Skip to content
Part 52 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Cikin fad’a Maman nata ta ce
“Ba ki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..”

Da sauri Mammy tace “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani.
Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”.
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice da sauri tana share hawayenta. Ko bi ta kan y’an parlourn bata yi ba, ta wuce sama abunta tana huci.

Tana fita Maman nata ta sauk’e ajiyar zuciya! A hankali ta kalli Hajiya Binta ta ce “Allah ya rufa asiri tunda tak’i jin maganata ni uwarta! Ni zan tafi yanzu, idan ta yarda aje wajen event d’in su Amaryar to ku raka shi Idan kuma ta hana sai ku zuba mata ido. Sannan ki samu y’an uwanki ki jasu gefe kice nace ‘ko me zata yi kar wanda yayi yunk’urin hanata’ Ita ta sani. Taje tayi yadda taga ya dace.” Tana gama fad’in haka itama tayi hanyar waje cikin y’ar tafiyar su ta tsoffi.

Sallama ta yiwa matan dake babban parlourn daga nan ta wuce abunta.
Har k’ofar mota ragowar sister’s d’in Mammy guda biyu k’annenta suka rakata, suka bud’e mata gidan baya
ta shiga suka rufe driver yaja suka tafi.
Su duk basu san wainar da ake toyawa ba Hajiya Binta wadda ta kasa fitowa parlourn tun tafiyar Mahaifiyar tasu ce kawai ta sani dan haka suna komawa aka shiga bidiri ana ciye ciye ana ta hotuna! Fitowar Ango da Aaima ne ya k’arawa abun armashi, ba a dad’e ba Mom da Ummi wadda ta d’an ji sauk’i suka shigo, nan suka had’u aka yi ta hotuna.

After kamar 30 minutes haka, aka fara shirye shiryen tafiya gidan su Amarya, anata had’a gifts. Daidai nan Mammy ta sauk’o.

Sai da gaban Arshaad ya yanke ya fad’i amman ya dake ya k’arasa inda take ya fara k’ok’arin jan hannunta yana cewa “ta zo su yi hoto”

Ko alamar zata motsa bata yi ba dan haka ya tsaya ya d’an kalleta yace
“Mammy dan Allah mana, mutane suna kallo fa, ki zo muje”. Ya fad’a yana sake k’ok’arin janta. Suna a haka sisters d’inta da Aaima suka iso wajen.
Fisgewa tayi da mugun k’arfi, kafin tace masa. “Idan baka je ka cire wannan wata kalar shigar ba wallahi Arshaad sai na ci ubanka!! Sannan
ni za ka mayar y’ar iska mai magana biyu? Mu gama magana da kai amma ka je ka wani shirya tsaf sannan dan tsabar raini kazo kana ce min wani muje muyi hoto? Da kai da hoton kun ci kutumar ubanku!”

Runtse idanunsa yayi da mugun k’arfi!
Daidai nan Mommy da Aslam waenda suka shigo yanzun suka nufo su, suka k’araso! Kusan duk sun ji furucinta.

Da mamaki suke kallonta, a hankali Aslam yad’an dafa kafad’ar Arshaad d’in, dukda bai gama sanin wainar da ake toyawa ba amman yad’an fahimci wani abun, hakan ya sanya shi jin mugun tausayinsa ya rufeshi.

Da mamaki Mommy take kallon Mammy kafin tace “Lafiya kuwa?
Me naji kamar kin ce?”

“Amin, wa alaiki Assalam Aisha!”
Mammy ta fad’a cikin tsareta da ido tana jin wani mugun tsanarta na taso mata.

Murmushi Mommy tayi kafin tace “Assalam alaikom, me yake faruwa ne Arshaad?” Ta yi maganar tana me mayar da akalar tambayar tata kan Arshaad saboda tsananin mamakin Mammy da ya rufeta. Tunda suke tare ko da wasa Mammy bata tab’a yi mata kwatankwacin irin haka ba.

Arshaad Yana shirin yin magana Mom ta k’araso tace “Ya dai? Kukayi cirko cirko duk anan?” Kafin ta kalli Mommy tace “Ina ta yi miki magana Mommy, kika k’i kulani kika wuce.
Ina wuni.” Daidai nan Ummi itama ta k’araso wajen nasu. Cikin kulawa Mommy tace “Yi hak’uri Adama,
hankalina ya yo kansu ne dan naga kamar ba k’alau ba.”

Da sauri Mammy tace “K’alau d’in…”

Cikin katseta da d’an k’arfi Mom tace
“Haba k’alau ne mana, komai normal Ina?” Ta fad’i hakan tana kallon Mammy da d’an sign d’in tayi calming down mana.

Tsaf Mammy ta fahimceta. Itafa ta rasa gane dalilin da yasa su Adama da y’an uwanta suke tunanin zata iya yin wata kissa a wannan stage d’in! Taya ma zata iya danne wannan duka dubu d’in da akai mata? Ya an dake ta kuma suna so su hana ta kuka??…

Mom na shirin yin magana taji Ummi tace “Arshaad akwai matsala ne?
Yi magana mana, kar lokaci ya k’ure!
LKaga yanzu tafiya za mu yi.”

Da sauri Mommy ta ce “Dan kuwa har na cewa Maryam d’in ma mun kusan fitowa, na san mu suke jira yanzu haka.”

Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e tana ji kamar ta shak’e Mommy ! ‘Wato irin ita har ta jone da Maryam d’innan’.

Mammy na shirin yin magana

Arshaad wanda ya ga b’oye b’oye shi ba inda zai kaisa dan kwata kwata ya kasa shawo kan Mammy kuma yana ganin in dai ya gayawa Mommy maybe a samu sauk’i ta hanyar Dad da Gramma ne, ya ce “Mommy cewa tayi ko a fasa auren ko ta tsine min”

Da sauri Mommy tace “Whatt!!”
Cikin firgici kafin ta juya kan Mammy tace “Rukayya wanne aure kike so a fasa?”

Ba tare da b’ata lokaci ba cikin b’acin rai da tarar numfashin ta tace “Auren Huda da Arshaad, Aisha! Shi nake so a fasa. Idan kuma kina da ja to sai in ji…”

Sai a sannan Aslam ya d’ago ya kalleta, bata san mai ya faru ba amman sai Yaron yayi mata kwarjini ta kasa ci gaba da magana.

Mommy ta yunk’uro za tayi magana kenan taji Aslam d’in ya rik’e hannunta, ba tare da yace mata uffan ba kawai ya juya da ita suka fara tafiya.

Har suka fice a parlourn bai ce uffan ba ita kuma bata yi mishi tirjiya ba, sai da suka isa tsakiyar compound d’in tukunna ya zaro waya ya danna kiran Dad! Ba tare da b’ata lokaci na ya gaya mishi halin da ake ciki…

Suna gama wayar, ya ga tana k’ok’arin komawa A hankali yace “Mommy please kar ki koma ciki, kina jin fa yanda take yi miki magana ba respect.
Please dan Allah kar ki je.”

Za tayi magana yace “Please Mommy, i can’t take it”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin a hankali tace “To kaini gidansu Huda. I have to be there, suna ta expecting d’inmu.”

Da k’arfi yaji zuciyarshi ta buga ! Sai kuma yaji zafi kamar an soka mishi wuk’a…

Sai da ta sake maimaita maganar tata tukun yace “Tam”. Daga nan suka fara tafiya suka wuce inda motarsa take a chan wajen gidan, suka shiga suka wuce.

A chan parlourn kuwa zuwa wannan lokacin gaba d’aya hankalin matan parlourn ya koma kan su Mammy.
Su Mommy suna fita Ummi ta hau lallab’a Mammy tana bata baki, ba su kulata ba sam daga ita har Mom dan
tun a cell daman sun fita harkarta saboda ta zama wata salaha doluwa wawiya! Kamar ba ita ba.

Arshaad kuwa ji yake kamar ya chaka wa kanshi wuk’a! Babu abunda yafi d’aga mishi hankali kamar kalmar ‘sai ta tsine mishi’ da taketa faman ambata, hakan yasa kawai ya juya zai bar wajen suka yi karo da Dad! Fuskarshi sam babu alamun annuri dan hatta Arshaad d’in sai da ya d’an tsorata da yanayin shi.

Ganin yana shirin fara zuba musu tujara a gaban jama’a ne ya sanya Mom tace “Dad da mun d’an shiga daga ciki ko mu hau sama. Kalla kowa ya zubo ido mu yake kallo” Juyowa yayi yana kallonta wanda hakan yasanya ta sha jinin jikinta. Da kakkausar murya yace “Granpa ya san kina nan?”

A hankali jikin a mace ta girgiza kai,
Snapping fingers d’inshi yayi
kafin ya nuna mata hanyar main door straight! Ba k’aramin sanyi jikin Mom yayi ba! Kunya da takaici kuwa kamar su kashe ta, a hankali tace “Sai anjiman ku” daga nan ta fara k’ok’arin wucewa taji Ummi tace “Adama d’an jirani in je in d’auko wayata a side d’in Granpa In zo mu wuce. Ya sallameni tun jiya.”

Ba tare da Dad ya kalleta ba yace
“Ki jirani zan maidake anjima, ina son ganinku tare, ke da Abba.”

“Ok” kawai tace, Mom kuma ta wuce ta fita.

Sai a sannan Dad ya kalli Mammy yace
“Magana d’aya zuwa biyu nake son gaya miki. Na farko shawara ce, Na biyu kuma zan iya kiranshi as treat.
Ki kwantar da hankalinki ayi auren Hudan da Arshaad cikin lafiya da kwanciyar hankali ko kuma wallahi idan kika yi wani abun da ya b’ata auren nan tou ki tabbatar sai na sauk’e igiyoyin aure na da suka yi saura a kanki.” Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce.

A rikice Aaima da sisters d’in Mammy suka hau cewa “Kawai ta hak’ura dan Allah kar ta b’ata aurenta”

Bata bi ta kansu ba, cikin b’acin rai ta kalli Arshaad tace “Arshaad kaje ka cire waennan kayan na gaya maka babu inda zaka je! Wallahi idan ka fita a gidannan yau ni da kai ne.” Daga haka ta juya ta wuce sama.

Sai a sannan Hajiya Binta ta k’araso
tana jin abinda tayi tace “Suje kawai a sallami y’an wuni suma su zo su wuce gida tunda ba za a je kaulun ba!”
Nan take gaya musu ma sak’on Mahaifiyarsu da tace a fad’a musu.
Jiki a mace haka duk suka bar gurin aka je aka rarraba souvenirs d’in k’atuwar jaka an rubutu sunan Amarya da Ango a jiki a cikin jakar an zuzzuba turaruka da atamfofi guda biyu da vail da jaka da takalmi,
a each bag. Mom, bata tab’a tunanin Dad zai iya yi mata hakaba! Wai me ya shigi mazan estate d’in nasu ne da duk suka bi suka rainasu suka tsanesu haka? Daddy ne kawai yake musu mutunci yake tausayinsu amma hatta Auwal da Arshaad sun rena su
Aslam kanshi tana gani d’azu yadda yayi musu sannan ya wani ja hannun uwarshi suka fita. Ala dole shi mai zuciya! Inaa, gaskiya rayuwa fa ba zata yiu a haka ba, dole su gyarawa mazan MT zama dan yanzun taga wani tashen rashin mutunci suke yi especially Abba, ta kanshi zata fara wallahi!
Wannan shine damuwar da ya kamata su tsaya su magance ba wai shirmen Mammy na hana auren Arshaad ba! Abunda sai sun so ma tukun Hudan zata zauna a gidan Arshaad d’in! Bata san me yake damun Mammy data kasa fahimtar simple abu ba.

Ji tayi kawai an yi hugging d’inta
A d’an razane ta zare wadda tayi hugging d’in nata tana shirin cewa wani abun suka yi ido biyu da Jalila..
B’ata rai tayi tamau ta tamke fuskarta.

Jalila ta lura da hakan sarai amman ta manna mata hauka cike da shak’iyanci tace “Oyoyo Mom d’inmu ashe kin dawo ni banma sani ba. Dama wallahi zaman gidan su Gwaggo Asaben chan ya dameni, girkin kuku fa nake ci
baki ga har na rame ba? Yanzu kuwa tunda Allah ya dawo dake na san k’ibata zata dawo. Taho muje, ko kayana ba zan d’auka ba wallahi Auwal yaa zo ya d’auka anijima, k’afata k’afar ki, mu tafi. Ashe alkhairin ganin ki ne yasa naji ina kwad’ayin lek’owa nan dan tunda naji Gwaggwo Asabe tace ana biki anan na kasa sukuni.”

Lumshe ido kawai Mom tayi,
sai da ta tabbatar da zuciyar ta ta dedeta tukunna ta bud’e idanuwanta da sukai ja ta zubasu akan Jalila wadda tayi mata k’urr! da ido.

“Muje” Shine kawai abunda Mom d’in tace, ba tare data sake bi ta kanta ba tayi gaba Jalilan ta bita a baaya
daman neman wanda zata k’untatawa take yi ta san watak’il ta samu tashin hankalin da take ciki ya d’an ragu!
Duk da Umma ta bata assurance d’in ‘ba matsala an tabbatar mata da babu aure tsakanin Huda da Arshaad
dan haka kar ta damu da wani bikin da suke ta yi. Amman ta kasa nutsuwa kuma zuciyarta ta k’i ta daina tafarfasa.

Sannan zata fita daga estate d’in nan, da Auwal ya maida mata shi kamar kurkuku. Murmushi tayi aranta tace
“Zan jefi tsintsu biyu da dutse d’aya!”

Driver ne ya jasu su duk biyun a baya, kamar yadda tayi zato kuwa masu gadin da kyar suka bari aka fita da ita.

Sai da Mom ta nuna mata d’akin da zata zauna a sama, daga nan ta wuce nata d’akin.

Sai da Ummi ta tabbatar kowa ya watse tukun tabi bayan Mammy Sisters d’inta( Mammyn) kuwa ko sallama basu yi mata ba suka wuce suka rabu da ita.

A d’aki ta sameta sai faman safa da marwa take yi ta hana zuciyarta sukuni sam!.

Ta ganta sarai taga shigowarta
amman sai tayi banza da ita taci gaba da kai kawon da yake yi.

A hankali Ummi ta nemi waje ta zauna tukunna tace, Mammy. Da sauri Mammy tace “Zainab tashi ki fita!
In dai shawararki kika san zaki sake bani to tashi ki fita tun kafin raina ya b’aci!”.

Murmushi Ummin tayi sannan ta fara magana “Dama ai in dai kinga mutum yana farin ciki idan ana bashi shawara in yayi ba daidai ba to ki tabbata ba gaskiya ake fad’a mishi ba! Na zo in baki shawara ne Mammy kuma zan yi matuk’ar farin ciki idan naga kina jin haushin shawarar tawa dan na san gaskiya ce nake fad’a. Bari ki ji in fad’a miki abunda na San Baki sani ba,
idanuwanki ne suka kulle ba kya ganin komai ba kya ganin kowa sai k’iyayyar Huda da Aisha wadda kika gani akan k’afafuwanta!”

Da sauri Mammyn ta kalleta kafin tace
“Magana zaki fad’amin? Me kike nufi?
Use your words! Ta fad’i hakan tana me k’arasowa daff da ita.

Mik’ewa Ummin itama tayi sannan tace “Ba zan yi using words d’ina ba Mammy dan na san kin san me nake nufi! So yanzu ba lokacin tashin tashina bane ba, yanzun lokaci ne wanda ya kamata ace kin farka idanuwanki sun bud’e sannan kin kalli rayuwa da idon gaskiya da basira.

Bari in baki wani d’an misali , watak’il ki gane abunda kowa yake son fahimtar da ke wanda kika kasa nutsuwa ki fahimta. For instance ace,
ki samu kare ki kulle shi yayi kwanaki baki bashi abinci ba! Rana d’aya ki samu dogon lungu, a k’arshen lungun ki ajiiye nama da k’asusuwa da ruwan sha sannan ki kawo zarto k’uso shi da wuk’a ki ajjiye a daidai ta saman lungun a saman wannan naman
sannan ki d’ana mishi tarkon da in dai yabi ta kai ya taka to wannan wuk’a da zarton zasu sauk’o su chakeshi su kasheshi murus har lahira ba tare da ya ci wannan naman ba.” Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin tace “Ki gaya min in akwai mahaluk’in da ya isa ya hana wannan karen cin naman nan? Ko kuwa shin wannan karen zai iya hankalta da wannan tarkon da yake a gaban naman? Amsar anan itace
‘a’a’, sai dai In d’auke shi za ayi ta k’arfin tsiya a sama mishi sabon nama a bashi yaci. Sannan ne za a samu sauk’i.

Wannan karen ba kowa ba ce face, ke.
Naman nan kuwa, Hudan ce da Aisha waenda k’iyayyarsu haushi da takaicinsu ya sanya kika kasa ganin komai da kowa hatta tarkon dake gabansu wanda in dai kika taka to tabbas wuka zata fad’o kanki ta kashe ki har lahira ba tare da kin tab’a su ba!
Wadannan tarkon da wuka’ak’e ba komai bane Mammy face Dad da Arshaad da auren ki da mutuncinki da k’imarki, da kike k’ok’arin lalatawa
ki kashe rayuwarki jin dad’in ki kwanciyar hankalinki da farincikinki da aurenki, duk akan rashin hak’uri.

Second option kuma da na baki na ‘sai dai a d’auke karen a bashi sabon nama’. Shine wanda ni, y’an uwanki da Aaima muke ta k’ok’arin fahimtar da ke!. Idan kika yi hak’uri kika sawa kanki da zuciyarki salama, zaki samu peace of mind za ki samu farin ciki
amman fa sai kin yi tunani irin na mutane bawai irin na karnuka da basa ji basa gani idan suna jin yunwa ba.

Ki daure ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari. Kar kije maybe akwai babban rabo a tsakanin Hudan da Arshaad ki kashe kanki ba tare da kin hankalta ba…”

“Attakhbir!
Allahu akhbar!
Mai k’aramar kwakwalwa da zuciya.
Naji na gode reformed Zainab!
Na lura tunda kika ji azabar cell shikenan zuciyar ta mutu. To bari kiji in gaya miki. Wallahi! Kin ji dai na rantse gara rabon dake tsakaninsu ya kashe ni! Akan in zauna a gaban idona a d’aura musu aure inaji ina gani
dan na tabbatar bak’in ciki ne zai k’arasa ni muddin Arshaad ya auri wannan Yarinyar!.

Kinji dai kankat! Kenan, ko? Oya jeki na gode duk ranar da fargabar cell ta bar jikinki, kya iya zuwa mu yi magana.” Cewar Mammy.

Bak’in ciki ne ya hana Ummi sake ce mata komai, dan haka kawai ta juya ta fita cike da takaici da tsananin mamakin Mammy.

Da harara Mammyn ta rakata, sannan tayi tsaki ta koma kan gadonta ta zauna.

Ummi na fita suka had’u da Daddy da alama d’akin shi zai yi amman yana ganinta yace “ta zo suje ya kaita kawai ya gama tukun ya huta.”

Ba ta san taya zata fuskanci Abba ba, bata san taya zata fara bashi hak’uri ba! Hakan yasa tunda taje ta yiwa su Granpa sallama suka d’au hanya zuciyarta take ta faman tsitstsinkewa.

Ba kowa a parlourn dan su Shuraim tun safe suka tafi gandun albasa.
Basu dad’e da gama waya da Dad ba yace mishi yana gida don haka suna zama ya kirashi yace “ya sauk’o gashi ya kawo Ummi” Wallahi Abba har ga Allah har cikin zuciyarshi shi mantawa ma yake yi da wata Ummi.
Mike’wa yayi kawai ya je jikin drawer inda yake ajjiye important documents d’inshi ya d’auko takardar da ya dad’e ajjiye da ita, ya fice yayi k’asa.

Da kyar ya iya daurewa suka yi cikakkiyar gaisuwa shi da Dad.
Ummi na shirin gaidashi da fara sake bashi hak’uri har da d’am zamowarta daga kan kujera taji yace “Ke! Zo ki karb’a nan”

Ganin ya mik’a mata farar takarda ya sanya gabanta ya hau dukan uku uku!

Ba ita ba hatta Dad sai da ya shiga rud’ani.

Bata gama gigicewa ba sai da ya daka mata wata uwar tsawa!

A take jikinta ya d’au rawa. Gudun kar ta b’ata mishi rai ya sa ta mik’e da kyar ta k’arasa inda yake tasa hannu biyu ta karb’a.

Dad ne yace “Abba meye wannan ka bata?” Yana mai tsareshi da idanu.

Cikin nuna halin ko in kula yace
“Ta karanta za ta gani”

Da kyar Ummi ta iya bud’e takardar, jikinta na karkarwa tana adduar Allah yasa ba abunda take tunani bane.

Zuwa yanzu ran Dad ya soma b’aci da attitude d’in Abba dan haka cikin b’acin rai ya yunk’uro da niyyyar fara zazzzage mishi ta cikinshi dan yaga alamun da renin wayo ya sauk’o k’asan shi kuwa yadda Mammy ta gama chaza mishi kai wallahi ba Abba ba ko waye ya shigo gonar shi yau sai ya ci ubansa! Ya bud’e baki kenan, yaji k’arar fad’uwa! Da sauri ya maida hankalinshi a direction d’in Ummi, ya ganta zube a k’asa. Dan haka ya mik’e a mugun firgice ransa na k’arasa dagulewa.

Abba kuwa ko gezau bai yi ba yana nan zaune a yanda yake ko motsi ma ba shi da niyyar yi.

A gigice Dad ya mik’e cikin sassarfa ya k’arasa inda suke yana cewa
“Subahanallah, Abba suma tayi ko me?
Duba ta mana, tashi mana, ya kamar baka ga abunda ya faru ba ne?” Ya fad’i hakan yana mai durk’usawa a inda Ummin take.

Cikin nuna halin ko In kula ya mik’e tsaye ya karkad’e farar jallabiyar dake jikinshi, kafin yace “At least na sakata tayi mai dalili ai yanzu ba fake ba.”
Yana gama fad’in haka ya juya zai hau sama.

Da sauri Dad ya mik’e ya sa hannu ya juyo da shi, bai yi wata wata ba ya d’auke shi da wani mahaukacin mari
dan tun lokacin daya durk’usa akan Ummi idanuwanshi suka sauk’a kan takardar saki biyun da Abba yayi mata.

Da sauri Auwal wanda ya shigo yanzun ya k’araso inda suke yana cewa, “Subahanallah, mai ya faru?
Dad wace..?” Maganarsa ce ta katse sakamakon Idanunshi da suka kai kan fuskar Ummi, da sauri ya durk’usa ya hau tattab’ata yana tambayar mai ya same ta?.

Cikin b’acin rai Dad yace “Maida ita yanzunnan ko ka fuskanci fushina Yakubu!”

Da mamaki Abba yake kallonshi jin yana yin yanda Dad d’in yayi mishi magana da kuma yanda ya kira sunanshi haka! Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace, “I can’t Dad, I’m really sorry Wallahi baz..”

Wani marin ya kuma sakar mishi kafin yace “Kar ma ka rantse! Dan ko ka rantse sai kayi azumi saboda Ummi sai ta koma d’akinta a yau wallahi! Kaji dai na rantse.”

Bai ankara ba yaji hawaye yana zuba ta idanunshi. Cikin kuka yace “Dad ba na son ganin fuskar matar nan, tayi ruining komai nawa saboda selfish reason d’inta! Ba zan b’oye maka ba
wallahi Ina having second thoughts akan auren Hudan da Arshaad saboda
kwata kwata bana son yin nesa da y’ata because i just knew her, all because of ummi.

Ka san irin azabar da Hudan ta sha a hannun Usman kuwa? All because of Ummi.

Ka san yadda nake jin Maryam a cikin zuciyata? Amma ba yadda na iya dole haka inaji Ina gani ta auri wani ta rayu da shi for almost 20 years!! All because of ummi. Komai fa Yaya ita ce sila! Ita ce silar ciwon zuciyana! Ita ce silar bak’in cikina! Ita ce silar lalacewar soyayya ta! Haba haba dan Allah, sannan yanzu ka ce In maida ita?
Gaskiya kayi hak’uri Yaya, ban tab’a maka gardama ba amman kam yau zan yi maka! Wallahi ko sunanta ba na son ji kwata-kwata…” Ya k’arashe maganar cikin d’acin zuciya sannan yana gama fad’in hakan ya wuce sama ya barsu shi da Auwal wanda yake ta yayyafa wa Ummin ruwa yana son yaga ta farka.

Da kyar Dad ya iya juyowa ya kalli Auwal d’in, sannan yace “Kama ta mu kaita asibiti, Allah yasa ba wani babban abun bane ya sameta.”

Gandun Albasa
(2:30 pm)


A tsakar gidan Madu, aka yi decoration na traditional kaulu! Wajen yayi masifar yin kyau. Taken wak’e wak’en Shuwa Arab ne ke tashi in a very low tone. Su Sudais da wasu Yaran sai y’an tsofaffi tsilla tsilla ne a zazzaune a kan kujerun da aka k’awata tsakar gidan da su.

Gabad’aya y’an mata da manyan matan suna ciki, wasu suna had’a takeaway da souvenirs wasu kuma suna shiryawa dayake mostly family ne sai na jiki sosai suka zo dan Mama ba wani taro tayi ba. Ita dama ba wani sanin jama a ma tayi sosai ba, sai y’an unguwa da suke ta zirya tun safe wadanda rabinsu duk munafurci ne yake kawo su dan an san yau za a kawo lefe.

Umma bata da lafiya tana fama da hawan jini amman tun sassafe suka zo ita da Baaba Laraba da yayarta Hansai,
kuma wani abun mamaki tunda tazo d’in tak’i kula Mama dan wani mugun zafinta take ji, sun dai gaisa da Shuwa da Ummu ita kuma Mama sun gaisa da Hansai da Baabaa Laraba amman Umma kam tama k’i bari su had’u dan tana hango ta zata kauce hanya
ko ta fad’a d’aki ta shige band’aki. Da Mama ta fahimci hakan kawai sai ta tattarata ta watsar ta shiga sabgar gabanta dan ita mamaki ma Sadiyar take bata duk tabi da d’aurawa kanta wahala gabad’aya a takure ma kamar ta ganta ga kuma rashin lafiyar Bp da take ta fama.

Sai da Anty Zainab ta zo tukunna ta d’an samu ta ware. Itama Anty Zainab d’in da kyar ta iya daurewa suka gaisa da Maman wadda tayi wani irin fresh! Sannan idan ka kalleta ba zaka tab’a cewa sa’ar su bace ita da Sadiyar Sai dai kace Antys d’inta ne dan ba za ma ka ajjiyesu a matsayin yayunta ba!
Musammam ma Sadiya wadda ta zama kamar wata mahaukaciya kwana biyun nan! Tun lokacin da taji labarin maganar auren Huda har yau bata san inda nutsuwarta take ba.

Mama na gama gaisawa da Anty Zainab ta juya ta wuce abunta.
Anty Zainab kuma ta nufi wajen Umma! Nan kuwa suka hau hassada da zagin Mama har da suna cewa wai “bazawari take nema shiyasa ta ci wannan uwar kwalliyar”. Laffaya Maman ta nad’a itada Ummu, kalar laffayar ja sai blue d’in flowers, sun yi kyau sosai dan har d’an light makeup sai da Sakina ta tirsasa su suka tsaya aka yi musu.

Itama Sakina laffayar ce a jikinta, amma bata nad’a ta har ka ba, instead sai tayi d’aurin Zahra Buhari da mandil a kan nata shi kuma mayafin layyafar ta nad’a a kafad’ar ta.

Amarya kuwa ta sha traditional kaya abunta! Hatta hair style d’inta ma irin nasu aka yi mata, daga sama ta nad’a wata had’add’iyar blue black d’in laffaya, aka yafa mata mandil akai.
Tun daga kan sark’ok’in k’afarta har na wuya da y’an kunneta da wanda ta sa a kanta na sisin gold duk na asalin gold ne! Wanda Madu ya bata kyauta jiya da daddare, ya ce “tun na mahaifiyar mahaifinsa ne! Maryam yaso bawa Allah bai yi ba. Ashe rabon ta ne..”

D’akin isu isu ne ita da k’awaye ta, anata d’aukar hotuna amman kallo d’aya za kayi mata ka san hankalinta baya ma gidan gaba d’aya! Tun da gari ya waye take jin fad’uwar gaba, gashi yanzu kuma sai kiran Arshaad take yi baya d’auka.

Shuwa ce ta shigo ita da Baabaa Talatu sanye cikin wata rantsatsiyar milk laffaya sun yi anko su biyu suma abun su ita da Baabaa Talatun.

Basu dad’e ba wasu mata suka shigo su biyu, daga nan suka umarci Hudan da ‘ta mike a fita da ita’ Aranta ji take kamar ta tambayesu ‘Ya arshaad ne ya zo? Sai kuma taga rashin kunya da zak’ewarta. Kuma ta tuna jiya Sakina tace mata ‘Ta bar nuna mishi ta damu sosai fa, idan ba haka ba tabar ganin wai yana sonta Wallahi wahala zata sha….’. Lumshe idanuwanta tayi ta dedeta nusuwarta sannan ta bawa Sakina wayarta ta mik’e, ta jaa
mandil d’inta ta rufe kaf fuskarta, su kuma suka tik’eta sukayi waje.
Suma su Sakina suka take musu baya.

Hudan, so take ta yakice tunanin Arshaad a kanta amman ta kasa!
K’arshema bigewa tayi da adduar Allah yasa tana fita ta ganshi amman yanayin yanda taji an zaunar da ita a doguwar kujerar da aka k’awata domin ita da shi ne yasanya ta fahimci bai zo d’inba.

Ummu ce ta fito ta bud’e taro da addua sannan ta fara gabatar da al’ada a Huda, A matsayin uwa.

Mama suna parlourn Madu, tun lokacin da Mommy da Aslam suka zo suka buk’aci ganinta har yanzu bata samu damar fitowa ba.

Wata distant relative d’in Shuwa wadda zata d’an girmi Shuwan kad’an ce ta k’arasa wajen sannan cewa Ummu “Ina uwar Angon? Ta zo ta zauna a kusa da ke yadda kina gamawa zata karb’a. Sannan ba ayi welcomin Ango ba kuma ba aga shigowarsu ba besides ai dole sai yananan ma tukunna za ayi komai.
Na ga bai riga yazo ba amman kin yi wuff kin fara abu haka bayan kuma akwai abubuwa da yawa before wannan.”

Karaf! A kunnen Umma. Daman neman abun yi suke yi ita da Anty Zainab shiyasa suka zo suka zauna a k’asa gefen kujerar Amarya. Da sauri sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar kowa zai ji Umman tace
“Eh kam tabbas!” Sannan ta mik’e tsaye kafin ta ce “Uwar Ango! Tana Ina? Ana buk’atar Uwar Ango a nan yanzu yanzu”. Da k’arfi ta yadda kowa ya iya jiyota tunda daman wak’ar da aka kunna a low tune yake kuma iya murya ne kawai babu kid’a.

Da sauri Ummu ta ce “Umma me ye haka? Idan kin yi min magana ba zan je In kirata ba ne ba? Ko hakan da kika yi kina tunanin shi zai sa ta fito?”

Still da k’arfi Umma ta sake cewa “A’a, ai ji nayi kamar kince ba ta zo ba! Gashi shima Angon shiru. Duk da dai ni ba Shuwa bace ba amman Tabbas na asan cewa Ango da Amarya a tare ake shafa musu lalle, manshanu, da ragowan abubuwa! Dan har yau ina tuno naki, a tare aka shafa muku ke da Muhammadu wanda ya zo wurwuri
bai tsaya b’ata lokaci ba, ita kuwa yayarki daman ba a yi mata ba
shiyasa gaba d’aya auren nata duk biyun suka tab’arb’are! To kuwa kinga ai ba zan so auren Huda itama ya samu matsala ba ko? Dan haka gara mu jira Angon ya zo ko nan da k’arfe taran dare ne mu masu iya jiransu ne
har sai shi da uwarshi sun zo an yi alada yadda ya kamata!”. Ta k’arashe maganar har wani karkarwa jikinta yake yi, wanda kana gani ka san bala’ine kawai yake cinta.

Ummu bata ga k’arasowar Sakina ba sai tayi tana cewa, “Eh tabbas kam Hajiya Umma kya zauna ai kiyi ta jira tunda daman kallon kwaf da munafurci ne ya kawo ki! Mu nan dukkannin mu muna da aikin yi kuma ba mu da lokacin zaman jira har k’arfe taran dare. In dai Ango kike son gani to ki bada nan da awa biyu zaki ganshi sun iso tare shi da iyayenshi maza da za su kawo lefe wanda na tabbatar abunda ya tsaidasu kenan ba wai abunda makirar zuciyarki ta shirya miki ba!” Umma na shirin k’arasowa inda Sakinar take taga Ummu ta d’auke ta da mari! Cikin yaren Shuwa Ummu ta hau yiwa Sakinar fad’a k’asa k’asa yadda ta tabbar ba kowa ne zai ji su, tace “Ba ki da hankali ashe? A cikin dangi da y’an uwa za ki bud’e baki kina yiwa babbar mata rashin kunya haka? So kike a tafi dake a baki?
Wuce! Wuce ki tafi chaan sama d’akin Shuwa ki rufe! Idan ba ni na neme ki ba wallahi kika fito sai ranki yayi mugun b’aci!”.

Juyawa kawai Sakina tayi ta wuce tana ji kamar ta had’iye zuciyarta! A kan Umma aka mareta a gaban mutane haka!? Kuma ta tabbatar tunda Umma ta fara wannan maganganun to fa idan taka mata burki aka yi ba ko kuma Arshaad d’in ta gani ba tabbas ba zata
tab’a barin mutane su sha ruwa ba.
Ita daman tun d’azu da ta ganta tazo da sassafe ta san ba alkhairi ne ya kawota ba. Ita da take da abun fad’a a gindi amma shine har take da audacity d’in yin magana! Wallahi yau da Ummu ta barta da sai ta yiwa Umma zazzagar kwanyo. Da wannan tunanin ta k’arasa d’akin Shuwa, sai a lokacin hawayen bak’in ciki suka samu nasarar zubo mata. Daga Shuwa sai Baabaa Talatu ne a d’akin suna
shirya tukuicin da za a bayar in an kawo lefe. Baaba Talatu tana ganin ta shigo tana kuka ta mik’e tana
“Subahanallah, mai ya faru? Ke da waye?” Da sauri ta k’arasa ta hau shafa fuskarta inda hannun Ummu ya fito tarr!! Ya kwanta akan farar fuskarta
Cikin fad’a Baaba Talatun tace
“Wanne d’an iskan ne ya mare ki??”
Fashewa tayi da kuka cikin kukan tace
“Umma ce take ta abubuwa a waje, shine Ummu ta mareni wai dan….”
Ai bata tsaya jin k’arshen ba, tayi waje.
Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina . Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.”

<< So Da Buri 51So Da Buri 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×