Sai da Arshaad ya dawo daga masallaci ‘sallar isha’ tukunna ya lura babu Mammy a gidan. A bakin cook d’insu ya ji komai bayan ya tambayeta.
Da kyar ya iya controlling kanshi dan ya san idan yace zai samu Abba ko Daddy a wannan lokacin a yanayin da yake ciki to tabbas za a samu matsala.
Dafe kanshi kawai yayi ya sallami cook d’in. Ya dad’e a tsaye! Bai ma san ta ina zai fara ba! Dan haka kawai ya sake komawa d’aki ya kwanta. Da kyar kuwa ya samu ya. . .