Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal.
A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya ga su Sakina sun fito daga ciki.
Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking.
A hankali kamar mai kuka yaji tace“Sakina shigo mana”. Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo ai ita a nan ma zata kwana yau’.
A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e kafin ya murza handle. . .
Labarin so da buri yamin dadi nakaranta litafi dayawa amma wannan yana daka shikin wayanda nagiso Allah ya Kara basira