Skip to content
Part 56 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Sakina ce ta yi knocking aka bata izinin shiga, tana shiga ta ce musu
“Masu d’aukar Amarya sun zo, suna k’asa.” Dumm!! Haka k’irjinsa ya buga hatta Shuwa.

Cikin dauriya Ummu ta cewa Sakinan “ta je, ga su nan zuwa”. Kallon ta Hudan tayi da idanuwanta da suka k’ank’ance suna zubar hawaye, da sauri ta juya ta fita tana share tata kwallar.

Shuwa na hannun damanta Ummu kuma ta ruk’ota ta gefen hannun hagu,
a haka suka sakata a tsakiya suka sauk’o parlourn da ita fuskarta a lullub’e.

Kauda kai Mommy ta yi ta share kwallar farin cikin data zubo mata! A hankali ta mik’e ta k’arasa wajensu ta kamo hannun Huda ta kawota kan kujerar da take akai gefenta ta zaunar da ita sannan itama ta samu waje ta zauna kusa da ita.

Ummi ce ta mik’e itama ta isa 3 seater da suke zaune su biyu ta zauna a kusa da Huda ta kamo hannunta tana murmushi (ya zamana sun sakata a tsakiya ita da Mommy )

Tsakin da Mom ta yi sai da ya d’an fito fili ba tare da ita kanta ta san zai fito d’in ba! Da sauri ta wayance ta sake yin wani sound kamar wadda abu ya mak’alewa a hak’ori sannan ta shiga gaida su Shuwa tana mai k’arewa gidan kallo! Dukda cewa gidan yana da girma gashi mai bene amman hakan bai hana Mom yiwa gidan kallon k’ask’anci ba.

Gaggaisawa aka shiga yi cikin barkwanci da mutunta juna, daga nan aka damk’awa su Mommy amanar Huda suka amsa hannu bibbiyu suna masu farin ciki…

Mik’ewa aka fara yi da niyyar tafiya amman Amarya furr! Ta k’i mik’ewa..
Da kyar Ummi tasa hannu ta d’agota sannan ta jawo ta jikinta ta rungume ta shiga lallashinta tana cewa “muje mana dota. Yi hak’uri kinji, kowa da haka ya fara.”

Cikin kuka, da muryarta wadda ta dad’e da dishashewa ta cewa Ummin
“Ban yi sallama da Mama ba. Dan Allah ku kaini wajenta. Zan biku amman sai na fara yiwa Mama sallama.”

Lumshe ido Ummi tayi tana jin yadda k’irjinta ya fara bugawa da sauri da sauri. A hankali ta juya ta sanarwa su Mommy abunda Hudan tace

Murmushi Shuwa tayi kafin ta cewa Ummu “ta tashi ta kamata su kaita mota. Za su yi sallamar a waya.”

Sai da suka yi da gaske kuwa tukunna suka iya janyeta. Tana kuka tana komai haka suka fitar da ita aka sanyata a mota Ummu da Ummi suka sakata a tsakiya Ummi sai faman lallashinta take yi.

Inda Mama take Mommy ta tambaya bayan fitar su. Sakina ce ta kaita har d’akin sannan ta juya ta fita dan itama tana so ta raka Amarya.
Mota guda suka yi ita da k’awayensu su hud’u waenda suka zo rakiyar Amarya.

A zaune Mommy ta sami Mama a bakin gado tana ta sharar hawaye..
Sai da ta k’arasa inda take ta dafa kafad’arta tukunna ma Maman ta san mutum ya shigo! Murmushi Mommyn tayi ta zauna a gefenta sannan tace
“Ai gara da Hajiya tace a tafi da ita ba sai kun yi sallama ba dan na san daa ta shigo ta ganki a haka to da sake tab’arb’arewa al’amarin zai yi”

Kukan Mama ne ya tsananta a hankali ta juyo ta kama hannunta tana sheshshek’a tace “Mommy, ga amanar Huda!Dan Allah ki kular min da ita.
Ina tausayawa Huda dan ban san ya zaman nasu zai kasance ba saboda na san duk su biyun basa k’aunar juna amman kuma idan na tuna ke ce surukar ta sai hankalina ya d’an kwanta na san at least

ko da ace bata samu soyayyar Miji ba na san zata samu ta Mahaifiyarshi
Hakan zai d’an rage mata rad’ad’i da damuwa.

Naso ace Huda ta auri mai k’aunarta amman kuma k’addara ta riga fata.”
Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka.

Murmushi Mommy tayi kafin tace
“Share hawayenki, ki d’ago ki bani hankalinki.”

Da kyar Mama ta iya tsayar da kukan nata sannan ta d’ago tana mai kallon Mommy da idanuwanta da suka k’ank’ance sukai jaa.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace
“Ki daina cewa Aslam ba ya k’aunar Huda!
Dan zan iya rantse miki ko shi kanshi Arshaad d’in ba ya yi mata kwatankwacin son da Aslam yake mata.”

D’an zaro ido Mama tayi tana kallonta da alamun mamaki.

“Kwarai kuwa”
Shine abunda Mommy tace
sannan ta d’aura da cewa
“Tunda na warke, although ban zauna da Aslam ba
ban kuma san yanayin shi sosai ba amman tashi d’aya na fahimci yana cikin matsananciyar damuwa!
Kullum yana fama da zazzab’i da hawan jini, anyi anyi da shi akan ya fad’i damuwar shi amma yak’i fad’awa kowa.
Sai da yaga yana shirin mutuwa tukunna ya zo ya samemu ni da Dad
yace mana ‘yana neman alfarmar mu barshi ya tafi uk
ya d’an yi y’an kwanaki’
Mu kuma ganin rashin dacewar hakan ne ya sanya muka hanashi tafiya.
Bayan Dad ya fita ne
na lallab’ashi akan ya fad’amin damuwarshi..
Da kyar ya iya gaya min
dan shi har ga Allah kunya yake ji…
‘He knows he’s selfish ta ko wanne b’angare
amma ya rasa yadda zai yi ya yakice soyayyar Huda a cikin zuciyarshi.’
Yace min ‘tun ranar da ya fara ganinta tun ba yanzu ba
Allah ya d’aura masa matsannciyar soyayyarta!
Kuma dede da rana d’aya k’aunarta bata tab’a raguwa a zuciyarsa ba
instead k’aruwa ma take yi.
Baya iya bacci baya iya yin komai cikin nutsuwa idan
ba hotonta ya saka a gaba ba yayi ta kalla.’
A ranar yace min
‘Muddin muka barshi aka d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi tou tabbas zai iya rasa ranshi!
Dan haka shiyasa yana ganin gara yayi nesa sosai kuma yana rok’ona ko da an d’aura auren to kar In fad’a mishi,
ko ya tambayeni kawai ince mishi nima ban sani ba’.

Naji matuk’ar tausayin Aslam a wannan lokacin tabbas, ba na so ya zama coward shiyasa na hana shi tafiya
na rok’esa Allah da Annabi ya zauna..idan yayi facing ya tabbatar da ta sub’uce mishi forever hakan will make him stronger and zai cire hope yayi moving on.

Ya yarda zai zauna bayan ya tabbatar min idan bai mutu a ranar ba to zai iya samun heart attack!
Ni kuma na duk’ufa gayawa Ubangiji
Ya saka mishi sassauci da dangana sanann ya zab’awa
Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu.

Tun jiya na hango silver lining.
Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d’aurin auren!
Idan an d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi
akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope!
Idan kuma an d’aura da shi to falillahil hamdu.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba
“Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to tabbas na san ba k’aramin so yake yi mata ba!

Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak’ura!

Na san Aslam tun yana Yaro k’arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie?
All that I’m trying to point out miki anan shine
Hudan ta tafi gidan wanda yake k’aunarta matuk’a!
Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi………”

Direct MT estate aka wuce da ita…
Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d’in Aslam sai tashin k’amshin turaren wuta yake yi.
Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d’akuna ukun akwai gadaje masu kyau!
Parlourn ma yana d’auke da duk wani abun buk’ata.

Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa.

Tun a gate na estate d’in Anty Zainab taji inama bata zo ba!
Gashi mata y’an Maiduguri da suka shigo mota d’aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi suna
“Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya” ita kuma tanajin kamar ranta zai fita!
Sannan kanta ya d’an juye
dan cewa aka yi gidanta ita kad’ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!.
A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba to ba zata tab’a gaya mata ba!
Sun sha yin fad’a da ita Khadijar ba sau d’aya ba akan su Hudan.

Ummi da Ummu ne suka ruk’ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta shiga da bismillah da k’afar dama, haka ma k’ofar side d’in Aslam da tazo shiga!
Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka.

Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah.

Bayan an d’an ragu a d’akin
Ummu ta k’ara mata da nitsatsiyar nasiha!
Basu wani dad’e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma mota kawai aka kai
dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa……
Jama’a da friends d’insu in banda santin estate d’in da side d’inta ba abunda suke yi,
a haka kowa ya watse.
Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d’insu guda biyu da suka zauna dan ragowar cewa suka yi ‘za su wuce saboda basa so su yi dare’…..
Da kyar da sid’in goshi Huda ta d’an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina ta yi shiru
ta bud’e fuskarta.
Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu
Istigfari kawai take tayi
saboda sam! Tunanin Arshaad yak’i fita daga ranta.

Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d’in Mommy.
Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d’in suka shigo.
Mik’ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa “ta dawo ta zauna
Nasiha za su yiwa Ango!”….
Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar
daga nan Dad ya mik’e yayi musu sai da safe.

Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki.

Mommy ce tace
“To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana.
K’awayenta fa kai suke jira su tafi”

Kamar zai yi kuka yace
“Mommy siyan baki kuma?
Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu,
Ina son ganin Arshaad
first.”
Ya fad’a yana mai mik’ewa zai fita.

“Baya nan”
Yaji muryar Mommy.

Da mamaki ya juyo kafin yace
“Ina ya je?”

“No body knows”
Mommy ta fad’a tana mai mik’ewa ta k’araso inda yake.
“Baka farin cikine?
Yau?”

D’an Satar kallon Gwaggo Asabe yayi yaga hankalinta sam baya kansu…. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Mommy ba wanda ya kaini farin ciki a kaff fad’in duniyar nan a yau!
Amman no matter how i tried sam! Na kasa ignoring some facts ne, If I were in Arshaad shoes I would have die by now.
Gara ka san abu ba naka bane ba tun farko akan ka saka rai kuma azo baka samuba daga k’arshe.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e
kafin ta shafa fuskarshi
ta d’anyi murmushi
a ranta ta raya
‘Inama ace kowa irin zuciyar Aslam d’inta gareshi, da
duniya ta zauna lafiya’….
Muryarsa ce ta katseta
jin yana cewa
“Bara inje In fara nemansa”

“Ka fara zuwa ko kai da Auwal ne ya rakaka ko?
Karka janyo mata abun magana mana a wajen k’awayenta”

Sunkuyar da kai yayi
chaan! Ya d’ago yace “okay”
Sarai Mommy ta san ba iya kiran Auwal d’in zai yi ba
shiyasa ta yanke shawarar ta kirashi da kanta.

Yana d’aki.
Shi kad’ai…
Ya gwada kiran Arshaad yafi sau nawa amma baya d’auka!
K’arshema kashe wayoyinshi yayi dan in ya kira sai dai yaji ance switchoff!
Babban abubda yafi damunshi shine rashin sanin inda Arshaad d’in yake…
Suna dawowa gidansu ya nufa
Aaima ce take fad’a mishi yadda suka yi d’azun dan haka hankalinshi a tashe ya fita nemanshi
amman ba inda bai dubaba ya nemeshi ya rasa!
Yana a haka kiran Mommy ya shigo wayarsa. Bayan sun gaisa ne
tace
“Yazo ya raka Aslam wajen
Amarya, k’awayenta suna jiransu ba su tafi ba sannan
ya d’an taho da snacks da kaji”
Da “to” ya amsa ta
daga nan suka yi sallama.

Ko da suka gama wayar sai da ya kusan minti biyar yana tunani tukunna ya mik’e
ya fita….

Kamar Mommy ta sani Aslam yana fita d’akin shi ya nufa ya zauna shi kad’ai yanata tunani..
Chan kuma ya zaro waya ya fara gwada kiran Arshaad amman sai yaji a kashe!
Har ga Allah yana son Huda
fiye da tunani dan
inda ace bai sameta ba
to da bai san ya zata kasance da shi ba
amman kuma
yana matuk’ar jin tausayin Arshaad! Bai san me yake going through ba!
A fili yace
“Wannan wacce irin k’addara ce?
Ya Allah Astaghfirullah.”

Ya jima tukun yaji knocking.
Izinin shigowa ya bada ba tare da ya san wanene ba.
Kallon kallo suka tsaya yi wa juna shi da Auwal bayan ya shigo, chaan kuma Auwal d’in ya k’araso yazo ya zauna kusa da shi.
Ko gaisawa ba suyi ba ya fara magana
“Yanzu ya za mu yi?
Su Abba sun k’ulla abunda zai iya janyo babbar matsala
su Mommy su kuma naga kamar they are okay with it!
Ko ka san yanzun nan ta kirani wai In taho da kajin Amarya muje in rakaka a yi siyan baki
As if ba abunda ya faru.
Aslam na san kaima baka son auren nan amma idan kace za kayi shiru ko kuma kace bara ka yiwa su Abba biyayya dan kar su ji ba dad’i to akwai matsala fa!
I can’t even begin to tell you yadda Arshaad yake son Huda.
You have to speak tun kafin a lalata muku future ku duka ukun.
Dubafa yadda kayi fainting
amman bayin Allah n nan ba wanda a cikinsu yayi yunk’urin yace a raba auren!
Duba kaga Arshaad is no where to be found
amma ba wanda ya damu!
Ita kanta Huda na san ba zata ganu ba yanzu, Iya event d’insu da bai je ba jiya sai da ta shiga tashin hankali!
Ku yi ending abun nan tun kafin ya janyo matsala Aslam
kar ka yi shiru ka cuci kanka.”

Tun da Auwal ya fara magana Aslam ya kafeshi da idanuwa,
sai da ya kai aya sannan ya d’auke idanunsa daga kansa ya mik’e tsaye kafin yace
“Like Mommy said!
Mu je ayi siyan bakin, a samu
a mayar da friends d’inta gida.”
Yana gama fad’in haka ya wuce yayi gaba.

Jiki a sanyaye haka Auwal ya mik’e ya d’auki ledar da ya shigo da ita ya bi bayanshi yana mamakin firgici, b’acin rai da tsananin tashin hankalin da ya hango a kwayar idanun Aslam d’in.

Auwal ne ya kira Sakina…
Kamar ba zata d’auka ba
sai kuma ta d’aga.
Tana d’auka bai jira jin tsiwarta ba yace
“Muna parlour, ku fito”

Tana ajjiye wayar, ta fad’a musu dan haka suka mik’e suka fita.

Yadda al’ada take ake siyan baki haka aka yi..
500 thousand suka yi demanding Auwal kuma ya basu
1M!

Kud’in k’in shiga account d’aya yayi tashi d’aya sai da
suka bada account wajen uku
tukunna ya juye musu…..

K’awayensu kasa hak’uri suka yi sai da d’ayar ta d’an matso k’asa k’asa ta tambayi Sakina “ya akai aka samu chanjen Ango ne?”

“Haka al’adar mu take!
Muna yin Angon bogi a wasu events d’in”
Haka kawai tace musu daga nan ta kauda kai.

Tabbas bata gamsu da ita ba
amman ganin yadda ta turb’une fuska kuma ta san halinta hakan ya sa kawai ta hak’ura ta koma gefe ta ja bakinta ta yi shiru.

Ita kuwa Sakina ba wani abun bane ya sake tunzurata
sai d’ayar k’awar tasu wadda ta lura da ita tun da aka fara siyan bakin! In banda
rawar kai da shishshigewa Auwal ba abunda ta saka a gaba.
Duk da ta lura da yadda yake d’an basar da ita…..

Har aka yi siyan bakin aka gama in banda gaisuwa ba abunda ya shiga tsakanin su da Aslam.

Ana gamawa
ba tare da b’ata lokaci ba dan dare yayi Auwal yace
“su taso a maidasu gida”
Dan dauriya kawai yake yi amman baya jin dad’i, kamar shi ne Arshaad haka yake jinshi gaba d’aya jikinshi yayi sanyi, kana ganinshi ka san baya jin dad’i duk yayi wani iri
gashi kanshi sai faman ciwo yake yi.
Ganin ba zai iya kaisu shi kad’ai ba yasa bayan sun fita ya nemi layin drivers d’in estate d’in mutum biyu yace “su zo akwai ragowar mutane su taya shi maida su”
Cikin minti k’alilan suka shigo da motocin compound d’in gidan su Aslam
su biyu.
Tun kafin su gama parking ya bud’e gaban motar shi ya juyo yana kallon Sakina, suna
had’a ido yace mata “bismillah”
D’auke kai tayi ta kama hannnun Khadija ta fara ja tana cewa
“Zo mu je mu shiga wachchar..”

Da sauri wannan k’awar tasu tazo ta wuce ta gaban Sakina ta shige gaban motar Auwal d’in inda ya bud’ewa Sakina ta zauna kafin ta juyo tana wani shu’umin murmushi tace mishi “thankyou”

Sakina bata san ya aka yi ba kawai ganinta tayi a bakin motar a tsaye!
Batare da ta kalleshiba ta bud’e baya ta shiga ta zauna
Khadijah ma ganin ta cikata ta nufi motar ya sanya ta biyota itama ta shiga ta zauna ta rufe matar dan tafiyarsu d’aya.

Ragowar y’an mata biyun kuma suka shiga motocin drivers d’in.

K’amewa Auwal yayi a wajen ya kasa motsi,
mamaki fal a ranshi,
da kyar bayan ragowar motocin sun fita ya samu ya ja k’afafuwansa ya shiga ya tada motar……

Da gangan ya saita madubin gaban motar daidai fuskarta
aikuwa ya ga ta had’e rai kamar an aiko mata da sak’on mutuwa!
A take ya ji
dariya ta taso masa, anya
kuwa abunda yake tunani shi d’in ne?
Sakina fa!?
Kenan daman ta san tana sonshi amma take ta faman wahalar da shi haka?
Woow!!
Allah yasa to hakan ne
dan in dai kuwa hakan ne da gaske to tabbas sai ya fi ko wanne d’an Adam farin ciki a fad’in duniya…..
Haka nan shi kad’ai yana ta sak’e sak’e a ransa sai faman murmushi yake yi shi kad’ai yana driving
wanda hakan kuma ba k’aramin tafiya da imanin k’awar tasu wadda ta shigo ta zauna a gaba gefen shi yayi ba.

Sakina tana ganinta har wani
juyawa tayi tana facing Auwal d’in tana murmushi itama,
ji tayi kamar ta shak’o ta! In banda tafarfasa babu abunda zuciyarta take yi tun lokacin da k’awar tasu ta shige motar ta zauna har kawo yanzu..
Numfashinta har wani d’ad’d’aukewa yake yi!
Itafa daman tun a school ta tsani Yarinyar nan dan ko ishashshen shiri ma basa yi
gata da k’aryar kud’i
tun suna school
dan duk waya idan ta fito a hannunta ake fara gani
(ta yi sneaking ta shigo da ita)
Gata da shegen rawar kai
da son a sani
shiyasa kwata kwata ita Yarinyar bata yi mata ba!
Ko inviting d’inta basu yi ba daga ita har Huda amma ba event d’in da bata zo ba!
Kalleta ba dangin Iya bare na Baba amman itace har kusan 11 a waje! Ta taho kawo Amaryar da ba wani shiri suke yi ba…
Kamar idanuwanta za su fad’o haka ta tak’ark’are take zabgawa Yarinyar harara….

Sarai Auwal yana sane da ita don yana kallonta!
Wani farin ciki yake ji kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha.
Wai da gaske Sakina kishinsa take yi har haka?
Tayay to zai tabbatar?
Ya yiwa kansa tanbayar.
Wani malalacin murmushi ya saki ta gefen bakinshi…
A hankali ya juyo ya kalli k’awar tasu wadda ita ma shi d’in take kallo, tun
ranar cocktail ya tafi da imaninta, jiya har mafarkinshi ta yi!
Yau kuwa ba zata bari ya sub’uce mata ba in sha Allah…

Murmushi ya sakar mata
ganin itama shi d’in take kallo,
a hankali but yadda ya san Sakina za ta ji yace
“Hey dear beautiful, where to?”

Da sauri ta koma baya ta jingina da jikin kujera jin zuciyarta zata faso waje.
Wani sanyi Auwal yake ji yana ratsa shi dan yana kallonta duk ta cikin glass,
he won’t lie
this is the best day of his life!.

Sai da budurwar gefen nashi ta sake cewa “Lamido crescent”
Cikin rangwad’a da kashe murya tukunna ya jiyo ta
dan gaba d’aya hankalinshi yana kan Sakina.
“Okay”
Kawai yace
yana mai karya kan motar dan har sun fara gocewa daga hanyar da za ta kaisu Lamido Crescent d’in.

Da mamaki Sakina ta mik’e ta zauna da kyau tana kallon yadda ya juya akalar motar ya d’au hanyar Lamido Crescent.
Bata gama shan mamaki ba sai da taji budurwa tana cewa
“Ko za ka saka min digits d’inka!
Sai mu dinga gaisawa”

Murmushi mai had’e da dariya yayi yana mai kallon fuskar Sakina wadda tashi d’aya idanuwanta suka cicciko da hawaye kamar zata fashe da kuka!
Har ga Allah yad’an ji tausayinta amma yana so yayi comfirming a yau d’innan
sannan idan ma bata saniba
to yana so yau ta san tana son shi. Dan haka ya juya yana kallon Yarinyar gefen nashi cikin wani kalar voice yace
“Yes sure, kamar kin shiga zuciyata dan nima i was just about to ask for your number”

Tana shirin yin magana
suka ji Sakina tace
“Um, idan ka sha kwana za mu sauk’a”
Da saura Khadija ta juyo tace mata
“Ke da wa??”

Cikin fushi Sakina tace
“Ni da ke!
Idan kuma ba zaki sauk’a ba to ni zan sauka!
Kina gani fa sai ya kaita tukunna zai dawo ya kaimu
saboda ga gantalallu.”

Ya so dannewa amman sai da dariya tayi nasarar sub’uce mishi, hakan kuwa ba k’aramin sake tunzura Sakina yayi ba
dan haka a zuciye ta sa hannu zata bud’e k’ofar motar a hakan ta tana tafiya ba tare da ta jira an tsaya d’in ba.

Shi kuma Auwal yayi maza ya danna lock!

Murmushi Yarinyar gaban motar tayi
kafin tace
“Kaga dear mu je ka fara ajjiye su, in yaso sai ka dawo ka kaini daga baya”

“Alright”
Auwal d’in yace
daga nan taga ya saka signal yana shirin juya kan motar, a cikin ranta sai kuma ta raya
‘Kuma fa idan ya sauk’e su
tare daga shi sai ita zasu dawo a motar, a hanya su yi ta hira!’
Dan haka da sauri sai tace
“Da yake ke gantalalliyarce ba?
Kin gwammaci a kaimu sannan a dawo da ke?”

Yarinyar taji zafin maganar ba kad’an ba amman gudun kar ta zubar da girmanta a gaban sabon saurayinta yasa taja bakinta tayi shiru
ta kawar da kai!.

Rai a d’an b’ace Auwal d’in ya juyo yace
“Sakina saboda ku fa tazo bikin nan!
Wanne irin attitude ne haka?”

Cikin fushi da bala’i tace
“Ban sani ba!”
Tana mai kauda kai.

Gani tayi ya juya kawai yana shirin d’aukar hanyar gandun albasa dan haka tace
“Wallahi baku isa ba!
Ka fara kaita ka ajjiye ta tukunna ka kaimu.”

Shiru ne ya biyo baya a motar
kafin Auwal ya juya ya nufi hanyar Lamido Cresent zuciyarshi fess…

Ganin yadda suka bawa iska ajiyarta suka shiga hirarasu kamar irin sun shekara da sanin juna d’innan ne
ya sake tunzura Sakina
tun ba ma da Yarinyar tazo sauk’a ba Auwal d’in
har da wani ce mata
“yana isa gida zai kirata in sha Allah”

Ita dai Sakina da kyar take iya jan numfashi, wani irin tuk’uk’i take ji zuciyarta tana yi mata,
bata tab’a jin b’acin rai da haushin mutun irin na yau ba!
Ji take kamar ta rufesu da duka daga shi har ita…..
Da k’arfi taji
gabanta yayi wani mummunan fad’uwa..tabbas abunda take ji
kishi ne!
Kishin Auwal take yi, kenan
sonshi take yi?
Innalillahi wa innailaihirrajiun
How?
Taya ta bari haka ta faru da ita?
A take sai kuma ta fara jin haushin kanta…tayaya
ma zata nuna ta ji haushi k’iri k’iri har haka
Allah dai yasa shima Auwal d’in bai fahimci abunda ta fahimta ba….

Ba tare da yace wata ta dawo gaba ba
Ya ja motarshi yayi gaba yana waving wannan Yarinyar da suka sauk’e..
Yana d’aukar hanya
yayi deleting number d’in nata da ya karb’a
sannan ya danna mata block!

Sai da suka yi tafiya mai d’an nisa sannan ya d’an juyo kad’an ya kalli Khadija yace
“Y’ar uwar, dan Allah ki zama alk’alin mu”
Ya fad’i hakan yana maida hankalin shi akan driving d’in da yake yi.

Murmushi Khadija tayi kafin tace “ok Ina jin ka”

Sai da yad’an juya ya kalli Sakina yaga yanda ta kumbura kafin yayi dariya yace
“2 months kenan yanzu, Ina bin Sakina da proposal amman tak’i accepting.
Inaso ki gaya min me kika fahimta a attitude d’inta na yanzu a game da ni?
Please.”

Murmushi Khadija tayi
zuciyarta d’aya,
a abinda ta fahimta
tace “Kishi!”
Dai dai nan yayi parking a k’ofar gidan Madu.

Da sauri ta bud’e ta fito!
Shima shi da Khadija suka fito suna yi mata dariya.

Ganin tana k’ok’arin wucewa ne yasa yayi saurin rik’o vail d’inta
Khadija kuma tayi masa ‘sai da safe’ ta wuce
Ya amsa yana dariya
dan still dariyar bata gama sakinsa ba saboda ba k’aramin nishad’i yake ji ba….
Cikin tsananin farin ciki
ya dawo ta gabanta ya tsaya yace
“Okay, no more pretends, kawai ki yarda…..”
Maganarsace ta mak’ale sakamokon had’a ido da suka yi, da sauri ya matso kusa da ita yana cewa
“Subahanallah Sakina daga wasa?
Yi hak’uri, goge hawayen dan Allah na daina”
Ya fada yana shirin sa hannu ya share mata hawayen nata
duk ya rud’e.

Da sauri ta buge mishi hannun
sai kuma wani sabon kukan ya taho mata wannan karon har da sauti! Cikin kukan tace
“Cika mini mayafi”

Da sauri ya cika yana
“Sorry Sakina, wasa ne fa.
Naji to ba kya kishina…”

Wucewa kawai yaga tayi
ba tare da ta waiwayeshi ba ta fad’a cikin gidan ta rufo k’ofar gate d’in da sauri….

A hanyar shiga parlourn taga Khadija tana jiranta su shiga tare amman kawai ta wuceta
ta shige, ko kallon inda take bata sake yi ba.

Bata yarda sun had’a ido da su Ummu da ragowar mutanen parlourn da suke zaune suna hira kamar rana ba! Haka nan
ta wuce su da sauri bayan tace musu “Ina wuni”
Bata damu da jiran amsar su ba, ta haye sama abunta.

D’akin da suke kwana ita da Khadija da Hudan ta shiga,
tana shiga ta ajjiye vail da jakarta ta fad’a toilet da sauri ta saka sakata
Sai a lokacin ta samu damar sakin kukan da ya mak’ale mata…..

Kuka take tun k’arfinta kamar ranta zai fita, tabbas son auwal take yi
wanda ita kanta bata san ya akayi soyayarshi tayi mata mugun kamu har haka ba!
Gashi bata tashi farga ba sai yau kuma babban abun takaicin shine shima ya fahimta, Infact ko waye ma yaga yadda ta dinga acting ai dole ya fahimta tunda
gashi ita kanta ta dalilin hakan ne ma yasa ta gane tana k’aunarsa.
Ba abunda yafi k’ular da ita irin yadda ta zubar da girmanta
ta fito k’arara ba tare da ta sakaya ba, kuma wani abun mamakin shine
har yanzu
zuciyarta tak’i yin sanyi
haushi da zafin budurwar nan k’awar su take ji..ji take yi kamar ta hau watsapp yanzunnan ta gaggaya mata magana..
“Damn it!
Tabbas Ina son Auwal”
Ta furta a fili tana mai fashewa da kuka.

Ko Auwal ne kad’ai d’a Namiji a duniyar nan ta riga ta yiwa kanta alk’awarin ba zata tab’a auren sa ba!
Tun ranar farko da ya furta mata yana sonta
Infact
ta san ma ba aurene ya kawoshi wajenta ba, idan
ma aurenne ita kam ba zata
tab’a iyawa ba!
Tayaya zata yarda ta zama surukar Granpa da wannan Mom d’in tasa da suka b’oye Huda!
Har gobe tana tuno wasu abubuwan da taji a bakin su Baaba Talatu waenda Granpa d’in ya yiwa Mama tun farkon auren su da Abba
besides ita tun kafin ta kai haka take adduar Ubangiji ya tsareta daga auren womanizer!
Auwal kuwa ta san yaci uwar womanizer ma tunda gashi har d’a Jalila take shirin ajjiye mishi….

Tana kuka ta yanke shawarar abunda zata yi, duk da
kuwa ta san zata sha wahala
amman its the right thing to do.

Da kyar ta iya cire kayanta
ta yi wanka, ta na fitowa ko goge jikinta bata yi ba ta d’au waya ta kira Ashraff….
Tun lokacin da suka fara dating yake cewa yana so ya turo
bare ma da yaji zancen bikin Huda, ya so ace an had’a da nasu
Ita tak’i yarda..

Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba tace masa
“Anytime from now yana iya yiwa Mahaifinsa magana sai a fara maganar auren nasu”

Ba k’aramin murna Ashraff yayi ba, tana jin yadda
yake ta faman zumud’i da rawar kai a cikin wayar
Ita dai sai murmushi kawai take yi, k’arshema kasa hak’ura yayi yace mata
“Bara yaje ya duba idan Daddyn nasu bai kwantaba sai yayi mishi maganar yanzun”
Da kyar da sid’in goshi ta lallab’ashi dan 12 ma ta kusa
tace yayi hak’uri ya bari gobe ya sameshi da safe ayi maganar.

Ba dan yaso ba ya hak’ura…
Ya yi ta janta da hira,
ganin kamar a gajiye take dan daga ‘um’ sai ‘um’um’
take iya amsashi da su
ya sanya kawai yace mata “ta huta” dan shi tunaninshi bashi yayi gajiyar biki ce take d’awainiya da ita.

Tana ajjiye wayar Khadija na shigowa, nan ta tusa ta gaba da zancen Auwal…
“Ta soshi mana, yana da hankali daga gani, ga
kyau, gashi zata zauna kusa da Huda…
Waye waye”

Ita dai Sakina k’arshe juya mata baya tayi, tayi mata banza kamar tayi bacci, ganin
haka yasa Khadijah kashe fitila, abunku da mai k’aramin ciki tuni tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita!
Sakina kuwa yadda taga rana haka taga dare
Wani abun mamakin shine
duk wani labari da plans da Ashraff ya gama gaya mata na bayan aurensu yanzun
she can’t help it but to picture it ita da Auwal!
K’ok’ari take yi ta danna k’iyayyar shi a cikin zuciyarta
sai dai abunda bata saniba
ta riga ta makara dan
already zazzafar soyayyarshi ta riga ta rinjayi y’ar guntuwar k’iyayyar da take k’ok’arin dannawa zuciyarta ta k’arfi da yaji…..

BULAMA ✍️

<< So Da Buri 55So Da Buri 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×