A hankali yake bud’e idanuwansa. Hasken da ya gani tarr!! A kansa ne ya sanyashi maida idanun nasa ya rufe su dan lokaci guda yaji kanshi yayi wani mugun sarawa.
Da sauri Mommy ta matso ta kama hannunshi tana murmushi tana goge hawaye ta ce “Dad, kaga ya farka,yanzun nan naga ya bud’e idanunsa.”
Da sauri Dad ya matso ya d’an shafa fuskarshi sannan ya juya da sauri yana cewa “bara in kira Likitan Alhamdulillah.”
A hankali yad’an damk’i hannun Mommy da yake a cikin nashi, da sauri itama ta d’aura d’ayan. . .