Skip to content
Part 54 of 72 in the Series So Da Buri by Bulama

Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?”

Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina ta ce “Kina da number Abba? Baban Huda.”

A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai, kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta, tana cewa “Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan”.

Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take daidai Sakina ta fara dialing number Abban, Mama ta sa hannu ta karb’a wayar ta kara a kunnenta.

Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna ya d’auka! A hankali ta ji ya ce, “Princess, how was your day?”

Sai da Mama ta lumshe idanunta na sakanni wasu zafafan hawaye suna zubo mata tukunna ta ce “Horrible, Abba! Her day was horrible!”.

Da sauri ya gyara zaman shi kafin ya ce, “Maryam”. Cikin son sake tabbatarwa.

Cikin kuka ta ce “lalata mini rayuwa da farin cikin da kayi bai isheka ba sai da ka had’a da Huda ko? A haka sai faman ik’irari da pretending d’in kana k’aunarta kake yi! Abba in dai har kana son ta mai yasa ka jefa ta a irin wannan relationship d’in? Da ka san mahaukaciyar matar yayanka ba zata so auren Arshaad da Hudan ba mai yasa tun farko kuka had’a? Saboda ku maidamu abun kwatance ko me??
An tara mutane k’iiri k’iri Ango yak’i zuwa! A Ina aka tab’a yin haka?

To bara kaji in gaya maka. Tunda har Mahaifiyar Arshaad da kanta ta furta cewar bata son y’ata a matsayin suruka, to wallahi ko ta dawo ta ce tana so, Ina so ka san cewa ‘maganar aure babu ita!!’ Sak’o ne wannan na baka, ka gaya mata ka gayawa Arshaad da wakilin shi! Dan ba zan tab’a yarda in kai Huda gidan da ba’a k’aunarta ba wallahi. Saboda na san zafin k’iyayyar surukai”. Ta fad’i haka tana fashewa da wani matsanancin kuka.

Da sauri Abba wanda yake jin zuciyarshi tana wani mahaukacin racing yace, “Maryam listen to me dan Allah ki bar wannan kukan”

Cikin tsananin b’acin rai tace “Abba kuka yanzu na fara! Na san zan yi kuka especially idan Allah ya kaimu gobe aka yi calling off auren y’ata na ganta a cikin tashin hankali dole zan yi kuka…” Kasa cigaba ta yi da maganar dan haka ta yi jifa da wayar akan gadon ta durk’ushe a k’asa tana kuka.
Sakina na shirin yin magana Ummu da Mommy suka shigo. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e tana ji itama kamar ta fashe da kukan, a hankali ta d’an matso Maman sannan tace “Wannan dalilin fa shiyasa nak’i gaya miki tun farko, kin yi min alk’awarin ba zaki d’aga hankalinki ba yanzu menene haka? Ki kwantar da hankalinki ni na san Mammy bata isa ta hana komai ba!
Dad ba zai barta ba.”

Cikin katseta Mama tace “Wallahi ko Dad ya barta ko bai barta ba babu maganar aure tsakanin Huda da Arshaad. Idan ita ta hak’ura to gobe ni zan hana! Ta yaya kuke tunanin zan bar y’ata ta rayu da surukar da bata sonta? Mommy na san mecece k’iyayyar surukai! Kullum addua ta Allah ya had’a Huda da surukan da zasu k’aunaceta. Ta ya za ki yi tunanin yanzu zan amince ta auri Arshaad??”

Cikin katseta Mommy tace “Kar kiyi haka dan Allah, kawai mu zuba ido amman kar ki ce za ki shiga tsakanin kaddara! Idan kika yi hakan ai kun zama d’aya ke da Mammy kenan.”

Cikin katseta tace “In zuba ido y’ata ta tafi inda ba a k’aunarta kome kike nufi? In zuba ido rayuwar Huda ta lalace kamar yadda tawa ta lalace?”

Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Haba Maryam, rayuwarki bata lalace ba, da ni da ke fa kusan mataki d’aya muka taka a rayuwar aure. Tabbas mun jigatu kuma mun sha wahala amman a ko da yaushe idan na kalli Aslam wallahi ji nake gabad’aya wahalar it’s worth it! Dan Allah yayi mana kyauta. Kuma dama a rayuwa dole akwai jarabta da kuma gwajin imani. Ni dai shawarar da zan Ba ki ita ce. Dan Allah kar kiyi interfering ki zuba ido ki barwa mazan komai, su sun san me za suyi.”

Cikin sharar kwallah Ummu tace “haka ne tabbas! Mama dan Allah ki gwada yin hak’urin da kika saba wata rana sai labari.”

Da sauri Baaba Talatu wadda bama su san ta biyo su ba ta k’araso ta ce, “Ta ya za ku ce mata haka? In dai uwar Yaro ta ce bata yi to muma ba zamu kai jikarmu mai tsada inda ba’a k’aunarta ba wallahi! Allah na tuba maza da yawa a gari. Ga mai sunan kakan ta nan, d’an wajen Jamilu, idan Arshaad d’in zai kawo matsala ana iya d’aura musu aure gobe in sha Allah.

Na san ba zai tab’a cewa a’a ba, saboda daman ni na d’an so in fahimci take taken shi tun ba yau ba.”

Gyaran murya Shuwa wadda ta shigo yanzu tayi, dan haka duk suka juya suna kallonta. A hankali ta k’araso cikin tafiyar ta wadda ke nuna tsufan da ya rufar mata. Sai da tazo gaban Maryam tukunna ta kama hannuwanta duka biyu ta fara magana.

“Dan Allah dan annabi kar ki yi komai kar ki yi kuka kar ki d’agawa y’ar ki hankali. Ki bar komai a hannun Ubangiji, tun kafin ki haifi Huda already an riga an gama rubuta k’addararta da komai nata. Kar ki yi interfering wai dan kina tunanin zaki iya kub’utar da ita! Ki zuba ido ki yi mata addua komai zai tafi bisa yadda Ubangiji ya riga ya tsara. Ba mu isa mu saka ko mu hana komai ba. Kin ji y’ar albarka?” Ta k’arashe maganar tana mai sa hannu ta share mata hawayenta duka biyu.

Kuka Mama ta sake fashewa da shi ta fad’a jikin Shuwa suka rungume juna. Ita kanta Shuwan k’arfin hali ne kawai da dauriya suka hanata kukan. Ta rasa gane wachche iriyar k’addara ce A rayuwar Maryam da Huda, Astaghfirullah.

Shigowar ta tare da matan da suka ruk’o ta ne ya sanya d’akin yin shiru. Har yanzu fuskarta a rufe take amman kana gani ka san kuka take yi. Sakina na ganinta taji kuka na shirin kufce mata dan haka da sauri ta fita a d’akin. Suna zaunar da ita a bakin gado Mama ma ta saki Shuwa ta fice.

Shuwan ce tayi k’arfin halin cewa “Mommy da Ummu da kuma mata biyun da suka shigo da ita “Su je akwai motoci a fara kwasar kayan Amarya ana kaiwa gidanta, dan ba zata yarda da ajjiye wannan dukiyar a gidanta ba, tunda kowa ya gani kawai su kai mata abunta gidanta.”

Murmushi Mommy tayi kafin tace “Ni kam gida zan wuce. Ina a matsayin uwar Ango ina ni ina ziryar gidansu. Ai nayi jere sai kuma in ta haihu nan da wata tara in sha Allah ni da in koma.” Da sauri cikin raha ragowar matan suka ce, “In shaa Allah”

Ba a wani dad’e ba suka fito dukkansu a tare Mommy ta d’anso ta sake ganin Mama amman kuma kawai sai ta rabu da ita, a cewarta ‘in ta d’an sauk’o zuwa anjima zata kira ta a waya’. A tare suka fito da Ummu, su suka fara yin gaba da akwatuna ita kuma ta shiga mota ta nufi MT estate dan already drivern ya zo tun d’azu.

NASARAWA GRA.

Daddy da Dad na zaune sai zazzagawa Abba fad’a suke yi akan ‘ya mayar da Ummi tun kafin zance ya isa kunnen Granpa’ shi kuma ya tubure ya k’i!. Suna a haka wayar Mama ta shigo. Tsaf! Duk sun ji abubuwan da ta fad’a, dan wayar a high volume take kuma suna kurkusa da juna.

Yana gama wayar Dad ya ce “Abba ka mayar da Ummi yanzun nan in dai na isa da kai.”

Haka shima Daddy same thing ya fad’a mishi.

Ba yadda ya iya haka ya maida ita yana ji kamar yayi ta kurma uban ihu!. Daga nan Dad ya mik’e! Kamar Daddy ya san meye a ranshi yayi saurin mik’ewa shima ya tsaya a gabanshi sannan ya ce “Dan Allah kar ka yi haka. Ka tsaya zan yiwa Adama magana, na san kafin zuwa gobe in sha Allah zata nutsu.”

Cikin fad’a fad’a Dad yace “Ba za ta nutsu ba! Sam ba za ta nutsu ba. Da a ce zata nutsu da tun tuni ta nutsu, ku bar ni kawai!!” Ya fad’i haka yana k’ok’arin zagaye Daddy ya wuce.

Da sauri Daddy ya kuma tare shi sannan yace “Ya abunda muka gama gyarawa yanzu! Da girman ka kake k’ok’arin aikatawa?”

Cikin tsananin b’acin rai Dad yace “This is a different case..”

Cikin katseshi Daddy ya ce “Ba wani different case anan duk abu d’aya ne! Idan kayi mata haka ma ai ka ji haushi kenan, wato ta ci riba ma kenan tunda har kaji haushi ka hukuntata, ai idan mata suna haukarsu ba a biye musu. Tabbas na san dole ana buk’atar albarkar ta amman ka b’ullo mata ta bayan fage.
Wani abun fa dole sai ka sauk’o, ka san yadda za ayi a d’aura auren shine ka ci riba! Amman yanzu idan ka biyeta ka saketa aka zo ta sake birkicewa. Wa gari ya waya? Abunda ya kamata kayi shine ka san ta inda zaka b’ullo mata ka bawa iska ajiyar ta ka nuna kamar bama ka san me take yi ba! Ka d’aure ta da jijiyoyin jikinta. Tana ji tana gani a d’aura auren gobe kamar bata existing a duniyar! This is the best punishment da tayi deserving, amma yanzu idan kayi haka( ka saketa) ai jagula komai za kayi, kuma itace zata yi nasara at the end of the day tunda Uwa ce.

Ka ga dai ga Granpa a gefe wanda a yanzu haka jira kawai yake yi a tab’a shi! Kai da kanka ka ce yayi mana warning a kansu duk mu ukun. I assure you wallahi idan kayi wani abun ba zai duba laifin taba zai bi takanka.”

Sannu a hankali Daddy ya samu ya shawo kan Dad da kyar! Ya hak’ura. Shi dai Abba yana nan zaune bai ce musu uffan ba! Dan ba fahimtarsu yake yi ba har yanzu ba abunda yake yi mishi yawo a kunne sai kukan Maryam da tashin hankalin da ya jita a ciki. Tabbbas sai ya gasawa Ummi aya a hannunta! Hakan ba halinshi bane ba kuma bai kamata ya yi mata haka ba a matsayin ta na mahaifiyar su Sudais amman ba yadda ya iya…Dole ta san waye Abba! Ba ita kad’ai ba har su Mammmy, kasancewar su yayu a garebshi ba zai hanashi ya ja musu fasali ba.

A hankali ya mik’e ya yiwa su yaya rakiya, daga nan shima ya fita ya bar gidan.

Dad da Daddy direct asibitin da aka kwantar da Ummi suka je, an samu ta farfad’o sai dai har yanzu jikin nata ba kwari.

Likitan ne ya ke gaya musu “jininta ne ya hau sannan tana da buk’atar rest mai kyau. Za su iya tafiya da ita gida idan suna ganin gidan will be more comfortable for her dan ba abunda za suyi mata anan (asibitin) sai y’an drip da y’an allurai da maganin bp d’inta. Hutun ta da kwanciyar hankalinta shine abun buk’ata a yanzu.”

Dad ne yayi signing discharge papers d’in daga nan suka nufi gida da ita.

Tunda aka kamo hanya Ummi take ji inama mutum zai iya kashe kanshi babu zunubi, wallahi da ba abunda zai hanata commiting suicide a yau d’innan. A time d’in da ta farfad’o taso a ce mutuwa tayi. Tun da ta taso tayi wayo ta san kanta. Soyayyar mutane biyu zuwa uku ta sani Abba Gramma sai Granpa! Yanzu kuwa da ta kawo yanzu ta san menene so ta san tabbas muddin babu Abba a rayuwarta to mutuwa ce tayi saura! Shiyasa kawai ta koma kamar mutun mutumi. Ba abunda ya cika zuciyarta sai d’umbin dana sani Ita inda Abba zai yarda wallahi ya auro Maryam uku! Ya kawo ya had’a da ita su zama su hud’u, ta san za tayi kishi tabbas amma kuma zata hak’ura ta daure ta danne zuciyarta su zauna lafiya.

Tana cikin wannan tunanin taji su Dad suna danna horn! D’ago kanta tayi ga mamakinta sai ta gansu a mansion d’in su Abba instead of estate, addua ta fara yi a k’asan ranta ‘Allah yasa su Dad su saka Abba ya mayar da ita’.

Ba wanda yace mata komai. Sai da suka shiga cikin parlourn suka zauna tukunna Dad yace mata “Ummi sai kin yi hak’uri da Abba a yanzu. Kar ki damu In sha Allah zai sauk’o. Kin ji. Ki tashi kije d’akinki ki huta. Ya gyara abunda ya b’ata d’azu. Ki kwantar da hankalinki. Na ki biyayyane, kin ji?”

A hankali take jan numfashi tana share hawayenta tana jin wani farin ciki yana ratsa ta.

“Tam Dad mun gode” Ta ce. Sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa dai dai nan su Sudais da Shuraim da Aslam suka shigo! Suna ganinta suka yi kanta da gudu suna Ihun murna. Shuraim harda y’ar kwallar shi. Itama sai da tayi kwallar murnar ganin gudan jininta. Daga nan suka gaisa da Aslam ta wuce tayi sama ita da su Sudais. Tun a hanya Sudais ya fara zuba surutu yana bata labarin event d’in, da kalar hotunan da suka yi da kuma yadda Ya Aslam ya zauna a kusa da Huda.

Gaisawa kawai Aslam yayi da su Dad daga nan suka fice gaba d’ayansu. Basu yi mishi zancen event ba shima daman hakan yake so. Iya kar abunda suka sani shine Arshaad bai yi attending ba!.

Shi da Dad suka yi gida Daddy kuma yayi side d’inshi. Sai dare Jalila ta farfad’o! Ba kowa a d’akin sai ita kad’ai. Jiri da ciwo a mararta take ji ba na wasa ba! Tana so ma ta mik’e ta d’an zauna amman ta kasa. A hankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata abunda ya faru da ita d’azu. Da sauri ta zabura ta dafa cikinta, dai dai nan nurse ta shigo. Cikin kulawa ta hau gwada ta tana mai tambayarta “ina da Ina ne suke yi mata ciwo?”

A hankali Jalilan tace mata “Mai ya same ni? Marata tana yi min ciwo.”

Cikin kulawa nurse d’in tace “I’m sorry ma’am, kin yi loosing baby d’inki ne”

“L lo Loosing, me?” Cewar Jalila.

Ganin kamar bata fahimce ta ba ya sanya tace mata “Kin yi miscarriage!
Cikin jikinki ya fita.”

Da mugun k’arfi ta mik’e ta zauna sai kuma ta fashe da kuka! Daidai nan Mom ta shigo. Tana ganin tana kuka tayi sauri ta k’arasa ta fara bata hak’uri sai kuma ta juya ta rufe nurse d’in da fad’a, tana cewa “Ba ance jinin ta ya hau sosai kar a d’aga mata hankali ba? Shine amma lokaci guda zaki zo ki fara zuba mata wannan mugun labarin? Asibitin gwamnati ya kamata ki koma ba private ba! Tunda baki iya tausar patient ba. Ai inda kin bari da mu da kan mu za mu gaya mata idan mun koma gida….” Hakanan dai Mom ta wanke nurse d’in tass!! Ta inda take shiga bata nan take fita ba daga nan tayi signing discharge papers taja Jalila suka nufi mota driver ya jasu.

Ita dai Jalila in banda kuka ba abunda take yi, har ga Allah bata son cikin nan ba taso ta haihu amma kuma yanzu da cikin ya fita ta san tabbas ba abunda zai shiga tsakaninta da komawa gandun albasa!! Sannan ta daina samun kud’i daga Mom da Auwal kenan har abada! Amman kuma yadda Mom take lallab’ata sai ta d’an ji zuciyarta ta d’an yi sauk’i! Maybe tausayinta take ji amma duk da haka ta san ba zai wuce na sati ba zata tarkatata! Dan haka a take ta yanke shawarar nemawa kanta mafita. Zata lallab’a Mom ta bata hak’urin abubuwan da ta dinga yi mata. Idan ta kama ma sai tayi k’aryar aljanune da ita tace mata su ne suke sakata yiwa mutane rashin kunya. Ta samu dai Mom d’in ta ara mata ko da sati uku ne daga nan ita kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa! Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba.

Tana ta sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida! Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta. Cook zata kawo mata abinci yanzu.” A hankali ta ce “Na gode Mom”

Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daga nan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace “Yarinya kenan! Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani. Ki jira nan da kwana uku. In sha Allah za ki san wacece Adama.”

GANDUN ALBASA
Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba!Ita dai ta san bata da nutsuwa sannan a mugun tsorace take amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba.

Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita.

Hankalinta bai sake tashi ba sai da k’awayenta suka zo sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata!

Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kira shi, wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya dan haka hankalinta ya sake tashi! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa! Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya akan yayi mata hakan.

Nasarawa GRA.

A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi amman ga mamakin shi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare! K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i.

Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba! Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yana ta watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi. Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai ka ce wani wanda aka ce mata zai b’ace! Daga shi har ita ba wanda ya samu bacci jiya. Idan ka gansu duk a gigice. Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzun nan.

Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu. Amman duk wani motsin shi idanunta na akanshi. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yadda ta kasa tashi ko sallah tayi. Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi
wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!

Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin.
Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace ya ce “Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?”

A hankali ya ce “Ina kwana Dad”. “Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace
“Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka”

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe. Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki! Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin. Suna had’a ido ya sakar mishi murmushi a hankali ya ce “Ango”

Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi yana mamakin ta yadda zai shirya a gaban wadannnan body guards d’in! Inner wears d’inshi ya kwasa ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet.

Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito!

Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi! Kana ganinshi kaga Ango. A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya. Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo. Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking. Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake. Da mamaki yake kallon Abba da Daddy da Auwal a bayansu. Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai Sai hulunansu zannah bukar
d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya. Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada.

Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba. Daddy ne yayi dariya yace

“Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?” Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi. Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya, ba k’aramin kyau yayi ba, har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi! Kawai dai shi d’in baya nunawa ne Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata “Ina ma inama! How i wish.” Ya fad’i hakan a ranshi sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad. Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba! Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba. Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi!

Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e dan har an fara jera musu kira. Aboka nan su sun fara zuwa venue d’in. Ba tare da Mammy ta motsa ba ta ce, “Arshaad!” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo ya ce “Na’am Mammy”

Mik’ewa tayi tsaye tace “Koma ka zauna”

Sannan ta dubi su Dad wadanda suke kallonta gaba d’ayansu ta ce “Kuna iya wucewa ku tafi! D’a dai ni na haifa ko?

To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi! Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba har kai Abba! Kalla Auwal shima, Aslam ne kawai ya gaida ni ya kulani a kaff d’inku saboda ka riga ka nuna musu ba ni da mutunci ba ni da daraja a idanunka! To Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!”

Murmushin takaici Dad yayi kafin yace

“Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya! Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba, ko kin gaida ni tunda na shigo?” Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace “Kaga Arshaad wuce mu tafi! Zan ga wanda zai hanaka fita yau”

Mammy ya kalla, suna had’a ido tace. “In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba! Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan to ban yafe maka ba!”

Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi.

A zafafe Dad ya yunk’ura zai yi magan da sauri Daddy ya katse shi ta hanyar cewa “Dan Allah dan Annabi ka kyaleta, Uwa ba abar wasa bace ba! Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta Dole.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace “Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata taso ba.
Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki, sannan da ita kanta Hudan, babu fa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace kamar a zo aurenta a fasa!”

Cikin katse shi Mammy ta ce, “Yi mini shiru Yusuf!” Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yadda ta kirashi . Bata damu ba ta ci gaba “Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu! Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!” Cikin tsiwa da masifa ta ce “Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita! Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.”

A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi. Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi.

Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan ya ce “Rukayya bani da ishashshen lokaci! Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.”

Cikin katse shi ido cikin ido ta kalle shi kafin ta ce “Yahaya! Ko da a ce ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba. Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa
sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo. Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa “ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya. Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu. Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito. “Wuce mu tafi masallacin”. Haka kawai Dad yace mishi daga nan kowa ya shiga motarshi sukai gaba.

Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace! Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity.

Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in.

Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in. A hankali yake driving, babu nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin.

Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin! Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce? Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo.

Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu cikin tsananin farin ciki da nishad’i. Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa Kwata-kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in! Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace “Aslam dan Allah idan sun zo ka ce.” “Ku wuce muje mana! Ya naga kun tsaya anan?” Muryar Dad ta katse su.

Kallon Auwal d’in ya yi ya kalli Dad sannan yace “Ok”. Kawai, ya juya ya yi gaba. Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarin shine! Tabbas bada ban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan! Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma furr! Ta ki yarda, ta nace ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan! He might look calm but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba! Wannan wacce iriyar k’addara ce? Mai yasa yake jin hakan har yanzu? Mai yasa yake jin haka? Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi? A hankali yaji Abba ya ce “Aslam”. Firgigit! Haka ya yi hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe, da sauri ya ja burki! Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai.

A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe..

Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana. “Watak’il yau in yi maka laifi!
Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido”

Da mamaki yake kallonshi zuciyarshi tana dukan uku uku! Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi daga jin furucin Abba na yanzun!Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin. Dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi.

Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga”. Yana gama fad’in haka ya wuce ciki. Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal.

Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata! Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi amman kuma ba a d’auka! A fili sannan da k’arfi ya ce “damn it!!”
Sannan yayi jifa da wayar tashi wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi. Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara. A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace “Sorry”. Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!. Ba musu ya mik’a mishi shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure.

Auwal k’ok’ari yake yi su had’a ido da Aslam sai dai kuma Aslam d’in yak’i d’ago da kanshi kuma kamar ma idanuwanshi a rufe suke.

A bangaren Aslam kuwa zai iya cewa ya jima bai shiga irin wannan tashin hankalin a rayuwarshi ba! Mai yasa ya yarda yazo nan? Wanne irin heartbreak zai yi facin? Yanzu kenan a gaban idanunsa yana ji yana gani za ayi komai. “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun….” Ya furta a hankali sosai! Baya ganin komai zuwa yanzu
shiyasa ya runtse idanuwanshi kawai yana jiran lokacin da zai farka ya ganshi a gadon asibiti ko kuma yaji ance mishi Man rabbuka?!

Yana jin su sama-sama Daddy ya gabatar da kanshi a matsayin waliyyin Amarya Dad kuma a matsayin waliyyin Ango!

Da k’arfi zuciyarshi ta buga jin limamin yace “Waliyyin Ango yana nemawa Yakubu Aslam auren
Maryam Huda!” Bud’e idanuwansa yayi tarr!!! Ya fara ganin komai.

Kaii inaa bai ji da kyau ba! Ko kuma dai sunan waliyyin Amarya aka ambata dai ko wani abun daban.

Da sauri ya d’ago jajayen idanuwanshi yana kallon Daddy jin ya ce “Mun bayar”.

Limamin kuma yana cewa “sun yarda cinta shanta suturarta komai ya koma hannunsu? Hannun Yakubu Aslam.”

Bai gama fita daga shock ba Ya ji Dad yace “Mun yarda! Mun karb’a!”

Zuwa yanzu gaba d’aya jikin Aslam in banda karkarwa ba abunda yake yi gashi ya had’a wata uwar zufa! Tashi d’aya.

Tun daga nan kanshi ya kulle jinsa ya d’auke! Binsu kawai yake yi da ido suna gudanar da d’aurin auren!.
Yana kallo Dad ya zaro kud’i ya mik’awa Daddy! Limami ya sanar shedu suka shaida.

Jin shi bai tashi dawowa ba sai da muryar limami ta fara tashin amo a cikin masallacin “Alhamdulillah!!!
An d’aura auren Yakubu Yahaya Umar Faruku MT Aslam Da Amaryarsa Maryam Yakubu Huda akan sadaki naira dubu d’ari biyu! Lakadan ba ajalan ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 53So Da Buri 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×