Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?”
Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina ta ce “Kina da number Abba? Baban Huda.”
A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai, kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta, tana cewa “Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan”.
Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take daidai Sakina ta fara dialing. . .