Skip to content
Part 59 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Sai da Ummi ta fita tukunna Huda ta fahimci Aslam baya d’akin…har ta fara murna sai kuma ta ji k’arar ruwa a toilet. Kamar mara gaskiya haka ta zauna ta k’ame a guri d’aya har ya fito.

Kallonta kawai yayi ya d’auke kai, ya fita. Sai a sannan ta sauk’e k’akk’arfar ajiyar zuciya sannan ta zabgawa k’ofar da ya bi ya fice harara kafin itama ta mik’e ta shiga toilet d’in tayi alwallah ta fito ta tayar da sallah. Ta jima tana adduar Allah ya dawo da Ya Arshaad, watak’il idan su Abba suka ga idonshi su raba wannan auren, ta samu ta auri wanda take so itama yake sonta. Bayan ta shafa ta mik’e ta fita zuwa dining.

Ummi da su Shuraim ne kawai akai, da alamun su Abba basu dawo daga mosque ba, Ummi tana ganinta tace
“Ai yanzu nake shirin mik’ewa in lek’o ki, na ji shiru”

Murmushi tayi ta k’arasa wajen, har ga Allah Ummi tana burge ta Ubangiji yana son bayin sa masu tuba bayan sun fahimci sun yi kuskure. Tana zuwa ta ja kujerar gefenta ta zauna suka
fara hira ita da su Shuraim waenda suke a opposite d’insu ita da Ummi.

Ko 5 minutes bata yi da zama ba su Abba suka shigo. Opposite d’insu Abba ya zauna , ga mamakin Huda sai taga Aslam ya ja kujerar gefenta shima ya zauna! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Abba ba dan har kasa b’oye farin cikin sa yayi ya fara zuba murmushi.

Ummi itama murmushin tayi kafin ta mik’e ta zagayo inda suke ta fara serving nasu. Har ta gama Hudan tana zaune kyam! Sai da Ummin ta dawo tukunna k’asa k’asa tace mata “Ta tashi ta zubawa Aslam mana”.

A hankali ta mik’e dan ita har ga Allah wani abun ma kunyar Abba take ji..Jiki ba kwari ta hau serving nashi, tana gamawa ta tura masa komai gabansa itama ta zubawa kanta abinci kala d’aya kawai d’an kad’an.

Baka jin k’arar komai sai cokula.. Although ba Hudan ba ce ta dafa abincin amma yadda tayi serving nashi da yadda take zaune kusa da shi tabbas zai iya cewa this is the best dinner da ya tab’a having a rayuwarsa! Lokaci lokaci yake lumshe ido yana sauk’e ajiyar zuciya ba tare da kowa ya lura da shi ba.

Abba ne ya fara jan tissue ya goge bakinsa ya sha ruwa yace “Alhamdulillah” daga nan ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita.

Yadda ta san zai ji xeji, Ummi ta ce “Abba fita zaka yi ne?”. Bai juyo ba, be kuma kalleta ba kawai yasa kai ya fice.
Ajjiye spoon d’insa Shuraim yayi ya mik’e ya bar wajen gabad’aya ba tare da ya k’arasa cin abincin nasa ba.

Jikin Ummi ba k’aramin sanyi yayi ba, ta san cewa tunda ta dawo Abba baya kulata amma tayi tunanin tunda a gaban su hudan ne zai kulata yau, ta samu ta d’an ji sanyi a ranta. A b’angaren Huda kuwa, ba k’aramin kunya taji ba shiyasa itama kwata kwata ta kasa ci gaba da zama a wajen dan bata so su had’a ido da Ummin, ta lura da yadda Shuraim ya had’a rai ya mik’e ya bar wajen, dan haka tana mik’ewa ta nufi sama side d’insu. Tana shiga ta tarar da shi yana kuka! Da sauri ta k’arasa inda yake zaune akan gadon ta zauna ta kamo hannunsa, k’ok’arin mik’ewa ya fara yi dan haka da sauri tace “Shuraim wait, let’s talk mana. Ka daina kuka ka fad’a min me yake damunka, ka ji?”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya share hawayenshi kafin yace mata “ba komai” kawai. B’ata rai tayi sanann tace “To shikenan!

Bara kaga in tashi in tafi kuma ina sauk’a zan d’auki akwatina in bar gidan nan gaba d’aya in dai baka gaya min ba. Sannan sai na gayawa Abba da Ummi kana d’aki kanata kuka”

Sai da ya gyara zamanshi ya fuskanceta sannan yace “Abba ne! Ya tsani Ummi. Tun lokacin data dawo daga tafiya baya kulata baya yi mata magana kwata kwata. Idan ita ta kula shima sai dai yayi mata banza ya wuce kamar yadda yayi yanzun. Kullum sai naga Ummi tana kuka not once sometimes a rana sai tayi kuka sau wajen biyar shi kuma he don’t care!
Ban san meyasa Abba ya tsani Ummi ba, dama chan baya sonta yanzu kuma ya sake tsanarta!”

Da sauri Huda tasa hannunta ta toshe masa baki, sannan tace “kar ka ce haka Shuraim, kar in sake jin irin haka a bakinka. Abba bai tsani Ummi ba, ka ji ko? Kawai maybe su d’anyi fad’a ne kad’an amman na san za su shirya soon, ka ji? Ka daina sakawa a ranka
zasu shirya ya zama kamar basu tab’a yin fad’aba in sha Allah soon kuma, ka ji ko?”

Still kuka yake yi, dan haka Huda tayi ta lallashinshi har sai da ta samu yayi shiru ta tilasta masa ya k’ara cin cookie a d’akin dan bai wani ci abinci sosai a k’asan ba tukunna ta mik’e ta d’auko mishi tooth brush d’inshi da bathrobe ta bashi tace yaje yayi wanka yazo ya kwanta idan ma game yake son yi sai su yi tare.

Shuraim a zuciyarshi ya ji ya sake jin k’aunar Hudan, yadda ta tsaya take k’ok’arin taga yayi farin ciki hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba.

Karb’a yayi ya fad’a toilet d’in ita kuma ta jona ps ta fara yi musu settings. Sai a lokacin Ummi ta bar bakin d’akin tana rik’e kukan da ya taho mata. Tana shiga d’akinta ta saki kukan, tabbas tayi kuskuren da ita kanta ba zata tab’a yafewa kanta ba! Kalla fa yadda Hudan take da hankali take k’aunar jininta amman haka nan tayi depriving d’inta childhood mai dad’i! Ta rabata da Mahaifinta! Ta sanyata ita da uwarta a k’unci basu ji ba basu gani ba duk saboda So da Burin mallakar Mijin da a yanzu ta riga ta hak’ura dan ta san ba zai tab’a accepting d’inta ba. Ummi ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita, tabbas zata samu lokaci ta ware ta rok’i Abba ya barta ta je taga Mama ta nemi yafiyarta sannan zata ta nemi yafiyar Hudan itama dan kwata kwata ta kasa sukuni tana jin zafi da dana sanin abunda ta aikata a baya
Inama ana dawo da hannun agogo baya.

Abba Yana fita direct side d’in Daddy ya nufa, yana shiga ya tarar da su suma suna dinner su uku abunsu. Yanzu Mom ta samu sauk’in Jalila biyayya take yi mata kamar zatai mata sujjada! Duk abinda tace shi take yi sannan ta maida kanta k’asa kamar wata y’ar aiki, yau ma ana gama abinci ta d’iba ta wuce d’akinta har da cewa
Mom d’in ‘ko akwai aikin da take so ayi mata?’ Murmushi kawai Mom d’in tayi mata sannan tace ‘ba komai’
already a ranta ta riga ta gama shiryawa akan gobe gobe za tayi mata korar kare! In sha Allah.

Kujera Abba ya ja ya zauna kusa da Daddy. Duk da ya k’oshi amma sai da Daddy ya saka shi yad’an tab’a wani abun.

Auwal ne ya fara mik’ewa saboda yana da tulin aikin da yake son yi and yanaso yau ma ya sake gwada sa’ar shi ko Allah zai sa Sakina ta amsa wayarshi. Dan haka yayi musu ‘sai da safe’ ya wuce sama.

Daga nan itama Mom ta mik’e suka fara tattare dining d’in ita da mai aikinta. Tana shigewa Abba ya dubi Daddy yace “Daddy magana na zo mu yi akan Maryam!”

Juyowa Daddy yayi ya bashi dukkannin attention d’insa kafin yace
“Ina sauraronka, what about her?”

Soundin so worried and disturbed Abba yace “Har yanzu bata d’aukar waya ta! Bata replying messages d’ina. I think kawai mu je mu samu su Abba Madun maybe shi zai iya bata shawara ta d’auka”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace “Abba, I know what you are going through amma sai nake ganin kamar Maryam tana buk’atar more time kafin komai. Ka duba kaga irin abunda Mijinta yayi mata sannan na san ta san Granpa ya sallame mu daga estate saboda Huda kuma na san yanzun ma Huda zata iya gaya mata ya sake korarta! Gaskiya bana jin su kansu su Abba Madun za su goya mana baya ko da ace mun je mun same su da wannan maganar Let’s assume ma sun goya mana bayan ni na san Maryam ba zata tab’a yarda ba a yanzu, kuma kaga idan suka bata shawara itama ta basu nata uzuri dole fa in aka auna aka duba za a ga ta fimu gaskiya ne. Sannan Granpa! Allah kad’ai ya san irin yawan y’an kallon da zamu kwasa da shi idan Maryam ta dawo gidan nan a yanzu!.

Bawai zan yi backing out bane in daina goya maka baya ba not at all Abba, all I’m saying shine Ka kwantar da hankalinka mu d’an jira kad’an tukunna, na san dole Granpa zai sauk’o kwanan nan tunda yanzu case d’in ya shafi har Aslam, kaga daga nan sai mu san abun yi”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Na ji kuma na fahimceka.
Amman nima inaso ka fahimceni…
Daddy, Idan akwai abinda na sani wanda yake dahir! To shin ko da ace Granpa ya huce mun koma yayi accepting d’inmu da Huda to fa ba zai tab’a accepting Maryam ba kuma idan aka taso da zancen wani sabon case d’inne zai kuma b’ullowa, kaga kenan an koma square 1! So ni a gani na this is the right time da ya kamata muje ayi magana a gyara komai, In yaso idan ma ya hak’ura kaga already Maryam tana nan so babu yadda zai yi. And another thing is wannan Usman d’in!
Na san yanzu baya nan saboda iyayensa sun ce ko k’afar gidan da Maryam take kar ya taka amma fa su suka haife shi, shekarun baya Maryam d’in ta tab’a bani labarin yadda Mahaifiyarsa ta murzawa idanuwanta toka ta fifita farin cikin d’anta akan na kowa, so yanzu idan ya dawo ya nuna musu bai hak’ura ba na tabbata hak’uri kawai za a bayar kuma na san Maryam ba zata iya ce musu a’a ba..

Waennan dalilai Daddy su saka sanya kaga hankalina duk ya tashi! I don’t want to loose her again.” Ya k’arashe maganar kamar zai yi kuka.

Gabad’aya sai tausayinsa ya rufe Daddy dan haka yace “Ba komai,
In sha Allah ba zaka rasata ba.
Za muje d’in, in Allah ya kaimu ko gobe da yamma ne idan na tashi a aiki zan biyo company d’in naku sai mu wuce.”

Sai a sannan Abba yayi murmushi yace “Thank you Daddy”

Murmushi shima Daddy yayi daga nan suka shiga tattaunawa

Tunda suka fara magana Mom ta lab’e a kitchen, babu abunda bata ji ba, gaba d’aya ta hada gumi kamar ita aka ce za a k’arowa kishiya. Sai da su Daddy suka bar dining d’in tukunna ta samu ta fito ta haye sama da niyyar d’aukar mayafinta ta nufi wajen Ummi amma sai aka yi rashin sa’a Daddy ya rik’e ta, ta so ya d’an fita ko ita ya barta taje ko parlour ne tayi waya amman k’iri k’iri ya kafa ya tsare yayi kane kane! Ba yadda ta iya haka ta hak’ura ta bari akan gobe suna fita office zata je ta samu Ummin.

Sai da Sudais yayi bacci tukunna suka yi sallama da Shuraim wanda zuwa yanzun ya ware kamar ba shi ne yake ta kuka d’azu ba! Haka nan ta fito ta barshi yana game d’in. Ta so ta wuce d’akinta kawai amman sai akai rashin sa’a suka had’u da Abba tana fitowa daga parlourn nasu.

Ajiyar zuciya ta sauk’e dan daman tana son ganinshi, duk da bata san ta Ina zata fara ba but they need to talk.

Kallonta yayi ya kalla inda yaga ta nufa, da sauri ta fara kame kame
“Um daman zz n”

Cikin katseta yace “It’s late, bara in je In kwanta. Good night.” Har ya wuce yaji tace “Abba”. Juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa.

K’arasawa tayi inda yake a tsaye tana wasa da fingers d’inta.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Talk mana, Um?” Yana mai bata full attention d’insa.

Da kyar ta iya ce masa. “Abba daman it’s about Ummi”

B’ata rai yayi sosai kamar bai tab’a dariya ba!

Kamar ta sani dama tak’i yarda ta kalleshi taci gaba da magana “Abba dan Allah ka daina yi mata abunda kake yi, ka dinga kulata please Abba kar..”

Cikin katseta yace “Ita Ummin tace miki bana kula ta?”

Da sauri ta d’ago ta hau girgiza kai kafin kanta tsaye tace “Shuraim ne, d’azu ko abinci bai k’arasa ci ba ya bar dining d’in. Ina hawowa na ganshi yana ta kuka, da kyar na lallab’ashi. Abba if this continues zamu iya samun matsala da brothers d’ina a gaba musamman ma idan suka k’ara wayo suka fahimci duk ata dalilina ne kake yi mata hakan. Dan Allah Abba ka daina Ubangiji ma ana yi mishi laifi ya yafe Ummi ta gane kuskurenta..kalla yadda take yi min, Abba please ko dan neman zaman lafiyarmu ni da su Shuraim ka dai na yi mata haka, no
matter yadda muke ni da su uwa uwa ce! Ko ni idan naga ana yiwa Mama haka akansu ba zan ji dad’i ba. Please Abba dan Allah” Ta fad’i hakan tana me matsowa ta kama hannunshi a nata ta rik’e.

Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e

Tabbas abunda Huda ta fad’a gaskiya ne, shi kansa saboda su Shuraim d’inne ma yasa yake sassauta mata abubuwan da ya shirya zai yi mata tunda ta nace sai ta zauna da shi!
Ummi tayi masa abubuwan da baya jin zai iya yafe mata, yana so ya yafe amman ya kasa, but kamar yadda Hudan ta fad’a kar aje a samu matsala ya raba kan y’any’ansa da kanshi dan haka dole zai dinga danne zuciyarsa. A hankali yaji Hudan ta sake cewa “please Abba”. Kamar zata yi kuka.

Murmushi yayi ya zare hannunsa a nata ya shafa kumatunta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya. Baya jin akwai uban da yake yi wa y’arsa irin son da yake yiwa Huda, she’s just like her Mom everything hatta halayyersu iri d’aya ce! Kalla yadda take yiwa kishiyar Mamanta campaign dan kawai kar ayi hurting kowa.

A hankali yana kallonta yace “Naji na daina I promise”.

Murmushi ta fara mai had’a da dariya kafin tace, “Thank you Abba”

Jingina kai yayi shima yana murmushin yace “Ai kin iya campaign dole in hak’ura, amma ina so nima kiyi min campaign a wajen Mamanki!”

Da sauri ta sunkuyar da kanta dan ita kunya ya bata.

Dariya yayi kafin yayi kalar tausayi yace “Please princess, Tak’i d’aukar wayana. Ko bakya so ta dawo nan ku zauna tare? Kin fi so koma gidan Usman?”. Da sauri ta girgiza kai. A hankali yace “Then you have to do something Huda ina buk’atar taimakonki, kin san Mamanki da kafiya dan haka dole sai mun taru akan ta tukunna za muyi nasara saboda ba zan iya shawo kanta ni kad’ai ba. I need your help”.

A hankali ta d’aga kai, cikin tsananin jin tausayin Mahaifin nata tace “In sha Allah Abba, I’ll try my best”

Murmushi yayi yace “to shikenan, na gode.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana tunanin ‘tabbas idan fa akai sake Mama fa zata iya komawa gidan Baba anytime from now, dan tana da labarin yadda Shuwa tayi kawaici a farko ta bi bayan Baba akan Abba. Sannan itama Mama a yadda suke yanzu da Baaba Talatu tsaf zata iya yin kawaici ta koma masa, ko lokacin bikinta sai da taji Baaba Talatu suna magana da Anty Zainab wai tunda Baba ya tafi port harcourt bashi da lafiya! Bara a gama biki zata samu Kaka da Abba Madu da maganar! Kar fa a ce tayi hak’uri ta koma zai shiryu tunda gashi har rashin lafiya yake yi which definately ta san akan Maman ne! Komai yana kanta daram! Na yadda Mama ta sha azaba a gidan nan, ba zata tsaya ta zuba ido a sake maida Mahaifiyarta cikin uk’uba ba besides ita dama ta dad’e tana da burin taga an maida auren iyayenta! Tana son ganinsu tare…’ “Good night, ko?” Muryar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

D’agowa tayi tace “Good night Abba”
So take ya wuce tayi d’akinta amman sai taga ya tsaya. Dakewa kawai tayi ta juya ta nufi side d’inta. Murmushi ya yi mai had’e da y’ar dariya kafin ya ce “A fatherly advice…kema ki daina gudun Aslam!”

Runtse idamuwanta tayi da mugun k’arfi! Wata kunya ta lullub’eta, sai da tayi dana sanin nufar d’akin nata da tayi.

Tafi minti biyar a tsaye, k’arshe tayi kalmar shahada ta juyo!
Kamar yadda tayi zato bata ga Abba a wajen ba.

Kamar wadda akace mata zai fito haka ta zo ta wuce da sauri ta nufi hanyar k’asa ko
globes d’in bata tsaya kashewa ba….

BULAMA ✍️

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 58So Da Buri 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×