Skip to content
Part 55 of 72 in the Series So Da Buri by Bulama

A hankali yake bud’e idanuwansa. Hasken da ya gani tarr!! A kansa ne ya sanyashi maida idanun nasa ya rufe su dan lokaci guda yaji kanshi yayi wani mugun sarawa.

Da sauri Mommy ta matso ta kama hannunshi tana murmushi tana goge hawaye ta ce “Dad, kaga ya farka,
yanzun nan naga ya bud’e idanunsa.”

Da sauri Dad ya matso ya d’an shafa fuskarshi sannan ya juya da sauri yana cewa “bara in kira Likitan Alhamdulillah.”

A hankali yad’an damk’i hannun Mommy da yake a cikin nashi, da sauri itama ta d’aura d’ayan hannunta a kai tace “Aslam, sannu mai kake so? Ya jikin?.” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya ce, “hasken yayi min yawa”

Da sauri ta mik’e ta rage hasken d’akin sosai sannan ta ce “Na rage”.

A hankali yake bud’e idanuwanshi da suka yi mishi nauyi sosai.

Fuskar Mommy ya gani tana kallon shi tana murmushi.

Murmushin shima ya sakar mata sannan ya fara k’ok’arin tashi.

Da sauri tasa hannu ta taimaka mishi, sannan ta saka mishi pillow a bayan shi ya d’an jingina. Yana gama gyara zaman shi tayi huggin nashi sannan ta ce “Congratulations Son”.

Shiruuu, yayi chan kuma yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin ya ce “Mommy dama ba mafarki na yi ba?”

Murmushi tayi ta kama kumatun shi ta d’an ja sannan ta ce, “Ba mafarki bane!
Angon Huda.”

Daidai nan Dad ya dawo da Likita yana binshi a baya.

Y’an gwaje gwaje Likitan yayi sannan ya tambaye shi “ina ke yi mishi ciwo? Ya yake ji a jikinshi?”

A hankali ya ce “Nothing much. Kawai kaina ne yake d’an sarawa kad’an kad’an”.

Y’an rubuce rubuce Likitan yayi daga nan ya basu discharge ya ce “su yi signing daga nan suna iya wucewa bayan an siya mishi wadannan drugs d’in. Ba wani abun bane yake damun shi. Like he said before Kawai shock ya shiga, shiyasa ya suma! But he’s okay now. Allah ya kare gaba” Daga haka ya juya ya fita.

A hankali Dad ya nemi guri ya zauna a kan kujerar daf da gadon sannan yace, “Aslam I’m sorry! So sorry. Ban yi tunanin abun zai b’ata maka rai har ya kaika ga haka ba! Shiyasa kawai da Abba ya zo mana da wannan shawarar muka amince daga mu har iyayen Mahaifiyarta. Aure an riga an d’aura! Ina rok’on k’a da kayi hak’uri ka danne zuciyarka kar kayi wani abun da zai musguna mata kaga itama Yarinyar ba so take yi ba! Wannan zab’in mu ne.

Ku zauna lafiya, in sha Allah wata rana za ku so junanku. Kar kayi anything da zai saka mu a kunya ko dan y’an tsofaffin nan Mahaifin Mahaifiyarta wallahi har ga Allah nayi tunanin idan aka gaya musu sauyin da aka samu da matsalar data taso ta wajen Arshaad ba za su yi farin ciki da kai ba amman sam ko a fuskarsu bamu ga komai ba a take suka goya mana baya d’ari bisa d’ari.

Sannan, na san Abba kamar uba yake a wajen ka kaima amman dan Allah Aslam ka daure kaga dai yadda ya daure duk da k’iri k’iri ya kusan jin kunya saboda d’a na amman bai damu ba haka ya sake yunk’urin ya k’ulla aure tsakanin y’arsa da kai! Kar ka bani kunya Aslam dan Allah”. Dad ya k’arashe maganar yana mai had’e hannuwanshi biyu yana kallon Aslam d’in alamun, roko.

Da sauri Aslam d’in ya matso ya kama hannun Dad d’in ya sauk’ar k’asa:

Shiru, d’akin yayi kowa ya kasa cewa komai. A hankali Dad ya mik’e ya ce, “Mu je. Idan mun fita sai Ado ya tsaya a karb’a maganin a pharmacy”. Yana gama fad’in haka ya juya ya fice.

Gabad’aya hankalin Aslam baya cikin d’akin har sai da Mommy ta d’an tab’a fuskar shi tukunna ya juyo yana kallon ta. Tana shirin yin magana ya riga ta ta hanyar cewa, “Ina Arshaad?”

Ita kanta Mommy sai da gabanta ya fad’i! Sam murna da farin cikin da take ciki sun hanata tuna Arshaad d’in ita kam tun d’azu da suka zo asibitin. In ba yanzu da Aslam yayi mata maganar sa ba!A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace, “He’ll be okay. Ka ji? Kar ka damu.”

A hankali ya lumshe idanuwansa yana shirin yin magana kiran Dad wanda ya shigo wayar Mommy ya katse su.

Tana d’auka yace “Akwai damuwa ne? Naga baku fitoba har yanzu”

Da sauri Mommy ta mik’e tsaye sannan tace “Babu, muna tahowa” Sannan ta ajjiye wayar ta kama hannun Aslam wanda yake jin gaba d’aya jikinshi yayi sanyi. A hankali ya mik’e ya bi bayanta suka fita tare.

A hanya aka tsaya drivern ya siya drugs d’in daganan suka wuce. Har suka isa gida kowa da abunda yake tunani! Suna shiga ya nufi side d’inshi yana mai cewa Mommy “yana d’an buk’atar ya huta”, “To” kawai tace suka wuce ita da Dad sama. Yana shiga d’akin shi ya fad’a toilet yayi alwala, ya fito ya hau jero nafilfili.

Su mommy suna hawa, Dad ya kira Daddy yace mishi ya cewa Auwal Mom da Ummi su taho da drivers da motocin mansion d’in duka a had’u a bakin estate za aje a d’auko Amaryar Aslam. Ya yiwa Granpa bayani ta watasapp, Granpa d’in ya ce masa ‘okay he’ll get back to him later’ So kawai a kawota estate d’in idan an tashi.”

Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mommy da Gwaggo Asabe suka shirya tsaf suka fito.
Suna fita a estate d’in suka had’u da su Mom da tawager su don haka suka yi convoy suka nufi gandun albasa.

12:00pm(earlier) Tun lokacin da su Dad suka fita, Arshaad ya kasa zaune ya kasa tsaye!
Gashi wani abun takaicin still Mammy ta hanashi fita. Yana ganin kiran Auwal yak’i d’agawa dan kwata kwata baya buk’atar wata hayaniya. Tunani kawai yake yi akan me zai yiwa Mammy ta barshi ya fita sannan a tunaninshi ya san Auwal d’in ce mishi zai yi yayi sauri ya san yadda zai yi ya fito kawai..
Duk da dai ya san cewa su Dad ba za su tab’a fasa d’aura auren saboda Mammy ba amma yana buk’atar zuwa. He needs to be there dan bai kamata ace ya zama absent a rana mafi soyuwa a rayuwarshi ba.

Suna a haka yaji wayoyinshi gaba d’aya ukun sun haukace da k’ara! Anfi minti goma amman duk ciki babu wadda ta huta, kiran yana katsewa wani yake kuma shigowa. A hankali ya k’arasa kan gadon nashi inda ragowar biyun suke zube ya fara dubawa. Jamil ne da ragowar Abokanayensa suke ta antaya mishi kira
Haka kurum yaji jikinshi ya d’au rawa sannan zuciyarshi ta fara wani kalan mahaukacin gudu!

Da kyar ya iya amsa kiran Jamil, tun kafin ya kaita ga kunnuwanshi ya juyo muryar Jamil d’in yana cewa
“Garin ya haka ta faru Arshaad???” Da sauri ya kai kunnenshi kafin yace “Sorry Jamiel,
wani abu important ne ya taso ya hanani zuwa” “Kamar ya, Wani abu important shi ya hanaka aurenta?”

Cikin rashin fahimta yace “ban gane ba! Ba a d’aura auren namu ba har yanzu?” Fahimtar da Jamil yayi Arshaad d’in bai san halin da ake ciki bane yasa yace, “Haba! Biri yayi kama da mutum. Ni daman na san kamar da wuya ace wai ka hak’ura da Huda! Anyways aikin gama ya riga ya gama yanzu kam. An d’aura wa Huda aure yanzunnan nima shaida ne, Amman ba da kai ba da Yayanka Aslam…”

Diff!!! Haka Arshaad ya d’auke wuta!

“Hello helloo helloo”

Haka Jamil yake ta maimaitawa amman shiruu!

Yadda ya k’ame ya k’i motsi sai da hakan ya d’an tsorota Mammy dan haka ta taso ta matso kusa da shi ta tsaya tace, “Kaii lafiyar ka k’alau kuwa??”

Sai a lokacin ya samu damar jan numfashi lokaci d’aya kuma ya saki wayar hannunshi ta fad’i k’asa ta tawarwatse!

Da sauri Mammy ta shiga gabanshi da kyau tayi cupping fuskarshi tace, “Kaii, ba dai hatsari suka yi ba ko?
Ka yi min magana ni duk kabi ka d’aga min hankali”

Wani irin jan numfashi yake yi wanda yayi mugun tsorata ta! Cikin tsananin b’acin ran da bata tab’a ganin shi a ciki ba yace, “Abunda kike so ai kenan! Kowa ya mutu kowa ya lalace, kowa ya shiga tashin hankali!
Ko ba shine abunda kike so ba? Ya k’arashe maganar cikin tsawa!

Cikin b’acin rai Mammy tace Kai!
Dan ubanka ni uwarka ce!
Kar In sake ji ka d’aga mun murya
idan ba haka b……”
Kafad’unta da ya kama duka biyu da mugun k’arfi ne ya sanyata tayi shiru.
Girgiza ta yayi da k’arfin gaske sannan yace
“Uwa! uwa!! uwaaa!!!
Shine kalmar da kika yi amfani da ita kika tarwatsa mini rayuwa
Tarwatsawa ta har abada!
Ki kasheni kawai Mammy na rok’eki da girman Allah ki kasheni in hutu!
Kin riga kin kasheni a bad’ini saura na zahiri.”
Yana gama fad’in haka
ya cika mata kafad’un nata da k’arfi
wanda har sai da tayi baya kamar zata fad’i, ji yake yi kamar ya d’agata sama ya kauce!
Da k’arfi ya fincike hular kanshi sannan ya cire babbar rigar ya jefar!
Yana juyawa yayi facin mirrow d’in jikin wardrobe d’inshi wanda gaba d’aya k’ofar wardrobe d’in mirron ne da mugun k’arfi ya dunk’ule hannunshi ya daki mirrow d’in rabi ya tarwatse!
Hakan bai yi mishi ba ya sake rarumo stool ya buga mirror d’in ya k’arasa tarwatsewa!

Da sauri Mammy wadda abun ya fara bata tsoro ta k’araso ta rike shi ta baya tayi hugging d’inshi..,
Gaba d’aya d’akin ya b’aci da jini kacha kacha dan ba k’aramin rauni ya yiwa kanshi ba daya daki mirrow d’in da hannu ba. Fincikewa yayi ya fasa mirrow d’in d’akin sannan ya d’aga centre table shima ya fasa shi!

Zuwa yanzu Mammy tayi mugun tsorata da lamarin Arshaad dan haka ta ware murya ta fara kwala kiran Dad da Aaima tana k’ok’arin rik’e shi tana cewa “Ka nutsu mana Arshaad, ka fara bani tsoro fa! Akan mace kake wannan haukar?”

Zare ta yayi daga jikin shi cikin tsananin b’acin rai idanuwanshi sun yi mugun jaa suna zubar da hawaye yace, “Mammy kin cuceni! Ban tab’a tunanin haka daga gareki ba!
Me nayi miki a rayuwa da nayi deserving haka daga gareki???
A iyaka sanina ban tab’a cusguna miki ba!
A kullum k’ok’ari nake yi inga na faranta miki na baki duk wata kariya ta ko wanne fanni…”
Matsowa yayi daff da ita yana kallonta kafin yaci gaba
“Bari kiji in tuna miki..
A ranar da kika jefo Mommy daga sama, na ganki!
Ina ga kina tunanin na manta ko?
Ko kuma ban gane ki ba?
Sarai na ganeki i was young Mammy very young at that time amma nayi zurfin tunani da hankalin In rufawa Mahaifiyata asiri dan a samu ta zauna lafiya cikin farin ciki da nishad’i!.

A lokacin da na had’u da Hudan. Ina ganin Mahaifiyarta na gane ita wacece dan dama tun farko Ina mamakin kamaninnta da Aslam da Abba da shigen kama da take yi da ni kaina! A lokacin daman kamar na sani na yanke shawarar neman ki mu fara tattaunawa amman kamar had’in baki Ina zuwa k’ofar d’akinki aka yi rashin sa a Mom ta zo wajenki babu abunda banji ba a ranar game da yanda kuka yi kuka rabata da gidannan! Everything. Ba ma iya kar case d’in Huda ba har da na Mommy a ranar duk na sake jin wasu sabbbin abubuwan da kuka aikata! Har abunda ban tab’a expecting za ku iya aikatawa ba duk sai da na ji!

But do you wat i did??” Bai jira ta bashi amsa ba yace “I kept quite!
Na yi shiru ban fad’awa kowa ba kuma ban nuna miki ba ke kanki, ko a fuska!
Ki duba kiga yanda muke ni da Aslam amman i choose to support you Mammy!
Ki dubafa irin halin da yake ciki amman nayi ignoring komai
saboda rufin asiri da farin cikinki! Because I love you! Bani da kamarki a duk duniyarnan!
Zan iya yin komai dan kawai inga you stay safe and happy!.

Ko kin san yaya mutum yake ji idan ya kulle maganganu a cikinshi shi kad’ai ba tare da ya amayar wa kowa ba?

To, haka nake ta fama da nauyin issues d’inki da guilt for almost 20 years……”

Durk’ushewa Mammy tayi a wajen ta fashe da wani irin kuka! Suna a haka nan Aaima ta shigo, da gudu ta k’arasa inda suke a rikice ta hau tambayar “mai ya faru??” Sai a lokacin Mammy ta mik’e ta kama hannuwanta sannnan tace “Aaima na yi laifi! Babban kuskure. Idanuwana sun kulle na kasa gane gaskiya, dan Allah dan annabi ki tayani bawa d’an uwanki hak’uri”

Da k’arfi Arshaad ya runtse idanuwanshi yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa….

“Ya arshaad mai y….” Da sauri ya juyo gareta ya d’aga mata hannu!

Shiru tayi maganar ta mak’ale dan tunda Mammy ta kawota duniya bata tab’a ganin Ya Arshaad d’in nasu a haka ba.

Ba tare da yace uffan ba ya isa jikin wardrobe d’in ya hau had’a takardu da kaya!…

Wani wawan kuka Mammy ta fashe da shi sannan tace, “Arshaad kar kayi mini haka dan Allah kayi hak’uri.
Wallahi na amince kaje ka auri Hudan Ai na gaya maka na tuba, Idanunane suka rufe amman yanzu sun bud’e! Son, dan Allah ka tsaya ka saurareni, ka yi hak’uri ka yiwa mamanka afuwar laifin da na kusan tafkawa da kaina nayi maka alk’awarin da kaina zan je har wajen Maryam In bata hak’uri sannan In bawa kakannin ta da su Abba hak’uri .A d’aura muku aure! Na san za su yarda. Beside ai har yanzu a matsayin fiancé d’inka take so kar ka damu ko Abba muka je muka samu ni da kai a yau d’innan za a iya gyara komai!” Magana take yi tana binshi duk inda yayi tana k’ok’arin rikeshi yayinda shi kuma ko alamar sauraronta ma bashi da niyya, ta had’a kayanshi kawai yake yi!….

Sai da ya had’a akwati da briefcase sannan ya d’au wayoyin shi ya zura a aljihu ya d’auki makullin motarsa ya nufi k’ofa.

Da sauri Mammy ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tace
“Arshaad na baka hak’uri kuma nace na yarda yanzu ka aureta.
Wallahi tallahi nima sai yanzu nake dana sani. Ban san me ya shiga kaina ba, na kasa duba ka da halin da zaka shiga amman yanzu idanuna sun bud’e. Ka tsaya ka jirani anan wallahi, ko k’iyayyar Huda zata kasheni wallahi zan hak’ura inje in bawa iyayenta hak’uri. I’ll not rest har sai naga ka aureta”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e!
Da kyar yana mai jin numfashinsa yana d’aukewa
ya iya fisgo magana yace mata “Mammy an riga an d’aura auren Huda da Aslam!
So dan Allah dan Annabi ki bani hanya in wuce kafin in yi abunda zan janyowa kaina bala’i!
Dan na rantse miki da girman Allah ko muryar ki bana k’aunar ji!
Ahalin yanzu ba abunda na fi buk’ata irin in yi nesa da ke,
mugun mugun nesa ma kuwa!!!”

Fashewa tayi da wani sabon kukan ta durk’usa a wajen.

Da sauri ya ja akwatin shi ya fita rik’e da suitcase d’inshi

ganin tana shirin ruk’o shi. Yana jin Aaima ta biyoshi amman yak’i tsayawa, sai ma k’ara saurin shi da yayi yana d’an had’awa da d’an gudu gudu…Itama Mammyn yanajin muryarta da alamun biyoshi tayi
hakan yasa yayi sauri ya danna key ya bud’e ya zuba kayanshi a baya ya shige ya tada motar ya nufi gate da mugun gudu. Allah yaso mai gadin yana nan dan haka ya na hangoshi ya wangale gate d’in, shi kuma ya f fice. Dai dai nan su kuma suka fito compound d’in! Basu tarar da shi ba sai iskar motarshi……

GANDUN ALBASA

Yinin biki Shuwa ta had’a mai rai da lafiya. Tun safe mai makeup tazo ta tsantarawa Amarya kwalliyarta
amman kafin ma lokacin d’aurin auren kwalliyar ta goge tas! Saboda tsabar hawayen da take yi tana sharewa. Zuwa yanzu kam Huda ta cire rai da Arshaad!

Ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda ya yaudareta for almost 4 years bayan ya san ba sonta yake yi ba!
“Don kawai ya ga wannan ranar?”
Ta yiwa kanta tambayar
Wata zuciyar ce tace mata
“Ai daman Mama ta fad’a, Abba ne ya turo shi”
Da sauri tace
“Astaghfirullah!
Inaaaa, Abba ba zai tab’a had’a baki a yi mini haka ba.
Sai dai in Arshaad d’in ne ya nuna mishi yana sona bayan ya san baya sona
shi kuma Abban ya yarda da shi.
Amma ai Abba ba zai tab’a turo shi ba
No matter what…”Kanta gaba d’aya ya d’aure ta rasa yadda zata yi.

Tana zaune daga ita sai Khadija a d’akin dan kwata kwata Sakina kwana biyun nan bata yarda su zauna waje d’aya ko had’a ido Hudan ta lura Sakinar bata so su yi. Ita kuwa Sakina ta san muddin ta zauna tare da Huda sai tayi kuka itama shiyasa taga gara tayi nesa da ita kar taje instead of ta dinga k’ara mata kwarin guiwa taje ta b’ige da karyar mata guiwa.

Suna zaune Khadija tanata lallashin ta su Madu suka shigo! Tunda suka shigo dama ta san ba lafiya ba dan bata tab’a ganin Madu ya shigo d’akin Shuwa direct haka ba, dan haka kawai ta lumshe idanuwanta tana jira taji yace ‘Arshaad ya fasa aurenta’

Murmushi yayi kafin taji yace “Amarya! Bud’e idon mana.”

Dumm!! Haka gabanta ya bada, da sauri ta bud’e idon taga yana kallonta shi da Baba bashir murmushi shimfid’e akan fuskokinsu. Da kyar ta iya gaishesu, daga nan taga Shuwa da Ummu da Mama suka shigo.

Su kuma su Abba suka ga bai dace ace Mahaifiyar shi tana ta ik’irarin tsinuwa a kansa haka ba, kuma kinga tabbas dole suna buk’atar albarkar ta!
Shiyasa Abba da yayyunshi maza suka yanke shawarar fasa d’aura auren da Arshaad
Instead sai aka d’aura da Yayansa Aslam mai sunan Mahaifinta wanda ya wakilci d’an uwan nashi jiya..

Mik’ewa Khadija tayi ta fita bayan ta gaidasu. Sai da kowa ya zazzauna
tukunna Baba Bashir yayi gyaran murya yace
“D’azu mun tafi da niyyar d’aura auren Hudan da Muhammad Arshaad
Sai aka samu matsala
Ita Mahaifiyar Arshaad d’in ashe tunda ta dawo ta d’aga musu hankali akan muddin aka yi gangancin d’aura auren d’anta da Huda tou tabbas sai ta tsine mishi! Ashe shiyasa ma bai samu zuwa jiya ba instead sai Yayanshi ya wakilceshi.
To su a tunanin su Yahayan za su iya shawo kan matsalar
shiyasa basu wani damu ba muma basu gaya mana ba.
To dai yau Mahaifiyar tasa ta tabbatar ta sake tabbatarwa
akan ita fa tana nan akan bakarta ba kuma wanda zai iya sakata ta sauk’a.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abunda Huda take ta faman maimaitawa tana hawaye.

Madu ne ya ce “Aslam bashi da wata makusa. Abunda yayi Arshaad shi yayi Aslam, sannan an an riga an tara mutane. Kuma tunda Mahaifiyar Arshaad ta furta bata k’aunar Huda to ko an dawo ance ta hak’ura aka d’aura tabbas Huda ba zata zauna lafiya da ita ba! Sannan Mahaifin Huda shi ne ya kawo wannan shawarar ya zab’a mata Aslam
It’s like kamar ma yafi farin ciki sannan hankalin shi yafi kwanciya da Aslam d’in
dan bakiga irin farin cikin da yake yi ba a lokacin da aka goya mishi baya aka kuma d’aura auren. To whare we to reject? Besides. Ni a ganina ma it’s for the best, In sha Allah. Tunda kullum zab’in Ubangiji muke nema, shi ya shirya hakan. Dan haka sai mu runguma mu kuma gode mishi mu bita da fatan alkhairi.

Banaso inji wata magana ta taso! Ku saka a ranku kawai Arshaad ba shine Allah ya tsara zai zama Mijin Huda ba. Aslam ne!. Sai kuyi mata nasiha ku shiryata, Yahaya yace min k’arfe biyar na yamma za su zo su tafi da ita in sha Allah. Allah yayi muku albarka gaba d’ayanku.” Yana gama fad’in haka ya mike suka fita shi da Baba Bashir.

A hankali sautin kukan Mama ya fara tsananta a cikin d’akin. Ganin Huda ta mik’e ta nufo inda take tana kuka ne ya sanya Maman ta mik’e da sauri ta fice daga d’akin tana kuka.

A tsakar d’akin Huda ta zame ta zauna ta fashe da wani kuka mai ban tausayi

Shuwa ce ta umarci Ummu da “ta je ta d’auko mata laffayar da za a nad’a mata
Sannan ta taho da turarukan wuta da kasko”

Ummu na fita Shuwan ta k’arasa inda Huda take zaune itama ta zauna sannan ta kamo hannunta duka biyu. Nasiha mai ratsa jiki tayi mata wanda ko Maman iyakar abunda zata gaya mata kenan!
Duk wani abunda ya dace sai da Shuwa ta fahimtar da ita dalla dalla.

A haka Ummu ta shigo ta samesu dan haka itama ta nemi waje ta zauna ta d’ora mata da nata darussan…,
Ita dai Huda zuwa yanzu muryarta ta disashe, hawayene kawai yake fita daga idanuwanta, sai faman sauk’e ajiyar zuciya take yi, a ranta tana tunanin. ‘Tayaya zata fara zama da mutumin da ba ya sonta bata sonshi?
Mutumin da ta lura ko inda take baya son zama…’

Umartarta suka yi da ‘ta mik’e’. Tana mik’ewa suka hau shiryata. Suna mata ruwan turarurruka
Khumra da na wuta.

A gigice Anty Zainab ta k’arasa gidan Baba. Tana shiga ko sallama bata yi ba ta fad’a d’akin Umma.
A kan gado ta sameta ta bararraje tana shan lemo da bredi da gyada .Ya Ja’afar kuma yana gefe a kwance yana bacci.

D’auke bredin tayi ta jefar, Umma na shirin yin magana Anty Zainab ta katseta ta hanyar cewa
“Jiya! Sai da nace miki kar ki k’arawa mutumin nan kud’i, yaudarar mu zai kuma yi amma da yake kunnen k’ashi gareki kika d’auki mak’udan kud’ad’e kika bashi saboda kinji Jalila duk ta rikice tana kuka ko? To albishirinki kice mini goro! Ga Huda chan ana shirya ta
In sha Allah nan da k’arfe biyar za azo a tafi da ita gidan Arshaad! Aure kam ya d’auru, ba d’an borin da yayi nasarar lalatawa.”

Kwarewa Umma tayi da d’an ragowar bredin bakinta wanda bata gama had’iyewa ba.
Da kyar ta dawo dai dai
Cikin tsananin tashin hankali tace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun!
Wacce iriyar masiface ni kam ta fad’amin?
Ni sadiya ina zan saka kaina?
Yanzu mutumin nan ya kyauta min kenan?
Tsofai tsofai da shi amman ya karkace yayi ta faman gilla mini k’arya?
Kin san tun yaushe muka sanshi kuwa? An dad’efa ana tare. Haba dan Allah
Allah ya isa kud’ina da lafiyata. Kiga fa jiya cikin dare muna barin asibiti haka muka je wajen shi.
Har da cewa ko dan halin da nake ciki zai yi mini aiki mai zafi! Shege ashe yaudarata ya kuma yi ya saka min rai. Allah sai ya saka min wallahi” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka..

Duk sai tausayinta ya lullub’e Anty Zainab, a hankali tazo ta zauna a gefenta kafin tace
“Yanzu menene abun yi? Kuka ba zai kawo mana solution ba.”

Hawayenta ta goge sannan ta mik’e tace “komawa za muyi! Ai ta inda aka bi aka hau tanan ake sauk’a.
Wallah ko dai ya lalata auren kafin ta tare ko kuma ya biya ni kud’ina”. Ta fad’a haka tana mai yafa mayafinta wanda ta d’auka yanzun.

Da sauri Anty Zainab ta mik’e ta tsaya a gabanta sannan tace, “Sadiya ki nutsu dan Allah. Na tabbata kafin mu k’arasa wajen nan mai uban nisa Huda ta riga ta shak’i iskar gidan Arshaad. Yanzu ni dai indai zan baki shawara ki d’auka to ki hak’ura da raba auren nan!
Kinga fa yadda muka yi ta k’ok’arin rabawarnan yak’i rabuwa to maybe wani babban rabo ne a tsakaninsu
Allah ne ma yake son mu shiyasa ya barmu da ranmu, kar muje mu sake yin wani yunk’urin, muje garin neman gira mu rasa idanuwanu.”

Cikin tsananin b’acin rai Umma tace “To matsoraciya! Kin san Allah wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru amman aure kam na raba shi na gama billahilazim! Ai In na barsu ma, To Maryam taci riba kenan! Idan zaki ci gaba da taimaka min to na gode, idan kuma ba za ki ci gaba ba
to kina iya yin tafiyarki, dan ni nan kin ganni wallahi sai inda k’arfina ya k’are!
Na tabbatar inda ace Khadija ce take cikin halin da Jalila take ciki da kema sai inda k’arfin ki ya k’are!”.

Anty Zainab taji zafin maganar amman kawai sai ta basar duba da halin da Umman take ciki kwana biyu..Jafar a haukace! Junaidu ya b’ata!! Baba ya gudu!!! Jalila kuma gata chan itama sai a hankali, sannan duk fad’in duniyar nan ita kad’ai Umman ta gayawa Jalilan cikine da ita amman har Laraba bata sani ba Umman tace ‘In ta fad’a mata tana iya gayawa su Hansai, daga nan su kuma su yayata ayi ta munafurci a cikin unguwa da dangi’. Waennan dalilan su suka sanya itama Anty Zainab d’in tayi sticking by her side take taimaka mata sannan tana tsananin jin tausayin k’awartata, shiyasa yanzu ma Mta kaawar da haushin da taji tace “Sadiya yadda na d’auki Jalila haka na d’auki su Khadija. Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kar muje muyi ba daidaiba cikin rashin sani.”

Da sauri Umma ta ce “Hankali na ba zai tab’a kwanciya ba Zainab! Ina cikin tsananin tashin hankali..
Jiya da Jalila ta kira ni gaya miki ne ban yi ba dan kaina ya d’au chaji ba kad’an ba!
Cikin jikinta ya zube, garin haukarta taje ta fad’o daga matattakala.
Kinga yanzu shi Yaron Auwal babu maganar karb’ar kud’i a hannunshi
kuma na tabbatar nan da kwana kad’an uwar nan tashi mara mutunci itama tsayayyiyar kanta
zata auno Jalila gidan nan! Ni na ma yi mamakin da ta barta har yanzu dan
kwata kwata ba shiri suke yi ba! Gashi ke kin san yadda Jalila take matuk’ar k’aunar Arshaad
sannan a haka kike tunanin zan bar Huda taje ta zauna tare da Arshaad a gaban idon Jalila?
Tana ji tana gani? Da wanne Yarinyar nan za taji saboda Allah? Sannan ni kaina me nayi ne haka a rayuwa da mugayen abubuwa suketa fad’o mini haka?”
Ta k’arashe tana mai fashewa da mugun kuka.

Rungumeta Anty Zainab tayi ta shiga lallashinta, Sai da taji tayi shiru tukunna tace “Sadiya ki nutsu ki bani hankalinki dan Allah mu yi magana”

Kamar wata k’aramar Yarinya haka Umma ta hau share hawayenta tana d’aga kai
duk ta rikice, ta manta rabon da ta shiga kwatankwacin tashin hankali irin wannan.

Sai da ta nutsu sannan Anty Zainab tace “Anjima idan na dawo daga raka Huda zan zo mu koma wajen mutumin nan, akwai wani ma shima za muje wajenshi.

I’m sorry to say amma raba auren Huda da Arshaad ba zai yiu ba Sadiya tunda an riga an d’aura.
Yanzu mu bar Huda mu ji da Jalila duk bala’i idan za muyi yawo tsirara mu san yanda za ayi a sati mai kamawa a aurawa Arshaad Jalila. Ke kin san wacece Jalila da kuma yadda take son Arshaad
da taimakonta da taimakonmu, na tabbatar Huda ba zata yi wata biyu a gidan Arshaad ba.
Na tabbatar hakan sai yafi yiwa Maryam zafi akan yanzu a fasa kai Huda gidanta kai tsaye!.
Yanzu ki cewa Jalila ta daure ta jure ta kauda kanta, za mu yi
nasara in shaa Allah.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 54So Da Buri 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×