Littafi Na Biyu
Kamar yadda Arshaad ya fad’a, mintuna ashirin d’in bama su cika ba! Ya gama abunda zai yi yasa komai a saiti sannan ya kira Granpa da landline d’in wajen ya sanar dashi ya gama, komai ya yi normal.
Daga nan ya nufi hanyar office d’inshi cikin d’an sauri saboda very important magana suke yi shi da Aslam kafin Granpa ya kira shi ya sakashi aikin.
Tun kafin ya k’arasa ya hango k’ofar office d’in nashi kamar a bud’e! Yana zuwa kuwa ya. . .