Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar, tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina. Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.”
“To” Kawai Sakina tace, tana mai sake goge fuskarta sannan ta koma gefe ta fara warware laffayar jikinta da d’aurin d’ankwalin dake kanta.Sai da ya rage daga ita sai long camisole d’inta wadda ta saka a ciki mai dogon hannu yayinda dogon gashinta ya kwanta a gadon bayanta sannan ta fara k’ok’arin kiran Arshaad.
Tayi. . .