Skip to content
Part 6 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Shiru Abba ya yi yana so ya gano inda kalmar ‘ka maida ita!’ Ta nufa, dan bai gane ba.Fusata granpa ya yi jin yadda yayi masa shiru dan haka ya daka mishi tsawa ta hanyar cewa, “ko baka ji na ne Abba!!”

Tuni Abba ya hau cewa “to Granpa in shaa Allah yanzu yanzu…” Duk ya bi ya rikice.

Ganin hakan ya sanya Ummi share fuskarta da ta jik’e da hawaye ta faki idon granpa ganin ba su yake kallo ba ya sanya ta d’an tab’a Abba ta ce
“ka taso mu tafi, yake nufi.”

Kallon ta Abba ya yi sannan ya mik’e ya ce “ta so mu tafi.”

Dan ba ya so ya fara zazzage mata ta cikinsa a gaban Granpa. Har ya juya sai kuma ya dawo ya zo ta gaban Granpa ya tsugunna ya ce,

“Dan Allah ka yi hak’uri na san na yi maka laifi, ka yafe mini, in shaa Allah duk abinda ka ce iny i zan yi daga yau ba zan sake k’etare umarnin ka ba.”

Kusan 1 minute tukunna Granpa ya juyo ya kalle shi sannan ya ce “yafe maka da na yi ba wai yana nufin na manta da abunda ka yi bane, na yafe maka ne saboda ni kaina in samu peace of mind na zama a same environment da kai tunda ka zame mini dole, it’s all for Ummi’s sake, so idan kanada hankali do your best to keep her happy hakan ne zai sa ka gujewa b’acin rai na, ka samu mu rabu lafiya.”

Yana gama fad’in haka ya juya ya fara dogara sandarshi har ya kai k’ofar d’akin shi ya juyo ya ce mata idan bai yi abunda nace ba, ko kuma ya yi trying anything stupid ki zo ki sameni.”

Daga nan ya shige ya barsu a palon.

Kallon ta kawai Abba yake yi, ji yake kamar ya shak’e ta ya huta, gashi ya yiwa Granpa alk’awari, idan ya fahimci kalmar Granpa ta ‘ka maida ita’ tabbas yaji Ummi ta yo ta karkad’e zani ta kawo k’arar sa kenan.

Sannan for her sake ne ma aka hak’ura zai ci gaba da zama a estate d’in.

Muryarta ce ta katse masa tunani
“Doctor is waiting” kawai ta ce ta kama hanyar fita tana d’an tafiya da kyar tana tari irin na marasa lafiya.

Ta zo daff da fita kenan ta ji muryar Gramma tana kiran Abba. Da k’arfi Ummi ta runtse idanunta domin ta san yanzu kam k’aryarta ta k’are.

Kamar kuwa yadda ta yi zato Gramma tana k’arasowa ta rufe Abba da fad’a akan sakin da ya yi, sannan ta hau bada umarnin ya maida ita nan take kuma karya k’ara.

A rikice yake kallon Gramma sannan ya juya a fusace yana kallon Ummi wadda kana ganinta ka ga mara gaskiya, gashi babu Mom a wajen bare ta ceceta, fahimtar rashin gaskiya k’arara a kan fuskarta ne ya sanya kawai ya juya ga Gramma ya fara k’ok’arin fahimtar da ita.

Hakan ne ya bata damar zaro wayar ta ta hau kiran Mom a rikice.

Abba kuwa hak’uri ya hau bata yana ta rantsuwa a kan “shi bai san da wata maganar saki ba ma, wato shiyasa Granpa ya zuciya sosai!!

Haba no wonder, ai kuwa yanzu sai an koma wajen Granpa an wanke shi wallahi”.

Ya k’arashe maganar a fusace yana kallon Ummi.

A fusace itama Gramma ta cillo masa takardar hannu nata tana cewa, “wallahi zan yi matuk’ar b’ata maka, ba na son rainin hankali, ko a mafarki in aka tasheni na san rubutunka kai da y’an uwanka.”

Durk’usawa ya yi ya fara k’ok’arin d’aukar takardar yana kallon gramma a ransa yana cewa ‘yanzu kam ya samu mafita k’arya Ummi ta k’are!!

Dama a ce cewa ta yi a baki ya fad’a mata to da da sauk’i, a rubuce kuwa ai ko hauka ake dole a gano inda rubutu ya bambanta.’

Hannu ya kai kan takardar ya d’auka, bai kalla ba sai da ya mik’e.

A take gabansa ya yi mugun fad’uwa ya k’urawa takardar idanu yana k’ok’arin tuno yaushe ya rubuta.
Tilastawa kwakwalwar shin da ya yi ne ya haddasa masa jiri ya tafi yuuuu zai fad’i.

Da sauri Likita da suka shigo tare da Mom yanzu ya yi saurin taro shi yana
“Be careful, wat happen again??”
Ya yi maganar yana kallon su Gramma.

Mom kuwa rufe Ummi tayi da fad’a sosai tana cewa, “wai ke Zainab so kike ki k’arasa shi ne? Ba ki ji abinda Likita ya fad’a bane? Ina ce magana ta riga ta wuce? Dan na tabbatar Granpa ya sanya shi ya mayar da ke! To hayaniyar kuma ta me ce ce?”.

Kuka Ummi ta saka sannan ta ce “Adama cewa fa ya yi wai bashi ba ne ba.”

Ajiyar zuciya Likita ya sauk’e kafin ya ce ki kwantar da hankalinki, ba shi d’in ba ne”

Da mamaki duk suke kallonshi.
Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa sannan ya ci gaba “yanzu haka takardun nan na dawo zan baku, ina ta sauri d’azu na hawo ba tare da ita ba. Ban so shi Abban ya sani ba gudun abunda ka iya zuwa ya dawo but now I have no choice…”


Hannu Gramma ta mik’a mishi sannan ta ce “ba ni nan.”
Cikin ladabi ya mik’a mata ta saka hannu ta karb’a, Abba bai yi wata wata ba ya lek’a suka hau karantawa suna dubawa a tare.

Sai da suka gama tukunna Gramma

d’in ta kalle shi da alamun buk’atar karin bayani.

Gyaran murya likitan ya yi ya ce “tabbas hakane, results d’in basu gama had’uwa ba sai d’azu da safe, daman a yadda na gansa yana behaving lokacin a asibiti na yi tunanin hakan shiyasa na yanke shawarar yi masa wadannan tests d’in and result d’in gashi yadda nake tunani suka fito. But wannan duk ba damuwa bane ba, ku kwantar da hankalin ku, in sha Allah babu wata matsala muddin aka kiyaye b’acin ranshi. Black out ne da d’an loss of time ya samu due to stress d’in da ya saka shi misbehaving wanda hakan ya janyo mishi loss of memory, minor.”

Tun a lokacin da ya farfad’o na yi mishi magana sai nake ganin kamar ma bai san me ya faru ba shiyasa na dan bincika shi. A nuna wa Granpa, shi ma d’azu mantawa nayi ban hawo da takardar ba, saboda yadda na ga Adama a rikice. Dan Allah a kiyaye, tun kafin in ga wannan result d’in ma sai da na ja musu kunne akan yawan b’ata mishi rai, yanzu haka kar yayi komai ya huta sosai for some days saboda kwakwalwarshi kanta ta samu sukuni, if not zai yi ta dinga loosing time gaskiya, dan abun yakan samu mutum ne mostly a old age sosai but shi gashi har ya fara, idan an yi tackling zai tsaya in ba a yi ba kuma gaskiya ban san ya abun zai kasance ba.”

“Abba kaima amman sai ka dinga taimakon kanka sosai kana kawar da tunani, Allah ya baka lafiya.”

Ya yi maganar yana dafa kafad’ar Abba wanda ya daskare a wajen.

“Na barku lafiya”.

Ya fad’a yana mai juyawa saboda ya bar patients da yawa a clinic suna jiransa.

A hankali Gramma ta ja shi ta kai parlourn sannan ta zaunar da shi ta fara lallashinshi da kalamai masu dad’i, dan ta lura maganar likita ba k’aramin girgiza shi ta yi ba, ita kanta ta girgiza ga kuma tausayin d’an nata da ya yi mata rufdugu lokaci guda.

Haka itama Ummi ta shiga tausar shi da kalamai har da Mom suka taru.
Suna a haka granpa ya fito da alamun masallaci zai je dan an fara kiran sallah.

“Wats going on” Ya tambaya yana mai kafe su da idanuwa.

A hankali gramma ta k’arasa ta je gaban sa ta hau nuna mishi takardar da bayani daga k’arshe ta d’ora da cewa “likita yace a guji b’ata mishi rai da abunda zai b’ata mishi ran.”

Granpa bai ce komai ba ya taka gaban Abba ya tsaya sannan ya fara magana
“Allah ya baka lafiya. But yadda baka da lafiya itama matarka haka, so karka bari inji wani abu ya taso daga gareka dan tabbas za a ji kanmu ba tare da na duba health problem d’in ka ba, tunda kai ne ka d’orama kanka since day 1.
Kana iya nemawa kanka sauk’i ta hanyar yayewa kanka idan kuma taurin kai da tirjiya ka zab’a! Ka dai ji abinda Likita ya ce.”

“Second option d’inka kuma ‘chanja uba da y’an uwa’ dan muddin nine ubanka to babu kai ba Maryam.”

Lokaci yana wucewa ku tashi ku wuce ka kaita asibiti.” Yana gama fad’an haka ya yi hanyar fita.

A hankali Abba ya juya ya share hawayen da ya taho ta gefen idonsa ba tare da ya bari wani ya gani ba.

Kamar minti biyu parlourn ya yi shiru.
Daga baya Gramma ta ce “su wuce kawai, Allah ya sauwwak’e.”

Haka nan suka tafi ba tare da wani ya ce da d’an uwanshi k’ala ba.

Ganin da ya yi ba zai iya tuk’i ba ya sanya shi kiran Arshaad, shi ya tuk’a su babu mai magana a motar shiru har suka isa aka shiga da ita dan yin investigations d’in, shi dai Abba yana zauna yana mamakin ciwon Ummi.
Ta ya aka yi Ummi ta samu ciwon zuciya? Matar da kullum burin shi ya faranta mata ko dan hakkin aure!! Sam ba ya so tana gani kamar bai damu da ita ba. Sannan ga sabuwar matsalarshi shima yanzu da aka ce. Tabbas ya yi mugun tsorata da jin wannan lamari dan ko lokacin da aka ce yana da ciwon zuciya abun bai tsorata shi kamar wannan ba.

Kiran sallar masallacin arean ne ya sanya suka mik’e jikin su duk babu kwari. A haka dai suka je shi da Arshaad suka yi sallah suka dawo suka ci gaba da jira yanata tufka da warwara.

Muryar Likitan ce ta katse mishi tunani jin yana cewa
“Ha’a Abba!!” D’agowa Abban yayi suna had’a ido da sauri ya mik’e ya ce “Dr ya aka yi haka? Da gaske heart problem ne da ita?”

Kafad’unsa Likitan ya dafa sannan ya zaunar da shi kafin ya ce “haba Abba!! Ba na ce ka huta ba? Kai da aka ce ka zauna ko hayaniya kar ayi a kusa da kai.” Shiru ya yi jin Abba ya ce, “Granpa ne yace in kawota da kaina shiyasa ka ganni a nan.”

Mik’a mishi takardun kawai yayi sannan yace na d’aurata akan magunguna ku tsaya ku siya babu a nan, Allah ya k’ara sauki. Dan Allah ku koma gida da wuri, sannan ka huta sosai.”

Yana gama fad’in haka ya yi gaba.

Kallon takardun Abba yake yi yana sake maimaitawa, da gaske Ummi ciwon zuciya ne ke damun ta. A hankali ta fito daga d’akin investigation d’in, Arshaad ne yayi saurin mik’ewa ya ruk’ota ya na jera mata sannu a haka suka fito suka wuce.

A wani pharmacy suka biya suka sayi drugs d’in masu mugun tsada sannan suka wuce gida, zuciyar Ummi fessss.

Arshaad yana gama parking Ummi ta bud’e k’ofa ta fita ta nufi ciki, kai tsaye d’akinta ta shiga ta rufe kofa sannan ta nemo wayarta ta danna kiran Mom, bugu biyu a na uku ta d’auka. “Har kun dawo?” Shine abinda Mom ta ce.

“Eh!yanzun nan.”

Ummi ta bata amsa.

“To ya jikin?”

Mom ta kuma tambayar ta. Murmushi Ummi ta yi kafin ta ce “ke ni kaɗai ce fa ina d’aki ma.”

Wata shu’umar dariya Mom ta yi kafin ta ce “kinga amfanin beetroot yau ko??”

“Hmm” Ummi tace sannan ta cigaba da cewa, “Ni fa na tsani abun nan, Abba ya sha gaya mini in dinga jik’awa ina sha yana k’ara jini amman ko ya saka an siyo sai dai ya bushe ko in bawa Lami idan ta tashi tafiya ta tafi da shi.”

Mom ce ta katse ta ta hanyar cewa “Aikuwa yau inda a ce za a gwada jinin ki da kaf estate d’innan sai kin iya yi musu donation.”

Dariya itama Ummin ta yi kafin ta ce “Aikam!! Ni da aka ce in dinga jik’awa Ina sha, yau nice na dinga taunashi Ina fitar da ruwan Ina had’iye tik’ar..”

A tare gaba d’ayan su suka kwashe da dariya kafin Ummi ta ce “Adama thankyou, komai ya tafi according to plan, zan shigo anjima.

Yanzu bara in je in wanke hannuna, kafin abin nan ya zame mini k’unshi.
Yau ba dan hijabi na saka ba da babu abunda zai hana asirina tonuwa.”

“Ok.”

Kawai Mom ta ce mata sannan ta kashe wayar tana dariya.

Ummi, tana fitowa daga toilet ta gama wanke hannunta tana tsane wa da towel ta ji bugun k’ofa. Ko ba a fad’a mata ba ta san Abba ne, dan haka ta d’an tsaya a gaban mudubi ta duba fuskarta kafin a hankali ta je ta bud’e mishi.

A hankali ya shigo ya k’arasa bakin gadon d’akin ya zauna jikinshi duk a sanyaye. Sai da ya d’ago ya kalle ta sannan ya ce “zo nan ki zauna, we need to talk.”

Sum sum ta zo ta zauna a daf da shi sannan tasa hannayenta ta kamo nashi tun kafin ta ce wani abu a hankali
ya ce “I’m sorry, so sorry! Ga drugs d’inki nan ki dinga sha akan time dan Allah and, I think zan tafi Uk.”

Da sauri Ummi ta kallesa.
Bai bata daman yin magana ba ya ci gaba da cewa, “I want to go and check on Aslam dama, duk da yabce mini zai d’an lek’o soon amman I just want to go and check on him, sannan Ina buk’atar serious investigation Ina tunanin za mu biya a yi mini checkup d’in a chan. Ummi I’m scared, so scared, kun ce na yi wuni d’aya ina misbehaving I even slapped you, and…”

Sai kuma yayi shiru, d’an numfashi ya ja sannan ya ci gaba “What if brain d’ina ya fara samun matsala ne? What if I hurt someone in the process?”

Da sauri Ummi ta d’aura hannunta a kan bakinsa sannan tabce “Abba duk fa zafin ciwo ne, ai tun ranar ya yi checking naka sosai, kowa ya tsorata matuk’a da marin da ka yi mini tunda baka tab’a yi ba. Ko d’azu ya tabbatar da zafin ciwo ne kawai nothing else, pls ka kwantar da hankalinka and I’m so happy da ba da gaske kake zaka iya rabuwa dani ba…I was scared hankalina ya tashi sosai shiyasa na tafi wajen Granpa, I’m sorry for that, ba zan k’araba, ka yafe mini.”

Ta yi maganar tana murmushi tare da sake matse hannunshi dake a cikin nata. Ganin da ta yi yayi shiru yana sauraronta ne ya sanya ta yi ta lalallashinsa, had’e da tsarashi. Ba ta barshi ba sai da ta tabbatar ya nutsu kuma ya yarda da maganganunta.

Gandun Albasa

Yau sunday, Jalila na gida kasancewar babu makaranta.

Tun safe take k’ulle k’ulle akan abunda zata yi domin chusgunawa Mama. Kamar an tsikare ta kuwa ta mik’e daga kan katifar da take kai ta fito tsakar gida kanta ko d’ankwali babu gashi ba kitso a kan gashin nan ya zubo wani yayi baya wani ya zubo ta gefen kafad’arta har saman k’irjinta..
Tana fitowa ya Ja’afar ya na shigowa cikin gidan, ya bugu ya yi nak!! yana tafe yana layi.

“Ke!!!”

Ta ji ya ce mata.

Tsaki ta yi kafin ta juyo ta kallesa ta ce “menene?”

Aikuwa kamar jira yake ya nufota, yana tafe yana magana cikin layi da muryarsa wadda ke fita da kyar ya ce

“Ni kike yi wa tsaki??

Amman Yarinyar nan ba ki da kunya! Kalli kanki ko d’ankwali babu, so kike ki shiga wuta?”

Tsaki ta k’ara ja, kafin ta ce “Wallahi Ya Jafar kana da damuwa! Ni yanzu ka wani kama ka shigo za ka b’ata mini plan.”

Tayi maganar tana lek’en hanyar kitchen tana so ta hango ko Hudan na chan ta fara wanke wanken ta kasancewar yau Mama ke da girki, ai kuwa chan ta hange ta a tsugunne bakin rijiya hanyar toilet har ta kusan gamawa.

Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan cikin sauri ta juya za ta nufi inda take ta ji Ya Jaafar ya rik’o hannunta yana cewa
“Ke Jalila, ban gama da ke ba. Dan ke kin samu Ina sarara miki ba na laftar ki kamar waccar Hudan? To kema idan ba so kike yau ki ji a jikinki ba ki biya ni kamar yadda kika saba, ko yanzun nan in sauya miki halitta. Dan ke na lura dake duk wani aikin zunubi kin iya kina yawo babu d’ankwali
Sannan ina a matsayin Yayanki amma kina yi mini tsaki, gashi yau na ga alamar baki da niyyar sallamata.”

Jalila kam zuwa yanzu ta k’ule sosai tana k’ok’arin kwace hannunta tana juyawa tana kallon Huda wadda ke aikin ta cikin nutsuwarta kamar yadda ta saba, har ta juyo za ta yi mishi masifa sai kuma wata dabara ta fad’o mata. Murmushi ta yi sannan tace
“To naji, zan baka kuma yau naira d’ari ma zan baka.”

Ai kuwa ba shiri ya hau fara’a yana mai sakar mata hannu ya ce” To to, kin ceci kanki, maza je ki d’auko.”

Juyawa ta yi cikin gudu ta fad’a d’akin nasu, so take ta samu ya kyaleta kafin Hudan ta k’arasa aikin ta dan wallahi yau sai ta kifar da kayan wanke wanken nan a cikin chab’in bakin rijiya tunda ta yi niyya.

Tana d’aga k’asan pillown ta, ta ci karo da naira Hamsin bayan ta san d’ari ta ajjiye a wajen(Hamsin biyu) Tsaki ta yi ta ce “Umma!!! Na san d’azu da za ta tafi gidan Baba Laraba ne ta d’auke mini, aikuwa bara ta dawo sai ta biya ni, da ace ta san kalar k’arya yunwar da na yiwa malamin maths shekaran jiya a makaranta ya bani d’ari uku, da ba zata tab’a mini kud’i ba.”

Cikin mita ta d’auko Jakarta ta makaranta ta zaro littafi ta bud’e tsakiyan, ta ci karo da y’an chanjin hamsin da ashirin. Tsaki ta ja ta ci gaba da mita.

“Gaskiya Umma ta b’ata min budget, yanzu ga wanchan shima yana jirana, dama tunda na dawo take ta faman tambayana ko na yi chanji na san kud’i take so, in banda abun Umma ko me naira hamsin zata yi mata oho. yanzu na san ina tambayar ta cewa za ta yi cikawa ta yi suka yi kud’in mota ita da Baba Laraba.”
T

anata mita haka ta d’auko ta fito.

D’an juyowa tayi jin motsi a bayanta suka hada ido da Mama da take k’ok’arin yafa mayafi ga jaka a hannunta kana gani ka san fita zata yi kuma cikin sauri take.

“Kaii!! Allah yana sona.”

Shine abinda Jalila ta fad’a a ranta, dan har wani plan d’in ya kuma zuwa kanta ganin Mama fita zata yi, “plan har biyu yau akwai show a gidannan.”

Ta fad’a a k’asan zuciyarta

“Huda! Huda!”

Mama ta kwala kiran Huda. Da saurinta ta iso inda Maman take tana goge hannunta da gefen zanin jikinta.
Mama da ta k’araso tsakar gidan ce ta ce “zan fita, yanzun nan Ummu ta kira ni Sumayya ba lafiya ciwon ciki take yi tun safe har da suma. Sun je asibiti an mata allura an ce ta je gida ta huta, yanzu suna gidan Hajiya Shuwa. Zan je in dubo ta.”

Shiru Huda ta yi, ganin Mama ta kama hanyar fita ya sanya tace “Mama dan Allah zan bi ki nima in dubo jikin nata.”

D’an tsayawa Mama ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce mata, “A’a, ki k’arasa aikinki, yanzun nan zan dawo.”

Takowa Hudan ta yi ta d’an biyota murya kamar za ta yi kuka ta ce “Mama na gama, share wajen kawai zan yi in d’auko hijabina.”

This time around da fad’a Mama ta ce
“A’a”

Still bata juyo ba.

Dariyar Jalila ce ta sanya Mama juyowa.

Cikin wata irin dariyar raini Jalilan ta ce “kai, amman Hudan ban tab’a ganin dabba mai kwakwalwar kifi kamar ki ba, shiyasa fa muka bawa Baba shawara ya cire ki a makaranta dan asarar uniform da kud’in break kawai za a dinga yi. In banda abinki, kwanaki fa har gidan nan ita kanta Shuwa ta zo ta samu Baba tace ‘kar ya k’ara barin ki ki taka mata k’ofar gida, tunda shi ya ga zai iya rik’e ki ya je yai ta yi ita bata buk’atar ko ganin ki’.”

Shiru duk suka yi ba wanda ya tanka mata illa Mama da ta juya ta fara k’ok’arin saita kanta ta hanyar danne abunda take ji yana taso mata. Jalila kuwa, cikin takun ta ta k’arasa gaban Hudan ta tsaya sannan ta ci gaba da cewa “ba ta son ganinki a gidanta, ba ta son ki Hudan, duk ba’a son ganinki kowa ba ya sonki. Yanzu ki bar Mamanki ta je gidan, Allah yasa itanma kar Shuwa ta yi mata korar kare! Ki je ki ci gaba da wanke wanken ki kinji k’anwata.”

Ta yi magnar tana dafa ta sannan ta ce “Domin shi aka haifo ki duniya, da shara da ragowar ayyukan gida.”

Sharkaf haka fuskar Huda ta jik’e da hawaye, da sauri ta juya ta nufi d’aki tana goge fuskarta.

Murmushi Jalila ta yi, sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar za ta jiyota ta ce, “Shegiya kawai.”

Sarai kuwa Maman ta ji ta amma ba ta ce komai ba kafin ma Jalilan ta juyo ta yi sauri ta fice daga gidan tana share hawayen fuskarta.

Ganin Mama har ta fice yasa ta ce” In kin gama kukan munafurcin ki yi sauri ki fito ki k’arasa tattare wajen wanke wanken nan, dan har k’udaje sun taru.” Sannan ta juyo ta mik’awa Ya Ja’afar naira hamsin.

Karb’a ya yi ya jujjuya ta kamar yana neman wani abun a jikin hamsin d’in kafin ya ce , “Hamsin nake gani!”

“Eh, ai wai da d’ari nace zan baka, yanzu kuma sai na ga sauran ashirin da hamsin biyu shine zan baka naira hamsin sai a siyo mana zob’on saba’in a gidan mai tuwo tuwo. Kaga kenan Naira d’ari da ashirin ma na baka.”

Shiru ya yi yana son ya had’a lissafin amma sam sai ya gagara. Ganin hakan yasa ta ce, “To ba ni kud’ina na fasa, kawai yau daki kud’inka.”

Da sauri ya ce “A’a, barshi kawo in je In siyo.”

Kallonshi ta yi kafin ta ce, “wato har ka manta da bashin da take bin ka ko?
Ranar nan fa har gidan nan wadannan k’artin mazan masu tuk’a mata tuwo suka biyo ka za su dakeka, da kyar Baba ya basu hak’uri.”

Shiru yayi kafin ya ce, “kuma fa hakane, to yanzu ke za ki je kenan?”

Da ido Jalila ta nuna masa Huda wadda ta fito yanzun nan ta ce “Ai ga k’arama chan, sai ni za ka aika? tsoronta kake ji ko?” Da sauri yace
“Haba deee!! A’a.”

Ganin ta fara cin nasara,ya sanya ta ci gaba da cewa , “To kirata mana ga kud’in ka bata, amman wannan Yarinyar ma na san k’arshenta tace ba za ta je ba saboda d’azun nan na ji Mamanta tana cewa indai ka sake aikenta kar ta je, kuma idan ka daketa ta rama!!”

Ai tun kafin ta k’arasa ya wafce kud’in ya hau kwalawa Huda kira yana hura hanci.

Da saurinta ta k’araso tana “Na’am” ta ce “gani”

Kud’in ya watsa mata ya ce ‘maza ta je ta siyo mishi zob’o a gidan mai tuwo tuwo’.

Zaro ido ta yi kafin ta ce “Maama ta hanani zuwa gidan saboda akwai y’an shaye-shaye da maza da yawa, kuma ni ban ma san hanya ba yanzu.”

Cikin zuga Jalila ta ce “Ai dama na san za a yi haka, ka ji ko?” Sai kuma ta kalle ta ta ce, “Tukunna ma shaye shaye me kenan??”

Ba ta jira ta bata amsa ba ta ce “Yaya irin fa d’an maganin ciwon kan nan da kake sha yake d’an saka ka jiri shine take zagi! Tab!! kaga kenan ta had’a har da kai ta zage tasss!!!.”

Ai kuwa Jalila ta yi nasara dan Ya Ja’afar cewa ya yi “wallahi yau idan Huda za ta suma sai ta je kuma wallahi ta dawo gidan babu zob’on gidan mai tuwo tuwo sai na lahira ya fita jin dad’i.”

Hakanan tana kuka tana komai ta zo ta wuce, sai da ta kai k’ofa ta juyo tace
“Yaya Jalila dan Allah to ko kwatance ne ki yi min.”

Cike da son sake dilmiyar da ita Jalilan ta ce “idan kika fita ki mik’e, ki yi kwana sau bakwai sai ki yi tambaya.”
Haka kawai Jalilan ta ce da ita sannan ta juyo tai hanyar d’aki har ta tura k’ofar sai kuma ta juyo sanin cewa Huda bata da wayo kwata-kwata, tunda ba shiga mutane take yi ba ya sa ta ce mata “kuma saura ki biya gidan shuwa ki kai k’ara, ranar da kunne na na ji ta ce ‘sai ta yanka ki a duk ranar da kika yi gangancin zuwa mata gida’.”

Hawayenta ta share cike da fargaba da tsoro ta juya ta fita daga gidan.

Kamar yadda Jalilan ta yi mata kwatance haka ta yi amman sai aka ce mata ‘ai nan arean kwata-kwata babu gidan Mai Tuwo Tuwo’.

                 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 5So Da Buri 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×