Skip to content
Part 31 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Cike da farin ciki Jalila wadda take ji kamar an tsundumata a Aljannah ta shiga cikin gida! A tsakar gidan ta tadda Umma da alama ita take jira.
Ko k’arasowa Jalilan bata yi ba Umma ta hango wayar hannunta da kud’in!

Tana zuwa ta bud’e baki zata yi magana kenan Umman ta rufe bakin, ta jata d’aki.

Har da rufe k’ofa bayan sun shiga wai duk dan kar a jiyo su!

Abunda bata sani ba ‘su Sakinan su kam ba ma sa cikin gidan’ dan tun safe Khadija ta kira su tace “dan Allah su zo ita da Huda su taya ta zab’ar kayan da zata yi amfani dasu da bikin nata.”

Suna shiga d’akin k’asa k’asa
Umma tace “Ya kuka yi da shi?baki yayi??” Tayi maganar tana kallon hannun Jalilan kafin ta sa hannu ta karb’i wayar ta hau jujjuyawa.

Ajiyar zuciya Jalila ta sauk’e sannan ta jefar da mayafinta a kan gado ta nemi guri kan kujera ta zauna kafin tace
“Ba Arshaad bane ba! Wai k’aninsa ne, sunanshi Auwal!”.

Da mamaki Umma take kallonta kafin tace “Ikon Allah, me ya ce miki tou? Me ya kawoshi? Arshaad d’inne ya turo shi?”.

“A’a, wai ce mini yayi wai Arshaad d’in aure zai yi, wai an zab’a mishi wata a gida. Shi kuma Auwal d’in wai yana sona ne zai aure ni! Sannan wai in yi shiru kar inyi magana da Arshaad d’in de komenene dai ni dai ban gane ba gaskiya.”

“Ikon Allah!” Shine abunda Umman tace kafin ta sake cewa “To ai Alhamdulillah.”

Nufar wardrobe d’insu tayi mai b’allalliyar k’ofa. Wajen kayanta ta hau bincikawa da alamun akwai abunda take nema…

Cike da son jin k’arin bayani Umma ta matso kusa da ita tace “Jalila ki juyo ki yi mini bayanin da zan gane dan ni sam ban fahimci zancen ki ba.” A d’an razane kuma sai ta tab’ata sannan tace
“Ince dai ba Hudan zai auraba ko? Shi Arshaad d’in!”.

“A’A” Jalilan tace, kafin ta sake cewa
“Kina jina fa nace miki ‘a cikin danginsu aka zab’ar mishi mata!
A yadda na fahimta kamar ma fa bai gayawa ita Hudan ba har yanzu.”

Wata kalar dariyar mugunta Umma tayi sannan tace “Allah shi k’ara!
Sai wani faman hura hanci suke yi su a dole y’arsu zata auri mai kud’i!
Ai ga irinta nan.” Sai da ta d’an yi shiru kamar mai tunani kafin ta sake cewa
“Ikon Allah, wani hanin ga Allah baiwa ne…Kiga fa babu yadda ban yi dake akan ki fita ku had’u da Yaron nan ba amma Allah bai yi ba! Yanzu fa da tuni ke zai yaudara ya gudu yaje ya auri wata kinaji kina gani. Daman nifa an dad’e ana gaya min cewa ‘In kwantar da hankalina, ba Mijinta bane ba!’.

To Amman shi wannan d’in in ce dai mai kud’i ne sosai shima, ko Arshaad d’in ya fishi?”.

Juyawa Jalila wadda ta nemo layin ta da kyar a k’ark’ashin hargitsatstsun kayanta, tayi, tana murmushin tambayar! Sai da ta amshi wayar daga hannun Umma ta k’arasa ta zauna a kan yagalgalalliyar kujerar d’akin ta fara neman inda zata saka layin a wayar tukunna ta fara magana “Ai Umma, ba wai Arshaad d’in ne mai kud’in ba Inaga kamar Babansu ne mai kud’in! Domin kuwa shima wannan Auwal d’in yadda kikaga Arshaad tou haka yake. Da had’add’iyar motar da gayun da yanayin turancin duk! Kina gani kin san ya tsumu a naira! Kinga fatar jikinshi kuwa? Tafin hannunshi laushi kamar.”

Shiruuu, Jalila tayi ta daina k’ok’arin neman inda zata saka layin a wayar, kamar tana tunani.

Mik’ewa ta yi taje inda Umma
take tsaye kafin tace “Amma Umma gani nake yi kamar d’an iska ne wannan d’in, ina shiga motar fa ya hau rik’e min hannu! Gabad’aya ma ni kasa sakewa nayi da shi sosai. Kuma ni Umma har ga Allah Arshaad nake so!
Inaga gara kawai ki san yadda zakiyi kawai a fasa auren nashi! Dan ni ya fi kwantamin a rai, shi wannan Auwal d’in gaskiya jinina bai wani d’auke shi ba! Watak’ila mafa kinga d’an iska ne!.
Idan ya zo kar In sake fita ko? Harda fa matsa mini hannun ya dinga yi!.”

Kallonta Umman tayi na y’an dak’ik’u, kafin tayi k’asa k’asa da murya tace
“Jalila anya kin san ciwon kan ki kuwa? Idan kika kuskura kika yi wasa da damar ki Wallahi ki kuka da kanki!
Tayaya aka samu kika yi saurayin ma?.
Kiga fa Yaron nan wannan shine zuwansa na farko amma kalli abun arzik’i!” Tayi maganar tana nuna waya da kud’in da Auwal ya bayar
sannan taci gaba da cewa “Su su Hudan kika san me suke yi? Ni dai a ganina dan dai rik’e hannu a wagga Yaro mai arzik’i ba laifi bane ba.
Yanzu fa rayuwar ta sauya ne gaba d’aya. A matsayina na uwarki!
Ina mai baki shawara ki samu a lallab’a ko ta halin k’ak’a ne a samu ayi auren nan! Muma mu samu muji dad’in rayuwa a dama damu.

Kina gani dai ga yayanki chan a kulle wanda na tabbatar inda ace mu wasu hamshak’an masu arzik’i ne wallahi da tuni sun sake shi.

Ki tashi ki tsayawa kanki Jalila,
Junaidu yanzu sai ta Allah wanda kin san shi ne yake taimaka mana da kud’i, kuma na san kin san ba don
kud’in da yake bani ba da tuni yanzu bana cikin gidan nan! Jiya banyi ishashshen bacci ba tunani kawai nake yi ta yadda zan biya malan Yusuf kud’in aikin da yake bina dan har ya fara yi mini tuni! Sai gashi Allah ya dubamu ya kawo mai bamu amma shine kike k’ok’arin yi mana bak’in ciki ko?

Ni dai ban ce kije kiyi abunda bai dace ba amma a iya tunani na da wayo ‘Rik’e hannu ba matsala bace ba’.”
Tana gama fad’in haka ta hau dudduba d’akin. Chaan! Ta rarumo mayafinta tana cewa “Bari ma kiga in tashi inje gida! Akwai maganar da ya kamata muyi da Baabaa Laraba. Kin san ance da zafi zafi a kan daki k’arfe.”

Shiruu, taga Jalilan tayi kamar mai tunanin wani abu hakan ya sanya ta koma ta zauna a kusa da ita ta dafa ta tace “Ki kwantar da hankalinki,
komai zai tafi dai dai. Ki cire wani Arshaad a ranki Allah na tuba me za kiyi da mayaudari? Abu na biyu kuma
Kin ga masu kud’in nan sun fimu iya shige shige Idan muka ce zamu raba aurenshi da wachchar y’ar uwar tashi tsaf sai y’an kud’ad’enmu sun kare tass!! Dan haka kawai kiyi abunda yake mai sauk’i, kin ji ko?” Har zata mik’e sai kuma tace “Yanzu shi wannan d’in a ina yace ya ganki?
Sannan shi Arshaad d’in ya aka yi yayi mishi maganar ki? Ni fa ban gane komai ba gaskiya ki fahimtar dani ta yadda zan iya yiwa Baabaa Laraba bayani dalla dalla.”

Tsaki Jalilan taja sanann tace
“Wallahi Umma yadda baki fahimta ba nima hakan take. Sam sam ban gane me yake nufi ba!.”

Da d’an fad’a Umman tace “Kuma baki damu da ki tambaya ba!?
Kan ki yanata rawa…”

“Umma wai so kike yi in disga kaina ne? Na fad’a miki da turanci yayi ta bayaninshi kuma irin mai saurin nan!
Kina ji kin san irin na turawa ne,
shiyasa nace miki shima akwai arzik’i dan daga ji ba a k’asar nan yayi karatu ba. Yanayin nasa kalar turancin ba irin nasu Ya Junaidu bane ba. Gashi shima kyakkyawa fari tass kalar hutu.”

“Tam shikenan, bara inje mu gani.”
Umma tayi maganar tana gyara mayafinta sannan ta d’auki wayarta tana cewa “Alhamdulillah wayata zata huta! Shegen malamin maths mai son bati, saura kuma inji kin kirashi da wannan wayar, ke! Ni kima fita a harkar shi dan yanzu kam kin fi k’arfin shi.”

Dariya Jalila tayi itama ta mik’e
tana cewa “Wallahi kuwa Ummata..
Bari nima ki ga yanzu inje gidan su Jidda sune masu manyan wayoyi in basu su sakamin sim d’innan dan na kasa. Sannan In d’an saka charji
inaga ya manta bai had’a min da charger ba, anjima ina kiranshi zan ce ya taho min da ita idan zai zo, kar in manta.”

Haka nan suka fice a gidan, Umma tayi gidansu Ita kuma Jalila ta nufi layin gidansu wachche ta kira da Jidda.

Umma tana zuwa gidansu ta tarar ana fad’a da Baaba Laraba da K’asimu da Anty amarya. Ganin kalar zagi da cin mutuncin da K’asimu yake yi wa Baaba Laraba a tsakar gida gaban Yara da ita kanta Anty amaryar ne
ya sanya Umma ta jaa Baaba Laraban suka shige d’aki suka bar su sunata rashin mutuncinsu!.

Umma ji take kamar tayi super ta dira kan Anty amarya taci ubanta, amma kuma gudu da tsoron karta janyowa uwarta saki yasa kawai ta ja bakinta tayi shiru, ta san duk bala’in ta K’asimu ya dama ta ya shanye! Yanzun nan zai yi musu abunda basu tab’a tsammaniba.

Suna shiga Baaba Laraba ta sa kuka, cikin kukan take cewa “Sadiya wallahi uban ki ba d’an halak bane ba!

Saboda Allah dan yaga yanzu amarya ke bashi kud’in kashewa shike nan ni sai in zama bola?

Wanne irin gata ne ban yi mishi ba?
Shifa ya karyani a sana’ar tawa saboda yadda nake bashi kud’ad’ena kyauta da bashi!

Amman yanzu dan yaga bani da shi shikenan na zama banza kenan??
Da gangan fa Yarinyar nan zata takalo ni da fad’a ina tankawa shikenan zai shigar mata su tisa ni gaba da cin mutunci tsofai tsofai da ni.”

Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin ta matso ta share mata hawaye sannan tace “Kiyi hak’uri, ki kyalesu, ki daina shiga harkar ta, komai zata yi miki ki kar ki kulata. Ki kwantar da hankalinki in dai na haifu y’ar halak to wallahi sai ta bar gidan nan!!

Dama ai babu ce tasa muka barta muka zuba mata ido ko? To yanzu Allah ya kawo mana mafita m”
Nan ta zayyano mata zancen Auwal da Jalila, da kuma maganar auren da Auwal d’in ya zo dashi, da maganar auren Arshaad!! Duk bata bar komai ba.

Murmushi Baaba Laraba ta hau yi sannan tasa hannu ta goge ragowar hawayen fuskarta kafin tace “Yanzu ba gwara hakan ba? Ai sai sun fi jin ciwon hakan yanzu akan ace an rabasu tun farko! Abunda nake ta gaya miki kenan tun lokacin da aka ce mana ‘ba Mijinta bane ba’ Wannan ranar nake kwad’ayi gani! Ke kuma duk kika bi kika d’aga hankalinki kika gaza nutsuwa ki fahimceni…akan yana kawo mata abubuwa kuma ita tana fita Jalila tana zaune. Yanzu tou ba gashi itama Jalilan Allah ya kawo ba?”.

Murmushi Umma tayi kafin tace “Ai dama Baabaa kin san ance duk abunda Babba ya hango Yaro ko kan dala ya hau ba zai ganiba. Yanzu menene abun yi? Dan idan muka yi sagegeluwar da su Maryam suka yi to fa muma hakan na iya faruwa da mu.”

“Kud’in hannunta da aka bata kin taho da su?” Cewar Baaba Laraba.

Baki Umma ta kama kafin tace
“Niiiii? Kin dai san halin Jalila da shegen son abunta! Yanzun ma ina lure da ita sai wani kaffa kaffa take yi dan kar ince ta bani. Shiyasa na kyaleta sai munje kwanciya tukunna zan yi mata wayo In karb’a. Kinga a ciki ma sai ki samu na jari.”

“Ya kamata kam”. Shine abunda Baabaa Laraban tace. Daga nan suka hau k’ulla yadda za suyi da Auwal, K’asimu da Anty amarya.

                     

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 30So Da Buri 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×