake fesa turare sannan ya zo inda Arshaad yake ya zaune tukunna ya sa hannu ya warce wayar!.

Kallon screen d’in yayi sai kuma da sauri ya mik’awa Arshaad d’in wayar sakamokon heart heart d’in da ya fara gani tun kafin ma ya kai ga karanta chat d’in.

Dariya Arshaad d’in yayi kafin yace “saikace kaga dodo?Shine surprise d’in da nake ce maka zan nuna maka, yau za muje ma ku gaisa, i’ve told her already.”

Shiruuu, Aslam yayi for some minutes, chaaan! Ya nisa kafin yace “Arshaad a brotherly advise. Ka tabbata Yarinyar da kake so is suitable for Granpa, kar kaje ka d’auko wadda kai da ita duka zaku sha wahala! Idan har ka san she’s not fit to be in this family to kar ma ka fara, kar ka wahalar da kan ka itama ka wahalar da ita. Saboda i’ve seen a lot! A duk lokacin da na zauna nayi tunani sai inga duk matar da aka auro cikin family d’innan ba tare da yarda Granpa d’ari bisa d’ari ba to sai tayi ending somehow! Take my Mom for example, ita da Anty Maryam Those two ladies, zan iya ce maka they are the nicest of all amman ka duba ka gani halin da suka tsinci kansu a ciki,
har gara ma Anty Maryam dan na san yanzu kam ita maybe tama yi wani auren kuma definately sun shirya da iyayenta, Mommy fa? She‘s still in hell!! Both me and her! I’m not saying wai Granpa ne ya d’aura mata rashin lafiya or something like that, tunda God knows waye ya jefota a bene that very day! But case d’in Anty Maryam da Abba kam laifinsa ne dan ranar ina nan a gaba na yace “ko Abba ya saketa ko kuma ya d’aureta a jail! Kuma bama a Nigeria ba, daga ita har iyayenta zai d’aure sannan kuma ya tsine mishi!
Wai ai daman ya gayawa ita Anty d’in cewa ‘babu ita ba gidan shi da family d’inshi kwata kwata!’ Amman shine relatives d’inta suka kwaso k’afa suka zo mishi estate, dan haka she has to pay a price, for not listening to him…”

Gramma tana kuka tana bashi hak’uri Abba ma haka amman tsohon nan haka ya tursasa su. The only person da nake jiyewa ni a wannan time d’in is Anty Maryam, saboda idan kaga kalar korar Karen da Mahaifinta yayi mata time d’in data koma gida zaka yi mamaki!”

Shiruu, Aslam yayi, chaan kuma ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “idan nace zan tsaya baka labari to ban san ranar barin mu d’akin nan ba. All I’m saying is kar ka zab’o wadda zaka sha wahala itama ta sha wahala, kuma azo ayi ta case! Shiyasa nake jiranshi nake kuma addu’a, saboda ni kam idan nayi mixing up issue na love da wanda nake ciki a yanzu! I don’t think i can make it out…”

Ahankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace “Thanks”
Kafin ya mik’e yace mishi “muje ka fara gaida su Granpa se sai wuce ko?”

“Not now, ai muna da aiki a gabanmu, although lawyer d’inka yace min za ayi postponding case d’in wai an kashe C J ko?”

“Eh fa” Cewar Arshaad.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ina son zuwa gaisuwa ma fa!”

Kallonshi Arshaad yayi kafin yace “Ka san shi ne?”

“Eh. Yayan wani classmate d’ina ne
Immediate i think! He’s not that old..
Da kyar ma aka bashi saboda age d’inshi, bai ma dad’e da yin aure ba.”

Da mamaki Arshaad ya d’an kalleshi kafin yace “Naji ance har da yaran shi biyar…”

Cikin katse shi Aslam yace “yeah, yana da triplets!” Cikin son kawo k’arshen maganar yace “Allah yaji k’anshi.
Let’s talk, na san ba za a d’u lokaci ana mourning d’inba. Mu san abun yi tun lokaci bai k’ure ba.”

A hankali Arshaad ya koma ya zauna ya fad’a mishi dalla dalla yadda Auwal yayi tricking d’inshi yayi signing pappers d’in da komai da komai…

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “to kayi mishi zancen zaka mayar da kud’in??”

K’asa Arshaad yayi da kai sannan yace “shiyasa yanzu nake so idan mun je ka tayani bashi hak’uri ya yarda ‘ya karb’i kud’in ayi withdrawing case d’in’. Kuma ai kasan Granpa yanzu abun ma fitar mishi a kai zai yi, tunda ka san yadda yake baya son jira kwata kwata, ina ga idan aka d’aga k’arar ba lalle yayi ta jira yana jira ba maybe ya hak’ura.

“Understood” Shine abinda Aslam yace sannan suka d’an sake tattaunawa kafin yace “muje in fara gaida Mammy tukunna kafin muje mu sameshi.”

Suna fita a babban parlour suka tarar da Gwaggo Asabe. Tana ganinshi ta mik’e kafin tace “Yau kam an sha baccin gajiya gaskiya ga d’an wake shima ya gaji da jira..”

Murmushi yayi sannan ya gaidata bayan ta amsa suka nufi dining ya zauna. Babu yadda bai yi da Arshaad akan yaci d’an waken ba amman yak’i, yace “shi yana reacting to kuka.”
Haka nan Aslam ya cinye abinshi daga nan suka mik’e suka nufi gidan Mammy…

Basu sameta a k’asa ba sai da suka haura sama a parlourn sama suka sameta a gaban makeken show glass d’inta tana zuba turaren wuta a burner! Arshaad ne gaba sai Aslam a bayanshi, shiyasa da Mammyn ta juyo bata lura dashi sosai ba. Kallon Arshaad d’in tayi tace “kai da waye? har ka dawo? Ya naga baka dad’e ba?”

Murmushi yayi sannan yace
“Eh, bak’o na kawo miki ne, shiyasa.”

Da fara’arta take k’ok’arin lek’a bayan Arshaad d’in tana cewa “waye? to matsa mana in gan shi….”“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!!” Shine abunda ta furta a mugun tsorace!! Bata san lokacin da burner d’in turaren wutan nata ya fadi daga hannunta ba a lokacin da Arshaad ya matsa Aslam ya baiyyana a gabanta!

Duk tsayawa suka yi suna kallonta…

Da sauri ta juya ta kaiwa Arshaad d’in duka kafin tace “Uban ka!!! wannan ai sai kasa zuciyata ta buga! Shekara bakwai ban ganshi ba kawai yanzu In ganshi a gabana ya kake tunanin zan ji?”

Dariya dukkan su suka sa kafin Mammy ta share kwallarta ta jawo Aslam d’in jikinta ta rungumee tace
“Welcome home son, we really miss u.”

A hankali ya zare jikinshi yana d’an murmushi kafin ya sa hannu ya share mata hawayen daya sake zubo mata
Yace “Miss u too, Mammyn mu.”
Yana d’an murmushi.

Kafin minti biyar tuni Mammy ta cika gaban Aslam da kayan chiye chiye sai tambayarshi takeyi “me za a dafa mishi?” Arshaad kam ya koma gefe sai faman kumbura yake yana mitar “shi an share shi daman ai ya san tafi son Aslam a kan shi!”. Suna cikin haka Aaima ta shigo. Ihun da tayi sai da suka tsorata duk suka d’ago suna kallonta ai kuwa da gudu ta taho ta fad’a kanshi tana murna itama har da hawaye, duk ta kanainaye shi.

Sai da yayi mata fad’an ‘bata san ta girma ba?’ tukunna ta d’aga shi tana d’an jin kunya ta koma gefe ta zauna…
Nan suka hau gasar bashi abinci a baki, sunk’i ma su bari yaci da hannun shi! Sai da Aslam ya cewa Mammy “zai yi amai!!” tukunna ta kyaleshi.

Ranshi fess!! Haka suka baro b’angaren Mammy a ranshi yana yaba so da k’aunar da familynshi suke yi mishi babu wani maganar y’an ubanci a tsakaninsu!.

Suna fitowa daga gidan da shirin shiga gidan Granpa suka ji ana kiran sallar la’asar! Hakan yasa suka nufi masallaci kawai, suna zuwa suka yi alwalla aka tada sallah.

Sun idar kenan Aslam ya juya yana y’an kalle kallen yadda aka tsara Masallacin aka sake gyarawa karaff! Ya had’a ido da Granpa wanda ya tsareshi da idanu, murmushi yayi sannan ya cewa Arshaad “taso mu je”
Suna mik’ewa suka ga shima ya mik’e ya fice waje, da sauri suka fito Arshaad yana cewa “da alama yau za kuyi fad’an farko kai da mutumin naka!”.

A bakin wata bishiya suka sameshi, suna zuwa Arshaad ne ya fara cewa
“Good afternoon Granpa” Banza Granpa yayi dashi bai ko juyo ba shiyasa ya koma gefe ya tsaya
Aslam ma ya matsa yace mishi
“Good afternoon Granpa.” Shima yayi banza da shi. Murmushi Aslam d’in yayi sannan ya k’arasa inda yake yayi hugging d’inshi ta baya…

Sai a lokacin ne na tab’a ganin murmushin Granpa!, ashe har dimple gareshi…

A hankali yasa hannu ya d’anyi tapping hannun Aslam sannan ya d’an juyo lokacin da Aslam d’in ya cika shi..
Still da k’ayataccen murmushi kwance a kan kyakkyawar tsohuwar fuskar shi.

Yana juyowa yace “yanzu ka dawo?”.

“A’a jiya around 2:00 am”.

“A time d’in da muka yi chat ma ka taho kenan?”. “Eh, ai its a surprise.”

Murmushi Granpa d’in ya sake yi sannan yace “I’m amazed! Welcome home. How have you been?”

“Alhamdulillah” Aslam yace.

A hankali Granpa d’in ya juya sannan yace mishi “walk with me..”

A tare suka d’an fara tafiya. Haka nan sai da suka kusan zagaye estate d’in, suna tafe suna hira, Granpa yana tambayarshi yanayin aiki da kuma zamanshi a chan shi kuma yana bashi amsa. Duk wanda ya ga Granpa a wannan rana to ya san yana cikin farin ciki. Zagayowa suka yi ta wajen gate d’in shi dan haka ya cewa Aslam d’in “bara ya shiga ciki akwai wasu y’an takardu da zai duba.” Har ya juya yaji Aslam d’in yace “Granpa pls i need a favour” Juyowa Granpa d’in yayi kafin yace “If it is about Arshaad don’t even go there, i won’t change my decision he must pay for wat he did!!”

Da sauri Aslam yace “Wallahi Granpa framing d’inshi aka yi, kuma zai dawo da duk kud’in suna accnt d’inshi bai tab’a komai ba tunda daman ba sata yayi ba ballantana ya tab’a.”

Shiruuu, Granpa yayi, na d’an lokaci, chaan! Kuma yace “Framing?”

With full confidence Aslam yace mishi “Yes, zamu iya maka presenting evidence! Please Granpa, give us a chance.”

“Aslam, today I’m in a very good mood saboda na ganka, so zan iya yi mishi sassauchi.

Sassauchi na shine ‘ya kawomin evidence d’in cewa framing d’inshi aka yi, ni kuma daga nan zan janye case d’in, for your sake!”

Durk’usawa Aslam d’in yayi cike da farin ciki yace “Thanks a lot Granpa, za a kawo evidence d’in in sha Allah.”

A hankali Granpa ya shafa lallausan gashin kanshi sannan yace “Allah yayi maka albarka.”

“Ameen” ya ce sannan ya mik’e
yace zai shigo zuwa anjima su gaida gramma in sha Allah.” Daga haka ya juya ya tafi, shima Granpa ya shige.

A bakin masallaci inda ya bar Arshaad a nan ya same shi “Sorry. Na barka kana ta jira ko?”

Murmushi kawai Arshaad yayi sannan yace “Um um! Someone kept me busy.”
Yayi maganar yana nuna mishi chat d’in da yake yi da Hudan.

Murmushi Aslam yayi kafin yace “muje dai inga Yarinyar da ta haukatamin kai haka.”

Dariya Arshaad yayi. Da sauri Aslam yace “Um good news! Granpa yace muyi presenting evidence to him daga nan case ya mutu!.”

Cikin murna Arshaad yayi hugging Aslam sannan yace “Thanks a lot na gode!”

A hankali Aslam yayi murmushi yace “NVM”. Sannan suka fara tattauna akan yadda zasu nemo evidence d’in…suna maganar suna tafiya…

A hanyar shiga gidansu Aslam Arshaad ya hango motar Auwal da gudu ta taho. Har Auwal d’in ya wucesu sai kuma yayi reverse ya dawo ya fito a motar ya zagayo ya zo inda suke. Yana zuwa ya kalli Aslam sannan yayi murmushi yace “Ashe ka dawo! Shine ba ko irin ‘Hi’ d’in nan?”.

Murmushi Aslam yayi kafin yace “Hi, Auwal. Ya gida?”.

“I’m gud, gida kuma ai tunda kana tare da little brother d’inka i’m pretty sure ya fad’a maka everything da cases d’in da suke faruwa da komai, right?”
Auwal yayi maganan yana kallon Arshaad yana murmushi! Kafin ya d’an juyo da sauri to Aslam d’in yace
“Oh I almost forgot, na san ba zai tab’a fad’a maka wannan ba or maybe shi kanshi bai sani ba”. A hankali ya matso kusa dasu yad’an kare gefen bakin shi da tafin hannunshi kamar bayaso a ji kafin a hankali yace “Because nima, i eavesdrop” Sannan ya matsa yana d’an murmushi kafin ya fara magana “last 3 months an fitar da Mommy India and her psychiatrist yayi conforming ‘she’ll never get better, domin kuwa duk wani therapy medication treatment duk sunyi amman duk a banza!’. I don’t know why you choose to come back now, saboda home is not a fit place for you anymore! Anyways, it’s gonna be fun dan zan dawo ma gidanku ne da zama saboda in dinga watching dram.”

Naushi kawai yaji Arshaad ya d’auke shi da shi yana huci!! Ya daga hannu zai k’ara mishi wani Aslam wanda idanuwanshi suka koma kamar garwashin wuta yayi saurin ruk’o shi..
K’ok’arin fisgewa Arshaad d’in ya fara yi, da k’arfi Aslam ya daka mishi tsawa yace “Mu shige ciki’” Juyowa Arshaad d’in yayi zai yi mishi magana amman sai ganin yanayin da yake ciki yasa kawai ya juya zai shiga yaji an ruk’o shi, ya riga ya san Auwal ne shiyasa ya juyo a fusace amman bai gama juyowan ba ya rama naushin da yayi mishi sannan yace “This should be the last time da zaka yi punching nawa, if not kaga ta wanchan gidan!?” ya yi magana yana nuna gidan su Arshaad d’in kafin yace “Wallahi a kanta zan rama, ko ban rama da hannu na ba zan saka ayi mata and it might not end well! So be very careful.”

Yana gama fad’in haka, ya juya ya shiga motar shi ya ja Aslam kuma ya ja hannun Arshaad suka shige cikin gidan. Direct side d’inshi suka wuce ba wanda yace ‘k’ala’ asalima Arshaad d’in d’aki ya shige ya bar Aslam a nan kwance a parlour kan 3 seater, dan ko had’a ido da shi baya son yayi sakamokon tausayinshi da kuma haushi da suka hadu mishi guri guda! Abun Auwal kullum k’ara gaba yake yi ya rasa dalili. Shi kuwa Auwal
Sai da ya koma gida ya chanja kaya dan waennan duk sun yi squeezing!
Tukunna ya saka turare ya zira wayoyinshi a aljihu ya fito ya fice daga estate d’in. Kamar yadda suka tsara..motar mike tana gaba tashi tana baya, suna zuwa unguwar gandun albasa layin su Huda, mik’e din ya fito daga tashi motar ya nuna mishi gidan daga d’an nesa. Sallamar sa Auwal yayi sannan yace mishi “zai iya tafiya”
Shi kuma ya tada motarshi ya k’arasa k’ofar gidan.

Da mamaki yake ta kallon gidan!
A take kuma sai yayi murmushi yana rayawa a ranshi ‘winning d’in Yarinyar da entire family d’inta will be an easy job ta hanyar kud’i tunda ya lura basu da shi!’.

Yaron da yazo wucewa ya d’an yafito alamar ‘yazo’. Yaron yana zuwa ya d’auko 1k a wallet d’inshi ya bashi kafin yace “ya shiga gidannan yace wai Jalila ta zo inji Arshaad.” Da gudu Yaron yayi cikin gidan bayan ya karb’i kud’in. Yana shiga ya tarar da Umma tana wanke wanke! K’arasawa yayi inda take ya gaisheta sannan yace
“wai ana kiran Jalila a waje inji Arshaad!” Umma da kamar bata ji ba tace “me ka ce?” Sake maimaita mata yayi, aikuwa da sauri tasa hannu ta toshe bakinshi gudun kar Mama ta jiyo.

Kallan k’ofar d’akin Maman tayi sai kuma ta juyo…k’asa k’asa tace “ka je ka ce gata nan zuwa yanzu.”

Sannan ta mik’e har tana tuntub’e ta nufi d’akinta har da d’an gudun ta!.

Tana isa ta tarar da Jalila ta bararraje akan gado tanata uban bacci!
Duka ta tak’ark’are ta maka mata..
Aikuwa da ihu Jalilan ta tashi.

Da sauri ta sa hannun ta toshe mata baki kafin ta jijjagata tace “Watstsake dan uban ki!! Ki tashi ki je ki wanke fuskar ki yanzun nan! Ga Arshaad chan a waje yana jiranki.”

Jin an anbaci sunan ‘Arshaad’ yasa ta bud’e idanuwa da sauri sai kuma ta mik’e tayi waje.

A bakin rijiya ta wanke idanunta da bakinta, kafin ta dawo cikin d’akin, tuni har Umma ta fitar mata da kayan da zata saka da powder da jan baki da turarurruka kala kala da takalmi, duk a cikin kayan da su Huda suka kawo mata.

Tana zuwa ko minti biyar ba tayi ba ta shirya. Har zata fita Umma ta sake janyota ta mik’a mata janbakin tace “ta k’ara bai yi ba, sannan ta sake fesheta da turarurruka har suna tari!

Tukunna tace “ta je!” Har da binta har tsakar gida ta karantto ta tofa mata alhamdu k’afa d’aya!

Daga nan ta dawo d’akin ta hau tattare inda suka zuzzubar da kayan da ta cire tana cewa “Yau gashi da kanshi yace Jalila yake son gani! Maryam sai naga ta inda zaki nunamin d’agawa yanzu ai!!

Shima Arshaad d’in shegen Yaro! Wato ya gama da Huda shine yanzu ya dawo kan Jalila! Ai kuwa baai san inda ya zo ba, dan nan kam idan mutum ya shigo to baya fita!

Na san yau kam har kakan had’a ido sai kun yi! Magana ta k’are! Kuka na ya zo k’arshe daga yau in sha Allah.”
Ranta fes! haka ta tattare d’akin ta fito domin k’arasa wanke wanken ta.

Jalila tana fita ta hango wata dandatsetsiyar mota a parke! Murmushi tayi sannan ta k’arasa inda motar take ta kwankwasa marfin…

Sai da ya d’an jima yana k’are mata kallo ta cikin tinted glass d’in…a ranshi yace “not bad tana da kyau! Amman bata yi yellow d’in da mike yake ta faman zuzutawa ba!”.

A hankali ya d’an zuge glass d’in iya idanuwanshi suka fito sannan yace “zagayo ki shigo mana.”

Jalila ba wani sanin Arshaad tayi sosai ba tunda duk ganin ta dashi ta lek’e ne
amman dukda haka taso ta gane ba shi bane ba daga yanayin muryar da idanun!

Jin hucin sanyi da yake tab’ota da wani azababben k’amshin turaren da yake fesowa ta cikin motar da kuma kwad’ayi shiga taga ya yanayin motar take ta ciki yasa kawai ta zagaya ta bud’e ta shiga ta zauna.

Tana juyowa kuwa suka yi ido biyu wanda ko da ace bata san shi sosai ba ta san wannan ba Arshaad bane ba, hakan yasa a d’an tsorace tace
“Waye kai? Kace sunan ka Arshaad!”.

Murmushi yayi, sannan yace,
“Relax ni k’anin shi ne.”

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e sannan tace “Aiko ka yayi?”

Girgiza kai yayi sannan yace “ni na aiko kaina.”

Bai jira jin me zata ce ba
dan yadda take kallon motar da yanayinta tun farkon fitowarta ya gano zata yi saurin shiga hannu! Musamman idan an yi amfani da kud’i.

A hankali yace

“Listen Jalila, ni mutum ne mai magana d’aya kuma idan zan yi abu kai tsaye zan yishi babu b’oye b’oye!
Farko farkon zuwan Arshaad ya tab’a zuwa dani sau d’aya amman ban fito ba a mota na tsaya thats when i saw u and since that day i have feelings for you!

Kawai daurewa nake yi saboda babu yadda zan yi. Har satar wayar Arshaad nake yi in yi sending pics ba tare da ya sani ba So something happened last week i don’t know if you are aware, ko kuma ya b’oye miki. An zab’a mishi matar da zai aura a gida har an kai kud’i Na san maybe baki sani ba dan naji yana cewa Mammy “he is going to hide it from you till after d wedding, honestly i don’t know wat he is planning on doing with you. Ni dai aurene ya kawo ni wajenki, kuma mu a family d’inmu idan Namiji yayi aure sai yayi 20 years ya zama stable sosai tukunna za a barshi ya sake yin wani auren Are u ready to wait for him for 20 years??” Yayi mata tambayar yana kafeta da idanuwa…

Matsowa yayi kusa da ita, ya kama hannayenta sannan yace “Ba zan taba yaudarar ki ba nikam, just trust me, zan so ki tsakani na da Allah and a shekarar nan in sha Allah za muyi aure!”

Ahankali yaji tace “Tam.” Sannan ta sunkuyar da kanta k’asa.

Murmushi yayi amman chan k’asan zuciyarsa yana mamakin saurin amincewarta haka. Cikin son k’ara gasgatar da wani abu taji yace
“But promise me, ba zaki gayawa Arshaad muna tare ba, saboda abun zai iya zama case, and na san definately sai ya rabamu, bayan shi yana chan da tashi amaryar!
Nafi so sai ranar da aka d’aura aurenshi, da kamar 1 week tukunna ya sani, muma kinga kafin nan an fara maganar namu auren ko?”

A hankali ta d’aga mishi kai, alamun amincewa.

D’an murmushi yayi kawai ya sake rik’e hannunta, a haka ya d’an dinga janta da hira yana nan rike da hannunta gam yana d’an matsawa lokaci zuwa lokaci.

Sama sama take amsa mishi iya wanda ta fahimta dan rabi da turanci yake magana kuma slanz, Gabad’aya ta k’agu yace zai tafi dan yadda ya matso gab da ita da yadda ya rik’e mata hannu kwata kwata she‘s not comfortable!

Sun yi kusan 1 hour a motar tukunna ya mik’o mata wayarshi yace “ta saka mishi numberta!”

Shiruu, tayi chaan! Tace “zan kiraka idan na saka layin a wayar Umma anjima, kai ka bani numberka.”

Shiru yayi yana d’an kallonta kafin yace “Baki da waya?” A hankali ta d’aga mishi kai. Da mamaki ya d’an kalle ta yace “Taya kuke waya to? Ko bakwa yi kwata kwata?”

Girgiza kai tayi alamar ‘a’a’ kafin tace
“Ai ina saka layi na a wayar Umma lokaci zuwa lokaci.”

D’aya daga cikin wayoyinshi ya zaro….wadda bai dad’e da fara anfani da ita ba!

Gf d’inshi ce ta bashi ranar birthday d’inshi.

Bincika wayar yayi sai da ya tabbatar bashi da wani abu important a ciki kafin ya cire sim d’in shi ya mik’a mata wayar sannan yace “Idan kin shiga sai ki saka layin naki a nan.”

Kallonshi tayi sai kuma ta kalli wayar kafin ta sa hannu ta karb’a. D’an zuba mata ido yayi alamun jiran godiyarta yake yi amman sai yaga ita murmurshima take ta yi tanata dudduba wayar tana juyawa
Ganin dayayi batama da shirin yi mishi godiya ne yasa kawai ya share
ya zaro card d’inshi ya bata yace “ta kirashi ga number shi” Kafin ya sake zaro y’an bandir d’in 5hndred ya mik’a mata yace gashi “ta saka kati!” This time around ko d’an jinkirin da tayi first time na karb’ar waya ma bata yi ba da saurinta ta sa hannu ta karb’a tana murmushi.

Shi kam kasa daurewa yayi hakan yasa ya ce mata “Ba ko y’ar godiyar nan?”

Kunya ta d’an ji sai kuma ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “Na gode.”

Murmushi yayi ya d’an kalli agogon hannunshi kafin yace “Bara in wuce sai naji kiranki ko?”.

D’aga kai tayi ta juyo ta kalleshi tana murmushi.

Shima murmushin ya mayar mata sannan ya d’an yi waving nata yace “bye” kafin yad’an matso ya bud’e mata marfin motar..

Sai taji kamar kuma kar ta fita
saboda bata son barin sanyi.

A hankali tasa k’afarta ta fita sannan ta d’an juyo tace mishi “sai anjima.”

Har zata fara tafiya taji yace
“Remember, don’t talk to him about me yet!” “To” kawai tace kafin ta juya ta wuce cikin gida.

Binta yayi da kallo yana mamakin ‘me Arshaad yake planning akan Yarinyar nan? Da farko da yaga gidan ya d’auka maybe ko saboda kyau ne! Da kuma ya ganta, thou se is beautiful but not to the extend da zaace a guy like Arshaad yayi laying down level d’inshi yazo nan ba Sai ya fara tunanin may be nutsuwa da hankalinta da tarbiyya ne ya jawo hankalinshi gareta! But in less than 1 hour ya fahimci kwata kwata Yarinyar bata da nutsuwa da kalan tarbiyyan da ya kamata ace Arshaad ya sota!.

So wat is he up to? Saboda ya san ko giyar wake yasha ba zai tab’a tuntub’ar Granpa a kan auren Yarinyar nan ba! Sai dai idan ko yayi secret marriage ko ya siya musu gida b4 the wedding Ko kuma ma kwata kwata ba aure ne ya kawoshi wajenta ba! Dan ya lura Yarinyar in dai za a bata kud’i to da alama zata yi komai ma! A ranshi kuma sai ya ce

“But ai Arshaad is not a humanizer”
Wata zuciyar ce tace mishi “Kai dai kawai kaga mutum ka kyaleshi, baka san me yake aikatawa behind closed doors ba!”.’

Murmushi yayi kafin yace “Koma dai menene, na san cewa its important to Arshaad! Ni kuma nayi alk’awarin sai na lalata komai in sha Allah.

But Yarinyar nan anya kuwa zan iya tolerating d’inta ko dai kawai mu dinga waya ina turo mata kud’i dan gaskiya she is not my type! Amman kuma anya zata yarda da ni yadda nake buk’ata? Ba tare da ina zuwa muna had’uwa ba kuwa?…”

Da waennan tunane tunanen ya ja motarshi yayi gaba.

                 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 29So Da Buri 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×