Skip to content
Part 51 of 72 in the Series So Da Buri by Bulama

Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta tana jin kamar an tsundumata a Aljannah! Suka barshi shi kad’ai a tsaye.

A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu. Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi,
yana d’agowa suka had’a ido da Dad.
Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki.

Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok’arin danne abunda ya tokare mishi k’irji ya ce “Ina wuni Dad”

Sai da Dad d’in ya d’an k’uraa mishi ido tukun yace “Lafiya kake kuwa?”

Murmushi kawai Arshaad d’in ya k’ak’alo kafin yace “Alhamdulillah!
All is fine na gaji ne kawai, bara inyi freshening off in kwanta”. Ya k’arashe maganan da k’ok’arin barin wajen dan
ya lura da kallon da Dad d’in yake mishi so yake ya gane yanayinshi ne.

Har ya d’anyi gaba yaji Dad d’in yace
“Arshaad”. Tsayawa kawai yayi ba tare da ya juyo ba.

Ajiyar zuciya Dad d’in ya sauk’e kafin a hankali shi ya taka ya k’arasa inda yake ya tsaya a gaban shi yasa hannu ya dafa kafad’ar shi, cikin kulawa ya fara magana. “Son, irin haka is normal! Most a times couple basa tashi samun matsala sai ya rage y’an kwanaki kad’an aurensu. Ka kwantar da hankalin ka kar ka sa komai a ranka, za ku hirya soon komai ya wuce kamar bai faru ba. Wannan duk aikin shed’an ne so karka bari yayi galaba a kanka. Allah yayi muku albarka.”

Cikin sigar zolaya ya ci gaba da cewa
“Nan da jibi fa ka zama magidanci, a nan ne zaka fara facing real life da real issues, So garama ka shirya! Kar ka bari small things irin haka suyi breaking naka.”

Da k’arfi Arshaad ya taune lip d’inshi na k’asa, yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa! Ba k’aramin kokawa yayi da makogwaro da harshenshi ba kafin ya samu su bashi had’in kai wajen furta kalmar “In shaa Allah Dad, thanks a lot.”

Murmushi Dad d’in yayi kafin ya d’anyi tapping kafad’ar shi da hannunshi ke a kai yace mishi “good night”, daga nan ya nufi hanyar side d’inshi, ya bar Arshaad tsaye a wajen…

In banda ajiyar zuciya babu abunda Arshaad yake sauk’ewa a jere a jere.
Ganin ya fara ganin duhu duhu, kar yaje ya fad’i a wajen yasa ya lallab’a ya nufi side d’inshi shima dake nan a k’asan.

Da kyar ya kai kanshi toilet
bayan ya ajjiye suite d’in hannunshi akan gadon. Ko agogon hannunshi bai samu ya cire ba ya yana shiga toilet d’in ya sakarwa kanshin shower ta ko’ina da ruwa mai mugun sanyi!

Ya dad’e a haka kafin da kyar ya samu ya fito kayan jikinshi na d’igar ruwa.
Daidai nan ya ji wayarsa ta hau ringing, hannu yasa a aljihu kafin ya zaro wayar k’irar iphone 13 ya kalla screen d’in! A take damuwar da ya samu ta d’an ragu ta dawo mishi sabuwa ta sake hauhawa sakamokon ganin mai kiran nasa. Har ta tsinke bai d’aga ba kuma bai daina kallon screen d’inba! Yana a yanda yake wani kiran ya sake shigowa. A hankali hannunshi na rawa ya d’auka ya kai kunnenshi kawai yayi shiru bai ce komai ba.

Cikin sanyin muryarta yaji tace
“Ya Arshaad.” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe idanuwanshi da suka yi jaaa wanda hakan ya bawa hawayen da yake ta addabar zuciyarshi daman zubowa ta ido d’aya! Kafin d’ayan idon shima ya samu damar zubo da nashi hawayen.

Ajiyar zuciya kawai taji yana sauk’ewa a jejjere. Hakan yasa a d’an rud’e tace
“Ya Arshaad ka yi mini magana pls, baka da lafiya ne yanzu? Mai ya faru”

Da kyar ya iya k’arasawa bakin gadonsa ya zauna dan ya fara rawar sanyi ba kad’an ba! Yana zama wata wawiyar atishawa ta kece mishi
wanda yasa Hudan mik’ewa daga kwancen da take, kafin tace “Mura ko? Sorry sannu ka sha magani tou?”

Sai a sannan taji yayi magana
“Hudan!” “Naam” tace da sauri dan daman so take taji ya furta wani abun dan shirun nashi ba k’aramin tsoratata yayi ba. A hankali ya d’an yi tari kafin yace,v“Do you love me??”

Ta d’anji kunyar tambayar amma jin yanayin shi da kuma muryarshi wata iri yasa tace, Yes, a lot”. A hankali yace
“Say it” Shiruu, ta d’anyi kafin a hankali yaji tace, “I love you”

Sai da yad’an lumshe idanuwansa kafin yace, “To what extent??”
Ya sake jeho mata wata tambayar.

Zuwa yanzu kam yad’an fara birkita mata lissafi hakan yasa tace “Ya Arshaad meye ne yake damunka?”
Tayi masa tambayar kamar zata fashe da kuka.

Cikin tsare gida yace “Just answer me!
How much?? To what extent za ki iya zuwa domin kiga mun mallaki junan mu??”

Ita dai ba abunda take fahimta daga shi zuwa yanzu, gashi tana jin yadda numfashinshi yake seizing sama sama!
Daurewa tayi tace “Kamar yaya?”
Dan da gasken bata fahimta ba.

Da kyar ya dedeta numfashinshi
kafin yace “Idan Mama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??

Sai da ya sake maimaita mata tambayar tukunna tace “Maama ba zata tab’a cewa In hak’ura da kai ba!
Meyene ya faru na kasa gane komai”

Bai bata amsar ba sai cewa yayi
“Idan Maama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??”

Ta kasa fahimtar inda ya dosa,
kawai sai ta yanke shawarar ce mishi
“Ya Arshaad ai albarkar iyaye shine abinda ake buk’ata! In basu da niyyar sakawa meye amfanin auren da za ayi babu albarka?”

Rintse idanuwansa yayi da k’arfi! Tuni numfashinshi suka fara korar juna.
She can feel it dan haka duk sai ta sake rud’ewa ta hau kiran sunan shi
amman yak’i kulata, k’arshema
wani irin tari taji yana yi, yayi kusan 3 minutes yana tarin Hudan tana kuka tana kiran sunanshi amman shiru
wanda hakan har sai da ya farkar da Sakina da Khadijah amarya y’ar Anty Zainab da suke d’aki d’aya da ita
daga bacci.

Ganin yanda duk ta rud’e ne yasa Sakina ta shiga tambayarta.

Karb’ar wayar Sakina tayi
itama ta shiga kiran sunan shi
tana. “Are you there? Are u okay??”
Amman tsit kake ji ko tari babu.

Rikicewa suka yi. Da kyar idea ta fad’owa Sakina hakan yasa da sauri ta d’auki wayarta ta danna kiran Aaima!
Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna aka d’auka, cikin gigita Sakina tace Aaima ina wuni,
sorry na tashe ki, Ya Arshaad ne bashi da lafiya, dan Allah ko zaki gayawa Dad in yana gida a duba shi ko kuma ki tura wani wanda yake kusa.”

Shiruuu, Sakina taji anyi! Hakan yasa ta sake cewa, “Aaima”

Ajiyar zuciya taji Aaiman ta sauk’e sannan ta fara magana. “Ki turo Hudan mana ta zo ta duba shi! Daga nan ma sai su yi sorting out decision d’in da ya kamata su yanke. Besides
a nan ba wanda zai kulashi saboda rashin lafiyarshi ba zamu iya yi mishi maganinta ba. Spoiler alert!! Bara kiji abunda na san ya jawo mishi ciwon.
Mammy ta dawo d’azu at last ita da su Mom! And tace masa ‘ya hak’ura da auren Huda ko kuma ta tsine mishi!’
Wannan shine abunda ya janyo mishi rashin lafiya na riga da na sani.”
Tana gama fad’in haka ta ajjiye wayar.

K’amewa Sakina tayi ta kasa cire wayar daga kunnenta! Sai da Hudan ta tab’ota tace “Ya ake ciki Sakina?”
Tukunna tayi firgigit ta dawo daga tunanin tashin hankalin data fad’a na y’an sakanni. Dama da ita bata tab’a fadawa kowa ba ne amma haka kurum idan ta tuna Mammy bata san dalili ba sai taji gabanta yana ta fad’uwa!
Dan bata san ya tsakaninta da Huda zai kasance ba. Kuma ta lura kamar Arshaad d’in yana ta saurin ayi ayi ai auren su samu su bar k’asar! Tabbas sai yanzu ta fahimci dalilinshi. To amma mai yasa Ya Arshaad zai so ya had’a ta da surukar da ba zata amsheta ba? Duk kuwa da tsananin k’aunar da suke yiwa juna ai da sun hak’ura! “Sakina, akwai matsala ne?”
Muryar Hudan cikin rauni, ta katse mata tunaninta.

Juyawa tayi suka had’a ido! A take wani tsananin tausayinta ya rufeta
dan bata jin a cikin shekaru ukun nan akwai lokacin da take hango tsantsar k’aunar Arshaad a idanun Hudan kamar wannan lokacin. Da kyar ta iya ce mata, “Aaiman bata gida, bara in kira Auwal kawai.” Ta fad’i haka tana me mik’ewa ta fice daga d’akin gaba d’aya. Hudan kwata kwata bata gamsu da maganar tata ba dan haka ta mik’e ta bi bayanta.

Suka bar Khadija wadda itama bata wani yarda da maganar Sakinar ba dan ta lura da yanayin da ta shiga tun fara wayarta da wadda suka kira da ‘Aaima’.

Tana fita ta samu damar zubar da kwallar da take ta k’ok’arin rik’ewa!
Yanzu Ina mafita? Meye abunyi ?
Sune tambayoyin da suka toshe mata kwanya sannan ta kasa samun mai bata amsar su. Daman y’an layi har sun fara k’ananan maganganu
suna cewa Allah dai yasa tarihi kar ya maimaita kanshi. Ita maryam bata daddara da family d’in Abba da abunda shi kanshi Abban yayi mata ba
shine zata aurawa Huda nephew d’inshi dan kawai taga yana da masifar kud’i! Ga dai Ummu ita da ta auri saffa saffa hankalinta a kwance rayuwarta gwanin ban shaawa
amman ita har yau bata samu kwanciyar hankali ba a ta dalilin So da Buri! Ta mannewa mutumin da yafi k’arfin ta nesa ba kusa ba.

Jin k’arar bud’e k’ofar d’akin nasu ne ya sanya Sakina goge hawayenta da sauri, sannan ta lalubo number Auwal
ba dan ranta yana so ba ta fara kiranshi.

Bacci bai dad’e da d’aukarsa ba dan bai dad’e da kwanciya ba amman yana fara baccin ya hau mafarkinta.

Yana cikin mafarkin nata k’arar wayarshi ta katse mishi mafarkin.

Kamar ba zai juya ba bayan ya farkan sai kuma yayi tunanin ko Granpa ne dan haka yayi tsaki ya lalubo wayar akan bedside ya amsa ya kara a kunnnen shi ba tare daya duba mai kiran nasa ba.

Jin shiru yasa tace “Ya Auwal”
A hankali. Bude idanuwansa yayi da kyau kafin ya zaro wayar daga kunnenshi ya kalla sosai ya tabbatar itan ce tukunna ya mayar da wayar kan kunnensa ya mik’e zaune
yana adduar ‘Allah yasa lafiya’
dan ya san ba k’aramin abu bane zai sanya Sakina ta kirashi kuma cikin daren nan ba.

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “How far” Dan lokaci d’aya ranshi ya b’aci bayan ya tuno ta Ita da Ashraff d’azu.

Ba tare da b’ata lokaciba tace mishi
“Ya Arshaad ne suke tunanin bashi da lafiya dan yanzu ma kamar suma yayi suna cikin waya da Hudan.” Ta san maybe Hudan ce ta fito d’azun kuma maybe tana tsaye a bayan nata dan haka sai ta tak’aita maganar tata
sannan tace “Dan Allah yaje ya dubo shi”

“Okay” Kawai yace daga nan ya kashe wayar ya mik’e ya fad’a toilet yad’an d’auraye fuskar shi ya chanja zuwa jallabiya tukunna ya fita.

Sai da ya daddannawa gate man d’in zagi, tukunna ya barshi ya fita
A cewar shi (gateman d’in) Daddy ya hana a na barinshi yana fita cikin dare.

Sai mita yake yi shi kad’ai a mota haka ya isa gate na estate d’in MT a ranshi yana aiyyanawa Da mutane sun san halin da yake ciki to da ko kallonshi ba zasu dinga yi ba! Komai b’ata mishi rai yake yi tun d’azu…’ Allah ya so shi bai samu matsala da mai gadin main estate d’in ba, sai dai ya rok’esa akan ‘ya bi a hankali kar ya bari Granpa ya ganshi dan zai iya cewa a bakin aikin shi’.

Jinjina kai kawai yayi ya wuce ciki.
Ya dad’e yana knocking jin shiru yasa ya yanke shawarar kiran Aaima yace mata ‘ta kira layin wata a cikin masu aikin gidan tazo ta bud’e mishi k’ofa.’

Tunda Sakina ta kira ta bacci ya k’aura daga idanunta, tana cikin chatting kiranshi ya shigo wayar tata.
Ta dad’e tana kallon number, kasancewar ta dad’e da goge numbershi amman ta na nan a kwakwalwarta bata gogu ba! A take jikinta ya mutu. Sai da wayar ta kusan tsinkewa tukun ta samu damar amsawa, cikin sanyin jiki ta kara a kunnenta tace “Hello”. Ba tare da ya amsa ba yace “Aaima Arshaad is sick, na zo duba halin da yake ciki kuma k’ofan ank’i bud’ewa.. Can you do me a favor ki kira wani wanda kika sani a cikin gidan yazo ya bud’e min?
It’s an emergency”

Tunda ya fara magana ta lumshe idonta har ya kai aya a hankali tace “to” kawai, ta tsinke kiran.

Kamar 5 minutes yaji ana k’ok’arin bud’e k’ofar, ana bud’ewa ya kutsa kai ciki ba tare da ya kalli bayan k’ofar ba inda take, yayi hanyar side d’in Arshaad direct kawai. “Ina wuni”
Yaji muryar ta. D’an juyowa yayi ya kalleta a ranshi yace,v“Ashe ta dawo.”
Ba yabo ba fallasa yace “Lafiya”
Kawai ya juya ya nufi hanyar part d’in Arshaad.

“Ya k’ara haske, sai dai yad’an rame kad’an! Ya k’ara kyau.” Ta fad’a a k’asan ranta! Bata san dalili ba amman taji zafin yadda yayi mata, taso ta koma sama kawai abunta amman sai ta tsinci kanta da kwad’ayin bin bayanshi, dan haka ta rufe k’ofar ta nufi side d’in Arshaad.

Direct main bedroom d’in dake side d’in Auwal ya nufa. Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya.
Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi.

Dai dai nan Aaima ta shigo,
duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki.
Da sauri Auwal ya juya gareta yace
“Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..” Ya fad’a cikin gigita da kid’ima.

Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi.

Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari! Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu. Da kyar ya samu tarin ya tsaya ya shiga jejjera ajiyar zuciya.

Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu.
Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa “Kar ka kira kowa Auwal, i’m fine. Please.” Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace
“Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan! Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.” Cikin d’an fushi Arshaad yace “Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina! Yanzu kuma na farfad’o…
Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in bayan wanda kukai min.”

D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi.

A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon sannan yace
“sorry”

Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e
kafin yace “Are you sure that’s all?”

Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi.

Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace “Shikenan,
Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai. And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.”

“Ok” shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa “Thanks a lot”

Murmushi yayi kawai yace mishi
“Good night” Daga nan ya nufi hanyar fita.

Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace “Ka kira wayana if you need anything”

Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi.

Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda har ya kusan ficewa. Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e.
Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi Ya sa kai zai fice.

Daurewa tayi tace, “Mun gode sai da safe”

“Allah ya kaimu” yace daga nan ya fice.

Ta jima a parlourn bayan ya fita.
Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki.
Da kyar ta samu bacci ya d’auketa.

Shi kuwa Arshaad yadda yaga rana haka ya ga dare! Yana jinta lokacin da ta shigo, baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’.

Kafin safiya ya gama deciding yadda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba ga tunani barkatai
shiyasa zazzab’i yace salama alaikom.

Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe! Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu….

Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’a shi yana zazzab’i mai k’arfi.

Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso. Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani, daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama.

Sai wajajen 11 drip d’in ya k’are
da kansa ya zare ya danne, bayan some minutes ya mik’e ya fad’a wanka.
Yaji dad’in jikinshi ba kad’an ba kuwa.
Yana fitowa ya d’an shafa mai da turaruka ya zura wata cream jallabiya mai gajeran hannu. A hankali ya k’arasa bakin gadon ya d’au wayarshi ya fara kiran Hudan dan tun da safe yaga message d’inta.

Bata wani dad’e tana ringin ba ta d’auka! Bayan sun gaisa ya tabbatar mata da ‘he’s okay daman kawai dan zazzab’i ne’. Tace mishi “Anjima around 1 ana buk’atar shi za suyi traditional event d’insu na yaren Shuwa kuma dole sai yana wajen!
Inda hali ya turo driver kafin nan, yazo ya karb’a mishi kayan tradition d’in da aka tana da domin shi (wanda zai saka a event d’in) Kayan ba su iso ba sai d’azu shiyasa bata bashi da wuri ba.”

Da “to” ya amsa ta daga nan suka hau hirarsu dan yaga kamar hankalinta still a d’an tashe yake.

Sun jima suna hira dan sun fi 30 minutes kafin suyi sallama.

A hankali yayi shiru, yana y’an tunane tunane.. Chaaan! Ya turawa driver d’in da zai karb’o mishi kayan nashi message daga nan ya mik’e yayi kalmar shahada ya fita ya nufi sama wajen Mammy.

A stairs suka had’u da ita tana k’ok’arin sauk’owa! Kamar bata ganshiba haka tazo ta wuce shi.

Hannunta yayi saurin rik’ewa ya juyo a hankali yace “Haba Mammy. Ki saurareni please mana.” Ya fad’i hakan kamar mai shirim fashewa da kuka.
Ba tare da ta kalle shi ba tace “Ka bari idan Allah ya kaimu gobe naga kayi abunda nace sai in saurareka”

“Meye abunda kike so yayi miki goben??” Suka ji muryar Dad a bayan su!.

Da sauri Arshaad ya juya yana kallonshi gabanshi na tsananta fad’uwa! Ba tare data juyo ko ta damu da Dad d’inba tace “Ai gaka ga shi nan!
Kana iya tambayarshi.” Tana gama fad’in haka ta nufi k’asa wajen bakinsa da take expecting dan sune ma suka ce mata sun kusan shigowa ba daban su ba da babu abinda zai sauk’o da ita k’asan! Tana buk’atar time ita kad’ai,
dan ita kanta bata san daliliba amman komai ya kunce mata.

Kame kame Arshaad ya fara bayan ta sauk’a. Babu yadda Dad bai yi da shi ba amman yace mishi “ba komai! Kawai sun d’an samu issue ne shi da ita lokacin tana cell shine yake so suyi settling”. Sam Dad bai yarda da shi ba
dan kwata kwata babu kamanceceniya a cikin maganar shi da tata!.
Fahimtar da Dad yayi Arshaad d’in ba zai gaya mishi komai ba ne yasa kawai yace “to, shikenan ka samu ku shirya d’in kafin ka bar gidan nan.”
Yana gama fad’in haka ya wuce shi shima yayi k’asan.

Sai a sannan Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya. He needs to talk to Mammy!
Idan tak’i ta lallashi tabbas zai b’ullo mata ta hanyar da bata zata ba! Akwai abubuwa da dama wadanda ya sani amma ya yi shiru kuma ta san ya sani but it’s like kamar ta manta, so he has to remind her!.

Sannan ya san ta inda zai b’ullo mata ta yarda dan yaga alamun ba lalle ta yarda cikin sauk’i ba gashi babu enough time!

Ya jima a wajen kafin ya juya ya wuce sama da niyyar d’an bata time Kafin ya sake ganinta! Yana da full hope d’in zai yi nasara bi izinillahi.

Mammy na sauk’a k’asan ta fara shan mamaki. Kulolin abinci kala kala da su drinks ake ta shigowa da su! Bata ida fita daga wannan mamakin ba taga friends d’inta da sisters d’inta har da Mahaifiyarta suna ta shigowa
har da ankon super d’in su da suka yi a jikinsu. Da sauri ta k’arasa kusa da yayarta ta kamota tace “Me kenan? Wats the big idea?”

Murmushi Haj Binta tayi kafin tace “Wunin d’an mu za muyi mana!
Anjima kad’an kuma muje muga Amarya naji Dad yace za suyi traditional day d’insu suma daga nan mu bata kyaututtuka. Naga ke baki son zancen shiyasa ma na zagayeki na kira Dad. Anko kuwa ni na fitar kuma gashi kowa yayi, ni da su Hajiya ( Mahaifiyar su) tun lokacin da aka sa rana dama muke ta shirye shiryen mu.

Matsowa Mahaifiyar tasu tayi kusa da su ( ita da sister d’in tata ) kafin itama ta fara magana. “Ki nutsu ki bari ayi komai a gama daga nan sai a san abun yi! Ni na hanasu su fad’a miki komai akan lamarin auren, gudun samun matsala dan na san halinki. In dai ni na haifeki to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi hak’uri, ni kaina ba wai son had’in nake yi ba! Amman ki bar ni da su kawai ai in sun san wata basu san wata ba! Kuma kar ki bari kowa ya fahimci halin da ake ciki, ki nuna kina so inda hali ma ki shirya muje ki bawa ita Yarinyar kyauta da hannunki a gaban kowa…”

Ganin friends d’in Mammyn sun tunkarosu ne yasa Mahaifiyar tata yin shiru ta fara yak’e. Suna zuwa kuwa suka hau tayata murna kowa na farin ciki tare da yi mata ya jiki (dan ce musu aka yi ita da su Mom duk sun yi inhealing dangerous abu shine aka fitar da su k’asar waje suka yi jinya sai jiya suka dawo).

Haka nan suka k’arasa tsakar falon aka zazzauna.

Masu decoration suka shigo suka hau d’an gyaggyara parlourn. Yayar tata ce tace “bara taje ta ajjiye abu daga nan ta cewa Arshaad ya shirya, su d’anyi hotuna a nan kafin a tafi event d’in su Hudan..” Sama ta nufa da niyyar ajjiye abu tukun ta je ta kira Arshaad d’in
Tana shirin hawa suka had’u da Dad yana sauk’owa. Cikin mutunta juna da barkwanci suka gaisa daga nan yace mata “Ta kirawo masa Mammy, su sameshi su biyu a side d’in Arshaad.”

Mammy na zaune a cikin friends da y’an uwanta amman kwata kwata hankalinta baya a garesu!

K’ok’ari take taga ta tirsasa zuciyarta ta aminta da abinda Mamanta tace mata yanzun, amman furr ta kasa.
A wannan yanayin sister d’in nata tazo ta rad’a mata sak’on Dad a kunne daga nan ta wuce ta nufi parlourn Arshaad.
Da kyar Mammy ta iya mik’ewa tabi bayan ta.. Sauk’owar Arshaad kenan yaga sun nufi side d’inshi,
A ranshi ya ce “perfect”
Duk fa bai san me za suyi anan d’in ba.

K’arasawa yayi ya gaggaisa da bak’in, kakarshi tana ta tsokanarshi, daga nan ya wuce shima. A parlourn suka tarar da Dad yanata faman kai kawo. Suna shigowa ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Binta, ga y’ar uwarki nan, ki tayani tambayarta. Akwai abunda suke b’oye min ita da Arshaad wanda ban sani ba!
Na san halinta da sana be kala kala dan haka idan akwai wani abun gara tun farko ta fito ta fad’a kar taje ta yiwa mutane shirme!”

Hajiya Binta tana shirin yin magana Mammy tayi caraf ta amshe ta fara magana “Ai kai da kanka yanzu me kace? Muna b’oye maka, ko? To kuwa ai kaga tunda muka b’oye maka d’in to bai shafeka ba kenan! Infact babu abunda ma ya shafeka na daga rayuwar ni da y’ay’ana. Da kace kana kirana i thought welcoming d’ina zaka yi”. Murmushin takaici tayi kafin ta juya ga Hajiya Binta tace mata “Ko kin san tun jiya dana dawo ban ga k’eyar bawan Allah n nan a kusa da ni ba balle ya tambayeni lafiyata ko ya nake? Ai ko ni kad’ai na aikata laifin b’oye y’ar gold d’inku wallahi ban chanchanci haka daga gareka ba ko dan darajar Arshaad da Aaima!”
Ta fad’i haka tana takawa inda yake, daga nan taci gaba “Sannan yanzu ka wani kwaso k’afa kazo kana wani waye waye. Kai har kana da kunyar yi min wannan maganar? Bayan abunda ka yi? To bari kaji bai shafe ka ba!
Ka zuba ido zaka gani tare da kowa idan Allah ya kaimu gobe.” Tana gama fad’in haka ta juya ta nufi hanyar fita.

“Idan kika taka k’afarki kika bar min parlourn nan ba tare da kin fad’a min abunda nake son ji ba to a bakin auran ki.”

Ba mammy ba hatta Hajiya Binta sai da gabanta ya yanke ya fad’i.

Juyowa tayi tana kallonshi da idanuwanta da suka fara chanja launi, cikin tsananin takaici tace “Namiji k’anin ajali! Ai Aisha ta dawo dole ka yi min haka. To bari kaji in gaya maka wallah ko ka sakeni babu inda zanje sai dai in kai ka fita ka bar mana gidan nan ni da y’ay’ana!”

Cikin katseta yace “Rukayya kar ki yi underestimating d’ina! Dan wallahi zan yi miki abunda ko me sunana aka kira sai kin ji kin tsani wanda ya kira sunan! Baki san a ya’ya nake ganin ki ba a halin yanzu, kar ki kaini bango!
Wallahi ba dan darajar Aaiima da Arshaad ba da tuni na dad’e da sauya miki rayuwa. Ba na son dogon magana dan ba na jin iya zama mai tsawo a inuwa d’aya da ke! Ki fad’amin abunda nake son ji in fita.” Ya fad’i haka cikin kakkausar muryar da take baiyyana tsanannin b’acin ran da yake ciki.

Haj Binta ce tace “Kayi hak’uri dan Allah, Mammy ke kuma ba a haka!
Ki bari wannan matsalarku ce daga baya za ku yi settling ke da shi
Yanzu ki fad’i abunda yake son ji tunda ya nuna yana da buk’atar hakan”

Cikin tsananin b’acin rai Mammy tace
“Ba zan fad’a ba! Wallahi ba zan fad’a ba”. Sannan ta juya gareshi tace
“In kana buk’atar ji Yahaya ka zo ka shak’eni sai in fad’i maka ta k’arfin tsiya!! Da kake wani maganar sauya mini rayuwa, na nawa kuma?
Bayan azabtar da mu d’in da ku kayi me ye kuma kuke tunanin za ku yi kuma wanda yafi wannan??. Ba dai rashin sanin ya kamata ka d’aurawa kanka ba, rana d’aya? To wallahi dede nake da k’ugunka! Maganace nace ba zan fad’a ba In kuma ka matsu to kazo ka shak’eni In fad’eta.”

Cikin tsannnin fushi ya tunkarota kamar wanda zai rufe ta da duka!
Da sauri Arshaad wanda shigowar shi kenan yanzun ya shiga gaban Mammy ya tsaya Hajiya Binta kuma taci gaba ta k’ok’arin hana Dad d’in k’arasawa inda Mammyn take!

Dukkannin k’arfin da Allah yayi mata tayi amfani dashi wajen ingije Arshaad d’in sannan kafin yayi nasarar tsaidata ta tafi gaban Dad ta tsaya! Tana mai jin wani tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata, babu abunda idan ta tuna yake k’ona mata rai irin yadda taga Daddy yana ziryar zuwa wajen Adama last zuwanshi da yayi har kusan kuka taga yayi daga nan ma yace ‘ba zai iya sake ganinta a haka ba’. Tun daga ranar kuwa idan bai kirata sau d’aya ba tou zai kira sau biyu! Amman ita ko lek’enta ko waya Dad bai tab’a yi yace a bata ba, ita tana chan tana tunanin sa ashe shi yana nan Aisha ta d’auke masa hankali! Kalli fa sarai ya san ta dawo amman ko lek’enta bai yi ba kuma suna cikin gida d’aya, sai yanzu dan rashin kunya da tsaurin ido ya buk’aci ganinta kuma ko alamar tambayarta ya take bai yi ba instead
ya hau wani tsattsare ido yana hucin banza. Wadannan takaicin ne suka sanya ta kasa cewa komai kawai ta zube a wajen ta fashe da wani mugun kukan bak’in ciki.

Cikin son kawar da lamarin Arshaad yace “Dad, dan Allah ka bar maganar nan, na fad’a maka ba komai fa”.

Banza Dad yayi da shi kawai ya juya ya fice! Yaso ace Mammy tayi mishi wani shirmen yau wallahi da sai ya yi mata abunda bata tab’a tsammani ba! Ya san at least zai samu peace of mind at last. Yana fita Mammy ta mik’e!
Tunda take a rayuwar ta bata tab’a jin kishi da takaici da tashin hankali da bak’in ciki irin na yau ba! Ta rasa dalili amma ko y’ar kissar da ta saba yiwa y’ay’an nata da Dad d’in ta kasa kuma bata jin zata iya, babu abunda take so kuma take buri irin taga ta b’atawa Dad rai ko ta samu zuciyarta ta d’anyi sanyi. Tayi imani yanzu haka wajen Aisha zai tafi yaje ya ganta yad’an samu nutsuwa hankalinshi ya d’an kwanta alhalin ita kuma gashi ya k’unsa mata bak’in cikin da bata jin zata iya mantawa da shi har abada!
Taya zai yi mata haka? Taya zai banzantar da ita har haka saboda Allah kamar wata dabba?
‘Inaaa!! Ba zai yiu ba Wallahi’
Shine abunda ta fad’a ta gyara tsayuwarta tana k’ok’arin yin hanyar waje.

Da sauri Hajiya Binta ta tareta tace
“Meye haka ne wai Mammy? Ba a isa a fad’a miki kiji bane? Ina za ki ji yanzun?” Cikin kukan Mammy tace
“Kina ganin fa abubuwan da Yahaya yake yi mini. Ya gama b’ata min rai ya fice ya tafi wajen uwar gidan shi ya bar ni ni anan zuciyata ta kama da wuta kenan ko me? Ki cikani kawai, wallahi bai isa yayi farin ciki ba, ba inda zai je yau, kullle k’ofar gidan nan zan yi sai dai mu kashe juna ni da shi a cikin gidan nan!”

Da sauri Arshaad ya matso kusa da su ya rik’eta, wani tsananin takaicin sa take ji hakan yasa ta juyo da sauri ta kifa masa Mari! Sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ai kaima baka kishina Arshaad, a tunanina ko Hudan y’ar gwal ce wallahi ba za ka so auren ta b. Taya za ka had’ani da ita mu zama surukai!? Ko kasan cin mutuncin nan da aka yi min shine abu mafi muni a rayuwata?. Na fad’a na k’ara fad’a yanzu ma zan maimaita maka
‘Wallahi idan ka aureta sai na tsine maka!’.”

Arshaad bai san lokacin da ya tsugunna a wajen ba ya fashe da wani mugun kuka.

Cikin b’acin rai da kafiya Mammy tace
“Kuma ko event d’in yau da suka gaiyyaceka ban yarda ka je ba!
In kaje kuma wallahi Allah ya isa ban yafe ba! Zan ga wa zaka zab’a tsakanin ni da ita.”

Da sauri ya mik’e yace “Haba Mammy ya kike so inyi ne? Ki tsaya ki saurareni kuma kin k’i. Dad ne ya nema min aurenta Abba kuma ya bani,
idan nayi miki biyayya su kuma bijire musu kike so in yi?”

Da sauri cikin katsesu Hajiya Binta tace “Rukayya ban tab’a tunanin baki da hankali ba sai yau wallahi! Ni, na fad’a miki! Mahaifiyarmu, itama ta fad’a miki! Amma ba za ki ji ba?
Waye a cikinmu zai fad’a miki abunda zai cutar da ke? Munce kiyi hak’uri ko?
Wadan ne irin y’an iskan aljanu masu shegan taurin kai kika kwaso a cell d’in ne wai?”

In banda gunjin kuka babu abunda Mammy take yi.

Cikin son su kad’aita iyaka su biyu dan ta samu damar lallashinta da fahimtar da ita Hajiya Binta ta cewa Arshaad “wuce ka tafi ka shirya ku je ku yi event d’in, idan ka dawo sai mu k’arasa”

Ai kuwa Mammy na jin haka ta tafi da gudu hanyar k’ofar fita ta tsaya tayi stretching hannunwanta sideways ta kare k’ofar tace “wallahi idan ka fita sai na tsine maka!!”

Da sauri Hajiya Binta tazo ta kama hannun tana k’ok’arin janyeta tana cewa “Arshaad zo ka wuce” a ranta tana aiyyanawa. ‘Tabbas akwai abu a kan Mammy’ “Zo ka wuce nace kar ka bari tayi maka spoiling day d’inka!”
Hajiya Binta ta sake maimaitawa ganin Arshaad d’in ya k’ame a waje d’aya abun tausayi.

A hankali ya k’araso ya shiga lallab’ata, Hajiya Binta itama tana yi, amman fur!! Mammy ta yi kane kane a hanyar tana ta faman maimaita kalma d’aya ‘Idan ka fita sai na tsine maka!!’

Basu ji lokacin da akai sliding k’ofar aka shigowa ba sai dai kawai suka ga an juyo da Mammy an wanke ta da mari! Diff!! haka parlourn yayi tsit!
Cikin b’acin rai Maman Mammyn tace
“Yi maza kaje ga Aaima chan driver ya bata kayan da zaka saka ta kawo.
Jeka ka shirya yanzun nan za muzo mu rakaka.”

Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace

“Tace fa In na fita sai ta tsi..”
Cikin katseshi Maman Mammyn tace
“Nace ka fita ko! Ta tsine makan in gani.” A hankali yad’an kalli Mammyn yaga ta d’auke kai daga kallonshi, cikin nutsuwa yayi sliding door d’in ya bud’e ya fice, yana mai share ragowar kwallar dake kwance akan fuskarshi.

Yana fita ta fashe da kuka, cikin kukan tace, “Da wanne kuke so inji ne wai?
Ya kuke son inyi? Wallahi ko sunan Yarinyar bana so a kira! Ji nake yi kamar zan mutu, ku duba fa kuga yadda yake kuka shab’e shab’e dan kawai nace ba zai aureta ba! Idan ya aureta kuma ya kuke tunani??”

Hugging d’inta Mahaifiyar tata tayi tana d’an bubbuga bayanta. Sai da ta tabbatar tayi shiru tukun cikin sigar lallashi tace “Ki yi hak’uri Rukayya,
ke fa da kanki kika ce Mijinki yana share ki! Ki duba fa ko wajen ki baya zuwa kuma da kika dawo bai neme ki ba, ko ya yi miki magana baya ga yanzun?”

Cikin sheshshekar kuka Mammy ta hau girgiza kai alamun ‘a’a’.
Ajiyar zuciya Maman nata ta sauk’e kafin tace “Kinga ko! Wannan ma kad’ai abu ne wanda ya kamata a tsaya a duba da kyau. Yadda kika ce Matar nan tasa ta warke, da kuma dalilin da ya sanya yake ta faman jin haushin ki wanda bamu san daliliba yanzu shine abun a tsaya a duba a gyara bawai wannan k’aramin alhakin ba.”

Da sauri Mammy tace, “Wallahi Hajiya Hudan ba k’aramin alhaki ba ce ba!
Ki duba fa ki ga tun daga ranar data shigo estate d’innan nake cikin tashin hankali.”

Cikin d’an b’acin rai Maman nata tace
“To yanzu ya za ki yi? Kinga fa wannan abun da muka san za kiyi wallahi shiyasa muka k’i mu fad’a miki maganar auren tun kina cell! Ki tsaya ki danne zuciyarki yadda kika saba, ki fara gano matsalar da ta shiga tsakaninki da Mijinki a samu a gyara a shawo kanshi in yaso daga baya sai kiyi yadda kike so. Amman yanzu idan kikayi yunk’urin hana auren nan, wallahi kowa bak’in ki zai gani, kuma hatta Arshaad d’in dakike ta haukar ‘kar Hudan ta janye miki shi’. Ke ce da kanki gashi kike k’ok’arin kawo matsala a tsakaninku da kanki gashi kina tura shi away from you
dan Wallahi kinji na rantse miki yadda Arshaad ya kwallafa rai akan Yarinyar nan muddin kika sake kika zama silar da ya rasata to kuwa ba zai tab’a yafe miki ba! Kuma sai kin yi dana sani.
Ki bari ayi auren sai mu san abun yi. Yanzu kar ki fito b’aro b’aro a matsayin wadda ta hanashi aurent.”

Cikin katseta Mammy tace “Ki kwantar da hankalinki ni na san ta inda zan b’ullo mishi yana jin maganata ai yana yi min biyayya. Matsalar da za a samu shine In har na bari ya aureta!
D’azu fa muka gama waya da Adama wai ashe ma k’asar za su bari gaba d’aya! Haba dan Allah taya ba zan yi kuka ba? D’a na kwalli d’aya a duniya zata d’auke shi su tafi sai ta gama mallakeshi tukun a dawo min da fanko? Dama yanzun ma ya aka k’are?? Ballantana kuma yaje yayi spending years da ita! Ni kawai ku kyaleni dan girman Allah, dan na tabbatar ranar da Arshaad ya aureta to ni kuma zan iya barin duniyar nan a ranar.” Ta k’arashe tana sake fashewa da wani sabon kuka.

Cikin fad’a Maman nata tace
“Babki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig.”

Da sauri Mammy ta ce “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani.
Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 50So Da Buri 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×