Skip to content
Part 36 of 71 in the Series So Da Buri by Bulama

Littafi Na Biyu

Kamar yadda Arshaad ya fad’a, mintuna ashirin d’in bama su cika ba! Ya gama abunda zai yi yasa komai a saiti sannan ya kira Granpa da landline d’in wajen ya sanar dashi ya gama, komai ya yi normal.

Daga nan ya nufi hanyar office d’inshi cikin d’an sauri saboda very important magana suke yi shi da Aslam kafin Granpa ya kira shi ya sakashi aikin.

Tun kafin ya k’arasa ya hango k’ofar office d’in nashi kamar a bud’e! Yana zuwa kuwa ya gasgata hakan sakamokon ganinta da yayi a wangale sosai.

Da mamaki ya kutsa kai ya shige ciki.
Tun bai gama shiga ba ya fahimci
babu Aslam babu alamar shi a cikin office d’in.

A hankali ya sanya hannu ya rufe k’ofar office d’in yana mamakin abubuwa guda biyu ‘tafiyar da Aslam yayi bayan ya san maganar da suke yi mai mahimmanci ce!’ Da kuma ‘yadda yazo ya samu k’ofar office d’in nashi a wangale’ Could it be Aslam d’in ne ya fita a rikice? Ko kuma dai bayan ya fitan ne wani ya shigo mishi office, may be Auwal? No it can’t be! Duk shi kad’ai yake ta sak’e sak’en shi a cikin ranshi.

Ganin babu inda wadannan tunane tunanen zasu kaishi ne ya sanya kawai ya yanke shawarar ‘gara ya kira Aslam d’in! Ya ji ko lafiya’.

Shafa aljihun shi yayi da niyyar d’aukar wayarshi yaji wayam. Yasan daman da guda d’aya ya fito d’ayar kuma tana gida bai ma fito da ita ba!
To ko dai ya jefar ne a inda ya baro…

Har zai juya ya fita dan yaje ya dubo wayar sai ya hangota a kan table d’inshi a ajjiye.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya k’arasa yasa hannu ya d’auka da niyyar kiran Aslam. Sai dai kuma bai kai ga bud’e wayar ba idanunsa suka ci karo da notification barr dinsa wanda yake nan cike da tarin misscalls d’in Huda!

A firgice yad’an zaro ido yana kallon wayar. Whatever it is da ya sanyata ta jero mishi wanann tarin misscalls haka ya san its very serious and important!!

Idanuwansa ne suka sauk’a akan message d’inta, dan haka cikin k’aguwa ya hau karantawa.

Tsayawa yayi cak!!! Kamar wanda aka dannawa pause. Dan ko numfashi kasa ja yayi. A hankali ya lunmshe idanuwanshi. Da kyar ya samu yace
“Ya subahanallah!!” Sannan ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya bud’e idanuwanshi da har sun kad’a sunyi jaaaa! Wani abu ne yaji ya toshe mishi mak’oshi! Da kyar ya samu ya had’iye ya ja numfashi ya fesar da mugun k’arfi! Yana nan tsaye rik’e da wayar a setin fuskarshi har yanzun ya kasa gota ta. A hankali kamar mai jin tsoro ya shiga Call log ya danna kiran Aslam.

Ya kirashi yafi sau biyar amman bai d’auka ba saboda a lokacin ba abunda yake da buri kamar ya gansu a asibiti! Ko ya samu ya daina jin kukan Huda wadda ta kasa yin shiru, sannan a samu a duba Anty Maryam a ga lafiyar ta! Shiyasa in banda gudu ba abunda yake tsulawa kamar shi kad’ai ne a akan titin. Tunda ya samu suka yi waya da Abba yace mishi ‘gashi nan zuwa’.

A hankali Arshaad ya zare wayar daga kunnenshi ya yi scrolling zuwa sunan Huda ya danna ya kara a kunnenshi
Sai da ta kusan katsewa tukunna ta iya d’auka tace, “Hello Ya Arshaad” Kana ji ka san kuka take yi.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya ce

“Kina ina?” Cikin kukan tace “Ga Ya Aslam d’innan ya zo, muna hanya zamu kaita AKTH yanzu. Na gode sosai.” Ta fad’i hakan, ita duk a tunaninta shine ya turo Aslam saboda maybe ko shi d’in yana wani abun important ne. A hankali ya ce “Umm!
Mu had’u a chan.” Daga nan ya yanke kiran. Mukullin motarshi kawai ya d’auka ya fice a office d’in! Yana zuwa ya shiga ya kunnata ya bata wuta ya fice ya nufi asibitin.

A mota Aslam yace “ta jira” Shi ya shiga, ya fito, da nurse guda biyu da gado aka d’aura Maman a kai suka shige ciki. Sai da ya tsaya aka yi komai tukunna ya cewa “Huda tazo taje ta zauna” Sai da ya tabbatar ta zauna
sannan a hankali ya d’an durk’usa ya shiga lallashinta!

Da kyar ta samu ta d’an yi shiru. Yana matsawa a wajen taci gaba da kukanta a hankali tana share hawaye. Bayan rashin lafiyar Mama har da abunda Hajiya Shuwa tayi d’azu ya daki zuciyarta ya b’ata mata rai kwarai!!

Bata tab’a jin zafin kalar abubuwan da Hajiya Shuwa take yi musu kamar irin na yau ba!

A hankali Aslam wanda yake ta faman k’ok’arin ganin bai sake kallon direction d’inta ba ya d’aura idanuwanshi a kanta yana kallonta. Ji yake kamar ya sake komawa yaje ya lallasheta tayi shiru! Har ga Allah kuka yana d’aga mishi hankali.

Nurse d’in data taimaka aka shigo da Maman ce tazo zata wuce ta kusa dashi har ta d’anyi gaba sai kuma ta dawo tace masa “kaje ka zauna ka lallashi matar taka mana! Ka barta ita kad’ai chan gefe sai faman kuka take yi. Kaje wajenta mana.” Tana gama fad’in haka ta juya ta wuce a bunta.

A hankali ya lumshe idanuwanshi a ranshi ya ce “Why am i too nice to her, yau?” Wata zuciyar ce tace mishi
“Saboda Mamanta bata da lafiya mana.” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai raya wa a ranshi ‘yadda yayi da yadda ya nuna tsananin damuwar shi! Tabbas kowa ya gani zai yi tunanin ita d’in matarsa ce’ A hankali ya sake lumshe idanuwanshi yace “damn it!” A chan k’asan mak’oshi!.

Cikin k’ok’arin son kawar da wani tunanin na daban ya fara k’are mata kallo yana mamakin kamannin ta da Abba! Gata kuma y’ar gidan Anty Maryam! Ko shekaran jiya ma sai da ya ga hoton Anty Maryam wanda suka d’auka ita da shi da Abba da Dad da Mommy lokacin a Saudiyya! Ko da ace ma bashi da hoton ta tabbas fuskar Anty Maryam ba zata tab’a b’ace mishi ba. Sauk’e Ajiyar zuciya ya yi, a k’asan ranshi yana zullumin k’arasowar Abba! Tabbas lissafinshi daidai yake ba shi! Ba shi da tantama.

Sai da ya sha d’an k’aramin yak’i! Da security d’in bakin k’ofar shiga emergency d’in tukunna da kyar!! Ya barshi ya shiga.

Yana shiga hankalinshi da idanuwanshi suka kai kan Aslam wanda yake a tsaye ya k’urawa Huda wadda take zaune tana ta faman kuka, ido!

Da sauri ya k’arasa inda yake. Sam Aslam bai lura da shi ba har sai da ya dafa shi, tukunnan yayi firgigit ya juyo yana kallonshi. Maimakon yace wani abun kawai sai Arshaad yaga ya k’ura mishi ido kamar wanda yake son hango wani abu, har sai da ya d’an tsargu! Kusan 2 minutes Aslam ya d’auka yana kallon Arshaad Wanda hakan ya sanya duk wani rikicin da yake ciki hauhawa jikinshi kuma yayi sanyi lokaci guda dan bai san me ya sanya Aslam d’in yi mishi irin wannan kallon k’urillar ba!

Kamar daga sama yaji muryarshi yana cewa “ka tab’a ganin Mahaifiyar Huda??” Da mamaki Arshaad d’in yake kallonsa kafin yace “Ba sau d’aya ba!.”

Shiruu, Aslam d’in yayi sai kuma ya runtse idanunsa da k’arfi kafin ya bud’e yace “How old is she? Hudan?”

“Close to 18” ya bashi amsa ba tare da ya fahimci inda tambayoyinshi suka dosa ba.

“Kwanaki kace min a gidan Mijin Mamanta take, and ba suyi maka maganar Dad d’inta ba ko?” Cewar Aslam. “Aslam what are u getting out of this ne wai??” Arshaad yayi mishi tambayar.

Da d’an fad’a yace mishi “Just answer me!!”

Shiruuu, yad’an yi sai kuma yace “Tun farko. Da na fara zuwa gidansu ta ce mini ‘ba su ma da number d’insa’ (her Dad) Uncle d’inta kuma ya ce “families d’in ne suka samu matsala shi yasa but ana hoping resolving in shaa Allah.”

Aslam, tafin hannayensa duka biyun aslam ya saka yayi cupping iya daidai hancinshi da bakinshi ya fitar da wani hucin da sai da na kusa dashi ya juyo yana kallon shi! Tukunna ya cire hannun ya dafa Arshaad kanshi tsaye yace “Hudan is our sister!! Daughter d’in Abba ce, ba ni da tantanma.”

Da kyar Arshaad ya daidaita kanshi daga shock d’in daya shiga, kafin yace

“How???” Aslam ya bud’e baki da niyyar bashi amsa kenan! Ya hango shigowar Abba! Kusan a tare suka ga juna don shima Abban yana shigowa idanunsa suka sauk’a akan Aslam d’in.

Da sauri ya k’araso yana cewa
“Aslam mai ya faru? ka ce in baro komai in zo asibiti emergency, duk na rikice, waye ba lafiy…”

Maganar shi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a akan Hudan wadda take ta faman kuka har yanzu.

Shi dai Abba bai san ya akayi ba dan kawai tsintar kanshi ya yi a gabanta a tsaye! Ana cewa yana kama da su Aslam da Yaya amman tunda yake bai tab’a ganin kamannin shi da wani mahaluk’i kamar na wannan matashiyar budurwar ba! Duk da fuskarta a yanayin kuka take hakan bai b’oye tsananin kamannin da suke yi da juna ba!

Ita kam Huda yanayin tashin hankalin da take ciki ne bai bata daman fahimtar kallon fuskar mutumin ba, amman tabbas tun lokacin da yazo gabanta ya tsaya taji wani bak’on al’amari ya shige ta! Tsintar kanta tayi da mik’ewa tana goge hawayen ta sannan ta shiga gaidashi.

Aslam bai bashi damar amsawa ba ya ce “ya biyo shi, yana so zai nuna mishi Mahaifiyar Yarinyar daga nan sai ya yanke hukunci da kanshi.”

Haka nan kawai Abba ya bi bayan Aslam kamar rak’umi da akala! Bayan aslam d’in ya cewa Huda itama ta biyo su! Arshadd ko ba shi da wani zab’in da ya wuce ya bisu.

A haka suka d’unguma inda aka kwantar da Mama ake duba ta suka tsaya suna jiran fitowar Doctor!

Kusan wajen 29 minutes ba wanda yace komai kowa ka gani da abunda yake yawo a kanshi. Suna a haka Doctor ya fito! Kallonsu ya yi one by one kafin ya k’arasa inda Aslam yake tukunna ya fara magana.

“Alhamdulillah An ci sa a ta farfad’o!
Za ku iya shiga ku ganta amman dan Allah kar kuyi hayaniya kuma kuyi k’ok’arin kwantar mata da hankali saboda jininta ba k’aramin hawa yayi ba!.”

Yana gama fad’an haka ya mik’awa Hudan takardun hannunshi ya wuce.

Abba bai san daliliba bai kuma san wacece a kwance a d’akin ba, amman yadda zuciyarshi take bugawa da kuma kalar karkarwa da jikinshi ya d’auka lokaci guda ne ya sake d’aure mishi kai! Dan tabbas ya san in da ace za a auna jininshi a yanzu to da za aga yafi na mara lafiyar da ake cewa su taru sun kwantarwa da hankali hawa.

Muryar Aslam ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “muje Abba. Bismillah.”

D’aga kai kawai yayi alamar ‘to’ sannan ya nufi inda yaga su Hudan da Arshaad sun shiga, Aslam ya mara mishi baya.

Shekaru goma sha takwas rabon shi da ita, amman ba a yanayin rashin lafiya ba ko a garin makafi idan ya had’u da Maryam ya shafa yaji to sai ya gane ta!
Lokaci guda yayi baya luu!! Ba daban Aslam yayi saurin taro shi ba tabbas da sai ya zube a k’asa!

A b’angaren Mama kuwa! Da farko da ya shigo ta ganshi ta d’auka gizo yake yi mata, sai da taga har Aslam ya taro shi yana cewa “Be careful” tukunna ta tabbatar da cewa shi d’in ne! “Mai ya kawo shi? Me yake nema? Me zai ce mata?” Sune tambayoyin da suka taru suka had’e da al’ajabi suka fara k’ok’arin tarwatsa mata zuciya! Da kyar ta k’ok’arta ta tashi ta zauna sai kuma ta fara k’ok’arin tsayuwa.

Da kyar ya iya daidaita kanshi sannan ya sake sauk’e idanuwanshi a kanta.
Babu abunda ta k’ara ko ta rage, tana nan kamar yadda ya santa 18 years ago! Fatarta ce kawai ta d’anyi duhu amma kyawunta da yanayin jikinta ba abunda ya ragu ko ya k’aru! “Astaghfirullah!!” Yayi saurin furta hakan, sakamokon tunawa da yayi ita d’in a yanzu mallakin wani ce! Sai kuma lokaci guda ya fara ganin duhu duhu sakamokon kishin da ya turnuk’e sa! Bai tashi dawowa daidai ba sai da yaji Hudan da Arshaad suna tambayar ta “Ina zata je?” Ba tare da ta kalle su ba tace “gida!!”

Sannan tasa hannu d’ayan hannunta ta cisge cannular k’arin ruwan da aka d’aura mata a d’ayan hannu nata, tayi hanyar fita (inda su Abba suke tsaye!).

Da sauri ya tsaya a gabanta ya fara magana “M mm Maryam Doc ya c ce jji kin kk ki ba kwari kark.” Mahaukacin Marin data d’auke sa da shi ne ya sanya hatta su Aslam sai da suka d’auke wuta na y’an sakanni! Cikin b’acin rai ta ce “That’s for Huda!!
Na duk wani kuka da bak’in cikin da ta fuskanta ata dalilin hukunci daka yanke tun kafin rayuwarta ta soma!”

Ba na so ta sanka! Ba na so taji komai!! Ba na so tasan komai!!! Ba ma buk’atar ka! Na rok’eka da girman Allah ka bar nan tun kafin raina ya k’arasa baci!”

Ta k’arashe maganar cikin b’acin rai da k’unar zuciya, wasu zafafan hawaye suna zubo mata.

Idan lissafinshi ya bashi daidai to maganganun Maryam suna nuni ne da irin kalaman da ya kamata a yiwa uban da ya gudu ya bar y’arsa.

Bai damu ba sam! Dan bata k’umbiya k’umbiyar magana yake ba a halin yanzu. Shi daman ko da a ce ya tambaya ance mishi Yarinyar ba y’arsa ba ce ba to fa ba zai tab’a yarda ba!! Ballantana kuma yanzu da maganganun Maryam suka sake tabbatar mishi da ‘y’ar’ tasu ce!.

Hakan yasa ba tare da yabi takan Mama wadda Aslam yake ta rok’o ta koma a saka mata cannula tak’i ba! (Ta nace akan sai dai Abba ya fita ko kuma ita a tafi) Ya nufi inda y’arsa take tsaye!
Yana zuwa bai yi wata wata ba kawai ya rungume ta sai kuma ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro.

Ita dai Hudan zuwa yanzu ta koma mutum mutumi! Dan kwakwalwarta ta kasa aminta da amsar da kalaman Mama da kuma reaction d’in wannan bawan Allah suke bata.

Shigowar Likita ce ya juyo da hankalin su gabad’aya, dan hayaniyar su ta fara damun ragowan patients d’in da suke gefen su. Dukda inda suke an yankashi da girma sosai dan yayi biyun ragowar inda patients d’in suke amman dole in sunyi magana za a jisu kasancewar labulaye ne kawai ake sakawa a tsakani.

Da mamaki yake kallon Mama a kan k’afafuwanta, sai kuma ya juya kan Aslam ya rufe shi da fad’a! Da kyar ya lallab’a Mama bayan tace “ba zata koma ta kwanta ba sai Abba ya fita”
Shi kuma yace wa Abban “yayi excusing d’insu” Bayan ya fita, aka samu ta tsaya ya maida mata cannularta. Har zai fita yace musu “banda hayaniya!” Sannan ya juya ya fita.

Yana fita kuwa Abba ya dawo! Dan haka Mama ta sake mik’ewa.

This time around Aslam ne ya k’arasa inda take ya rik’e mayafin da take k’ok’arin yafawa ya fara magana
“Mama dan Allah ki tsaya ki sauraremu, babfa ke kad’ai ya kamata ace ranki ya b’aci a lamarin nan ba, shi kanshi Abba yana da ikon yin fushi kawai dai daurewa yake yi dan yaga an zauna lafiya!! Amman na tabbatar ko kotu aka je to kina da laifin b’oye masa y’arsa da kika yi tsawon shekaru ba tare da ya ma san akwai ta a duniyar ba! So i think its about time da ta kamata ki nutsu! Whatever it is that happen between you and Abba destiny d’inku ne, so don’t mix it up da issue na laifin ‘b’oye mishi y’a da kika yi’ kiyi putting blame d’in ankan shi, wannan laifin ki ne ba nashi ba!
And if kika ci gaba da acting stubborn muma zamu biyo miki ta hanyar da baki tab’a tunani ba!”

Da sauri Arshaad ya ce “haba Aslam wanne irin magana ne kake yi haka?? At least ai she is an elder watch your tongue mana!!!”

Tabbas daman ko Arshaad bai fad’a ba Mama ta gane wannan Aslam ne, dan kamanninbshi basu chanja ba kwata kwata, kenan Arshaad d’in shima realative d’insu ne maybe ma brother d’inshi ne dan gashi suna kama sosai!!
Ta yiwu Abba ne ya turo shi ko kuma me kenan hakan yake nufi? idonshi yana kansu all this time amman sai yanzu yaga ya dace ya nuna kanshi ko ya ne abun yake? Gaba daya kan Mama ya d’aure tamau!!!

Maganar da Aslam ya fara yi a fusace ne ya dawo da hankalinta wajen

“Elders! elders!! elders! Shin duk meye ne farkon issue d’in nasu?” Bai jira jin amsar da Arshaad zai bashi ba yace
“biyewa son zuciyan elders d’in da akayi ne ai duk ya jawo haka!! Itan ma kuma I’m pretty sure idan aka yi musu laga laga problems d’in da zata kawo ba kad’an bane ba!

Tun ranar da Granpa ya nunawa Abba video d’in d’aurin aurenta Abba yake fama da ciwon zuciya har yau d’in nan!! Kuma all those years bai samu sauk’i a wajen kowa ba! Fama yake yi da rashin lafiyanshi ba wanda ya damu!! Sannan yanzu kuma itama zata b’ullo da nata issue d’in? Da wanne ake so Abban yaji da?” Ya yiwa Arshaad tambayar yana kallonshi.

Bai damu da jin amsa daga gareshi ba dan daman ya san ba lalle ya samu ba, ya juya ya kalli Mama sannan yace
“Ba zan d’agawa kowa k’afa ba! daga yau, ke ko Ummi, hatta Granpa!!
Therefore I’m advising you to drop this attitude and stubbornness da kuma haushin Abba da kike ji, ki tsaya ku dedeta akan issue d’in Huda If not, wallahi kinji na rantse miki da kaina zan kaiki kotu!! Kuma sai inda k’arfina ya k’are!! Da ni za ki yi ba da Abba ba…”

“Huda mik’o mini purse d’ina” Shine kawai abinda Mama tace ba tare da ta zare kwayar idanunta a cikin na Aslam wanda tunda ya fara magana suke kallon juna ba!.

A hankali Hudan ta zare hannunta daga cikin na Abba sannan ta d’auko jakarta ta zaro y’ar k’aramar purse d’in Maman a ciki ta mik’a mata
ta ce “gashi”. Hannu Mama wadda har yanzu take kallon Aslam ta mik’a ta amsa sannan ta d’auke idanunta daga kanshi ta sauk’e akan purse d’in ta zuge ta! Bayan wayarta ba komai a ciki sai chanjin naira talatin ashirin da biyar biyu.

Zip d’in dake a gefe acikin purse d’in ta zuge sannan ta zira y’an yatsunta ta fara lalubawa. Wasu takardu an ninke su ninkin k’anana guda biyu ta zaro ba tare da ta rufe ba ta mik’awa Hudan purse d’in.. Ta farkon ta fara bud’ewa ganin ba ita take nema ba yasa ta mik’awa Hudan tace “ta ninke ta mayar mata ciki” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e ta biyun. Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta share bayan ta gama karantawa sannan ta cillawa Aslam a dede setin fuskar shi.

Da sauri jin takardar tana shirin sauk’a k’asa yasa hannu ya cafe ta sannan ya d’ago ta ya fara karantawa.

Mama bata jira ya k’arasa karantawan ba ta fara magana. “Aslam za ka iya kaini kotu! amman ka sani ni ba zan biye ka inyi shariah da kai ba, nasan kun fi k’arfi na ta ko wacce siga, sai dai kuma ni kotun Allah zan kaiku! Nan ce k’arshe kuma shine zai bi mini hakkina! Dan ba zan yarda ku dake ni kuma ku hanani kuka ba!”

Tana gama fad’in haka kuka ya kufce mata ba tare da ta shirya ba.

Da mamaki Abba wanda ya k’araso ya karb’i takardar ya hau karantawa yake sake maimaitawa. Shiru, ya d’an yi sai kuma kawai ya ninke takardar ya sa a aljihun gaban rigarshi! Dan tabbas yau za a yita ta k’are a estate d’insu!! Ba zai yiwu ace yana rubuta takardun da bai san lokacin da ya rubuta su ba! A daa yana kokwanto yanzu kam ya samu clue.

Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya k’araso gaban Mama ya ce “Maryam! na rantse da girman Allah ba nine na rubuta wannan takardar ba! Ban san da zamanta ba kuma ban san dalilinta da ranar data iso gareki ba!”

Cikin kuka Mama tace “naji Abba baka san da takardar nan ba ita kuma Hudan laifin me tayi maka!? Ko sau d’aya fa baka tab’a lek’ota ba! Cinta shanta suturarta duk baka sansu ba!
Idan ni nayi maka laifi ka datse igiyoyin aurenka a kaina ita kuma laifin me tayi maka daka kasa koda
lek’o ta ne?”

Kamar Abba zai yi kuka da ihu yace
“Maryam, zabi aka bani ko in fita harkar ki for ever ko kuma ku k’are rayuwanku a jail ke da family d’inki har abada! Daman kuma an riga anyi agreement dani ke kin sani an yi agreement akan ‘duk ranar da wani naki ko ke kuka je inda yake dole akwai consequences!’ Duk da haka ban hak’ura ba. Inata k’ok’ari da adduar in samu a gyara abun sai kawai naji d’aurin auren ki bagatatan!! Ya kike so in yi??”

“Ni fa duk ba wannan nake son ji ba, tsakani na da kai it’s over! Ko ma menene ya faru ya riga ya wuce!
Laifi yanzu da nake magana a kai ba ni ka yiwa ba! Y’ar ka ka yiwa, kuma ko ita ta yafe maka ni ba zan yafe in yarda ba!! Dan haka kawai ka juya ka tafi dan ban san me ka zo yi anan ba!.”

Aslam wanda yake ji kamar zuciyarshi zata tarwatse ne ya ce “wai sau nawa zai yi miki bayanin ‘bai san kin haihu ba’. Hatta shi kanshi Granpa d’in bai san kin haihu ba!! Kuma da kike ta cewa bai zo inda kike ba, was it not you da kika yi ta aika mishi da threats kala-kala ba?”

Shigowar Doc ce ta katsewa Arshaad maganar da yake shirin yiwa Aslam akan attitude d’inshi towards Mama!! He’s is not like this kwata-kwata, he wonders why yake yiwa Maman haka.

Ba tare da Likitan yace “k’ala ba ya juya ya fita, ko minti d’aya bai yi ba ya dawo da takardar sallama ya bawa Aslam sannan ya ce, “kuje gida kuyi solving issue d’inku, dan har ga Allah kun hana marasa lafiya sukuni!! Ba sai kun rufe file ba, zaku iya tafiya kawai.

Yana gama fad’an haka ya kama hannun Mama ya cire mata cannular yana cewa “kuna gama cases d’inku ki tafi asibiti, dan ina jin tsoron jikin nan naki a haka!.”

Yana fita Mama wadda daman abunda take so kenan, ta yafa mayafinta, sannan ta cewa Huda “wuce mu tafi!”

Kasa sauk’e kafarta data d’aga da niyyar tafiya tayi jin Abba yana cewa “Babu inda Huda zata bii ki!!”

Da mamaki ta juyo tana kallon Abba kafin tace “ban gane ba!”

“Babu inda zata je, tare da ke!!” Abban ya fad’a yana mai k’arasowa inda take sannan ya zuba mata idanuwanshi da ta kasa jurewa kalla tayi saurin yin k’asa da kanta.

Cikin tattaro dukkan ragowar k’arfin jiki kuzari da jarumtar ta, ta zagaye shi taje inda Hudan take ta fara k’ok’arin kama hannunta amman kafin tayi hakan tuni Aslam ya juyo da sauri ya rigata, sannan ya tura Hudan bayansa, shi ya zamana yana a gaban Maman!!
Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi da ya runtse!! Tun lokacin da ya rik’e hannun Hudan ya zuba su a kan Mama! Cikin wata iriyar kasala data dirar masa lokaci guda ya ce “You have to pass through me first!”

Arshaad kam zuwa yanzu ya zo wuya!!! Dan haka cikin fushi ya kalli Aslam d’in yace mishi “let her go!!”

“No” Ya ce ba tare da ya kalle shi ba!
Sannan ya dakawa Hudan wadda take ta k’ok’arin kwace hannunta tana kuka tsawa “Ki nutsu!!”.

Wani irin irin kuka Mama ta fashe da shi a take ta durk’ushe a wajen abin tausayi.

Abba ne ya umarci Aslam da “Ya kai Hudan mota dan in dai yaci gaba da ganin Maryam a haka tou za a samu matsala!”

Da sauri Arshaad ya ce “babu fa inda zata je ba tare da Mahaifiyarta ba!!! Haba Abba! Kasan kuwa shak’uwar dake a tsakanin y’a da uwa?? Ka san abubuwan da suka yi going through tare, lokaci d’aya kawai kazo ka ce zaka d’auketa haka nan? Why are you trying to be selfish???”

Kallonshi Abban yayi da idanunsa da suka fara rinewa. He‘s tired so tired of everything!! A yanzu yadda yake jin zuciyar shi tabbas idan ya tsaya kula Arshaad to zai iya yi mishi illa! So yake yi kawai ya isa gida tare da Huda ya fuskanci kowa da komai! Masu laifi kuma ya hukuntasu dan bashi da tantamar cewa akwai wadanda suka san da zaman Huda a dunyia a cikin estate d’in su. Apart from that ma inda ace ya san yana da y’a tun farko to da ko kwana d’aya ba zai barta tayi a gidan Usman ba which definitely ya san anan take da zama. Tabbas ya san bai kyautawa Maryam ba, but she’s not ready to listen!! Ba ya jin kuma zata yarda ta bashi Huda a cikin sauk’i! Shi kuma a halin yanzu ya kai peak!! Edge!!Limit!! Na tolerance.

So yake kawai ya isa gida. Shiyasa cikin k’ok’arin danne zuciyar shi da yake ji tazo masa iya wuya!!! Ya cewa Aslam. “Kai ta mota!! Idan tayi tirjiya ka d’auketa!” Yayi maganar ba tare da ya d’auke idanunsa da suka koma tamkar garwashin wuta daga kan Arshaad ba! Ya ce masa. “Do your best ka lallashi Maryam sannan ka maidata gida.” Yana gama fad’an haka ya juya ya bi bayan su Aslam da Huda wadda ta bisa salin alin dan, gani tayi ana cewa ‘ya d’auketa’ ya durk’usa ya fara k’ok’arin ciccib’arta. Amman fa kukan da take yi still tana k’ok’arin zame hannunta ana Aslam ya sanya gaba d’aya hankalin duk mutanen da suka wuce ta gabansu ya dawo kansu, da yawa tunanin su rasuwa aka yi mata, shiyasa ba wanda yayi k’ok’arin tsaidasu! Sai dai ‘Allah ya ji k’an rai’ kawai da wasu mutanen suka dinga cewa, Wasu kuma kallon tausayi suka bisu dashi.

Aslam yana isa bakin motar yaiyi mata key ya bud’e ya dan nata a ciki ya rufe sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya bata wuta, ba tare da ya jira Abba ko Arshaad ba ya d’auki hanyar MT estate da ita.

Arshaad gabad’aya ya tsorata da ganin yanayin Abba dan tabbas bai tab’a ganinshi a irin wannan yanayin ba!
Duk inda bacin rai ya kai b’acin rai to yau ya hango shi a kwayar idanun Abba! Shiyasa ya kasa tsaidashi.

A hankali bayan fitar shi yaje inda Mama ke durk’ushe tanata faman kuka shima ya durk’usa gabad’aya ranshi ba dad’i! A hankali yace “Mama dan Allah k…” Kallon da ta d’ago tana yi mishi ne ya sa ya had’iye ragowar maganar sa! A hankali ta mik’e ta gyara mayafin jikinta sannan tace
“Arshaad mai yasa kayi mana haka?”

Da mamaki yake kallon ta kafin yace
“Mama ni kuma mai nayi?” Cikin fushi tace “kafi kowa sanin me kayi!

Kuma ina so ka sani Allah sai ya bi ma Hudan hakkinta dan wallahi kaji na rantse ita d’in son gaskiya da tsakani da Allah take yi maka! Amman duk da hakan zan yi k’ok’ari inga na cire mata kai a ranta!. Sannan ga sak’o ka gayawa Abba! “In duk duniya ce zata taru a kaina to ba zan yarda ba!! Nima ina nan zuwa karb’arta, daga nan in Mahaifinsa yaga dama ya kulle kaf jinsina ba wai iya dangina ba!!”. Tana gama fad’in haka ta wuce ta bar shi nan, a daskare!!

Da kyar ya iya tattaro ragowar kuzarinsa ya fice shima a d’akin, saboda iya yadda yaga ta fita tana layi ya tabbatar mishi ba zata iya kai kanta ko da nan da gate ba! Sai dai kuma, ko da ya fita d’in sai bai ganta ba bai ga alamartaba kamar wadda tayi layar zana ta b’ace!

Duddubawa ya hau yi har buildings d’in gefen emergency amman babu ita babu alamar ta! Abun ba k’aramin sake d’aga mishi hankali yayi ba dan babu inda bai duba Mama ba amman bai ganta ba har unguwar su yaje a tunanin shi ko ta koma amma tun kafin ya k’arasa gidan ya hango ana (Baba) datsa kwad’o a gidan, ya fitar da machine da alamun fita zai yi.

Sanin da yayi in dai napep ta hau to ba lalle ta rigashi isowa gidan ba ne, ya sanyashi zaman jiranta, anan cikin mota! Sai dai almost 2 hours amman bata dawoba.

Zuwa yanzu kam hankalinshi ya kai k’ololuwar tashi! Tun farkon had’uwar shi da Hudan yake k’ok’arin toshe duk wata hanyar da zata kawo musu matsala, yanzu haka ya ware millions zai siya musu gida, ta yadda In su Mammy sun zo ba zasu samu abun kushewa ba balle har Granpa yaji ya hana, su Abba kuwa ya san su zasu zo nema mishi aure, so gidan uncle Muhammad ba zai zama matsala ba!
Dan anan aka shirya za a had’u dan ba daban jiran Dad d’in da suka tsaya yi ba ma to da tuni sun zo an gama magana.

Har ga Allah ba zai tab’a iya rayuwa babu Hudan ba, kwata-kwata, shi baya jin ma a tarihi akwai wani mahaluk’in da ya tab’a yiwa wata kalar son da yake yiwa Huda since day 1, gashi kuma yau Mahaifiyarta da kanta ta kalle shi ta ce ‘zata rabashi da ita!’

Bai ankaraba kawai yaji hawaye yana wanke mishi fuska! Sunayen Allah ya fara ambata yanayi yana kuka, kamar k’aramin Yaro. Da kyar ya samu zuciyar data yunk’ura mishi ta d’an lafa.

Ganin babu Mama ba labarin ta, ya sanya kawai ya yanke shawarar komawa gida yayi wanka daga nan ya kira Ummu a san abunyi! Dan in ba ruwa ya samu ya sakarwa kanshi ba baya jin kalmar ‘A’ zata iya futowa daga bakinshi a halin da yake ciki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 35So Da Buri 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×