Skip to content
Part 42 of 71 in the Series So Da Buri by Bulama

Yadda side d’insu yake, haka na Daddy shima yake, komai da komai iri d’aya, kawai de akwai k’ofofi da corridors d’in da suke a nasu wanda babu a na Daddyn.

A parlourn suka tarar da Daddy d’in da alamun su yake jira.

Abba ne ya fara gaidashi tukun su Huda.

Yana jin Yarinyar a jikinshi matuk’a dan haka bayan ya amsa ya hau tambayarta “ya take? Tana jin dad’in zaman? Akwai abunda take buk’ata?”
A hankali tace “komai Alhamdulillah.

“Ma shaa Allah” yace sannan suka k’arasa.

Nan d’in ma abinci wajen kala hud’u akayi. Cikin nutsuwa da nishad’i suka yi serving kansu suka fara having breakfast d’in.

Basu dad’e da fara cin abincin ba, Hudan taji yanayin bugun zuciyarta ya chanza! A hankali ta runtse idanunta tana k’ok’arin saita kanta, da kyar ta samu ta bud’e idanunta tana mai jin wata nutsuwa tana sauk’ar mata sakamokon k’amshin turaren da ya sakarmata da kasala lokaci guda!

Basuma lura da shigowar tasa ba, sai da ya matso su sosai da k’amshin turaren shi ya yi musu sallama, tukunna suka lura da shi.

A hankali yace “AsSalama alaikom”

“Wa’alaikassalam, d’an albarka!”

Daddy yace yana mai ja mishi kujerar kusa dashi. Zama yayi, a lokaci guda kuma yana mai amsa gaisuwar su Shuraim sannan yace Daddy Ina kwana” Da kulawa Daddy ya amsa haka shima Abba bayan ya gaidashi.
Sannan ya juya ya mik’awa Auwal hannu, suka yi musabaha.

A hankali Hudan ta gaidashi ba tare da ta yarda sun had’a ido ba! Juyowa yayi ya kalli inda take, sai kuma da sauri ya kauda kanshi, a hankali yace “lafiya”

Hira suka d’an fara sama sama, kusan rabin hirar akan maganan company d’in da Aslam da Abba za su bud’e ne.

Ita dai Hudan kasa ci gaba da cin abincinta tayi, tun lokacin daya shigo! Bata san daliliba amma in dai yana waje to sai ta dinga jin kanta uncomfortable, ga yadda k’irjinta yake yi mata shima, wanda ta rasa dalili.

Abba ne ya cewa Aslam, “Ina Arshaad ne? Ban ganku tare ba.”

“Ya tafi d’aurin auren wani Abokin su, and wai za su kai amarya Kaduna, around 2 haka.” Aslam d’in ya bashi amsa. “Ok” Abba yace kafin ya kalli Huda ya ce “Ko a bari sai gobe kuje park d’in ko? Tunda yau Arshaad d’in yana busy.”

Kafin ya rufe bakin shi Auwal yace “Ba ni da aiki sosai yau, zan kaisu.”

Hudan ta d’anji sauk’i saboda daman ba zata so su fita itada Arshaad ba, kuma ba za ta so a ce Aslam ya kaita ba! Amman kuma ba ita kad’ai ba hatta su Daddy sai da suka fahimci akwai wani abun da Auwal ya shirya duba da yadda baya son ta yanzu kuma lokaci guda ya ce ‘Zai kai ta’

Daddy wanda ya san halin kayan shine ya ce “a’a! Ka barshi goben Arshaad d’in ya kaisu”

“Daddy i volunteered fa.” Auwal d’in ya fad’a yana kallonshi. Cikin d’an fad’a Daddyn ya ce “And i insist akan ka barshi Arshaad ya kaisu.”

Murmushi Abba yayi kafin yace “Daddy tunda ya nuna zai kaisun a barshi mana ko? Please.”

Baya son jan magana dan haka yace “ok” kawai duk da ya san Auwal bai Isa yayi mata komai ba tunda tare za su tafi ita da su Shuraim amma baya so su je Auwal d’in yayi mata wani kalar rashin mutuncin da zai ja yaji kunya ne.

Murmushi Auwal d’in yayi ya kalli Hudan kafin ya ce “Ki shirya around 2:30pm haka”

Yana gama fad’an haka ya mik’e yayi hanyar sama, da alama ma ko “to” d’in data ce mishi bai ji ba.

Shuraim ne ya mik’e, ya ce “Abba zanje in yi assignment d’ina kafin mu fita”
Da sauri itama ta mik’e daman hanya take nema saboda sam bata k’aunar zamanta waje d’aya da Aslam kwata kwata, gashi ta lura sai faman kallonta yake tayi, sannan anyi rashin sa a ya zauna a kujerar da take opposite d’in tata ne a hankali cikin nutsuwarta tace “Abba nima bara inje” sannan ta juya ta yiwa Daddy sai anjima. Sudais shima binsu yayi, suka fice a tare…

Da murmushi Abban ya bisu da kallo yana jin wani tsananin farin ciki a ranshi.

Gyaran muryar da Daddy yayi ne ya juyo da hankalin su inda yake. Ganin yanayin shi yasa duk suka maida hankulansu a kanshi. Cikin rauni yace “Abba jiya da daddare naje wajen su Mammy, and thier situation is bad! Very bad!! Nasan abunda suka yi was wrong but anyi saurin yanke hukunci cikin fushi gaskiya. Thou they deserve it, but matsalan shine they can’t survive in there most especially ma Ummi, dan a yanzu inda zaka je ka kalla jikinta to ba zaka so ka k’ara kalloba sakamokon k’uraje da borin jinin da suka fito mata ta koina! Ka san dama ita tana da allergy tun tana y’ar k’arama tanada kyankyami sosai!
Ko fa 1 week ba ai ba amman in kaje ba lalle ka iya gane ta ba! I don’t think zata iya kai 2 months a wajen nan gaskiya, jiya da naje ruwa ake k’ara mata, amai da gudawa take yi, gashi ko abinci mai kyau in mutum ya kai musu Granpa sai ya sab’a maka. Kar garin punishing d’insu kuma muje mu shiga hakkinsu, after all they are our wives..”

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Daddy inda case d’in nan a hannu na yake, tou da zan iya sassauta musu, not because of wai na yafe musu ko na huce, NO! Only because of maganan da kayi min yanzun. Amman Granpa ke rik’e da case d’in, already ni da kai masu laifine a idanunsa a yanzu, Ina tunanin In muka yi interfering, za a iya samun matsala.”

Cikin katse shi Daddy ya ce “Ba interfering za muyi ba! Gramma za muyi wa magana, na san ya san yadda za tayi ta d’an shawo kanshi, at least a d’an sassauta musu, ya bari a dinga kai mu su abinci daga nan, sannan a ajjiye su a tsaftataccen waje, dan gaskiya jikin Ummi ya ba ni tsoro jiya.”

Numfashi Abba ya fesar, sannan yace “ba komai zan kira Gramma d’in a waya zuwa anjima in shaa Allah.”

A hankali Aslam yayi k’asa da kanshi sannan yace. “Zan yiwa Granpa magana, in sha Allah zai sauk’o, zan lallab’ashi.” Shiruu, suka d’an yi, chan kuma Daddy yace “ok, hakan zai fi.”

Abba yana shirin mik’ewa, Daddy yace “akwai wata maganar still fa. Jiya bayan mun rabu Arshaad ya kira ni, wai yana son yin magana dani, i think kunyar ka yake ji shiyasa ya bari sai da na koma.”

Da mamaki Abba yace “Arshaad? Kunya ta kuma? Ikon Allah!”

Murmushi Daddy yayi, sannan yace “Bayan yace ‘yana son magana dani’ shine nace masa ‘ya zo tou muyi face to face’ Mun dad’e tare dan tare ma muka je station d’in da shi.”

D’an kallonshi Abban yayi sosai ya bashi dukkanin hankalinsa alamun yana buk’atar k’arin bayani.

Murmushi Daddy ya sake yi, kana ganinshi ka san yana cikin farin ciki da jin dad’in al’amarin, fuskarsa cike da annashuwa ya ce “Good news ne,
Ashe wai ya san Huda, for the past 3 years, and suna dating ne, ita ce Yarinyar da muke da shirin zuwa nema masa aurenta! So yanzu ya same ni ne akan ko za a fara maganar tasu tund…”

Kwarewar da Aslam yayi ne ya hanashi k’arasawa. Da sauri Abba ya mik’a mishi ruwa dan haka ya karb’a ya d’an kurb’a yana tarin kad’an kad’an still, su kuma suna ta jera mishi “sannu!” D’aga kanshi kawai ya iya yi
Idanunsa sun yi jaaaa! Alamun ba kad’an ba yaji azabar kwarewar.

Sai da suka ga ya d’an nutsu tukunna
Daddy ya kalli Abba yace “ya ake ciki?Shiruu, Abba yayi, kamar mai nazari, kafin yace “all those years kuma bai gane ta ba?”

“Abun mamaki ko? Suna tare amman basu gane junan su ba!” Daddyn ya fad’a, kafin ya ci gaba da cewa
“Ya yiwa Dad ma maganar!
Wallahi baka ji yadda lamarin nan yayi mana dad’i ba! Ni kam na riga ma na bashi ita.” Ya k’arashe maganar yana murmushi mai kama da dariya wanda ke baiyyana tsantsar farin cikin da yake ciki.

A hankali Abba yayi k’arfin hali ya d’an k’ak’alo guntun murmushi kafin yace “To Allah ya zab’a mana mafi alkhairi” Ameen Daddy yace
sannan ya juyo ya kalli Aslam wanda ya runtse idanunsa ya kwantar da kansa da bayansa a jikin kujerar! Cikin zolaya Daddyn yace “wannan azumin da kaina zan buga maka wak’ar gauro!! Arshaad yayi maka wayo.”

D’an murmushi kawai yayi ba tare da ya bud’e idanunsa ba.

Abba baya son maganan shiyasa ya sako wata maganar daban dan haka suka hau tattaunawa. Shi kam Aslam mik’ewa yayi yayi musu sallama ya kama gabanshi.

A b’angaren Hudan kuwa bayan sun gama dabdalar assignment d’insu dasu Sudais ta tafi d’akinta, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Sai wajen 1:30 ta samu ta farka.
Alwalla tayi tayi sallah, sanin da tayi ba a gida za tayi sallar laasar ba ya sa ta karanta izu hud’u, tayi doguwar addua ta tofa, itama ta shafa.

Tana idarwa Shuraim yazo ya kirata ya ce “taje inji Abba, yana parlour”
Jikinta ba kwari ta fito, dan still ta sake gwada number Ummu tana shiga amman tak’i d’auka! Gashi har yanzu Sakina itama bata kunna wayarta ba, ba kuma ta k’araso ba, Allah yasa ba hanata aka yi ba!. Tana wannan tunanin tana tafiya domin amsa kiran Abban nata.

A parlourn saman inda sides d’insu yake ta sameshi. Tun daga yanayin ta ya fahimci tana cikin damuwa. Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya amsa gaisuwar ta kafin ya ce “Zauna, i want to talk to you”

Zama tayi, a one seater d’in parlour da yayi mata nuni da. Ba tare da b’ata lokaci ba , ya fara magana “ɗ’azu Daddy yake cewa wai Arshaad ya sameshi akan maganar ku!”

Da sauri ta d’ago ta kalleshi, a zuciyarta ta hau mamakin Arshaad da kalar nerve d’inshi! Despite abunda yayi da kuma fushin da suke yi da juna amman shine yaje ya samesu da maganan! Me kenan yake so? Auren yake so a yi ko tana so ko bata so kenan ko me!?

A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa, jin Abban ya sake cewa “Yace wai you two knew each other for a while ko?”

Sai da ta taushi zuciyarta, tukunna ta iya d’agawa Abba kai alamar ‘eh’ sannan ta bashi labarin yadda Arshaad d’in ya kaisu makaranta.
Hatta wayoyin daya siya musu sai da ta fad’a mishi bata b’oye komai ba a labari da tarin alkahairan da yayi musu tun daga had’uwar su har kawo yanzu. Dan ita bata kasance mai manta alkhairi ba kwata kwata.
Tana so ta fad’a mishi issue d’inshi da Jalila amman sai ta kasa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e bayan ya gama jin bayaninta yana k’ok’arin fassara lamarin Arshaad amman ya kasa! Tabbas akwai abinda Arshaad ya sani tun farko kuma yayi shiru wanda shi kad’ai ya san dalilin yin shirun da yayi! Dan a cikin labarin da Huda ta bashi yanzun yaji inda Arshaad ya had’u da Mama ba so d’aya ba, and in dai Arshaad ne ya tattare mishi d’akinsa kwanakin baya da za suyi parking ya kai personal kayayyakin shi gidan shi na kwandila, tou tabbas ya san wacece Huda!

Ahankali yaji tace “amman Abba yanzu bama tare mun yi fad’a sosai..”
Ta k’arashe maganar tana kuma yin k’asa da kanta. Murmushi Abban yayi kafin ya ce “Ai kuwa ke kad’ai kike fad’anki! Don shi gashi yazo yana binmu one by one yana expressing how much he loves you.”

Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta. Tashi d’aya Maryam ce ta fad’o mishi arai, yanayin kunyarsu iri d’aya ce, kalli fa fad’a ta ce suna yi amman kuma anyi magana ta hau jin kunya. Murmushi yayi kafin yace
“Kije ki shirya dan na san yanzu Auwal zai zo, Shuraim yace min “zai bada hadda yau a islamiyyarsu da suke zuwa duk asabar da lahadi so nan zai je shi ba zai samu daman binku ba.
Sai kuje da ke da Sudais kawai.”

“To” ta ce, sannan ta mik’e,
har tayi gaba sai kuma ta juyo
Ta ce, “Abba Allah da gaske nake yi munyi fad’a dashi, fad’an gaske!”

Dariya ta bashi ganin yanda ta dage akan ita fa sun yi fad’a, amman ko a cikin bayaninta, yadda take yabon Arshaad d’in, ya sanya ya fahimci still tana son abunta.

Murmushi kawai ya sake yi ya ce
“Tam na yarda kun yi fad’a, shikenan.” A hankali ta juya ta wuce don taje ta shirya.

Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da bayanshi da kanshi jikin kujerar. Zai fara yin magana da Arshaad first! He just hope yanada kwakkwaran reason ba munafuntar su yayi ba all this time.
Saboda in dai hakane tou gaskiya zai murzawa idanunsa toka, ya hanashi Huda! Dan ba zai bari y’arsa ta rayu da Namiji mai b’oye b’oye ba.Ya lura da tana sonshi, so yana adduar Allah yasa Arshaad d’in ya zamana yana da reason d’in da zai kare kanshi kwakkwara! Zai yi farin ciki da hakan
domin kuwa ya san that’s wat she wants. Duk da kuwa yana da wani buri da ya d’aura akanta tun lokacin da ya fahimci yanada y’a mace mai shekarunta amman tunda he’s late ta riga ta zab’i Arshaad, shikenan ba komai, yana yi mata fatan alkhairi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 41So Da Buri 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×