Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta tana jin kamar an tsundumata a Aljannah! Suka barshi shi kad’ai a tsaye.
A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu. Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi,yana d’agowa suka had’a ido da Dad.Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki.
Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok. . .