Cike da farin ciki Jalila wadda take ji kamar an tsundumata a Aljannah ta shiga cikin gida! A tsakar gidan ta tadda Umma da alama ita take jira.Ko k’arasowa Jalilan bata yi ba Umma ta hango wayar hannunta da kud’in!
Tana zuwa ta bud’e baki zata yi magana kenan Umman ta rufe bakin, ta jata d’aki.
Har da rufe k’ofa bayan sun shiga wai duk dan kar a jiyo su!
Abunda bata sani ba ‘su Sakinan su kam ba ma sa cikin gidan’ dan tun safe Khadija ta kira su tace “dan Allah su. . .